Free chapter · Read without an account

Page 6

by Farnanah · BAZLA❤️

Page 6


Abie na gama fadar haka ya tashi ya wuce dakinsa. Kallonta Bazla takeyi cikeda son jin karin bayani.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Ammi ta sauke,jikinta yayi sanyi, zuciyarta tayi ba dadi saboda ciwon da Abie ya fama mata na tsawon shekaru, amma kuma koma me zaije ya dawo tabbas…..


Bazla ce ta zauna a kusada ita wanda shine dalilin katsewar tunanin da ta shigayi, dago kanta tayi tana kallon tilon ‘yar tata. “Ammi meya faru ne?me Abie yake nufi da maganar da yayi?” Murmushin yaqe Ammi tayi tana tashi tsaye tace “kinga Bazla bakomai fa,ranshi ne kawai ya baci amma nasan zuwa gobe ze sauko, ki tashi kije ki kwanta dare yayi yanzu” saboda batason musu da Ammi shine kawai dalilin da ya sanya tayi mata sallama ta shiga dakinta.


Koda ta shiga Yasmeen tana danna wayarta bayan sallama batace da ita komai ba ta shiga bandaki ta watsa ruwa tazo tayi shirin kwanciya kawai ta kwanta. Itama Yasmeen cigaba tayi da abunda takeyi batayi mata magana ba saboda batason ta takurata, ta karasa Itama ta kwanta. Tunani ta dingayi iri-iri har batasan lokacinda bacci yayi awon gaba da ita ba.


____________________


Wasu irin hawaye ne masu zafi suka zubo daga idonta bayan tafiyar Bazla, bata fatan wani yayi irin rayuwar da tayi a baya, ita kadai tasan me takeji a yanzu. Ba wai batason Kamal bane ko auren a’a, Kamal yaron kirkine kuma salihi gashi da tausayi kuma bashi da girman kai, duk wasu nagartattun halaye Kamal ya tara, ko ita tana yiwa Bazla fatan samun miji na gari kuma nagartacce kamar kamal.

Amma kuma bataso ayiwa ‘yarta tilo auren dole, dukda kuwa tanada yakini akan cewar ‘yarta ta bazata cutu ko ta wulakanta ba agidan, amma kuma zafi da radadin da zatayi ta dawainiya dashi take tunani. Share hawayen tayi ta tashi ta shiga dankin Abie.


Da sallama ta shiga dakin, bai ko dago ya kalleta ba ya cigaba da abunda yakeyi. Zama tayi kusada shi tana jiran ya kammala suyi magana ta fahimtar juna.

Bayan ya karasa ya tashi yaje yayi shirin bacci yazo ya kwanta batareda ya kula Ammi ba, sauke ajiyar zuciya tayi ta gyara zama tace “Abien Bazla magana fa nakeso muyi” “ina jinki” ya fada idonshi a lumshe yana gyara kwanciya. Batareda ta hakura ba ta sake cewa “ka duba fa maganar nan Abien Bazla, duka duka nawa Bazla take da za’ayi mata auren dole?, ba wai ina jayayya da maganarka bane ko wani abu, nasan illar hakan da abunda hakan zai iya janyowa, Bazla yarinyace qarama har yanzu bai zama lalle zata iya daukar ko wane irin kalubale ba a yanzu. Na sani cewa daga Kamal har iyayenshi ba zasu bari wani namu ya wulaqanta ba bare kuma jininmu, amma kuma ita abun a zuciya zai tsaya mata,ga Bazla da saka abu a rai”ta nisa sannan ta kuma kallonshi wanda shima din ita yake kallo ta cigaba da “Dan Allah Abien Bazla kar ayiwa yarinyar nan dole ko dan gudun abunda zaije ya dawo” ta karasa idonta yana mai cika da hawaye.

Tayi tunanin ma ba zaiyi magana ba kawai sai jinsa tayi yace “naji duk abunda kika fada amma ki sani..”ya fada yana tashi zaune daga kwanciyar da yake “ke kanki shaida ce babu abunda mahaifin Kamal zai nema a gurina da bazan iya yimishi ba, saboda haka idan dai har ni na haifi Khadija kuma na İsa da ita to kuwa aurenta da Kamal babu fashi, se dai in shi yace ya fasa baya sonta ko kuma wata kaddara daga Allah“ ya koma ya cigaba da kwanciyarsa bayan ya gama fadar haka.


Shiru Ammi tayi ta kasa magana tana Kallonsa na wasu daqiqu, daga bisani ta tashi ta kashe wutar dakin ta koma dakinta. Salloli ta dingayi saboda ta rasa wata mafita ta miqawa Allah lamuranta, kusanma duka addu’o’inta akan Allah ya zabawa ‘yarta abunda yafi zama alkhairi ne a cikin addu’o’in nata.

Bayan ta gama shiru tayi ta cigaba da laziminta kafin ta tashi taje ta kwanta kafin lokacin sallah ya qarasa.


_________________________


       WASHE GARI


“Babana yau babu aiki ne da yawa?” Ummah tayi maganar tana kallon Sufyanu da yau bai fita da wuri ba kamar yanda ya saba. “A’a Ummah yanzu zan fita ai” ya qarasa fada yana saka takalmansa, sallama yayi musu ya fita.

 

Da Maryam ya hadu akan hanya take tambayarsa jikin Abba “jiki da sauki sosae Alhamdulillah, anata samun cigaba Alhamdulillahi” “Masha Allah nima yanzu nake cewa zan biya na gaishe shi da jiki, amma naga yau kamar ka makara?” Murmushi yayi yace”eh wallahi yanzu haka ma so nake nayi sauri na karasa” “Kuma gashi na tsaidaka zansa ka kuma makara, bari na wuce Allah ya kiyaye ya taimaka ya kuma bada sa’a”. Kara fadada murmushinsa yayi har fararen hakoransa suka bayyana, ba kadan yaji dadin addu’arta ba ya amsa mata sannan sukayi sallama ya tafi.


Maryam kuwa murmushin da yayi mata har sau biyu ji tayi tamkar ana kara mata wutar sonshi a zuciyarta,saboda komai yayi ita kyau yake Kara mata, juyawa tayi ta cigaba da tafiyarta.


_____________________


Tunda Ammi ta tashe su Sallar asuba bayan sun gama itada Yasmeen, bayan azhkar dinsu rana ta dan soma fitowa suka koma suka kwanta, Yasmeen ce kawae ta koma bacci amma Bazla ta kasa domin kuwa har yanzun tunani takeyi meyasa Abie yace idanma auren dole ne tarihi ze maimaita kansa? Kenan Ammi auren dole akayi mata da Abie kenan? amma ita ai bataga alamar hakan ba! To ko dai ita din ba ‘yarsu bace ba?!!!!

Rasa tayi ta inama zata fara gano bakin zaren tayi gashi kanta har wani sara mata yakeyi, kokarin yakice kowane irin tunani tayi domin ta samu ta huta kuma ta kudiri aniyar tambayar Ammi idan safiya ta waye. Da wannan tunanin ta samu ta kwanta.


Bayan sun shirya itada Yasmeen suka fito domin su karya, koda suka fito Abie yana zaune yana karyawa Ammi kuma tana kokarin zuwa ta taso su, gaishe su sukayi sannan suka zauna suka fara karyawa.

Daga Ammi har Bazla babu wanda ya iya saka wani abu a bakinshi saboda kowannensu da abunda yake tunani a zuciyarsa! 


Tun bayan da suka zauna yana hankalce dasu sunkasa cin komai sai wasa suke da cokali, tabbas da ace wani ne daban da ya dade da bashi hakuri kodan farincikin iyalinshi, amma ba zai taba iya hanashi ba, kallon Ammi yayi wadda fuskanta ma ta nuna alamun damuwa da kuma rashin isasshen bacci, ga kuma maganar da yayi jiya yasan ya fama mata ciwon da tayi shekaru tana jinya, tashi kawai yayi ya bar wurin saboda yanajin zai iya sauya ra’ayinsa wanda yake ganin tamkar rashin kyautatawa ce ga aminin nasa.


Bayan tafiyarsa da ‘yan wasu mintuna Yasmeen ma tashi bayan ta gama ta amsa wayarta da ake kira, ya rage daga Ammi sai Bazla ne kawai zaune a gurin. “Ammi” Bazla ta fada tana me ajiye cokalin hannunta wanda bata wani ci abincin da yawa ba saboda yadda ta saka maganar a ranta.

Dagowa kai Ammi tayi ta kalleta batareda ta amsa mata ba, “Ammi tambayarki nakeso nayi Dan Allah” “inajinki” ta gyara zamanta sosai domin tana so taji gaskiyar al’amarin. “Ammi me Abie yake nufi da yace tarihi ne zai maimaita kansa? wane tarihin kenan?” sauke ajiyar zuciya Ammi tayi sannan tace “Bazla yanzu ba lokacin wannan maganar bane,zan gaya miki daga baya in sha Allahu” “tou Ammi amma Abie ya janye batun auren?” Ta tambayi Ammi domin kuwa cikin kaso dari na damuwarta maganar auren tanada kaso sittin a ciki dukda kuwa maganar da Abie ya fada itama tayi mata tsaye a rai.

“Bai janye ba Bazla, amma shawarar da zan baki shine ki cigaba da neman dacewar ubangiji kuma koda ya dage akan batun auren karki sake kibi ziciyarki kibi umarninshi kinji ko?” “amma kuma Ammi ai bana sonshi”ta fada tamkar zata fashe da kuka, Ammi ta taso daga inda take ta zauna a kusada Bazla din tana mata nasiha akan Bazla ta barwa Allah komai ta cigaba da gaya masa damuwarta ita kuma in sha Allahu zatasan yadda zata shawo kan Abie ya yarda. Da haka Ammi ta samu ta rarrasheta taci abinci, ta karasa kenan zasu kwashe kwanukan se ga Yasmeen ta dawo ta kama musu suka gama gyara gurin.


Bayan sallar azahar Yasmeen ta shirya zata tafi Ammi ta dauko turaruka dana wuta dana jiki tace tagaishe da Mamin tata sukayi sallama Bazla tayi mata rakiya har mota sannan ta dawo bayan taga fitarta, wanda in banda damuwar da take ciki da tare zasuje domin ta kwana biyu bataje ba.


__________________



“A’a ba matsala naji dadi sosai, hakan ma ai yayi, Allah ya kaimu ya kuma tabbatar mana Alkhairi”cewar wani kamilallen dattijo wanda kallo zaka mishi ka tabbatar da tsantsar kamanninsa da Kamal. Mommy ce tayi sallama ta shigo da sallama ta ajiye mishi shayin data hado mishi, bayan ta zauna ta zuba mishi yake fada mata yadda sukayi da mahaifin Bazla.

Murmushi tayi sosae tana cewa “kai amma wallahi naji dadi Alhaji, amma me yasa baka bari kawai an saka har rana kaga an huta se shirye-shiryen biki ne kawai zaiyi saura” “A’a hajiya na dai fi son abi komai a sannu kinga nan da dan wani lokacin ai sun riga da sun fahimci juna sosai da sosai” ya karasa fada yana Shan shayin da yake hannunsa se kamshi yake me dadi.

“Kuma gaskiya da maganarka Alhaji, to Allah yasa Albarka” suka amsa da Amin gabadayan su.


______________________


Kusan sauke wayarsa da kuma sauke ajiyar zuciyarta a lokaci dayane, ta daga kai ta kalleshi tace “Amma Abien Bazla ba’ayi gaggawa ba a lamarin nan ba kuwa? Bazla fa har yanzu basu gama fahimtar juna ba ita dashi.” “Idan anyi auren zasu iya fahimtar junansu daga baya” zata kuma magana ya katse ta yace “Dan Allah Lubah mubar maganar nan na rigada na gama magana” “To Allah ya zaba muna abunda yafi zama Alkhairi” Amin kawae Abie yace yayi shiru daga bisani kuma ya dan dinga janta fira kadan-kadan domin kawae ya rage mata damuwa saboda gudun kada ta janyowa kanta ciwo.


_______________________


Bayan kwana biyu Bazla taga Abie bai kuma mata magana ba, kuma taga Ammi ma haka sai tayi zaton ko an janye maganar ne gabadaya, se ta warware ta dawo normal tamkar ba ita ba har tana lisaafin yau saura kwana biyar su koma makaranta.

Shiryawa takeyi zataje gidansu Yasmeen, tayi kyau sosae cikin atamfa mai matukar kyau da tsada tasha dinkin A shape,tayi kyau sosae dukda kuwa ba wani dauri ta iya ba sosai amma kuma a hakan tayi kyau sosai, gyalenta, jakarta da kuma takalminta duka iri daya ne. Ta fito tayiwa Ammi sallama ta tafi.


_________________________


Yau bai fita aiki ba saboda baya dan jin dadin jikinsa amma idan ka ganshi bazaka taba tunanin bashida lafiya ba, zaune yake a tsakar gidan ya dan kishingida bayanshi da gina ya lumshe idanunshi, “sannu yaya” cewar Hajara tana ajiye masa abincinshi, gyada mata kai kawai yayi ta tashi ta cigaba da aikin da yake gabanta.


Sallama Maryam tayi ta shigo amsa mata sukayi, batayi tsammanin ganinshi saboda tasan baya fashin zuwa gurin aiki sai da dalili, ta gaishe da Ummah sannan ta gaishe shi, su Hajara ma da Ameer suka gaishe ta ta amsa musu. “Yaya lafiya yau bakaje aiki ba?” Maryam ta trambayi Sufyanu ganin kamar bashida lafiya, “lafiya kalau kawai dai yau ina hutawa ne kuma ina dan jin zazzabi shiyasa banje ba” duk sai taji ba dadi dukda kuwa ba wani ciwo bane yakeyi tayi mishi Sannu suka dan taba hira da Ummah da kuma Hajara tayi musu Sallama ta tafi.


________________________


Se kusan Magrib ta dawo gida duk ta gaji a napep ta dawo saboda haka kawai taji shi take ra’ayin hawa ta dawo gida.

Baqin motoci guda biyu ta tarar a harabar gidan nasu, bata kawo komai ba saboda a tunaninta Abie baqi yayi ta shiga parlorn nasu bakowa a ciki amma kuma tana jiyo muryoyi sama-sama daga parlorn baqinsu. Har tazo zata shiga dakinta taji tamkar muryar Daddyn su Hafsa tazo zata sauko kenan taji yana cewa “Ai Allah ya tabbatar mana da Alkhairi ya sanya ayi damu yanda ya nuna mana ranar nan ya nuna mana ranar da za’a daura da rai da lafiya, ai auren Khadija da Kamal nikam ai sai dai nace tuwona mai na ne za’ayi” kafin ma ta karasa guntun tunanin data fara taji Abie yana cewa “ai kuwa dae Alhaji, yanzu kawae abunda ya rage shine Allah ya nuna mana ranar kawai”. 

“Kenan hakan yana nufin Abie ya saka mun rana da yaya Kamal? Auren dolen zeyi mun kenan?” Haka ta dinga tambayar kanta ba me bata amsa. Haka taja jikinta ta karasa dakinta ta kulle kofar, rasa tayi me zatayi gashi ta kasa samun mafita.

A haka har akayi Sallar magrib ta tashi taje tayi arwala tayi sallah, haka ta cigaba da zama har akayi kiran isha’i tayi. Mafita daya ce take ganin ta dace da ita shine kawai ta gudu to amma idan ta gudu din taje ina? “ko dai gidansu Yasmeen zanje?” “Kai ina wannan ba mafita bace” ta bawa kanta amsa, haka ta cigaba da tunanin ina zataje, can ta sauke wata ajiyar zuciya tana godewa Allah, ta gyara kwanciyarta se barci.


Asubar fari ta tashi ta shirya tana jiran a shiga masallaci kawai tayi ta tafiyarta. Haka kuwa akayi seda ta tabbatar kowa ya fita sannan ta fito da ‘yar karamar akwatinta tana fatan Allah yasa kar a ganta har ta fice daga shiyar.


_______________________


A bangaren Ammi kuma ganin har anyi isha’i bata dawo ba se tayi tunanin ko a can zata kwana, ta kira wayoyinsu duka basa shiga kawai sai ta barshi tana tunanin yadda zata fadawa Bazla batun zuwansu Daddyn Kamal tambayar aurenta, dukda kuwa ba’a kai ga saka rana ba!


Da safe tana cikin hada breakfast taji wayanta tana ringing koda ta duba se taga ashe Yasmeen ce ta dauka, suka gaisa, “Ammi Dan Allah Bazla tana kusa?” ”Bazla kuma Yasmeen?” Ammi ta tambayeta cikeda mamaki” “eh Ammi tun dazu nake kiranta bata dauka ba may be ko ta saka wayar a silent” Ammi rasa tayi me zatace kawai se ta kashe kiran.


Fita tayi ta trambayi Abu me gadi ko Bazla ta dawo? “Eh Hajiya tun jiya ai bata sake fita ba bayan ta dawo kusan magrib”. Ammi batace dashi komai ba ta juya ta koma ciki ta fatan Allah yasa ba wani abun ne ya samu Bazla ba daya hanata fitowa ba tun jiya.

Ta bincike ko ina na dakin amma ba Bazla ba alamarta idonta ne ya sauka akan wayarta data bari akan gado da sauri ta juya ta kuma kallon dakin, se a lokacin ne ma ta lura da ba abubuwan ta na amfani da kuma daya daga cikin akwatinta ba daya………..


______________________

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol