Free chapter · Read without an account

Page 13

by Farnanah · BAZLA❤️

Abba ya qara da cewa “Maryam yarinya ce mai kirki da natsuwa na tabbatar zamu sa’ar suruka kaima zakayi sa’ar mata” ya qarashe maganar yana kallon fuskar sufyan, Sufyan da ya rasa mai zaice yace “to Abba Allah ya tabbatar mana Alkhairi” Abba yaji dadin maganar yace “Ameen Allah ya maka Albarka, idan na samu lokaci zanje muyi magana naji ko babu wani da aka tsayar” Sufyan yace “to Abba nagode” 


Sufyan yana komawa dakinshi ya rasa mai yake mishi dadi, shi dai yasan ba wata soyayya tsakaninsu, ya kawar da abun yana Addu’ar Alkhairi


_____________________________



Yasmeen tana komawa gida, ta tarar anata shirye shiryen dawowar daddynta, ta shiga qawataccen dakinta mai dauke da wani lafiyayyen gado, dakin yayi kyau sosaii kamar dakin wata amarya, sai qamshi dakin yakeyi, ta jefa Jakarta da mayafinta akan gadon, ta zauna kan gadon ta kira number Inna da Ammi ta bata, tana fara ringing aka dauka


Inna ta dauka tace “Assalamu Alaikum” Yasmeen ta amsa da “Wa’alaikissalam Inna ina wuni” Inna tace “lafiya lau” Yasmeen tace “Inna sunana Yasmeen Ammi ce ta bani number zanyi magana da Bazla” Inna tace “Allah sarki tana daki bari akai mata wayar” Yasmeen tace “to inna nagode” Inna ta bawa Sa’adatu dake kusa da ita tace ta kaiwa Bazla din, Sa’adatu ta karba ta kai mata a dakin


Bazla da ta zaci Ammi ce, ana bata ta saka wayar a kunne tace “Ammi ina wuni” Yasmeen tace “ba Ammi bace Yasmeen ce” Bazla da mamaki tace “Yasmeen ina kika samu number inna, ya kuma akayi kikasan ina nan” Yasmeen tace “ban sani ba, Ashe bakida hankali har haka Bazla zaki saka qafa ki bar gida saboda qaramar magana, menene amfanin tafiyar taki” Bazla da ta tsaya saurarenta har ta gama tace “sannu uwata zaki kirani kina mun masifa, ni ba wannan ba ya akayi kika San ina nan” Yasmeen tace “kin bani mamaki wallahi, to Ammi ce ta gayamun” Bazla tace “kinje gida kenan” tace “naje mana, ina kiranki baki dagawa, Ashe nan kika bar wayar” tace “yasmeen banida mafita ne, nasan Abie sarai idan ya dage akan abu, zuwa na nan ne kawai zai sa ya fasa” Yasmeen tace “koma minene Bazla bai kamata ki bar gida ba, wannan ba mafita bace” tace “toh Yasmeen aikin gama dai ya gama, na so ma yau na dawo Ammi tace kar in dawo” Yasmeen tace “ai ta gayamun, yanzu dai sai mu dage da Addu’a Allah ya kawo mafita a lamarin nan, amma ni banga dalilin da zaisa fa kice bakison kamal” tace “wai kowa da anyi magana sai yace dalili dalili, ba wani dalili kawai bana ra’ayin aurenshi bai mun ba bana son shi” Yasmeen tace “Allah ya sawwaqa, ni zan je na tayasu aiki yau daddy zai dawo” Bazla tace “to sai munyi waya ki gaida Mamie, Da daddy idan ya iso, Allah ya kawo shi lafiya” Yasmeen ta amsa da Ameen ta kashe wayar ta koma wurin Mamie da ke parlor zaune itada junior


Mamie tace “ya kika samu Bazla din” Yasmeen tace “hmmmm Mamie bari kawai” nan ta gaya mata komai, Mamie tace “to ai anyi sa’a da tayi tunanin zuwa wurin kakarta” Yasmeen tace “wallahi kuwa Mamie” Mamie tace “to Allah ya sawwaqa” ya amsa da Ameen


Yasmeen tace “Mamie daddy ya kusa ne” Mamie tace “eyh sun kusa gida ma ai, ko yanzu kina iya ganinshi” suna nan zaune kusan 10minutes sai ga horn na motoci alamun shine, junior ya tashi da gudu ya bar parlorn zuwa parking space


Motocin suka gama shigowa, ya bude ya fito, dattijo ne wanda ko baiyi shekaru sittin ba to sai kadan, wanda da ganinshi kasan yana cikin daula, junior ya qaraso kusa dashi yana mishi sannu da wuce, suka jera suka shigo cikin parlorn, yana shigowa Yasmeen ta tashi tana oyoyo daddyna, ya shafa kanta yana murmushi yace “Yasmeen na sameku lafiya” tace “lafiya lau daddyna” Mamie tace “sannu da zuwa Alhaji” yace yawwa “Mamien yara mun sameku lafiya” tace “lafiya lau” 


Sai aka shigo da Kayan shi, Mamie ta dauka takai dakinshi, junior yace “daddy ina tsarabar mu” daddy yace “junior ka bari na huta sai a dauko tsarabar ko” ya tashi yace bari ya shiga ya samu yayi wanka


Yaje yayi wanka, Mamie tazo qara gyara dining din suka zauna suna jiran fitowarshi, yana zuwa ya zauna, Mamie tayi serving dinshi da kanta, Yasmeen ta zubawa kanta da junior, suka fara cin abincin suna hira, suna gamawa su Nasiba suka gyara wajen, suka koma parlor suna cigaba da hirarsu, Daddy ya bawa kowa tsarabar shi, yace “idan ban baku yanzu ba junior sai ya hadiyeni” duk sukayi dariya suka cigaba da hira cikin so da qauna 

_____________________________________



Abdulhakeem ya kira Kamal ya tambaye shi idan yana gida, ya ce mishi yana nan, Abdul yace “ina kusa da unguwarku yanzu zaka ganni InshaAllah” kamal yace “to sai kazo” 


Baa fi minti goma ba sai ga shi ya qaraso, suka gaisa yace “nifa zuwa nayi naji ya za’ayi ka samomun number Yasmeen don Allah, tunda mukaje na ganta yarinyar ta tafi dani” Kamal yace “nawa zaka biya a samo maka” Abdul yace “nifa ba wasa nake ba, kace Bazla ta turo maka mana” yace “ni tunda muka dawo ko waya banyi da ita ba” Abdul yace “bangane ko waya bakuyi ba” yace “eyh na bata time ne don ta samu tayi tunanin da tace” Abdul yace “amma dai kai wani iri ne, idan ta gama tunanin itace zata nemeka bakai zaka dinga nemanta kaji ko ta gama” Kamal yace “kuma fa hakane, banyi wannan tunanin ba” Abdul yace “ai sai ka kirata yanzu, daga nan ka tambayarmun number” kamal ya dauki wayar shi ya danna number Bazla amma sai yaji a kashe, Abdul yace “may be batada charge ne” kamal yace “to kila” Abdul yace “amma dai naso na samu number nan yau wallahi, ko zaka tambayi hafsa ko tanada ita” yace “kar ka dameni fa kaje ka tambayeta da kanka” Abdul yace “haba abokina don Allah” kamal yace “basa nan fa sun fita dukansu” Abdul yace “ka kirata a waya to” Kamal yayi tsaki ya kira hafsa yace “turo min number Yasmeen qawar Bazla idan kinada ita” tace “to yaya” ya kashe wayar, Abdul ya dameshi da surutu yace “kai wai baka gajiya da surutu ne” Abdul yace “eh bana gajiya” ya kyaleshi bai ce komai ba, sai ga message ya shigo hafsa ta turo number, ya miqa mishi wayar ya kwashe number, ya tashi yace “abokina nagode, ni zan tafi gida


______________________________




Abdulhakeem yana komawa gida bayan La’asar yana kwance a dakinshi ya dauki wayar shi ya kira Yasmeen, har ta gama ringing bata dauka ba, ya qara kira bata daga ba, a ransa yace ko bata kusa ne, ya qara kira sai a na ukun ne shima sai da ya kusa tsinkewa Sannan ta daga da sallama a bakinta


Ya amsa sallamar kuma sai yayi shiru, ta ce “hello” yace “Yasmen ykk” a taqaice tace “lafiya” yace “baki gane mai magana ba ko” tace “ya za’ayi nan gane” yace “Abdulhakeem ne” ta maimaita sunan tace “ban gane ba gaskiya” yace “abokin kamal da mukazo tare” tace “ohhhh Allah Sarki Ina wuni” yace “lafiya lau, ya kwana biyu” tace “Alhmdulillah, ya gida” ya amsa da “lafiya lau” 


Nan suka gaisa sosai kafin suyi sallama, yace mata “kiyi saving number na, idan an ban dama kuma zan cigaba da kira muna gaisawa” tace “Bakomai” sukayi sallama 



__________________________________



Abba ya gayawa Umma yadda yayi da sufyan din taji dadi, ta dade tana son taga yaron nata yayi aure, tace “yarinya mai kirki kuwa Mallam” Abba yace “sai na samu lokaci gobe ko zuwa jibi sai naje nayi magana da baban nata” Umma tace “Allah ya tabbatar da Alkhairi” Abba ya amsa da Ameen



Sufyan dai ya kasa samun sukuni, Addu’a kawai yake Allah ya kawo mafita, idan auren nata Alkhairi ne Allah ya tabbatar 




**********************



Maryam ta dawo daga makaranta, Napep ta ajiyeta a gefen titi, tazo tsallakawa ba ta Lura da motar da ke tafe ba tazo zata tsallaka, Saura kadan motar ta buge ta, Allah yasa motar ba gudu take sosaii ba, matuqin motar yaja burki, ita kuma nan jakar hannunta ta fadi ta rufe fuskarta tana jiran taji motar tabi ta kanta 


Ta tsorata sosaii, matuqin motar ya fito yana mata masifa, ta tashi tana kallonshi, irin kallon rainin nan ya kusa bugeta bama ya mata sannu ba sai masifa, ta juya taga ba mutane a layin nasu, kar ta mishi rashin kunya ya zaneta babu mai kwatarta sai tayi shiru tana kallonshi, wanda aka tuqo a motar ya fito yace “kangiwa wane irin shashanci ne wannan, tunda babu abunda ya sameta da mu kanmu sai kazo mu wuce, kasan meeting ne dani na gaggawa ka tsaya shashanci” sai a lokacin Maryam ta daga kai ta kalleshi, a yanda ta gaanshi yana da tsayi amma bai kai tsayin sufyan ba, yana da qasumba dauke a fuskar shi, yanada haske amma ba fari bane, qasumbar fuskarshi ta qara mishi kyau, yana sanye da Kaftan ne wanda suka yi mishi kyau sosaii, a qalla zai yi 34 years, ta sauke idonta a lokacin da idanunsu suka hadu, tace “kuyi haquri” mutumin da ake kira da Junaid yace “bakomai bakiji ciwo ba ko” tace “eyh” sai ta wuce ta shiga layin da zai sadata da gida


Suka koma mota, tunda ya hada ido da ita yaji wani abu ya darsu a zuciyarshi, yayi murmushi ya cigaba da danna wayarshi


_____________________________



Da dare Abie yake cewa Ammi, sunyi magana da Alhaji Abdullahi akan yaran nan Ana tunanin saka auren nan da wata biyar, Ammi tace “amma kasan yarinyar ba’a San inda take ba, kuma naga kamar hakan bai dameka” yace “wannan bai shafeni ba in ma har lokacin yayi bata dawo ba to fa sai an daura shi, idan ta dawo sai ta tare” Ammi da maganar ta bata haushi, waton bai damu ba shi maganar auren ma yake, ta tashi ta bar mishi dakin ta koma nata 


Tana fita yayi ajiyar zuciya yace “Khadija ina kikaje” ya dafe kanshi ya qara kallon qofar yace “kiyi haquri Lubabatu ni kaina Nafi ki Jin zafin tafiyar yarinyar nan, amma zan nuna mata kuskurenta” yayi ta magana kamar ana jinshi har ya gaji yaje dakin nata ya bata haquri, kar abun ya mata yawa ga rashin yarinya ga bacin rai



_______________________________



Da safe Ammi ta kira Inna suka gaisa tace mata “Ina son Bazla ta shirya taje gidan kakarta tayi mata bayanin komai nasan ita kadai zata mishi magana yaji, batun saka ranar auren suke” Inna tace “tunda yanason auren nan ku bari ayi mana” Ammi tace “Inna tunda har t iya saka qafa ta bar gidan nan ai kinsan tabbas bata so, yarinyar da ko menene baban nata yakeso tana mishi, tunda yanzu ta nuna bataso ai sai ayi mata uzuri” Inna tace “to zan turata anjima, Allah yasa a dace” Ammi ta amsa da Ameen



_________________________________



Junaid ya shirya wuraren qarfe 2:30 ya saka drivern shi ya kaishi unguwar da suka bi jiya suka tashi buge yarinyar nan, ya dauke shi sukaje, suka tsaya daidai layin da ta shiga, ya rasa to ta ina zai fara nemanta, yana wannan tunanin kamar an jefota daga sama sai gata ta sauko Napep ta dawo makaranta kuma, tazo ta wuce don bata ma lura da su ba, ya fito daga motar yabi bayanta yaga gidan da ta shiga


____________________________

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol