Free chapter · Read without an account
{62..}
Bai daɗe da fita ba Hajar ta farka daga baccin da take sakamakon cramps din da yake sukarta a cikin baccin, ta yamutsa fuska ta miƙe zaune tana kallon duvet din jikinta, muttsuke idonta tayi ta kalli couch din ɗakin, ta fara yaye duvet din sai kuma ta tsaya tana kallonsa, a hankali ta kai duvet din hanci perceiving the scent, ta taɓe baki gami da yin wurgi da duvet din kafin ta tashi a hankali, ƙarewa ɗakin kallo kawai take sai kace mai neman wani abun, walking like a chameleon ta isa bakin ƙofar toilet, she want to use it amma kuma tana tunanin may be yana ciki tinda dai bata gansa a ɗakin ba, kara kunnenta tayi da jikin ƙofar wai ko za taji wani sound, ɗipp ba taji anysound ba don haka ta samu courage din murɗa handle, ta shiga toilet din tana jin kamar ana mata ruwan allurai a cinye, daman tin tini haka cramp yake wahalar da ita, ganin she is still clean kawai ta ɗora alwala ta fito, ta gyara rolling dinta da ya sakwarkwace wajen bacci da yin alwala kafin ta kabbara sallah, tana idarwa ta kalli ledojin dake kan carpet har lokacin, turo baki tayi ta fara buɗewa, rolls din satchet of white coffee ta gani wajen uku sai milk sai kuma black coffee, taɓe baki tayi ta janyo wata ledar, anan taga toothbrush and toothpaste da detergent, zamewa tayi ta kwanta ta ringa twisting toes dinta shallow in pain, after 40mins lokacin ma takwas ya gota taji ana knocking door a hankali, ta tashi zaune tana kallon ƙofar, saida aka sake knocking snn ta miƙe ta isa bakin ƙofar, tana buɗewa waiter dake riƙe da park din Abinci cikin leda yace "good morning maam..", tace "morning..", ya miƙa mata ledar hannunsa yace "here is your order", kallon ledar ta tsaya yi bata amsa ba, waiter yace "gashi fa Maam", sai a lokacin ta amsa ta mayar da ƙofarta ta kulle, jingina tayi da ƙofar, after few seconds ta bude ƙofar tana leƙa waje wai ko za taga waitern ta tambayesa whereabout din wnda take jira tin dazu, wayam taga long Aisle din mai ɗauke da ƙofofi rututu, idonta yayi rau rau ta juya ta koma ɗaki, a kan couch ta zauna ta fara buɗe ledar, Irish ne da kidney sauce sai golden yam, ga bottle water da lemon kwali, tashi tayi ta dauki ledar da ta ga toothpaste da toothbrush, without second thought ta farke brush din ta matsa masa paste ta shiga toilet, bayan ta gama brush ta kuskure bakinta da mouth rinks da ta gani gefen sink, fitowa tayi ta zauna taci lafiyayyen breakfast dinta, kuma sosai taci abincin don ya mata dadi, saida ta gama ci ta ajiye ragowar snn ta fara tunanin wanka, sai a lokacin ta dubi box ɗinta dake bakin ƙofa tin daren jiya, ta janyo box din ta shiga da ita cikin ɗakin sosai, a hankali ta zuge zip tana kallon kayan ciki, ta harari kayan bayan ta tina ydda aka haɗasu, zaro ido tayi ganin harda undies sai kuma ta juyar da kai tana turo baki, sponge da shower gel dinta ta ɗauka ta shiga bathroom, tayi amfani da towel din da ta gani a jikin hanger, bayan tayi wanka ta fito ta shirya abinta, zaune tayi kan couch idonta ƙif akan ƙofa, tunani iri iri ya ringa zuwar mata ka, toh ko dai nan ya kawota shi yayi tafiyarsa, da sauri ta miƙe ta isa gaban closet ta buɗe, tana ganin bag dinsa taji wani mugun relief, tayi ajiyar zuciya kafin ta rufe closet ta koma ta zauna, ƙarfe sha biyu cleaner mace ta shigo ta gyara ɗakin, Cleaner ta gama aikinta ta fita, Hajar dai ta gaji da zama ta kwanta, saida taga har biyu na rana ta gota amma babu alamar zai dawo, da sauri ta miƙe jin anyi knocking door, har tana harɗewa sbd sauri taje ta buɗe door din, tayi turus tana kallon waitern da ya kawo mata breakfast, this time around ma ya gaisheta kafin ya miƙa mata ledar hannunsa, ta amsa tana jin wani ƙululu ya tsaya mata a throat, har waitern ya juya zai tafi tace "dan Allah ji mna..", ya juyo yana kallonta baice komai ba, da kyar ta ƙaƙalo mganar tace "emm dan Allah wane yace a kawo min wnn...?", yace "daga restaurant ne..", tace "Amm shi ina wnda yace a kawo..?", yace "sorry maam but i don't know aikina kawai shine delivery..", wani irin saki guiwarta tayi tace "Okay" da haka ta rufe ƙofarta, ko buɗe abincin ba tayi ba ta ajiyesa kan mini fridge dake ɗakin, saida tayi sallahr la'asar snn ta ɗan ci abincin kaɗan, tin daga cin abinci sai ciwo kuma ya motsa, ta ringa murƙususu a kan carpet, gashi idan baizo ba toh fa cramps din bazai lafa ba, daga yazo mgana ta ƙare, da kyar ta samu ya lafa mata, ta jingina da jikin gado ta ɗora kanta a guiwa, after few minutes ta ɗago kanta ta kalli door, gani kake sharr sharr hawaye sun fara gudu a cheeks dinta wani na bin wani.
★Ruqayyah ce zaune a Nurse station ta zabga uban tagumi, yau tana shigowa hospital direct office dinsa taje taga baya nan, tin ranar Tuesday last week da tazo bata sake zuwa ba sbd bata jin daɗi, sai yau ne ta samu tazo wajen aikin, Nurse Jiddah ce ta iso station din, tapping Ruqayyah tayi tace "Rukky yada zabga tagumi haka..?", Ruqayyah exhale heavily bayan ta fito daga duniyar da ta lula, Nurse Jidda ta zaune still tana kallon Ruqayyah tace "what wrong friendy you look dull..?", Ruqayyah tayi ajiyar zuciya ba tace komai ba kawai kallon Nurse Jiddah take, Nurse Jiddah tace "Okay idan bazaki gayamin ba shiknn amma dai karki sakama kanki damuwa, naga duk ba kya cikin walwala ƴan kwanakin nan...", Ruqayyah ta dafe goshinta kafin tace "Jiddah", Nurse Jiddah tace "na'am", Ruqayyah tace "yau ke ce ku ka shekara sama da biyu da saurayinki kuna soyayya har an saka muku ranar aure, toh a ranar auren sai wani abu ya tasowa shi saurayin naki wcca a dole sai an fasa aurenku a ranar, sai ya turo miki da message ya baki haƙuri yace ki jirasa yana nan dawowa gareki, dan Allah Jiddah wani hukuncin zaki yanke..", Nurse Jiddah dake kallon Ruqayyah ta saki baki kafin ta tafe hannaye tace "chaɓɗi jam..", Ruqayyah ta gyara zama tace "wani mataki zaki ɗauka...?", Nurse Jiddah tace "toh kamar yadda na bar nonon uwata haka zan barka wllh tllh, nida kai saidai hange daga nesa..", Ruqayyah ta katseta da faɗin "haba Jidda akwai fa soyayyah mai ƙarfi a tsakaninku kun fahimci juna sosai snn ya baki haƙuri fa..", Jiddah ta taɓe baki tace "meye kuma haƙuri, aini bbu wani haƙuri da zaka bani na haƙura don ka gama tozarta ni duniya da lahira, ranar ɗaurin auren mu ka tsallake ka tafi ka barni chab..", Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Nurse Jiddah, gaba ɗaya karsashinta ya zagwanye gami da tsiyayewa ta guiwarta, tace "toh naji, bayan wani lokaci sai ya dawo daga inda ya tafi, yazo har inda kike ya baki haƙuri bayan wnda ya ringa turo miki ta waya..", wani murmushin rainin hankali Nurse Jiddah tayi tace "hmm Rukky knn, ai na gaya miki kamar yadda na bar nonon uwata haka na barka, kuma soyayyarka wllh na riga nayi fatali da ita akan kwalta..", Ruqayyah tace "nidae idan nice zan haƙura.." Nurse Jiddah tace "sbd kin wurgar da zuciyarki kare ya lashe ko..?", Ruqayyah ta haɗe gira tace "let me land mna malama..", Nurse Jiddah tace "Ohk", Ruqayyah tace "zan haƙura sbd fahimtar da na maka da kuma girman soyayyar dake tsakaninmu..", Nurse Jiddah ta miƙe tana kallon agogon hannunta tace "haka fa... Rukky wnn tmbyar naki is meaningless.. kuma in gaya miki duk wnda zaki tambaya irin amsar dana baki zai bayar.. kinga tafiyata zan duba ward C" tana gama faɗin haka ta bar station din. Ruqayyah ta ciro wayarta dake ringing daga pocket, da sauri tayi picking ganin Momy ce ke kiran, bayan sun gaisa Momy tace "kina jina..?", Ruqayyah da zuciyarta ke racing tace "Eh", Momy tace "toh ki taho gida yau..", Ruqayyah tace "toh", da haka Momy ta katse kiran. bayan Ruqayyah ta gama dutyn ta ta wuce gidan Haj Safiyya, kayanta kawai ta ɗeba ta yiwa mutan gidan sallama ta tafi. tana isa gidansu haka nan saddan taji zuciyarta na bugawa, shahada tayi ta murɗa ƙofar palour ta shiga, tayi sallama a hankali kafin ta shiga, Momy dake zaune palour ta amsa ba tare da ta dubeta ba, Ruqayyah ta ƙarasa cikin palourn ta duƙa ta gaida mahaifiyarta, Momy ta amsa mata a fixge sai kuma ta tashi ta bar palourn, Ruqayyah ta saukar da kanta kafin ta wuce room dinta, wanka ta shiga bayan ta fito ta tarar da missed call from Kulsoom, saida ta shirya snn tabi bayan kiran, kiran na shiga Kulsoom ta ɗaga tace "ina kika shiga sai kira nake..?", Ruqayyah tace "i was taking my bath at that time..", Kulsoom tace "Okay... sai yau Momy ta gayamin kwaɓar da kika tafka.. wai ke wace irin dabba ce da baki san gabanki da bayanki ba bare kisan inda kika dosa, wai sama kike cizo ne ko kuma kin fara tsince tsince a bola bamu sani ba, shi mahaifin naki kika kai ƙara sbd yana ƙoƙarin saita miki rayuwa, banza kawai wcca bata san inda yake mata ciwo ba, toh ai sai a barki da maganar auren tinda daman ynxu ke kin zama tsohuwar guzuma, yo to tsohuwar guzuma mana shekara ashirin da shida kin ƙi auruwa kuma duk ke kika ja ma kanki don Allah ya baki dama kikasa ƙafa kikay fatali da ita... kuma ƙaryar da kika shirgawa Momy akan mganar Dr marmaza kije ki sanar da ita da bakin ki cewa ƙarya kika giggila mata idan ba haka ba wllh saina tayar miki da mummunan bomb kin ji na gaya miki..", Ruqayyah ta fara girgiza kai tace "Sister wllh bazan iya gaya mata ba, bazan iya ce mata ƙarya na mata akan cewa babu wani sasantawa da mukay da Dr", Kulsoom ta juya hannu tace "oho can ta matse miki a matsematsin matsalarki, ko ki faɗa da bakinki ko na bunka miki bomb nonsense.." tana gama faɗin haka ƙitt ta kashe wayarta, Ruqayyah ta ringa kallon wayarta da idanunta kamar zasu faɗo, tana ɗaga kanta sukay ido huɗu da Momy wacca take tsaye bakin ƙofa tana kallonta da wani irin expression, darammm zuciyar Ruqayyah ta buga da ƙarfi, tini lips dinta suka fara zikiri tana ƙif ƙif da ido, juyawa Momy tayi ta bar dakin without saying anything.
★Hajar ta ɗaga kanta sakamakon murɗa door handle da akay, ta zubawa ƙofar lulu eyes dinta da suka haura, yana shigowa tayi sauri ta miƙe tsaye duk da irin murɗawar da cikinta yayi, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai yana taɓe baki yayi sallama ciki ciki, ba ta ko amsa ba sai wata shegiyar harara da ta shiga banka masa, shi ko baima san tana yi ba, Laptop bag dake hannunsa ya ajiye kan couch kafin shima ya zauna yana stretching kansa, ajiyar zuciya yayi ya fara massaging neck dinsa, Hajar ta koma ta zauna don tsayuwar na ƙoƙarin tayar mata da ciwo, after 10mins ya tashi ya buɗe closet, jakarsa ya zuge ya ɗauki black sweat pant da white shirt, bathroom ya shiga ya rufo ƙofar, Hajar na zaune inda take sai kace mage, bayan 15mins ya fito, yayi wanka kuma ya shirya a bathroom din kafin ya fito, sai a lokacin ya yiwa Hajar seconds look tin shigowarsa, yana kallonta yace "an kawo miki abinci..?", ta ɗan kallesa sai kuma ta haɗe rai ta juyar da kanta, ganin he start coming towards her tayi sauri ta gyaɗa kai tace "ai an kawo min fa..", yayi slight smirk murya ƙasan maƙoshi yace "Silly girl", Atm card da phone dinsa ya zura a pocket, Hajar na ganin ya saka takalmi ya nufi ƙofa zuciyarta ta buga, da wani irin zafi nama ta miƙe da gudu ta sha gabansa ta danne ƙofar da bayanta, da mamaki ya ringa kallonta, ta sha kunu tana turo baki, yace "ke.. get out of my Way", lips dinta na rawa tace "saidai mu fita tare... ni bana son zaman nan din, ka mayar dani gida", yace "anƙi ɗin...", cike da tsiwa tace "is that so.. to kwa kaima bbu inda zaka", smirk yayi yana auna ƙarfin halinta, ga ta dai wata ƴar tsugul a gabansa amma sai tsaurin ido, hannu ya kai zai matsar da ita, da sauri tace "haram.. karka taɓani.." tana karkaɗa ɗan yatsanta manuniya irin a'a din nan, kallon slim finger din nata yayi, tsaf zai karyasa idan ta bari ya riƙesa, girgiza kai yayi don baya son ya biye mata ya bar wajen, powering TV yayi ya zauna a kan couch yana latsa wayarsa, Hajar ta turo baki ta bar bakin ƙofar ta dawo ta zauna, har wani bouncing take wai ita ta hanasa fita, babu jimawa magrib tayi, Nurain ya tashi yana jan rigarsa, wuff mutuniyarku ta miƙe itama, gani tayi kawai ya shimfiɗa prayer mat ya kabbara sallah, hakan yasa taji relief ta koma ta zauna tana kallon Tv, ya idar da sallah ya gama addu'oinsa, yana ƙas ƙas da fingers ya tashi ya koma position dinsa ya zauna, a hankali Hajar ta miƙe tana satar kallonsa, saɗaf saɗaf take tafiya har ta isa ƙofar toilet wai ita a nata tunanin bai lura da ita ba ashe ba tasan yana kallon duk wasu moves dinta ta wutsiyar ido ba, da sanɗa ta shiga toilet din ta rufe ƙofa a hankali, ko second biyu bai ƙara ba ya tashi ya bar room din, bashi ya dawo ba sai takwas da rabi, ya ajiye ledar abincin dinner da ya taho mata dashi, Tv ma take kallo abinta don haka ko ma ƴar hararar ta na kula ba tayi masa ba, yana kallonta yace "hey.. ga dinner dinki..", tace "na ƙoshi", ya ringa kallonta kafin yace "ur cup of coffee", bathroom ya shiga ya canza kayan jikinsa zuwa Pajamas, bayan ya fito ne ya fara ƙoƙarin haɗa sahibin nasa, ruwan zafi ya jona a kettle dake kusa da fridge, a jakarsa ya ɗakko mug da spoon, ya shiga toilet ya wanko mug da spoon din, da white coffee powder da ya siyo da ita yayi amfani ya walwala sahibin, da cup din a hannunsa ya rage wutar ɗakin yabar dim, ya zauna kan couch ya kunna Laptop, Hajar dai har ta ɓingire nan kan carpet amma kuma ba bacci take ba, operating system din yake at same time yana sipping coffee, kallon inda take kwance yayi, kawai ya ajiye mug din hannunsa ya tashi ya isa inda take, ya duƙa yayi tapping dinta, ta buɗe idonta tana zarosu waje don ynxu baccin ya fara figarta, bed ya nuna mata yace "koma can ki kwanta..", ta buɗe baki zatay magana, da sauri ya ɗora yatsansa akan lips dinsa yace "shhhh do what i said ko kuma na fanshe duk rashin kunyar da kikay min", ai kam ba musu ta tashi tana turo baki ta hau gadon ta kwanta daga gefe, pillow da ƙaramin duvet da ya kwanta jiya ya ɗauka ya koma kan couch ya cigaba da abinda yake, har 11 bai kwanta ba yanata danna Laptop. Hajar tayi wani juyi mai kauri sbd azabar cramps, ba ta san lokacin da ta sakko daga kan gadon ba ta fara murƙususu tace "wayyo zan mutu cikina" sai kuma ta fashe da kuka, ture laptop din yayi daga gabansa, ya tashi ya kunna hasken ɗakin sosai, da sauri ya ƙaraso inda take durƙushe ya sunkuya yana kallonta yace "mene ne..?", ta yarfe hannu tana cigaba da kuka tace "wayyo Allah na zan mutu...", haɗe thick eyebrows dinsa yayi ya ɗan ɗaga murya yace "am asking mene ne..?", ganin yadda ta dafe lower abdomen dinta ya fahimci problem din daga ciki ne, ya ɗaga ƴar rigarta sai kawai ta ji soft palm dinsa a bare tummy dinta, tsabar shock da ta shiga ji kake ɗiff ta shanye kukan da take......✍️