Free chapter · Read without an account
Chapter 27 & 28
*SU MA 'YA'YA NE*
Da
Alkalamin Ummulkhair Abba Muhammad.
*Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai*
Page 27 & 28
Macen da na yayewa mayafi ta fafaɗa murmushin da take yayin da kwalliya mai ɗaukar hankali ke bayyana a fuskarta sannan wani irin ƙamshi na tashi a sassan jikinta cikin fari da ido tana lumshe ido ta ce da ni: “Zan amsa miki tambayoyinki. Na farko aminiyarki Lubna kike gani. Kuma ba gizo ba ne ba mafarki ba gaskiya ce, ta zo gare ki a matsayin abokiyar zamanki. Ko kina da wata tambayar bayan wannan?” Ta ƙarashe maganar tana murmushi ta lumshsu idanunta ta ci gaba da cewa, “Abin ya ba ki mamaki ko? Hakan nake so da ma lamarin ya zo miki a bazata. Amma yanzu kin gaskanta maganata ta waya da nake ce miki na yi aure ko?”
Ta kashe mini ido ɗaya tare da kyalkyalewa da dariya ta ce, "A al'adance ango ke fara buɗe fuskar amaryarsa a daren farko, amma saboda amintakar da ke tsakaninmu na sadaukar da hakan gare ki, ke kika fara buɗe wa. Fatan za ki karɓe ni da hannu bibbiyu.” Ta saki guntuwar dariya.
Jujjuya kaina na fara yi saboda ƙoƙarin tarwatsewar da ya fara yi, sosai na diriri ce wannan lamari ba ƙaramin ɗaci da ciwo ya yi mini ba.
“Aminiyata a matsayin kishiyata!” A zuciyata na furta hakan.
Lubna cikin fari da ido ta nuna Abban Sumayya da yatsa tana cewa, “Habibina yi mata ƙarin bayani faɗa mata ni da ita a yanzu matsayinmu ɗaya ne a wurin ka.”
Murmushi ya yi sannan ya ce, “Point of correction my dear ya za ki daidaita kanki da wannan sakaryar, kin mata zarra, saboda ni Abba a yanzu ne zan san na yi aure da na aure ki, na farko mun haɗu akan ra'ayi ɗaya, sannan na auro tsatson da suke haihuwar 'ya’ya maza.”
Miƙa masa hannu ta yi alamar ya zo, yana zuwa ya zauna a gefen gado kusa da ita ta rungume shi tare da sakar masa sumba a wuya, ya kwantar da kansa akan kafaɗarta ya fara goga mata kasumbarsa a kuncinta. Idan idanuna suka ci gaba da kallon wannan fitsarar tabbas zuciyata za ta buga, na yi saurin juyawa domin na fice.
Lubna cikin ƙasa da murya ta ce, “Mijina ka ce da matarka ta dawo.” Cikin tsawa ya ce, “Ke Ummi dawo nan!”
Idanuna cike da kwalla na dawo ya dube ni, “Kar ki yadda ki bar wurin nan idan ba ni na ba ki umurnin tafiya ba.”
Yana zagaye laɓɓanta ya ce, “My honey wato idan har za ki gaji Ummarki ai na taƙi sa'a, maza goma fa ta haifa ke kaɗai ce ɗiya mace.”
Ƙara ƙanƙame shi ta yi tare da cewa, “Me zai hana ka rubuta ka ajiye Lubna zaratan sojoji za ta dire maka don ita ba tsatson masu haihuwar ‘ya’ya mata ba ne. Zaratan sojoji za ta haifa maka, amma fa bayan kwashe shekaru biyar da aure ana soyayya.”
Wani irin ihun daɗi ya sake wanda Ummi har ta yi firgigit.
Tsaki ta yi, “ 'Yar ƙauye don ya yi ihu shi ne da firgita. Anya kina sa shi ihu idan kuna raya dare?”
Ya nuna ni da yatsa, “Wannan jakar, kana kusantarta kamar da dutse kake tare, ba abin da ta iya. Ke ce dai za ki sani ihu da kukan daɗi.” Ɗora hannunta ta yi bisa ƙirjinsa ta cire masa bottle tana shafan ƙirjin kuma tana satan kallon Ummi.
Da na ga cin fuskar za ta yi yawa sai na juya don na fice na bar musu ɗakin a ƙaro na biyu duk da an yi mini sharaɗin kar na kuskura na fita, kafin na kai ga kofar Lubna har ta dire a gadon ta sha gabana ta sa wa kofar muƙulli.
Na tsaya cak ganin abin da ta yi mini, sai na jiyo muryarta tana ƙyalƙyalewa da dariya shi ma sakaran na taya ta.
A daidai wannan gaɓar na katse ba su labarin na dubi Samha, “Ki je fridge ki ɗauko mini faro mai sanyi.”
Samha ta miƙe, Muhibbat ta ce, “Umma ina mamakin matan da idan miji yana cin fuskar abokanan zamansu ko wulakanta su suke jin daɗi ba su san yau a kan wani gobe a kanka ba ne.”
Sumayya ta ce, “Ba sa wannan tunanin da wannan lissafin ai, ni kin gan ni lokacin da nake budurwa akwai wani mai mata da ke so na kullum yana cikin kushe uwardaginsa idan ya zo hira, tuni na fita harkarsa na ce wannan ina auransa munafukin mata ne.”
Samha ta kawo ruwa ta buɗe ta durƙusa ta ba wa mahaifiyarta.
Muhibbat ta ba wa ‘yar’uwarta amsa da, “Haka mafi akasarin maza suke kushe uwargida a gaban matar da suke son aura, yin haka kuma buɗe kofar raina uwargida ne, idan amarya ta shiga aka dinga fitina miji ya gaza gane kan gidansa alhali shi ne silar haifar da fitinar.”
Umma ta ce, “Allah ka shiryi maza masu irin wannan halin, maza jigo ne a rayuwarmu, haka muma wasu bigire ne a gare su. Rayuwar ɗaya ba ta inganta ba tare da ɗaya ba, saboda haka da mu da su Allah ya gyara mana zuƙatanmu.”
Dukkaninsu suka amsa da amin daga nan Umma ta ci gaba da ba su labari.
Ya yatsina fuska cikin tsawa ya ce, “Wai ke Ummi wacce irin yarinya ce haka? Kin manta kashedi da na yi miki ɗazu ko? To ki dawo ki zauna wallahi idan kika kuma tunzura ni zan sassaɓa miki a daren nan.”
Ban motsa ba daga tsayen da nake, “Ban fa canja ba daga Abban da nake, don na kwana biyu ban fasa jikin naki ba shi ne raini ya shiga tsakaninmu ko? Muddin kika bari na miƙe za ki tsinci kanki a gadon asibiti.”
Na juya na koma inda suke amma na kawar da ganina a kansu saboda abubuwan da suke a kan idanuna, kunnuwata ma da ina da yadda zan yi na toshe su ba za su dinga jin kalaman cin fuska ba da na yi amma babu dama.
Lubna kamar ta san dalilin juyawar da na yi sai na ji ta ce da Abba, “Mijina aminiyar tawa fa juya mana ƙeya ta yi, ni kuma saboda amintakar da ke tsakaninmu ba abin da nake son yawan gani yau kamar fuskarta ya kamata ta juyo mu gan ta ta gan mu.” Cikin marairacewa da nuna shagwaɓa ta furta hakan.
“Kin ji ƙunya Ummi, ki ga yadda aminiyarki ke yin ki, ke kuma sai nuna mata mugun hali kike nuna mata. To ina umurtar ki da ki yi abin da ta ce.”
Haka na juyo da fuskata,
ta kyalkyale da dariya.
“Mu koma kan maganar zaratan samari nawa kake so na suburbuɗo maka 12 ko?”
Ya zaro “Kai! Kai! Kai! Ina zan kai su? Ɗangote da yake cikin jerin masu kuɗin Afrika ma bai tara haka ba sai ni. Ki haifa mini zaratan samari uku ma sun wadatar sun ishe ni rayuwa.” Ji na yi zuciyata kamar za ta fashe saboda maganganun nan, sai na ji na zaɓi na saɓa masa ɗin ya farfasa mini jiki na kwanta a gadon asibitin da yake faɗa da maganganun. Ɗauƙar key da ke gaban madubi na yi na nufi kofa kai tsaye na buɗe na fice.
Abba yunkurin tashi ya yi don ya ci mutuncin Ummi Lubna ta dakatar da shi.
Jingina na yi da murfin kofar ina kuka mara sauti.
Lubna ta sauka a gado tana murmushi.“ Ka ga dear bari na je na rarrashi aminiyata na lallaɓata duk zafin kishi ne ya hana ta samun nutsuwa.”
“Yau fa so nake idonki da kunnuwanki su ji abin da zai sa zuciyarki ta buga.” Lubna a zuciyarta ta furta hakan, sai ta ƙyalƙyale da dariya.
Abba ya dube ta,“Dariyar me kike?”
“Ba ruwanka, kai dai ka fiye son jin gulma. Da zuciyata muke hira kuma ba za ka ji ba.”
Da suka fito suka tarar da Ummi tsugunne a ƙasa tana kuka mara sauti. Lubna ta durƙusa a gabanta.
“Haba aminiya irin tarbar da za ki yi mini kenan? Idan ni ce kika auri mijina ba zan yi miki haka ba.”
Na dube ta sama da ƙasa na jinjina kai, “Ni ba zan ma fara auren cin amana ba, ballantana na dinga cin fuskar wacce na ba ta yarda. Allah ya tsare ni.”
Lubna ta lumshe ido ta kama hannuna da mu tafi sai ta ce,
“Wannan dare ba wannan batun ba ne ya tara mu, saboda haka ba zan ba ki amsar ba.”
Na fizge hannuna Lubna ta dubi Abba, “My husband, ka yi mata magana ko za ta fi jin naka.”
Cikin tsawa ya ce,“Ke ki kama hanya mu tafi, a kanki a ka fara kishiya, wallahi idan ba ki bi mu ba, za ki tafi gidanku a daren nan tafiya na har abada.”
Lubna ta zaro ido, “Rufa mini asiri, kar a buga ni a jarida ƙawa ta aure mijin kawarta kuma ta sa an saki uwargida a daren farko. Kana sakinta ni ma sakina za ka yi. Ban aure ka don ka rabu da aminiyata ba, face ƙarfafa zumuncin da ke tsakaninmu.”
Ban ce komai ba na riga su yin gaba. Lubna ta bi ta da gwalo.
A take na ba wa zuciyata haƙuri gudun kar ta kuma harzuƙa daga wannan rubutacciyar ƙaddara da ta same ni, tabbas rubutu ne daga sarkin da ba ya kuskure. Na ƙudurta a raina duk abin da zan gani ko zan ji zan yi ƙoƙarin danne zuciyata, zan yi haƙuri kamar yadda na saba a baya, ina da yaƙinin komai zai wuce.
Zama na yi a gefen wata karamar stool, ita kuwa Lubna da Abba a bakin gefen gado.
Wasannin motsa sha'awa suka fara aikawa junansu a gaban idona, ji nake kamar na haɗiye zuciya na mutu don takaici.
Wannan wacce irin baƙar rana ce da ta fi kowacce rana a tarihin rayuwata muni. Mijina da aminiyata ke yi mini haka. Kaicona!
Duk da sanyin iya kwandinshan da ya dabaibaye ɗakin, zufa na fara nan take, na haɗa gumi sharkaf kamar wacce take gaban maƙera, zuciyata ta fara bugawa, nan take kaina ya fara sarawa, a zuciyata na ce, “Da wanne zan ji da raɗaɗin ƙarin aure ko da cin fuska da fitsara?”
Wannan iskancin a gabana ko addini bai ba da damar haka ba, ba zan iya ba, ba zan jure ba sai dai komai zai faru ya faru da ni, ni ko a tarihi ko a fim ko a littattafan Hausa ban taɓa cin karo da wanda aka yi masa abin da aka yi mini ko kuma makamancin haka.
A zabure na fice ina kuka na doshi bakin kofa na fice. Na motsa laɓɓana a zuciyata na furta, “Godiya ta tabbata ga Allah, Allah ina gode maka a duk halin da na tsinci kaina. Allah ka ba ni ikon lashe waɗannan jarabawowi da nake fuskanta.”
Na fara tafiya ina dafa bango saboda sarawar da kaina ke yi, har na ƙarasa ɗakin da ‘ya’yana ke kwance.
Lubna ta dubi Abban Sumayya.
“Dear yadda uwargidanka ta fita na tsorata ka san mata da zafin kishi musamman a irin wannan rana ta yau, kar ta far mini, ni kuma ban zo gidanka da shirin yaƙi ba face da so da kauna.”
Kyalkyalewa da dariya ya yi.
“Matsoraciya, gaskiya kin ba da ni. To bari ki ji wannan da kike ganin ta ba abin da za ta yi miki, ta san zaman haƙuri nake da ita, ta isa ta far miki da kuwa na sake ta, ita kuma da na furta saki a kanta gwamma ta haɗiye duk ɓacin rai ta zauna da ni.”
Ya fara miƙa, “Kai jikina fa duk ciwo yake yi mini, bari na watsa ruwa na zo ki yi mini tausa.” Ya shiga toilet.
Lubna a zuciyarta ta ce, “Ummi ki sani ban shigo gidan nan don mu zauna a ƙarƙashin inuwa ɗaya ba, burina shi ne na gallaza miki na wani lokaci na ɗaiɗaita ki sai fice ki bar ni. Wallahi duk yadda kika so zama a gidan nan sai kin fice na shigo wannan katafareren gidan ne don in rayu ni kaɗai da mijina, 'ya’yanki kuma sai sun zama bayi a wuri na, daga ƙarshe na kashe wasu, wasu kuma na ɓatar da su, bayan mun haihu da shi, shi ma na aika da shi lahira ba shi da dangi da ma a nan kusa daga ni sai 'ya’yana za mu ci dukiya mu yi wadaka mu fantama. Wannan yana ɗaya daga cikin manufata na auran mijinki. Duk irin wulakanci da za a yi miki kina nan ko? To ko ke ce ƙasƙa sai na raba ku manakisa da kisisinar da na shigo da su gidan idan na fara dole ki fice, fita na har abada tun da ba gidan ubanki ba ne shegiya. Idan kuma wannan hanya ta gagara akwai boka na’ibin shaitan da gudunmawarsa na samu shigowa to da gudunmawarsa za ki fice.”
Bayan ya fito daga toilet ya zo kusa da ita yana ambatar sunanta ba ta amsa ba, ya kuma ƙira ya ji shiru, sai ya bugi bakin gado firgigit ta yi, ya saki murmushi sannan ya ce, “Kin ga na fuskanci kina son ki ƙarar mini da daren amarcina a tunani to ba zai yiwu ba. Dawo cikin hankalinki domin mijinki yana buƙatar dukkanin nutsuwarki gare shi.”
Ya kashe wutar lantarkin duhu ya mamaye ɗakin.
Ta kai masa hot kiss a wuya tare da tambayarsa, “Honey ko ina aminiyata ta yi?”
“Ba za ta tafi sashinta a daran nan ba, kin san akwai tazara muma da mota muka zo, ina ga tana ɓangaren da muka ajiye 'ya'yan kafin mu shigo.”
Lubna na jin haka uwar kisisina ta nunawa mijin ta gaji da wannan bedroom kuma ba ta son gado ta fi sha’awar su yi sha'aninsu a katifa. ya amince, kasancewar gidan akwai wadatattun katifu ta tambaye shi ta wanne ɓangaren Ummi take da yaran ya nuna ta jefa katifar ta inda Ummi za ta ji sautin komai, ta sa bedsheet ta sanya turare iri daban-daban.
Na dubi ‘ya’yana da suke sharara bacci.
Allah sarki ‘ya’yana su kaɗai ne farin cikina, a duk lokacin da na shiga damuwa muddin na gansu sai na ji ya yaye a fili na ce “Da na san irin wannan tashin hankalin zan shiga da ban bi ka inda ka gayyace ni ba, da ma ka gayyace ni ne don ka cusa mini bakin ciki, ka ƙara aure ba tare da na sani ba, duk da abin da ka yi halaƙ ne amma ka rasa wacce za ka auro sai aminiyata. Ke ma Lubna ki rasa wanda za ki aura sai mijina. Shin yaushe kuka fara soyayya ban sani ba? Har aka yi shagalin biki muna gari ɗaya ko da wasa ban ji ba sai dai ganin ki kawai da na yi a matsayin amaryar mijina.”
Kunnuwana ne suka fara jiyo ihun Abba da Lubna abin ya ba ni mamaki muddin a ɗakin da na bar su suke babu abin da zai kai ni ga jin muryarsu. Tabbas zuwa suka yi kusa da inda nake kuma ba don komai suka yi haka ba, sai dai don kunnuwana su ji abin da zuciyata za ta tarwatse.
Abba kamar a kanta ya fara sanin mace sai wani ihu yake, ita kuma mara kunya sai cewa take wayyo tana nishi, shi ma yana ce da ita dear daɗinki ya yi yawa ban taɓa gamsuwa da wata mace kamar ki ba.
Wani irin kishi na ji ya turnike zuciyata kamar na ɗauki wuka na je na daɓa musu saboda yadda zuciyata ke tafarfasa, ido rufe nake neman bacci ko idan ya ɗauke ni kunnuwana su daina jin kazaman maganganun da suke amma bacci ya kauracewa idon gabaɗaya.
Ina jin Abba ya ce da ita, “Karɓa.”
Ban fahimci me za ta karɓa ba, sai na ji ya kuma ce, “Saboda daɗinki matata na ba ki kyautar motar da na saye ta don ɗauko ki a matsayin amarya.”
Wani irin daɗi ta ji don wannan motar sai attajirin da ya amsa sunansa na attajiri ke hawa wannan motar.
“Ahayye!” Ta rangaɗa guɗa tare da cewa, “Wayyo mijina! Wayyo daɗi! Thank you my love.”
Miƙewa na yi na shiga toilet na ɗora alwala na dinga nafilfili ko raɗaɗin da zuciyata ke yi mini zai daina. Ban runtsa ba har aka ƙira sallar asuba ina jan carbi.
Mu haɗu a next page.
Love You all.