Free chapter · Read without an account
30
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*ALLON ƘADDARA*_
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*PAGE 30*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
Gudu sosai nayi cikin mintuna kaɗan na isa Gida duk da kuwa akwai ƴar'tazara tskaninmu da Gidan Hamma Jabeer. Kai tsaye sashenmu na nufa na shige ɗakina, ina jin wayata na ƙara amma na share don bana cikin yanayin da zan amsa waya. Hijabin jikina na cire na aje saman gado nima na kwanta saman gadon zuciyata cike da tunanuka. 'Me Matar nan take nufi ne da cewa duk wanda muka taso gaba sai ya mutu? Abin a buɗe yake itace sanadin rashin lafiyar ɗanta har ya zama ajalinsa amma sabo da son zuciya irin nata ta tattara laifi ta ɗora mana ni da Ammy . Aunty Kalisat kuwa kowa ya sani tun samun cikinta take fama da larura har Allah ya ɗauki ranta bayan ta haihu, to me zai sa a zargemu don kawai na zauna a gidansu? Me yasa zasu ɗauki maganar da Aunty Kalisat ta faɗa cikin zafin ciwo susa a ransu har su riƙa ƙoƙarin ƙuntata min ta dalilinsa?'.
"Wannan wace iriyar lukutar masifa ce? Gaba ɗaya mutane basa tsoron Allah, to a wannan karon kam na shirya yaƙi da duk wanda yace zai takura rayuwata da ta Mahaifiyata ko waye kuwa haba!" Na faɗa da ƙarfi bayan na gama yiwa kaina waɗancan tambayoyin a zuciyata.
Wani kiranne ya ƙara shigomin min a fusace na ɗauka don na san ba mai min wannan nacin kiran sai Alhaji Bilal don haka ban ko duba ba na fara sauke masa masifa, na bal-baleshi da faɗa "akan me zaka takura min da kira ne? Tun da ka kira ban ɗauka ba ka kuma ba sai ka ƙyale ni na sha iska ba, haba don Allah ka bi ka takura min ka barni naji da halin da nake ciki, an bi an sako rayuwata a gaba kowa ya buɗe baki Hanan!Hanan!! Hanan!!! Na rasa mai na tsare wa mutane?!" Na ƙara sa cikin ƙaryewar murya wani kasashshen kuka na kufce min.
Tun da ta fara masifar ya lumshe ido yana sauraron ta zuciyarsa na karyewa tausayinta na kama zuciyarsa, sai da tayi kuka sosai yana sauraron ta zuciyarsa na bugawa da wani irin ƙarfi yanayinsa na ƙara ta'azzara da abinda shi kaɗai ya barwa kansa sani. Sai da tayi shiru don kanta kafin cikin silent voice ɗinsa yace "Sofiyyah! Are you Ok? Kin je Gida lafiya ba abinda ya sameki ko?". Shiru nayi jin muryar Hamma Jabeer bayan ba kiransa nayi tsanmani ba, ciro wayar nayi daga kunnena na duba. Number ɗinsa ne dai da ban yi saving ba amma tsaf na gane su don ƙwaƙwalwata ta riƙe su ko don sun kasance special ne oho.
Jin nayi shiru naƙi cewa komai ya saka shi ƙara faɗin "Sofiyyah say something mana, are you Ok?". Kuka kawai na saka masa sosai hada shesh-sheka. "Ya Allah! Baky tausayina ko? Kinga ina cikin damuwa sosai kuma bana da mai rarrashi na Auntynki ta tafi ta barni kuma ta bani amanar kulawa da ke da Babaynki gashi kuma kina ta kuka Babaynki ma haka, ki taimake ni ki dai na kukan kinji sai na kawo maki ƴarki itama ki rarrasheta, ko ba kya so?".
Da sauri nace "A'a ina son ka kawo min ita don ba ƙara zuwa Gidanka zanyi ba!" Na faɗa kamar zan sa wani kukan. Kansa ya dafe da yaji yana sara masa, a hankali yace "Ok zan kawo maki ita amma sai kin min alƙawarin ba zaki ƙara kuka ba, kuma zakici abinci kisaha magani ko kuma in zo innmaki allura". Wani lalataccen kuka na ƙara saka masa ina faɗar "Allah ni dai bana son allura baza ayi min ba".
"Rigimarki tayi yawa Sofiyyah shikenan to ki tabbatar kin sha magani, zan gane kuma idan baki sha ba". Ya faɗa cikin sanyin murya.
"Zan sha to". Na faɗa kamar zan yi kuka. "Good girl" ya faɗa yana ƙoƙarin aje wayar na kira sunansa. "Hammah!". "Um menene?" Ya tambaya yana lumshe ido jin yanda ta kira sunan na ratsa masa ƙwaƙwalwa. "Hammah kai ma kaci abinci kasha magani to". Na faɗa ina jin tausyinsa na kamani. Idanunsa ya lumshe wani abu mai kama da samun relief na ratsa shi, a ƙasan maƙoshinsa ya ce "Ai bana da mai bani abinci yanzu!" Ya faɗa da kalar tausayi wanda hakan ya shigeni fiye da yanda ya turo saƙon don matsanancin tausayinsa ne ya kamani da na tuna yanda Aunty Kalisat take tattalinsa kamar gold.
Tunawa da roƙon da ta min da amanar da ta bani yasa nace "To kazo sai na baka abincin".
"Are you sure zaki bani?".
"Yes amma kazo min da Little".
"Ok" ya faɗa kafin ya aje wayar yana samun natsuwar jin ba abinda ya sameta, sannan kuma sosai ya samu sauƙin damuwarsa bayan yin magana da ita. Tashi yayi ya fita daga ɗakin dama kawai kasa natsuwa yayi da yanda yaga ta tafi shi yasa ya shiga ciki ya kirata sai kuma aka yi Sa'a ya taka sawun ɓarawo ashe wani ya dameta da kira shima ya kira a lokacin aka sauke masa masifar da aka tanadar wa wani. Wani guntun murmushi ne yaso kufce masa a hankali yace "Fitinanniya kawai, dole sai tayi halin". Da haka ya koma wurin ƴan'uwansa.
A ɓangarena nima na daɗe riƙe da wayar a hannuna ina juyata. Gaba ɗaya Hamma Jabeer ya sauya min a kwanakinnan kamar ba shi ba, ya zama mai sanyi da tausayawa a gareni. Tashi nayi na shiga kiching na haɗa complex na sha na sha maganina da ƙyar kamar yanda nayi masa alƙawari kafin na kwanta ina ta faman saƙe-saƙe har barci ya ɗaukeni ban sani ba.
***** Da dare bayan na tashi a barcin da na kwanta wanka nayi na gabatar da Sallar magrib na fito don duba ɗakin Ammy ko ta dawo, motsin da naji a kiching ne yasa na nufi can. Ita ɗin ce kuwa na samu tana haɗawa Baba Malam abinci kasancewar yau ita ke da turaka. "Sannu da aiki Ammy ashe kin dawo". Na faɗa ina ƙarasawa kusa da ita.
"Yauwa Hanan na dawo na samu kina barci sanin da nayi bakya jin daɗi ne yasa ban tasheki ba, yaya jikin naki". Ammy ta tambaya cike da tsananin kulawa da soyayyar da take min.
"Jiki Alhamdulillah Ammy na warke ai". Na bata amsa ina amsar albasar da ta ɗauko zata yanka na shiga yankawa. "Masha Allah haka ake so, abinda nake faɗa maki kullum shi zan mai-maita Hanan, ki rage wannan zafin zuciyar taki ke ɗiya mace ce gidan wani zakije, sannan ki daina saka damuwar abinda mutane zasu faɗa a kanmu kina barin shi a zuciyarki yana damunki har ki riƙa wasa da lafiyarki, ke kaɗai Allah ya bar min a cikin yara biyar da na haifa, sai dai ke ɗin ma ba cikakkiyar lafiya gareki ba, ki taimakeni ki daina bari ɓacin rai na saka ki ƙoƙarin rasa numfashinki wata ran idan akwai wani a kusa dake da zai baki taimakon gaggawa to wata ran ban san a ina hakan zai faru dake ba, bana son rasaki kema Please Habibty ki riƙa ɗaukar abubuwa da sauƙi kinji, in sha Allah komai zai wuce!" Ammy ta ƙara sa maganar cike da rauni.
Sosai jikina yayi sanyi tsananin tausayin Ammyna da ƙaunarta na ƙara ratsa illahirin jikina, ni shaida ce Ammy tana tsananin so da ƙaunata duk da tana yin kawaici da kara amma kowa ya san matsayina a zuciyarta. Duk sanda na kwanta ciwo to ni iya ciwo ne a jikina ita kuma damuwa da fargabar halin da nake ciki kaɗai sun isa hanata sukuni da walwala har sai ta ga na samu lafiya, sau da yawa in bani da lafiya to itama sai Baba Malam ya tsaya ya kula da ita don ko abinci bata iya ci.
Ajiyar zuciya na sauke kafin na aje albasar da na gama yankawa naje na wanke hannuna kafin na matso kusa da ita na riƙe hannunta ina kallonta cike da soyayya nace "In sha Allah ba za ki rasani ba Amma, zamu rayu tare zan haifa maki Jikoki kamar yanda kike burin gani". Murmushi Ammy ta saki tace "Allah ya a nuna min wannan lokacin Hanan zan yi matuƙar farin ciki da ganin lokacin".
"Ameen ya Arrahaman zaki gani in sha Allah". Na faɗa ina murmushi ganin lokaci ɗaya Ammy ta sake tana wal-wala daga jin nace zan haifa mata Jikoki. Maganar Ammy ita ta dawo dani daga tunanin da na tafi. "To ai Habibty kece kin ƙi ba maganar auren mahinmanci kin tsaya tunanin wanda ya riga ya shuɗe, yanzu don Allah miye laifin yaron nan Alhaji Bilal mutumin kirki ne Babanku ma ya shaide shi, amma ban sani ba ko kishiya kike tsoro" Ammy ta faɗa tana tsare ni da ido don ganin reaction ɗina. Ai kuwa take fuskata ta canza daga yanda nake, sai dai nayi matuƙar ƙoƙarin dannewa na ƙir-ƙiro murmushi nace "Ba haka bane Ammy kawai dai manta Ya Nabeel a gareni abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba, maganar Alhaji Bilal kuma ai na amince tunda duk kun amince da shi, kishiya kuma Ammy ni bata gabana bare har ta dame ni" na ƙarasa faɗa ina kallon ƙasa.
Numfashi Ammy ta furzar kafin tace "Ai ba iya amincewarmu ake buƙata ba Hanan duk yanda muke son haɗin idan har ke bakya so baza mu yi maki dole ba".
"Ammy ni ai na rufe babin soyayya a rayuwata kawai zan yi aure ne don inyi bautar Allah ba don soyayya ba". Murmushi Ammy tayi kafin tace "Hanan kenan yau da gobe ai tafi ƙarfin wasa, ni na san wata rana zakiyi soyayya fiye ma da wacce kika yi a baya". Murmushi kawai nayi bance komai ba amma a zuciyata na san hakan ba mai yiwu bane. Da haka muka ƙarasa aikin na fito dasu gaba ɗaya na jere a dining na koma na gyara kiching ɗin tsaf na shiga ɗakina don gabatar da Sallar Isha'i. Bayan nayi sallah na fito don cin abinci sabo da jalop ɗin macaroni da zallar ƙoda Ammy ta dafa dahuwa mai kyau da yaji vegetables da spices sai tashin ƙamshi yake don haka ina yin Sallah na fito don inci.
Kwata-kwata na manta da Hamma Jabeer yace zai zo in bashi abinci sai da na fito kawai na ganshi zaune a palour suna gaisawa shi da Ammy. Turus nayi na kasa ƙarasawa sai da Ammy tace "Ƙara so mana Habibty". A hankali na je kusa da Ammy na zauna ina lafewa a jikinta cikin sanyin murya nace "Sannu da zuwa Hammah ya ƙarin haƙuri?".
Jabeer da tun da ta fito idonsa ya sauka a kanta, ƙasa-ƙasa yake kallo ta yanda ba wanda zai fahimta, ganin yanda ta fito tana yatsuna fuska tana tutturo baki gaba ne ya sa shi tunanin wa kuma ya taɓo ta don yasan halin ne take. A hankali ya furta "Alhamdulillah". Miƙewa Ammy tayi ta nufi sashen Baba Malam dake tsakiyar sashenmu da na Mammah tana cewa "ki tashi ki kawo ma Hammannaku abinci".
"Muje to in baka abincin". Na faɗa ina kallonsa. Idanu ya zuba min yana kallona, a cikin ransa yake magana 'Wai muje in baka abincin, kamar zata ba wani ɗanta abinci'. A zahiri kuwa sai ya miƙe muka nufi dining. Kujera na jawo masa ya zauna ni kuma na shiga serving ɗin sa, sai da na haɗa komai na tura gabansa kafin nima na saka kaɗan na zauna zan fara ci yayi gyaran murya. "Ɗagowa nayi ina masa kallon "Menene kuma?".
"Ba kince zaki bani ba sai kuma ki zauna zaki bawa kanki, wannan kulawar? Haka ake kula da amanar dama?" Ya faɗa yana tsare ni da ido. Gaba ɗaya naji ina ƙoƙarin ruɗewa, ni nama rasa yanda aka yi ya san Aunty Kalisat ta bani amanar kulawa da shi da Little. Kamar ya san mai nake tunani sai ji nayi yace "Ko ba amanata ba Auntynki ta baki ba?".
"Ta bani mana amma ai kayi ƙato da yawa ace na baka abinci a baki sai kace wani Little". Na faɗa ina turo baki gaba. "Shikenan tunda baza ki iya riƙe amanar ba bari in tafi ni, sai an jima" ya faɗa yana ƙoƙarin tashi. Da sauri na miƙe ina riƙo hannunsa nace "To ka zauna zan baka". Zaman kuwa yayi ya buɗe baki na shiga bashi abincin ba yanda na iya. Kaɗan yaci yace ya ƙoshi, fuska na marairaice kamar zanyi kuka. Dole ya ƙara karɓa kafin ya kwace spoon ɗin yace "Tun da kika min ɗura sai na rama.
Abincin ya shiga bani ina karɓa wanda hakan ya tuna min da moment ɗinmu da Ya Nabeel a irin wannan yanayin da yake bani abinci a baki idan yaga na tsaya wasa, ban san sanda wasu hawaye masu zafi suka zubo daga idanuna ba. Baice min komai ba sai hannunsa da yasa ya ɗauke hawayen ya ɗebo abincin ya nufi bakinsa na kauce, mayar wa yayi ya dauko kwalin peak yoghourt ɗina da Ammy ta aje min ya buɗe ya shiga bani. Sai da nasha da yawa kafin ya sauke yace. "Kike ki kwanta ki huta banda kuka banda tunani". Ya faɗa yana nufar hanyar ficewa, har ya kai ƙofa na kira sunansa. Juyowa yayi nace "Baka kawo min Little ba".
"Zan kawo maki ita in sha Allah sai kin ƙara girma". Yana gama faɗa ya fice ba tare da ya bani damar fahimtar abinda yake nufi ba....
Barkanmu da dare, asha hutun weekend lafiya sai Monday in sha Allah zaki sake jina.
Taku Kansa'u Bello (Oum Fatima)