Free chapter · Read without an account
Chapter 13
✨ *ALLON* *ƘADDARA* ✨
*OUM FATIMA*
*DASHEN ALLAH* *WRITERS* *ASSOCIATION*
*PAGE 13*
**** Lokacin da su Baba Malam suka dawo sashen Ammy ya nufa muna zaune a falo nida Ammy tana min manyan Kalba a kaina da yasha wanki a Salon abin yanayin zafin da garin yake ciki ne yasa naji yana takura min shiyasa nace Ammy tayi min manyan Kalba.
Zama yayi saman kujera fuskarsa ɗauke da damuwa yana sauke ajiyar zuciya "sannu da zuwa Baba" na faɗa lokacin da Ammy ta gama tuɓke min kalbar ƙarshe da ta kama.
"Sannu da zuwa Malam, lafiya kuwa nagan ka a sanyaye?" Ammy ta tambaya bayan ta dawo daga wanke hannunta da taje yi. "Ki bari kawai Malama, yaron nan Nabeel ne yake bani tausayi Wallahi, daga Asibiti muke yanzu mun yi magana da likitan da case ɗinsa ke hannunsa, sosai yake jin jiki abin tausayi ya kasa yin haƙuri ya manta da komai, gashi Likita yace ba'a son yawan saka tunanin da yake a ransa sabo da ana buƙatar jininsa ya sauka a samu bugun zuciyarsa ya dai-daita".
"Subuhanallah Allah ya bashi lafiya" Ammy ta faɗa. Tashi nayi na nufi ɗakina duk suka bini da kallon tausayi "itama har yanzu ta kasa cire shi a ranta" Baba Malam ya faɗa yana kallon Ammy.
"Aikinta kenan sai abin yayi kamar yayi sauƙi sai kuma ta koma ruwa, ni abin ya ishe ni haka Malam kawai ta fitar da wani a cikin manemanta ayi mata Aurenta, ta tafi ɗakinta kowa ma ya huta" Ammy ta faɗa tana kallon Baba Malam da jiran amsar da zai bata. Murmushi yayai yace "abita a hankali in sha Allah komai zai wuce Malama, ke dai kici gaba da yi mata addu'a".
"Ina kan yi Malam kullum addu'a ta akanta ne" Ammy ta faɗa. "To ki ƙara dagewa addu'ar Mahaifiya a kan ɗanta karɓaɓɓiya ce, yauwa Alhaji Bilal ya same ni akan magar Mamana na kuma bashi izinin neman ta idan Allah yasa sun dai-daita shikenan bashi da matsala mutumin kirki ne".
"Allah ya zaɓa abin da yafi alkairi"
"Ameen" ta faɗa sukaci gaba da wata hirar akan shari'ar da yayi yau a Kotu yake bata labarin abinda ya faru abin abin dariya "ai sha'anin Mata sai a barsu" ya faɗa yana murmushi.
"Me kuma ya faru?" Ammy ta tambaya tana murmusawa itama "wata baiwar Allah ce ta kawo ƙaran mijinta akan ya sauwaƙe mata, sai da aka kira mijin yazo aka faɗa masa abin da ta buƙata, yace shi gaskiya ba zai iya sakin Matarsa ba. Buɗar bakinta sai cewa tayi Allah sai ya sake ta yace a'a ta dage akan maganarta, yace to shikenan taje ya sake ta saki ɗaya wai kuma yana faɗar haka ta fashe da kuka tace Allah sai ya maidata dama Babarta ce tace sai ya sake ta, da na tambaye shi zai iya maidata yace sosai daman shi yana son Matarsa a taƙaice dai ya maidata a nan take ta kuma amshe diyarta dake bayan Maman nata tabi Mijinta ya ɗauke ta a Babur suka tafi suka bar Uwar da baki buɗe mutane na dariya, ƙarshe dai kuka uwar ta fashe dashi tana faɗin sai ta biyata kuɗin ƙararta".
Dariya sosai Ammy tayi kafin tace "shiyasa akace ba'a shiga tsakanin Mace da Mijinta, domin kuwa Mata da Miji sai Allah".
"Ai kuwa dai yau mun shaida hakan" Baba Malam ya faɗa yana miƙewa yace wa Ammy ta kai masa abincin can ɗakinsa.
***** Kuka sosai nayi bayan shigata ɗaki sabo da tausayin Ya Nabeel, tunanika suka taru suka toshe min kaina, tarin tambayoyin da na rasa amsar su. Idan har sabo da rabuwa dani ne ya jefashi a cikin wannan halin to mai zai sa ya sake ni?, Wata zuciyar ke faɗa min ko dai Momy tasa ya sake ni?, Kai bana tunanin haka tunda a gaban kowa aka tambaye shi yace ba wani dalili, "koma dai menene Allah ya bashi lafiya ya tashi kafaɗunsa" na faɗa ina tashi na shige toilet na dauro alwala nazo na kabbara Sallar magrib da aka kira. Qur'ani na ɗauka nayi ta karatu bayan na gama sallar nice ban tashi ba har sai da nayi Isha'i kafin Ammy ta leƙo tace in shirya muje mu dubo Ya Nabeel "to" kawai nace mata sai da na gama addu'oi na sannan na tashi na canza kayana zuwa riga da siket na Atamfa na saka dogon hijabi ɗinkin Jilbab Maroon color na daure shi ta ciki yayi min cif a fuskata yayi mata kyau. Turare nasa kaɗan mara hayaniya na ɗauko wayata na fito.
A falo na haɗu da Ammy ta fito daga kiching ɗauke da ɗan ƙaramin kwando da ta shirya abincin mai sauƙin ci. Amsa nayi nayi gaba zuwa inda zamu hau Mota da yake duka zamu fita hada su Mamma da wasu daga ɓangaren Hajiya Mama da kuma Hajjo.
Sai da na fito muka haɗu da Aunty Kalisat Hamma Jabeer yazo da ita zai kaita itama tayi dubiyar don haka Motarsu muka shiga nida Hajjo Ammy ta shiga Motar Ya Shaheed da zai kai su Mammah sauran kowa ya shiga Motar da zai bi muka tafi. Tunda na gaishesu naja bakina nayi shiru sai Aunty Kalisat ce ke joho min hira ina amsa mata da eh, a'a har muka ƙara sa.
Ɗakin da yake muka nufa kasancewar wadatacce ne duk ya ishe mu, gaishe da Momy muka shiga yi da tambayar mai jiki ta amsa wa kowa amma nida Ammy ko kallo bamu isheta ba sai Aminatu ce ta amsa mana. Oho ko a jikinmu tunda ba sabon abu bane a garemu, bacci yake sanda mukaje sai gab da zamu taho ya farka.
Ya jiki muka shiga yi masa ya amsa da Alhamdulillah, tashi nake ƙoƙarin yi domin tuni Ammy ta fice duk gida zamu tafi har Momyn ma saboda ba anan take kwana ba. Hannuna naji an riƙe min na duba naga Ya Nabeel ne ya riƙe a hankali ya furta "ki tsaya ina son yin magana dake don Allah!" Duk ido aka zuba mana ana kallon mu musamman ma Momy da ta cika tayi dam. Ƙoƙarin kwace wa nake naji muryar Hajjo tana cewa "ki zauna ki saurare shi Hanan, ku kuma ku muje" ta faɗa tana kallon su. Wani kallo Hamma Jabeer yayi min mai kama da gargaɗi kafin ya fice Matarsa tabi bayansa, sai da kowa ya fice banda Momy sai da Hajjo tace "muje ko Habiba" sannan ta fice ranta a ɓace.
Tunda abinnan ya faru bamu taɓa zama mun yi magana da Ya Nabeel ba sai yau da ya faɗa min maganganun da suka taɓa min zuciya, maganganun da suka sa nayi kuka sosai a ƙarshe ya nemi yafiyata muka yafe wa juna na fito jiki na a sanyaye ina share hawaye. Haka nayi ta kuka a cikin Mota a hanyarmu ta komawa gida sai da Hamma Jabeer yayi min tsawa sannan nayi shiru ina ta faman sauke ajiyar zuciya har ya sauke mu a gida suka wuce shida Matarsa da tace cikinta na ciwo.
**** Bayan na gama komai na kwanta barci kasa yin Barcin nayi ina ta juya maganganun da Ya Nabeel ya faɗa min a raina "nasan kina jin haushina a kan abinda na aikata maki Hanan, kiyi haƙuri ki yafe min bani da wani zaɓin ne bayan haka, na kuma roƙeƙi don Allah kar ki tambaye ni dalili sabo da nayi alƙawarin bazan faɗa da baki na ba, abin da kawai nake nema a wurinki shine ki riƙa yi min addu'a ko bayan raina kar ki manta dani ki kuma yafe min, na soki Safiyya zanci gaba da sonki har numfashi na na ƙarshe kada ki manta dani ki riƙa sakani cikin addu'oinki itace alfarmar da zaki yi min, a ƙarshe na bawa Abba saƙo zai baki na gode sosai da soyayyar da kika yi min!" Kuka na fashe da shi lokacin da na gama tuna abin da ya faru tsakanin mu. Sai da nayi kuka na gaji kafin na tuna da nasihar Baba Malam a gareni da yace a duk sanda naji zuciyata ba daɗi to in tashi in faɗa wa Allah damuwata shine mai maganin ko wace irin damuwa.
Alwala nayi nayi sallah raka'a goma sha ɗaya nayi karatun Alqur'ani nayiwa Ya Nabeel addu'a kamar yanda nayi masa alƙawari kafin naji sanyi a raina na samu barci ya ɗauke ni.
★
Da asuba na tashi nayi sallah na koma barci sabo da yau weekend bana zuwa wurin aiki, kuma jikina duk a sanyaye na tashi ba daɗi. Ban tashi ba sai wurin ƙarfe 10:00 na safe nayi wanka na fito ina karyawa aka zo mana da mummunan labarin da ya tada hankalinmu muka shiga firgici da ɗimaucewa....
Oum Fatima