Free chapter · Read without an account
Chapter 3
✨ *ALLON* *ƘADDARA* ✨
*OUM* *FATIMA*
*DASHEN* *ALLAH* *WRITERS* *ASSOCIATION*
*PAGE 3*
Washe gari na tashi da wuri kamar yanda na saba, kiching na shiga na haɗa mana abin ƙari kasancewar Ammy bata barin masu aiki yi mata girki sabo da haka nima ta hore ni akan girki tun ina ƙaramar yarinya nake bin ta kiching duk da cewa ina fama da ciwon Athma tun ina yarinya, amma da yake bama kunna wutar hayaƙi kwata-kwata a ɓangaren mu, ko wani aiki ne za'a yi mai yawa kamar Sallah, ko dai wani taro babban kiching Ammy take zuwa ita da masu aiki suyi, sabo da sam Ammy bata sakewa ƴan aiki ragamar girkin da tasan Mijinta zai ci. Wannan yana ɗaya daga cikin ɗabi'unta dake ƙara mata kima a wurin Baba Malam.
Ashirye tsaf na fito cikin shigar Abaya ƙirar Egypt baƙa da aka yi wa kwalliyar wasu fararen duwatsu masu kyau sai ɗaukar ido take, kallabin Abayar na naɗe kaina da shi ina fitar da daddaɗan ƙamshi.
Dining na nufa kai tsaye domin na san a wannan lokacin Iyayena suna can don karyawa, kasancewar yau Ammy ke da turaka, kuma ƙa'idar Baba Malam duk wacce ke da girki to zai zo sashenta suci abincin safe tare. Kamar yadda na zata kuwa ina doso wurin na hango fuskar Mahaifina mai cike da kwarjini da hasken Muslunci. A natse na ƙara so da sallama ɗauke a bakina. Baba Malam ne ya ɗago fuskarsa cike da fara'a yace "Mamana, ƙaraso ki zauna maza" ya faɗa cike da kulawa da tausayawa harma da tsantsar soyayyar da yake min.
Ƙarasawa nayi najawo kujerar dake kusa da shi na zauna fuskata ɗauke da kyakykyawan murmushi nace "Barka da safiya Baba".
"Barka Mamana, fatan kin tashi lafiya, yaya jikin naki?".
"Alhamdulillah Baba" na faɗa ina kamo hannun Ammy dake kusa da Baba ta ɗayan gefen nace "Ina kwana Ammy", "lafiya lau, yaya jikin?".
"Alhamdulillah Ammy na ware ma". "To Allah ya ƙara lafiya, maza ki karya ki tafi kar kiyi late".
"Ok Ammy" na faɗa ina jawo kofin shayin da Ammy ta miƙo min. A natse muka gama karin muka fita tare da Baba Malam muka shiga sashen Mamma. duka a dining muka same su suna karyawa. Gaba ɗaya na haɗa na gaishesu inda suka amsa min ba wata sakewa, Aunty Zainaba kuwa ko kallon inda nake batayi ba.
Ban damu ba nima nayi musu sallama nayi ficewata, dama sabo da Baba Malam ne na shigo don ba shigowa sashen su nakeyi ba. Ba wani ƙaunata sukeba. Don haka nima ban damu da yin shishshigi agaresu ba, sabo da duk wanda yayi min bana ɗaga masa ko kaɗan, dukda a ƙasan zuciyata ina ƙaunar ƴan uwana kuma bana jin daɗin yanda suke nuna rashin damuwarsu a kaina.
Kai tsaye ɓangaren Hajjo na nufa na gaisheta, ban zauna ba saboda Hamma Jabeer da na gani a ɓangaren suna tattauna maganar aurensa dake matsowa shi da su Alhaji Babba, da Abba. Gaishesu kawai nayi na fito, a haraba muka haɗu da Ya Nabeel cikin shirin tafiya aiki. Fuskarsa ɗauke da fara'a ya tareni da kulawa, gaisheshi nayi cikin natsuwa ina kallonsa cike da tsantsar soyayyar da nakeji tasa a cikin raina. "Menene?" Ya faɗa yana tsareni da idanu.
"Ba komai Muheeb, muje ka kaini Office yau bana jin driving".
"Are you sure ba abinda yake damunki".
"Babu, muje" na faɗa ina yin gaba, wurin motar muka nufa ya buɗe min da kansa na shiga ya rufe sannan yaja muka ɗauki hanya motar shiru ba mai cewa komai sai sautin gidan rediyo da ya kunna suna gabatar da shirin tambaya mabuɗin ilimi tare da shek Malam Aminu Ibrahim Daurawa. Kasa jure shirun nata yayi, cikin sanyin da yake halittarsace ya buɗe baki a natse yace "kin haɗu da Momy ne ko Aminatu?".
"A'a" na bashi amsa ina fuskantar sa "to meke damunki? Gaba ɗaya yau baki da walwala, wanene ya taɓaki?!". Kicin alamun damuwar da ta gauraye fuskarsa lokaci ɗaya na rashin walwalar da ya gani a tare dani ya haifar masa yayi maganar a sanyaye.
"Ba wanda ya taɓani Muheeb, kasan bana ƙyale duk wanda ya shiga gonata, kawai ina shiga fargaba ne a duk lokacin da da na tuna da ƙalubalen dake zagaye da soyayyarmu, na tuna da furucin da Momy tayi wanda zai iya raba tsakanina da kai sai inji tsoro ya kamani, bana son rabuwa da kai Ya Nabeel, kai kaɗai nake son yin rayuwa da kai, me yasa Momy bata son alaƙa ta da kai? Menene dalili? Miye aibuna?!". Cikin kukan da ya kwace min na ƙarasa maganar ina ɗora kaina saman ƙafafuna.
Tunda na fara magana ya samu wuri yayi parking zuciyar sa na tsin-tsinkewa da kalaman da take faɗa, in akwai abinda yake ɗaga masa hankali a duniya bai wuce ganin damuwa a saman fuskarta ba, bare zubar hawayenta. Tunda ya taso yake tsananin yiwa mahaifiyarsa biyayya, yana bin umarninta akoda yaushe sai dai akan Hanan ya kasa yi mata biyayya, ya kasa rabuwa da ita kamar yadda ta buƙata baya jin kuma zai iya rabuwa da ita matuƙar yana numfashi, domin da soyayyarta aka halicci zuciyarsa idan akace za'a cireta daga ciki, to sai dai a cire zuciyar gaba ɗaya. Waɗannan tambayoyin da tayi masa a yanzu shima amsoshinsu yake nema, ya tambayi Momy sau ba adadi amma taƙi ce masa komai, abinda kawai take ce masa shine ya rabu da HANAN ba haɗin sa bace ita, matuƙar ita ta haifeshi to ta haramtamasa auren HANAN har abada.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da sautin kukanta ya ratsa ƙwa-ƙwalwarsa, hannayenta ya kama duka biyun cikin sigar lallashi yace "kinga kalleni nan Hanan", ɗago jiƙaƙƙun idanuna nayi na zuba masa ina sauke ajiyar zuciya. "Kiyi haƙuri hajjonah kibar kukan hakanan domin yana matuƙar taɓa zuciyata" iska ya furzar kafin yaci gaba da cewa "nima kaina bani da amsoshin tambayoyinki domin kuwa nima ina buƙatar su, abinda kawai na sani shine duk wuya duk rintsi babu abinda zai rabani dake sai mutuwa wannan shine alƙawarin da zan miki muci gaba da addu'a insha Allah komai zai wuce, yanzu ki goge fuskarki muje in saukeki kinga har munyi late" ya faɗa yana duba agogon hannunsa.
Kamar yadda ya buƙata nayi sannan ya tada motar mukaci gaba da tafiya a hankali yana ta faɗa min daɗadan kalamai har sai da yasani dariya kafin ya samu natsuwa, a haka ya saukeni ya wuce bayan ya sanar dani zai dawo ya ɗaukeni.
Haka dai yau nayi aikin ranar ba wata wal-wala har na tashi, Abokan aikina sai tambayata suke akan mai ke damuna nace musu bana jin daɗi ne kawai.
**** Tun daga maganar da mukayi da Ya Nabeel da alƙawarin da ya ƙara jaddada min na manta da komai naci gaba da sabgogina ina zuwa wurin aikina kullum inda nake ta ƙara samun suna da masoya ta ko ina a cikin birnin Kano, inda Ya Nabeel yaci gaba da kame zuciyata da sassanyar soyayyarsa da tasa bana kula duk tarin masoyan dake kawo ƙoƙunan bararsu a gareni, gefe ɗaya kuma ana ta shirin bikin Hamma Jabeer dake ta matsowa nanda sati biyu masu zuwa, kasancewar shine aure na farko da za'a yi a Familyn Alhaji Sale yasa ake ta ɗoki da jiran lokaci, inda ƴammata da samarin gidan muke ta gudanar da gagarumin shiri domin zamu raƙashe dai-dai gwargwado.
★
A hankali nake takawa ina amsa wayar Samha da ta kirani, yau weekend ne banje wurin aikiba shiyasa na fito nake ɗan zazzagayawa daga layinmu zuwa na bayanmu don in motsa jikina, Baba Malam na hango a ƙofar gida ƙarƙashin wata kyakykyawar rumfar da akayi a ƙofafar Gidanmu inda yake yiwa dattawan unguwar karatu duk ranakun week end. Tsugunne nakai sanda na karaso kusa da Baba Malam na gaishesu suka amsa min da kulawa "Mamana daga ina?" Baba ya tambayeni da kulawa "Baba na ɗan zagaya na ɗan ware ƙafafuna, jikina naji yayi nauyi"
"To maza ki shiga ciki, ki kula kinji ko Allah yayi maki albarka" "Ameen" na furta ina miƙewa nashige inda ina jin idanun ɗaya daga cikinsu da tunda nazo wurin suka addabamin da kallo har na ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofa aka buɗe min na shige ciki ina jan tsaki.
Na tsani nataccen kallo a rayuwata amma na fahimci mafi yawan mutane nan sukafi kwarewa akai, wancan mutumin da ban san sunansa ba a nan cikin unguwar mu yake da zama a ƴan kwanakin nan na fahimci ya sakoni a gaba, ina yawan jin idanunsa a kaina duk lokacin da muka haɗu. Muna yawan haɗuwa da shi kullum in zan tafi wurin aiki, dai-dai lokacin da zan wuce ta ƙofar Gidansa shima yake fitowa a motarsa, kamar wani tsafi kullum sai mun haɗu, haka duk sanda yazo wurin zaman su Baba Malam to idanunsa akan ƙofa yana kallon mai shiga da fita don ganin ta inda zan ɓullo.
Ɓangaren Hajjo na wuce ina zuwa na samu Anisa yarinyar Aunty Surayya tazo tana ganina ta taso ta rungumeni cikin murnar ganina, da yake muna ɗasawa da ita sosai kaf cikin Familyn mu munfi jituwa ana cewa ai halimmu ɗaya dama sai hali yazo ɗaya ake abota.
Mantawa nayi da wancan mutumin da ya tsaya min a rai mukaci gaba da shan hirarmu da Anisa sai da magrib na janyeta muka tafi sashenmu, can zata kwana bayan munci abincin dare muna hira su Asiya, Kadija da Rahima suka zo muka ɗora da shirye-shiryen bikin Hamma...
*OUM* *FATIMA*