Free chapter · Read without an account

Chapter 4

by Na'ima sulaiman Sarauta · MUTALLAB

Ƙarewa office ɗin kallo ya yi yana buɗe idanunsa akan Fiyya wacce ta ɗan ja da baya tana ɗauke kanta gefe. "Ya Allah i really missed her, Safiyya A. Marafa" ya furta yana kallon makaken photon Fiyya dake cikin office ɗin kafin ya ƙarasa ciki murya a hankali ya ce 


"Wa kike tunanin zai zo banda mijinki Fiyya? You're enjoying teasing me" sai a lokacin ta sauke ajjiyar zuciya a ɓoye tare da ɗan yin murmushi mai kyau wanda ya saka shi lumshe idanunsa ya buɗe "Like this.... I missed you completely Fiyya ba shiri na dawo gida fa"


"Ina yini ya hanya?" Ashraf na kallon files ɗin gabanta ya ce "Allahamdulilah. Ya naki aikin Manager?" Ta ce "Lafiya, me ka zo yi a kamfanin ko kana da business damu ne?"


"Eh, babban business ma" tana kallon system ba yabo babu fallasa ta ce "Ohh" kallon ta ya dinga yi yadda take operating system ɗin cike da nutsuwa fuskarta a kame ba wargi hakan bai hana kyan fuskarta bayyana ba ya ja numfashi ya sauke yana jin wani abu sosai na fuskarsa a kan Fiyya ya kalli agogon hannunsa ya ce "Ko gida ban je ba, ina son na samu nutsuwa da kallon fuskarki dear" kamar baza ta ce komai ba sai kuma ta ce "Ok" mamakin halinta na ko ina kula yana damunsa cikin damuwa yana sassauta murya ya ce "Fiyya" ta ɗago ta kalle shi sai kuma ta zame idanunta.


"Na kasa fahimtar me kike nufi dani Fiyya anya kina so na kamar yadda nima nake son ki? I told you na dawo saboda ke amma ki ce mini wani ok? To hell with the ok ɗin na tsani irin wannan ɗabi'un naki, da na yi miki uzurin rashin sabo ne amma for good 5years muna abu ɗaya dake? Idan customers ne kya musu fara'a ki yi welcoming nasu, amma ni da zan zama mijinki kwana kwana nan kike ma haka, ko wanne gardi ya zo office naki kin zama wata kamar jerry abar kallon kowa" ya girgiza kai cikin damuwa da ƙunci yana zare gilas ɗin idanunsa tare da buga table ɗin gabanta ya ce 


"A cikin abu biyu dole ne a yi guda"


Kallon Ashraf kawai take ta tabbatar yana da anger issues tama rasa me za ta ce masa don takaici ya zo har office ɗin ta kuma yana yi mata hayaniya, yana ƙoƙarin tara mata jama'a. Ko motsi ba ta yi ba, tana juya kujerar da take kai a hankali idanunta zube a kansa. "Ina ji Ashraf" bata taɓa kiran sunansa ba sai yau hakan ya saka ya kalleta da sauri ransa ya ƙara ɓaci.


"Aure ko aiki, ya zama dole ki zaɓi guda ɗaya a ciki"


"Ok" ta sake cewa tana miƙewa tsaye tare da ɗaukar jakarta da wayarta da makullin mota ta zaga a hankali zata shige shi ya yi saurin saka hannu ya riƙo nata hannun cikin sauri ta kalle shi tare da jefa masa wata iriyar harara sakinta ya yi ya matsa dab da ita yana sauke mata hucin numfashin ɓacin ransa dake fitowa tun daga ƙasan zuciyarsa.


"Ki bani amsar abin da na buƙata kafin ki fita, aikin ki ko aure"


Ta taune leɓenta tana ware masa manyan idanunta sai kuma ta kalli wayarta tare da buɗewa ta shiga wajan photos pictures ɗinsa ta nemo wanda ya yi kyau sosai ya saka ƙananun kaya lokacin bashi da lafiya ta je duba shi ya fito harabar gidan tana murmushi ta ce "My patient, bari na ɗauki photo as evidence karka mutu bani photon nunawa yarana masoyin da ya tafi ya bar Fiyya" a lokacin juyawa ya yi ya kalleta daga kwancan da yake ya wurga mata harara sai kuma ya miƙe tsaye yana nufar inda take ta yi saurin yin baya tana masa wani irin murmushi ya tsaya yana kallon ta sai kuma ya ce 


"To make you clear, ba ki da wasu yara sai na Ashraf, ba ki da wani miji sai Ashraf ba wanda za ki yi wa takaba sai Ashraf.... Ashraf na Fiyya ne Fiyya kuma ta Ashraf ce in sha Allah" murmushi kawai ta yi bata ce komai ba ta ɗauke shi photon yana langwaɓe kai gefe.


Fiyya ta shafa screen ɗin wayarta tana kallon photon kamar yanzu ta ɗauka cikin muryar mara hayaniya idan tasu ta ce "Ya ce wai na zaɓa aiki ko shi, kar ya buƙaci jin amsar daga bakin Fiyya" fisge wayar ya yi "Dole ki bani amsa yanzu ba sai anjima ba" ta gyara tsaiwa tana fuskantar shi da kyau a hankali ta matsa dab da shi ta ce "Allah Ya baka wacce ta fi Fiyya" Ashraf ya yi sak can ya ce "Me kike nufi?"


"Ina nufin na haƙura da auren, na zaɓi aikin" tana kaiwa nan ta fisge wayarta cikin sauri ta yi waje ya bita da kallo zuciyarsa na ta fasa. Tana fita ta kalli security ta ce "Idan ya fito a rufe mini office" waje ta yi ko Elevator bata tsaya shiga ba ta sakko ta bene dake a wajan 5 floor office ɗin nata yake. Sai gaisheta ake yi amma ba wanda ta saurara idanunta har dishi-dishi yake saboda ɓacin rai.


Misalin 1:43 dare ya nutsa ana samawa zuciya nutsuwa ya yinda kowa yake bacci a lokacin ne safiyarsa ta waye. Ya tsaya a ƙofar gidan yana kallon gate sosai ya jima a wajan kafin ya juya ya kalli Goge da Darma cikin hanzari Goje ya shiga buga gate ɗin gidan kamar zai cire shi, sun jima kafin daga bakin ƙofar suji an ce "Waye?" "Buɗe" Goje ya ce yana zare wuƙa tare da matsawa jikin ƙofar mai gadin a ruɗe yake sosai ya ce "Kamarya na buɗe a wannan zamanin da muke cikin insecurity na sani ma ko ƴan fashi ne?" 


"Sune" Darma ya ce yana yin muzurai shi kaɗai ne a cikin su yake a buge shi Moh abin da Mangal ya bashi har yanzu bai gama sakin shi ba, shi ya sa ba komai yake ganewa ba. "Wallahi ba zan buɗe ba, babu mamaki kun ji Alhaji Wada ya dawo gari shine za ku yi masa fashi"


"Ko ka buɗe gidan nan na rantse da Ɗan Amina na shigo sai na yi maka ɓalli-ɓalli" ai kowa mai gadin ya ce "Ka yi mini ɗari-ɗari ma amma babu abin da zai saka na buɗe daman ƙasa babu lafiya ga yaron can daya dawo abin tsoro ana ta surutu a unguwa ya kashe matarsa kuma ya shigo cikin al'umma zai lalata jama'a..." Kafin ya ƙarasa faɗa Moh ya saka ƙafa ya daki ƙaramar ƙofar nan take ta ɓalle ya faɗa cikin gidan, da sauri mai gadi ya ja baya ba wani sanin Moh ya yi ba kawai zancen ya dawo kunnensa da labarin kisan daya game ko'ina a shekaru uku da suka shige. Goje ya daƙo mai gadin ya falle shi ya faɗi "Kai har ana cewa ka buɗe ƙofa kana ƙi?"


"Goje"


"Sai godiya" Moh ya numfasa yana durƙosawa daidai fuskar mai gadin "Me ya ce a yi masa?" "Sai godiya ɗari-ɗari ya ce yana buƙatar tsini" ihu mai gadin ya saka ya ce "Wallahi tallahi ƙarya nake"


"Zaɓi ɗaya" cewar Moh yana fito da askira ya ajjiye gefe ya sake fito da wata wuƙar ya ajjiye ya jima a duƙe kamar mai tunani sai ya ce "Ko ɓalli-ɓalli ko ƴan uku ko na jaki"


"Ɓalli-ɓalli" mai gadin ya ce da sauri ya ɗauka wani abun za a ɓalle da idanu ya kalli Goje da Darma suka riƙe mai gadin tare da juya shi yana ihu da komai Moh ya ɗauki ankarar ya dinga tsaga masa a baya jini na fitowa shi kansa zuciyarsa ce kawai ke ingiza shi ya yi hakan kuma daidai gani yake yanzu daidai yake da tsarar kowanne mutum haka ƙwaƙwalwarsa ke karantar da zuciyarsa. Tun mai gadin na kuka har ya yi laƙwas sai nishi yake fitarwa, suka yar da shi a wajan cike da tafiyar taƙama yana taku ɗaiɗai jikinsa na buɗewa cikakken namiji a tsaye matashi dake kan lokacinsa. Cikin sa'a ya samu ƙofar shiga babban parlon gidan a buɗe ya kutsa kai yana kallon tangamemen parlon ya dinga kallon komai, iya haɗuwa ya haɗu sai ƙarar a.c ya lumshe idanunsa ya buɗe ya jima kafin ya ƙara shiga cikin ɗaya parlon su Goje na biye dashi.

Alhaji Wada na zaune shi da iyalansa basu da jima da sauka daga ƙasar ba. Yana saman kujera matarsa na gefe sai yaransa guda biyu mace da namiji kayan ciye-ciye fal a gabansu bama su damu da cin abincin ba sai ice-cream dake hannunsu suna sha. Da sauri Alhaji Wada ya miƙe tsaye yana kallon matasan da suka shigo ya juya ya kalli matarsa da yaran ya ce "Su waye ku? Me kuka zo yi mini a gidana a irin wannan lokacin?"


Moh bai ce komai ya zaga ya zauna saman kujera ya jingina ya ɗora ƙafarsa a saman table ɗin yana kallon abincin Goje da Darma na tsaye sai muzurai suke yi cikin sauri Alhaji Wada ya ɗauki wayarsa zai kira ƴan'sanda "Ba wani abu da zai bani tsoro, yadda aka fara dakai dole a ƙare da kai Alhaji Wada"


"Waye kai? Me aka fara dani" fuskar Moh a rufe ya saka hannu ya zame abin da ya rufe fuskar da shi "Idan maye ya ci ya manta ai uwa ba zata manta ba, idan kare na yawo zabo na yawo za a haɗe ya ranar" ƙirjin Alhaji Wada ya buga ya yi baya da sauri ya ce "Kai ne? Me na yi maka"


"Ba labari na zo baka ba, ba fansa na zo ɗauka ba na zo ka ganni kasan ina raye ina numfashi ka san cewa na cika ɗan babata Ammo Mai dawa nake sarki mai jeji, na gode Ɗan Amina da ka zama kai ne silar da ya saka na gano wasu abubuwan" Alhaji Wada jikinsa rawa kawai yake ya ce "Don Allah kar ka yi mini komai kar ka taɓa yarana basu san abin da ya faru ba" "Idan zan yi mana jira, idan na yi sai ta ɓaci. Ina je store ɗin gidan nan?" Da hannu Alhaji Wada ya nuna masa hanya ita kam matar ta kasa motsi saboda tashin hankali bata taɓa ganin fuska mai ban tsoro irin wannan ba, yaran sai takurewa waje guda suke yi ko haɗa idanu da Moh basa son yi" ganin har lokacin Moh bai tashi ba ya saka Alhaji Wada cewa "kar ka ce zaka mini komai" shi dai Moh kallon Alhaji Wada kawai yake zuciyarsa na tuna masa irin zaluncin da ya yi masa da hannu ya nuna masa yaran cikin kakkausar murya ya ce "Ko dan waɗan nan, ba zan so su zama abin da na zama ba" ya juya ya kalli Goje ya yi masa fito da inkiya suka nufi store ɗin kayan abinci kamar hauka haka suka dinga fito da buhun shinkafa katon na taliya da maroni su magi da galan na mai suka jide waje guda. 


Yana bada faɗi ya miƙe tsaye ya nuna kayan abincin "Ka raba a masallaci ka haɗawa mutane da haushin kare guda goma-goma, ka kai har gidanmu" Ya juya zai fita sai ya tsaya ya saka hannu a aljihu ya zaro kunama ƙatuwa baƙa ƙirin da ita ta ɗaga ƙari sama ya damƙi hannun Alhaji Wada ba tare da yaran sun gani ba, ya cilla kunamar ciki ya damƙe hannun. Azaɓa ta saka Alhaji Wada zubar da hawaye zufa na yanko masa sosai da sosai a hankali cikin ƙasa da murya ya ce "Ka kira cinnaku ƴan'sanda kenan ka faɗa musu an yi maka fashi, idan sun tambayi waye karka yadda ka ce Mai dawa, ka ce SCORPIO" yana kaiwa nan ya kashe kunamar ya soke jikin bango da sauri ya fice kamar walƙiya, su Goje suka mara masa baya.


Fiyya na durƙushe a gabansa kanta a ƙasa ji take dama tana da ƙarfin yin kuka a yanzu, ta kasa fahimtar sai yaushe ne komai zai daidaita ya tafi daidai? Tana haɗiye abubuwa da dama ba tare da kowa ya sani ba bata bari a san rauninta amma yau ita aka saka gaba akan abin da sam bai kai ya kawo ba? Ita zaiwa haka?.


"Safiyyerh A. Marafa"


Ya kira sunanta a karo na uku sai a lokacin ta ɗago kai ta kalli Daddy dake zaune saman kujera hannunsa riƙe da carɓi fuska ba wasa ya lura sai ya dage sosai akan Safiyyerh. 


"Ya kuka yi da Ashraf me neman auren ki?" A hankali ta ce "Ba komai Daddy"


"Ba komai Daddy, na gaji da jin wannan daga bakin ki Safiyyerh ke kina nuna mini ke mai wayo ce kuma kin girma kin isa ki yi handling dukkan wasu matsalolinki ko? Ke jaruma mai experience akan aikinta Managern FS WORLD INVESTMENT COMPANY? na yarda kina da wayo tunda na kasa sanin damuwarki tsayin shekaru na yarda kina da experience hakan ya sa cikin ƙaramin lokaci kika zama Manager but amma.." ya yi shiru yana kallon ta sai kuma ya ce 


"Safiyyerh kina buƙatar aure shine cika da ƙimar kowacce mace, me kike buƙata a rayuwa da ba a yi miki ba, wanne gata ban yi miki ba da kika ce kin fasa auren Ashraf?"


"Daddy ya ce na zaɓi aiki ko aure"


"Sai kika zaɓi me?"


"Aiki" Daddy ya dinga kallon ƴar tasa shi ya rasa gane wani mataki zai ɗauka a kanta. 


"Ba za ki yi auren ba kenan, baƙin cikin jikoki kike mimi Maama? Sai na faɗi na mutu za ki yi auren me ya sa kika kasance stubborn ne, ko don kinga ina biye miki?" Fashewa ta yi da kuka sosai ita kanta bata san kukan ya ƙwace ba, kalmar mutuwar da Daddy ya faɗa ya firgitar da ita sosai idan Daddy ya mutu ta shiga uku.


"Daddy gasu Yaya J, su Marafa, su Captain Daddy me ya sa sai ni za a yi aure ne? Ni ce ƙarama fa nawa nake gabaɗaya ko aure za ka mini ka ƙara mini lokaci Ashraf zafin zuciya ne dashi baya fahimta ta a kodayaushe"


"Maama kuma taurin kai, ji da kai while zafin zuciya, Safiyyerh dole za ki yi aure" runtse idanunta sosai kenan duk abin da take ya tashi a banza? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un me ya sa Ashraf zai yi mata haka me ya sa zai haɗata da mahaifinta? Ta kasa cigaba da kukan abu ya tsaya mata a wuya sosai. Har Daddy ya je bakin ƙofar shiga sashinsa ya tsaya ba tare daya juya ba ya ce 


"Cikin satin nan zan ɗaura miki aure da Ashraf in sha Allah"


Dum! Haka ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi har tsakiyar kanta kuma ta ji hakan, ta runtse idanunta sosai take ƙoƙarin jan numfashi ta kasa ta yi saurin riƙe wuyanta da take jin kamar an soka mata abu a ciki saboda zafin da yake. Cikin sauri J ya ƙarasu parlon daman ya shigo da nufin yiwa Daddy sai da safe ya nufeta yana riƙo hannunta ya ce "Manager lafiya? Mene?" Kafin ta bashi amsa Marafa shima ya shigo ya nufe ta, haka Dr Hash gabaɗaya suka zagaye ta suna tambayarta lafiya kasancewar suna mugun son ƙanwar tasu kamar rai. Hannun J ta riƙe gam tana nishi hawaye na zubu mata sosai ta kasa magana hakan ya saka Dr Hash miƙewa ya ɗakko ruwa mai sanyi ya yiwa J alamar ya ɗago ta, a hankali ya dinga bata ruwan tana sha ya zame rubar ruwan.


"Junaid kwantar da ita saman kujera ko ka kai ta ɗaki" 


"Bari ta ƙara jin dama dama a dai ƙaro gudun acn ta fi shaƙar iska da kyau" cikin sauri Marafa ya nufi wajan ƙaro a.c a hankali suka ji an ce 


"Kar ka ƙaro" ya juya ya kalli Captain dake zaune kan kujera abin shi yana dannawa, yana zaune Daddy ya kira Fiyya duk maganganun da sukai yana zaune har halin data shiga. "Captain daman kana ciki kana kallo Maama ba lafiya?"


"Ni na ɗora mata?"


"Amma baka ce mata sannu ba, she's our little sis our favourite" kallon da Captain ya yi wa Marafa ya saka dole ya yi shiru dukkan su ba wanda ya iya cewa Captain komai domin sun san hali basa shiri da Fiyya bai shiga sabgarta ba, duk abin da ya shafe ta babu ruwansa da shi. Ko magana bai fiya yi ba ana ganinsa kowa ke nutsuwa domin shine babba a cikin su Fiyya kuma Auta. Fiyya ta yi lamo jikin J tana sauke numfashi Dr Hash na riƙe da hannunta jin jikinta ya fara ɗaukan zafi sosai. Da ƙyar ta lallaɓa J na riƙe da ita suka haura sama duka sauran mazan suka bi bayansu banda Captain da yake harkar gabansa.


Wajejen 2:30 Daddy ya sauke numfashi yana kallon yadda take sauke numfashi a hankali ko a baccin bata da walwala ya juya ya kalli Captain dake tsaye hannunsa zube cikin aljihu "Aliyu me na ragi Maama da shi a duniya dana kasa fahimtar meke damunta? Ita ɗaya ce mace ƴata laifi ne don na so ta yi aure?"


Captain dai ya yi shiru idanunsa a saman fuskar Fiyya Daddy ya miƙa hannu ya taɓa goshinta ya ji har lokacin da zafi daman ya fi ƙarfin awa guda zaune a wajan, yana cikin Captain ya buɗe ƙofa ya shigo da tunanin babu kowa cikin ganin Daddy ya saka dole ya tsaya. "Maama ki yi mini alfama ki yi auren nan, shi ne abin da za ki yi ki faranta rai na" ya gyara mata hannunta daya lanƙwashe kana ya miƙe tsaye zai fita 


"Aliyu mu je"


"After you daddy" 


Daddy ya jinjina kai ya fita yana janyo ƙofar. A hankali Captain ya nemi waje ya zauna a gefen gadon ya zuba mata idanu sosai, a nutse a kamo hannunta ya riƙe cikin nasa jin jikinta zafi sosai ya saka ya saki hannun ya ɗakko towel da ruwa ya dinga goga mata a goshi har lokacin yana riƙe da hannunta har sai da zafin ya ragu, bai tashi ba yana zaune aka fara kiran sallar farko cikin sauri saki hannunta ya miƙe tsaye yana haɗe fuska J ne ya shigo a hankali ya bi Captain da idanu har ya fice daga cikin bedroom ɗin na Fiyya.


*****

Cikin gidan ya faɗo babu ko sallama Inna Binta na zaune har za ta yi magana ganinsa tsaye ya saka ta yi shiru da bakinta. Yau ranta fari tas an yi musu rabon abinci Malam ya basu ya ɓoye sauran. Ɗakin Ammo ya nufa yana ɗaga labulan ɗakin ya ganta zaune tana ɗaura kuɓewa tun kan ya shigo jikinta ya bata yana hanya saboda gabanta daya tsananta faɗuwa.


Ya shiga ɗakin ya zauna ita dai bata kalle shi ba, sai kallon ta ya ke yi can ƙasa da murya kamar ba shi ba ya ce "Ina yini Ammo?"


Miƙewa ta yi maimakon ta amsa masa, ya cije bakinsa yana rufe idanu kwanon abinci ya jenyo ya buɗe yaga taliya ce jallof ta ji albasa nan da nan yawunsa ya tsinke ya tuna rabon shi da abinci har ya manta.


"Alhaji Wada ya bawa Malam, idan da zuciya ai ba za ka ci abincin daya bamu ba" cak ya tsaya yana kallon abincin kamar zai tashi sai kuma ya nutsa hannunsa ciki ya ɗebo lauma zai kai bakinsa cikin sauri aka ce "Allah Ya isa ban baka ba ida ka ci abincin nan" Malam ya kalli Ammo ya ce 


"Bana ce kar ki yarda ya shigo gidan nan ba? Wato har abinci kika bashi ko?" Ta girgiza kai ta ce "Ɗauka ya yi"


Jiki a sanyaye Moh ya miƙe ya fice daga cikin ɗakin yana saka ƙafa ya banko ƙofar da ƙarfin gaske yana zuwa daidai inda Inna Binta ke gyara shinkafa ya saka ƙafa ya yi fatali da farantin shinkafar ta tarwatse ya yi waje kamar zai tashi sama. Ta dafe ƙirji tana rafka salati "Ƴar gwamnati ce fa Allah ya isa wallahi".


Goje ya dubu Mangal ya ce "Me ka bashi wai? Yake wannan sambatu da mimmiƙar haka?"


"Sha fara kaga aljan ce, ita za ta yi aiki a jikinsa, daga sama aka bani ita" Goje ya juya ya kalli Mai dawa ya sauke numfashi cikin damuwa ya ce "Dole sai ka koya masa shan waɗannan abubuwan ne?"


"A'a ina zaune ya zo mini kamar an koro shi yana huci ya ce na bashi irin abin da na bashi kwanaki saboda damuwar zuciyarsa ta kau ya manta da komai ni kuma na bashi sha fara kaga aljan"


"To gashi nan yana ganin aljanin ai" da ƙyar ya samu ya yi bacci a wajan. Bayan ya farka Mangal ya bashi abinci ya girgiza kai "Mai dawa idan kuɗi kake so ina da hanyar da zan yi maka ka dinga samun kuɗi sosai cikin sauƙi har ma ka taimaki wasu" tunda ya farka sai lokacin ya ɗaga kai ya kalli Mangal alamar ina ne? "Bangar siyasa kasan yanzu muna gab da fara shiga sabgogin siyasa uban gidana cikakken ɗan siyasa ne, shima yana da uban gida kuɗi zaka samu sosai a sabgar nan ina faɗa maka"


"Kai ni" kawai ya iya cewa yana miƙewa tsaye. 


Suna zaune a wani haɗaɗɗan parlo inda suke karɓe wa su yi meeting na sirri. Gabaɗaya suka kalli MUTALLAB TAHHB SCORPIO ɗaya daga cikin su ne ya ce.


"Mene sunanka"


"Mai dawa"


"Kai mafarauci ne?" Ba tare daya kalli mutumin ba ya ce "Darr" babban mutumin ya jinjina kai sosai ya zaro wani photo a aljihu ya ce "Kafin mu yi maka bayanin su waye mu, me muke buƙata da kai, fara ganin wannan ka saka dai a ranka mu ƴan siyasa ne"


Shi dai Mai dawa bai ce komai ba, aka ajjiye masa photon a gabansa "Ɗauki ka buɗe ka gani mana" 


Wani daga cikin mutanen ya ce "Manager ce a FS WORLD INVESTMENT COMPANY aiki za ka yi mana a kanta kafin mu faɗa maka aikin mene ka fara ɗaukan photon kaga wacece" a sanyaye ya ɗauki photon kafin ya kai idanunsa kai....




***

For more information 

WhatsApp only

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol