Free chapter · Read without an account
Thriller
Mutane ne Uku a tsaye biyu maza sai mace ɗaya sanye suke da Uniform ɗin ƴan sanda. Daga gefe Babbar Mace ce wadda zata iya kaiwa kimanin shakaru saba'in sai wata budurwa mai tsananin kama da ita idonta yayi jaa sosai da alamun kuka take yi, "Yanzu sai da kika aikata abinda kike furtawa da ikirari Nu'aymah?" Mama ta faɗa tana share hawayenta. Matashiyar mace ce Ɗurkushe take a ƙasa, kuka take yi har shiɗewa tana yi gawa ce kwance a gaban ta. Sa hannu tayi tana yaye mayafin da aka rufe gawar wata gigitacciyar ƙara ta sake saka tana matsawa baya tare da cewa
"No, It can't believe" da karfi. "Mama jiya fa muka rabu baya don tafiyar nan ni na takura sa yanzu a dawo da shi ya mutu, ku ce min suma yayi ba mutuwa ba" ta faɗa tana wani irin kuka
Ɗaya daga cikin mutanen dake tsaye ne ya fara magana yana cewa
"Madam You Are Under Arrest" ya faɗa yana ciro ankwa daga aljihun sa yana nuna mata
Duk juyowa suka yi suna kallon wanda yayi magana sai kuma suka waiwaya ganin side ɗin da take yake kallo, ɗimaucewa, firgici, tashin hankali mara misaltuwa ta shiga da ƙyar ta Iya buɗe bakin ta tana cewa "Arrest? For What?" ta faɗa jikin ta na rawa. Gyara tsaiwar sa yayi sai kuma yace
"For Murder of your HUSBAND"
a firgice ta kalle shi tana nuna shi tare da cewa "Innalillahi wainnaillaihir-rajiun Wallahi bani bace, BAN AIKATA BA, How can I kill a Husband of mine?"
"Madam iya binciken da muka yi daga lokacin da muka samu gawar sa zuwa yanzu ya nuna mana ke kika yi kisan nan, Mahaifiyar sa tace kina cewa sai kin kashe shi"
A zabure ta kalli Mamma tana mata wani irin kallo sai kuma ta hau cewa "Mamma how can you say that, kin san ina matuƙar Ƙaunar mijina ba zan iya kashe shi ba, ba ma shi ba ba zan iya aikata kisa ba
"Shut up, get up now you're westing our time Ma" macen ta faɗa tana Matsowa kusa da ita da sauri Nu'aymah ta miƙe tana yin baya tare da girgiza kanta tana furta
"ki saka baki Mama kar su tafi da ni, wallahi BAN AIKATA BA"...... Sai ki suka yi yiiif ta faɗu kasa sumammiya
_Shin ita ta AIKATA?
_Zasu ta fi da ita ko kuwa?
Duka amsoshin nan dama wasu da dama suna cikin littafin *🔥💦 BAN AIKATA BA 🔥 💦* littafin dake cike da dunbin al'ajabi, zalunci, cin amana, da kuma ƙaddara. Ku kasance da alƙalamin Fateyzahraah👯 On 10th October Dan ayi tafiyar nan da ku💃 kar ku bari a baku labari 🤩💥