Free chapter · Read without an account

Page 10

by Fatima Muhammad Gurin · GAMON JINI

⚡️*GAMON JINI*⚡️


   *NA FATIMA MOH'D GURIN*

        *GUREENJO*


*E.W.F*


*PAID BOOK*


*FREE PAGE TEN*


*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*


*****


Tana shiga parlorn ta ta tarar da Nadra da Hajiya Yaya a tsaye hindu a duke a gabansu, had'e fuska tayi tace

"Hindu lafiya?"

Charab hajiya yaya tace

"Lafiyar kenan yasa kika ganmu haka, zuwa nayi na d'auki Tsintacciyar chan take min aiki bazata zo ta zauna sede taci arziki tayi kashi ba baze yiwu ba, Ke!!"


Se a lokacin Amah ta lura da Amatullah dake jikin kujera tsawar da hajiya yaya ta daka mata yasa ta rud'e gabad'aya tana shirin fita hayyacinta.


"Mike mu tafi daga yau kin zama er aikina an zo cin banza ko, to be samu ba Tsintacciya wacce tushenta bashi da tabbas" cewar hajiya yaya.


"Dakata Yaya, kin san dae yarinyar nan Amanar waye duba kigani ba lafiya ne gareta ba hayaniyar ki gabad'aya tasa tana shirin rasa numfashi a kirjinta, kaman yadda kika san matsayin wadda ya bani ajiyarta a wurina haka nake kiyaye komai nashi sbd 'bacin ranshi baze muku daad'i ba, so please ku kama hanya ku tafi nan kam baza ku samu abinda kuke so ba, Amatullah bazata ta'ba zama er aikin kowa bama bare ke"

Cewar Amah


Baki sake Hajiya Yaya ke kallonta yadda take kallonta take gayamata magana hakan ba Saudat bace, wacce sede in aka zaga ko ya'ba mata habaice habaice tayi kuka ta share hawayenta idan abun kuma ya mata zafi sede su ji ta a asibiti to me ke faruwa yau? (Nide Gureenjo nace da alamu kun fara kaita bango dan dama shiru shiru ba tsoro bane...)


Kirjinta Hajiya Yaya ta nuna tace

"Eyyee ni saudat kike gayama magana haka?"

Tana karasawa wurin Amatullah ta d'agota tace 

"A'a uwata"

Se ta sake kallonta tace 

"Wai nikam dame kurna tafi magarya ne? Yadda fa kike takama nan d'in gidan mijinki ne haka nima nake takama kaman yadda aka sa sadaki aka auroki haka nima, so enough is enough karku bari raina ya kai karshe a 'baci dan baze muku daad'i ba"


Gabad'aya se hajiya yaya ta rasa kalaman bakinta, bata san sadda ta lailayo wani ashariya ta narka ba jin Amah tana cewa Hindu 

"Please in sun gama haushin sun fita ki tabbatar kin tsabtace min parlor sbd kin san bana son wuri da karni da bashi"


Daga haka ta shige daki abinta, yau ko ba komai ta san kaman yadda Hajiya Yaya ta lalata mata zuciya itama tayi mata daidai dukda har ranta ba wai taji daad'in sa'insar bane sbd ba d'abiarta bace sede ko gobe ta san hajiya Yaya ta gane ba wai tsoronta ne ke hanata magana a duk abinda suke mata ba girman wadda ya had'asu ne yasa bata cewa komai.


Da kyar ta samu Amatullah tayi bacci sbd sossai ta tsorata dasu jikinta ba inda baya rawa har tayi bacci be dena 'bari ba ko da ta sha magani ne bacci yayi nasarar d'auke ta..


Maganganu ta fara ji duba wayanta dake ringing tayi taga Lamido, picking tayi suka fara gaisawa take tambayarshi wurin aikin ba wani matsala ko, ze yi magana kenan aka fara buga kofar bugun hauka, cike da mamaki yace 

"Amah lafiya kuwa?"

Tace

"Ba lau ba babana, karka damu bari na sauraresu kar su tada Amatullah da da kyar na samu tayi bacci sbd tsoratata da sukayi ba jimawar nan"


Da sauri yace

"Please Amah don't hang up.."

Sauke wayar tayi ba tare da ta kashe ba ta fito, Hajiya Babba ke zaune kan kujera yayinda Hajiya Yaya da ta gama buga mata kofa take tsaye gefen kujera.


"Assalamu Alaikum" Amah tace tana kallonsu ba wadda ya amsa, se Hajiya Babba ce tace

"Kin cika saudatu kin tumbatsa wato sbd kina ganin yanzu yaranki maza duk sun girma shine bari ki fara mana fitsara ko? To baki isa ba, Muhammad dae ni na haifi abina umarni kuwa dole ya bi nawa in ma dan ya gayamiki kudurina ne kike tada jijiyoyin wuya ya kamata ki mayar ki kwana da sanin kaman rubutacce ne aure tsakanin Nadra da tuzurun d'anki se an yishi, sannan ki fito da wanchan tsintacciyar aikatau se tayishi in dae har zata zauna a gidan nan, abu na karshe ki baiwa Yawuro hakuri"


Ajiyar zuciya ta sauke bayan gama jin kalaman hajiya Babba, ta kalli Kasa tace

"Ina me Neman Afuwanki idan kalaman da zan furta yanzu zasu kasance marar dad'i gareki, A gaskiya Hajiya babu wadda zan iya ciki, kaman yadda na fad'awa Abbunsu Da miyau na dae wallahi lamido baze auri dangin Hajiya Yaya ba ko bayan rayuwata, abu na biyu Amatullah Amanar Lamido ce wacce nayi alkawarin riketa kaman yadda ita hajiya yayar ta sani ko kare ne Lamido ya kawo ya bani amana se inda karfina ya kare wurin kula da kare wannan kare bare biladam, hakuri kuma ni banga laifin da na aikata ba da zan bata hakuri ita ba Sarauniya Aisha ba(mahaifiyarta)"


Daga haka tayi shiru, Chabb ina wuta Hajiya Babba ta saka Amah tashin hankali sabo suka bud'e hajiya yaya har ikirarin kiran yaranta su yiwa Amah duka take, ita kuwa ko a jikinta se kallonsu da take d'aya bayan d'aya.


Abrar dake zaune jin maganganun Amah be san ya mike ba, shi karan kanshi mamakin Amah ne yayi mugun lullu'beshi be ta'ba tunanin Amah ta iya fad'a ko cacar baki ba sbd ganin yadda suke take ta take kyalesu, sun kai mishi Amah makura tabbas... wait a minute..! kaman shi yaji ake zancen wani aure da wa? Shrugging kafad'anshi yayi irin chan su ta shafa a yanzu dae ba wadda ze mishi auren da be amince ba, murmushi me kayatarwa Wadda har hakorinshi seda ya bayyana ya saki yana jin sanyi a ranshi at least Amah ta bashi kwarin gwiwar kar'bar mata enci wurin mutanen nan.


Yana ji Hajiya Babba na ta rusa kuka kaman wacce aka yiwa mutuwa, Yana kuma jin sadda Hajiya Yaya ta baiwa Nadra umarnin kiran Abbu da daddy wai tayi sauri Saudat zata kashe musu uwa da alamu hawan jininta ya tashi, wassafa yadda ze yi da hajiya babba yake sbd duk tafi matsawa mahaifiyarshi murmushi ya saki da wani idea ya fad'o mishi nan take bari ya samu hutu se ya tabbatar ya dasa mugun tsoronshi a zuciyar tsohuwar.


Tabbas hankalin Abbu ya tashi jin yadda akayi, kallon I'm disappointed in you yayiwa Amah, bata damu ba sbd ta sani maganar fatar baki kad'ai na rana d'aya be yi kwatar kwata cikin abubuwan da suka mata ba bata manta wani lokaci da Khalid yayiwa Hajiya babba 'barna sbd sun tafi da baban ya barshi a parlor ya shiga wurinta cikin d'aka har parlornta tazo ta mareta abinda bata ma san sadda akayi ba, kuma a gabanshi hakuri kawai ya bata to menene don yanzu ta maida mata magana bayan ta bata hakuri kan ta fara? 


Hakuri Abbu yayi ta bata tace ita fafau bazatayi hakuri ba se ya amince da auren Nadra da Abrar, Daddy da ya shigo ne y'a sanya baki da wayo da dabara suka samu da kyar ta hakura, suka fice Amah ta shige d'akinta, tsaye ta tarar da Amatullah tana zubda hawaye, zatayi magana Amatu ta zube a kasa cikin shesheka tace


"Amah Dan Allah kiyi hakuri kuna zaman zamanku lafiya na zo na shiga tsakani gashi ana fad'a a kaina wlh na amince zan yi aikatau d'in in har hakan ne kwanciyar hankalin kowa."

Murmushin takaici Amah tayi tace

"Bamu ta'ba zama kalau ba Amatullah kuma na san da wuya ayi hakan abinda ba'ayi tun shekarun baya ba ba lallai hakan ya yiwu yanzu ba karki damu"


Kanta ta dukar tana me cigaba da zub da hawaye tabbas ran Amah a 'bace yake kuma bata son abinda za'a ce itace sila sam, hindu Amah ta kira tace ta rakata d'akinta itama zata d'an kwanta zuwa la'asar, seda suka fita ta tuna Abrar na kan waya karawa tayi a kunne tace

"Hello"

Yace 

"Amah are you fine? I mean baki jin alamun ciwonki?"


Ajiyar zuciya ta sauke tace

"No ba wani abu, me kake gani? Na san kaji komai"

Yace

"Ba zan ta'ba auren Nadra ba, Amah ba zan ce kiyi hakuri ba sbd kin yi isasshe amma bana son wani abu da ze 'bata tsakaninku da Abbu sam Amah"

Cike da damuwa yayi maganan ya sha fad'a mata ko itace takewa matar da yake mugun so Abunda hajiya Babba take yi mata ranar da matar tace zata mayar mata ko suyi sa'insa zamansu ya kare, ta tabbatar abinda yake son tuna mata kenan, Ko min lalacewa hajiya Babba Uwa ce ga Muhammad baze so abinda ze 'bata ranta Ba ko menene shi.


Hawaye ne ya silalo mata tace 

"Lamido I can't take it anymore, ni kad'ai na san irin zafin da nake ji a duk sadda zasu bud'i baki su jefeka ko iyayena da munanan kalamai, sbd yanzu na tanka shine matsala? Na gaji lamido, Duk abinda suka kasance suna min Baba be ta'ba sani Ba amma wannan karon matukar Mahaifinka yace se ka auri dangin Hajiya Yaya wlh se mun je gaban Baba ba ze ta'ba yiwuwa ba"


Shiru yayi da gaske Amah ta kai kololuwa kuma ta kyamaci had'a d'angi da Hajiya Yaya Ba kad'an kad'an ba, sun kara tattaunawa da kyar ya lalla'bata ta amince zata je ta baiwa Abbu hakuri ta amsa ne kawai amma ita bata ga abinda tayi na bada hakuri ba, bayan sun yi sallama ta kwanta bacci hayaniyar Su Amrah ne ya tasheta seda tayi wanka tayi sallah kan ta fito bata gansu a parlor Ba, tsohon d'akin Abrar da yanzu Amatullah ke ciki ta shiga jin daga nan ne hayaniyar ke tashi.


Aiko nan ta same su suna ta zubawa Amatullah surutu tana murmushi hannunta d'auke da Afrah, cike da mamakin yadda nan da nan yaran suka sake da Amatullah take, wacce wanzuwarta cikinsu kuwa ke mugun sata nishad'i, fita tayi cike da tunanin menene ya raba Amatullah da iyayenta? Menene labarinta? Ita kuma wacce iriyar kaddarar ke sarkafe cikin rayuwarta? Babu me bata wannan amsa dole se Amatullah ita kuwa bata tunanin tayi lafiyar narrating rayuwarta don bata yarda ba ma sunanta Amatullah dukda ta sani Lamido da matukar wuya yayi karya.


Har aka kwana biyu rikici ake a gidan, sam be da cikakken walwala shi Abbu yana fushi fushi da ita akan rokon da ya mata taje ta baiwa Hajiya Yaya hakuri kaman yadda hajiya babba tace bazata sauko ba se Amah taje ta baiwa hajiya Yaya hakuri ko an tilasta Abrar auren Nadra wadda a ciki babu wadda ta ga zata iya, tun su khalid basu gane ba har suka fahimta tunda dukkansu sun mallaki hankalin kansu babu wadda be san rayuwar Abbu da Amah ba sede kaman ja baya yake shirin yi.


Zama na musamman sukayi su uku, Khalid, Abdulkadir da jabir suka kira Yayansu suka zayyane mishi abinda ke faruwa yayi mamakin kafiyar Amah shi a tunaninshi tunda ana Neman 2weeks da rikicin an wuce wurin komai yayi daidai, ce musu kawai yayi ze kirata suyi magana sun sanshi so basu zauna jiran amsarshi ba dan bazasu samu ba kowa ya kama harkar gabanshi.


Ya kuwa kira Amah d'in sede ga mamakinshi tace babu wadda zatayi ciki kuma ta rantse, yayi mugun gamsuwa da dalilinta dukda durkusawa wada ba gajiyawa bace sede ita an ta'ba tilasta hajiya Yaya ta bata hakuri akan abubuwan da take mata? 

Sallamar Amatullah ne ya katse mishi abinda yake shirin fad'a, yayinda Amah dake d'auke da mamakin ganinta a lokacin ta sauke wayan kunnenta tace


"Amatullah..! Jikin ne?" Sbd tana complain na ciwon ciki tun safe d'in.

Kai ta girgiza tare da zama a kasa cike da natsuwa ta fara magana.


"Amah Dan Darajar Allah da manzonsa ki taimakeni ki kawo Karshen wannan zama da kukeyi, a fahimtata tun dama baku da cikakken zaman lafiya sede yadda kike yayyafawa zuciyarki ruwa a ko yaushe shi ke haifar da zaman lafiyar to me yasa a dalilina kike kokarin taurara ranki Amah? In har hakan zata cigaba bazan iya yafewa kaina Ba, inde ni ce zan tafi zan koma ko da kuwa cikin kangin bauta da wahala na bakar rayuwa da na fito ciki ne..."


Kuka ne yaso cin karfinta tayi kokarin mayarwa tare da cigaba 

"Na san kin fini sani sede zan d'an miki tuni a koda yaushe Allah na tare da masu hakuri, kaman yadda ya fad'a cikin ayoyi bila adadin, kuyi hakuri, kuyi hakuri, Allah na tare da masu hakuri, masu hakuri sune da riba da sauransu sannan a lokacin da wani bawan Allah ya zowa Annabi da tambayar me ze yi Dan cin ribar zaman duniya se yace mishi karkayi fushi sau uku, kinga kenan fushi bashi da riba sbd daga shed'an yake, babban dalilin kuwa Amah idan har su Uncle Khalid zasu ga kuna hakan su kuma ya zasuyi? Se in ga kaman kunyar matansu ne ze kama su, ba kowani d'a yake jure fad'a a tsakanin iyaye ba, kiyimin rai ki gafarta min idan abunda na fad'a ya kona miki rai banyi don reni ko wani abu ba"


Ta karasa tana share hawayen dake zarya saman kuncinta, ajiyar zuciya Amah ta sauke kan tace

"Na fahimci sakonki Amatullah, Idan Matayen 'ya'yanmu suka ga mu da muka tara su zuri'a guda ma bamu zauna lafiya ba su to in suka yiwa mazajensu ba wani abu bane, me anfanin fushin da bashi da riba tunda na san Abbunsu dae baze ta'ba chanza uwa ba?"


Kallonta Amatullah tayi se Amah ta sakar mata murmushi tace

"Kai tsaye haka kike son furtawa, na sani Amatullah sede tunda daga ke har Lamido kun matsa dole in je in bada hakuri don bana son Amatullahi na ta koma rayuwar kunci, gwara in ganta tana wasa da su Afra dimples d'inta na lo'bawa sbd dariya ko?"


Murmushi kayattacce Amatullah ta saki hakan yasa Amah ma sakin murmushi cike da nazarin irin baiwar da Allah yayiwa yarinyar na tsantsar natsuwa da hankali, a kiyasinta Amatullah bazata wuce sadiq ba amma dubeta sa'banin sadiq da har yanzu be san inda ke mishi ciwo ba.


Mikewa Amatullah tayi tare da yi ma Amah se da safe ta fice, d'aga waya Amah tayi da nufin duba time sbd yau d'in itace da mijin sede bata je ba, d'an wara idanu tayi tare da manna wayan a kunnenta tace

"Afuwan Babana, shaff ganin Amatullah cikin yanayin damuwa yasa gabad'aya na mance waya mukeyi"


Cikin wani yanayin narkewa yace

"Ai ba naga tana kokarin kwace min matsayi ba.."

Murmushi sossai Amah ke yi sbd wannan nature na Abrar da matukar wuya yake nunawa gareta kad'ai yake iya wannan shagwa'ba a ranta ta tsinci kanta da Adu'ar Allah ya bashi mace da zata sakankatashi ta sangartashi yadda ze bud'e wani faifai na rayuwarshi ba tare da ya sani ba...


"Duuuuuum" wani mummunan kara ya karad'e kunnenta kan taji diff wayar ta d'auke a lokaci d'aya zuciyarta tayi wani bala'in dokawa.

"Lamido....!"

Ta ambata a gigice cikin karaji..


****


*Ko kin shirya mallakar Wad'annan TAURARI Guda biyu😉 Da Naira Dari biyar kachal zaki mallaki gawurtattun littatafan nan guda biyu...


*GAMON JINI Na Fatima Muhammad Gureen (Gureenjo)*


*Da Kuma*


*SABABI Na Amina Ibrahim (Oum Ameer)*


*Akan Naira D'ari uku kuma zaki mallaki Guda d'aya cikin biyun, karku manta mun shirya tsab domin Nishad'antar daku, fad'akar daku da kuma Nishad'antar da ku masoya, Mallaki naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali er uwa👌*


Zaku iya biya ta account number kamar haka

3118518476

First bank

Fatima Muhammad Gurin

  Se a turo shedar biya ta wannan layin

***

Note: Banda Recharge card. 




          🖤Gureenjoh🖤

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol