Free chapter · Read without an account

KUSANCI PAGE 9

by Habiba Abubakar imam · KUSANCI BOOK 1



KUSANCI


NA


HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM 

(Mrs Aliyu mayere)



 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


   ............page 9


    Sai dai duk wannan abin, Bakil bai zo Ɗandume ba, duk da ana ta hada hadar baikonsa da Sajeeda 

   Sai dai kuma tuni Haj Aseeya ta canja shawara, a ganinta gara Sajeeda ta ci rabonta sosai kafin auren don haka ta zauna da Sajeeda ta fahimtar da ita ko anyi baikonsu yanzu to zasu ja lokacin da za'ayi bikin saboda su samu su kwashi garar arziki, irin hudubar da Haj Aseeya ta yi mata yasa ta yarda da abinda ta zo mata da shi .

    Bakil ya dade bai je gida ba har akayi baikon shi da sajeeda watanni huɗu kawai aka diba za'a yi bikin.zuwa wannan lokacin kuwa sajeeda jin ta take tamkar zata auri shugaban ƙasa,su Maryam da take kulawa a gidan duk ta daina , ba ta shiga harkar kowa, ta ɗauki uban girman kai ta ɗorawa kanta.

   Ayayinda Haj Aseeya ta zama yar amshin shatar Haj Hadeeza kullum tana manne a dakinta tsabar kwadayi ya yi mata yawa, ta kuma tilasta sajeeda ƙara daraja Haj Hadeeza har turata take tana yi mata shara da ƙananan aikace aikace, tuni izzar Haj Hadeeza ta ƙara hawa tana jinta tamkar itace me arzikin duniya, tana daga kai tana dagawa abu kaɗan ta hau yin gorin ɗan ta ke ci da gida.

  Saura watanni uku bikin, sannan Bakil ya shigo Ɗandume saboda aiki da ya yi masa yawa kasancewar an maida shi office din da ya fi ko wane office hada hada da kuma samun kuɗi saboda iya aikinsa da kuma kokarinsa, Allah ya ba Bakil kai yana da matuƙar kokari duk abinda ya fara sai ya zo ya doke kowa, hakan yasa daga fara aikin nasa ya fi waɗan da suka dade a office din iya aiki, hakan yasa ogansu ya maida shi shine komai ɗin sa domin hatta aikin ogan shi yake masa, Don hska ya rasa lokaci domin ko ba ranar aiki bace ogan su yakan ba shi aiki wani lokacin shi kaɗai zaka ga ya fito office yana aiki, wanda ya iya dai ya huta sai dai akwai tarin kalubalen da zai dinga fuskanta.

  Tun da Bakil ya shigo Ɗandume, yake kwance dakin Dada sai da ya huta, ya sha fura, ya ɗan taɓa hira da Dada sannan ya shiga sasan Alh Nasiru Malami ya gaida haj Bintu, daganan ya wuce sasan Alh saluhu Malami, nan fa Haj Aseeya ta rasa inda zata sa shi, a yayin da sajeeda take tsumar aje masa abinci da abin sha dama tunda tasan da zuwansa ta tanadar masa komai, amma Bakil nunawa ya yi baya jin yunwa babu abinda zai iya ci. Haj Aseeya tace "zuwa anjima ai zaka ci, bari ta kai maka dakin Dada", ya jinjina kai lokaci ɗaya ya tashi ya fice. Haj Aseeya ta dubi sajeeda tace "ki kwashe komai ki kaima Dada nasan zai ci a wajenta", sajeeda ta ɗan yi sakwale alamar akwai abinda ke damunta tace "Ni ko umma sai na dinga ganin tamkar yaya Bakil baya so na", tayi saurin kallonta tace "ki daina wannan maganar, wane irin baya sonki baya sonki ya yarda zai aure ki , yammata nawa ne a cikin gidan baice zai auri kowa ba sai ke, tun daga nan maganar so ai ta ƙare", ta ƙara kallonta tace "to wai me yasa ma kika fadi haka?", 

  Tace ta na kallon Haj Aseeya "kawai dai Umma naga bai damu da ya dinga nuna min kauna ba ne, kina ganin ko waya sai dai na kira shi ko idan nayi masa flashing maimakon ya kira ni kawai sai dai ki ga ya turo min kati, sannan ki duba ki gani tun zuwan da ya yi bai ƙara dawowa ba sai yanzu duk tsawon lokacin nan , idan yana so na ko don ni ai ya dinga zuwa akai akai", ta dubi mahaifiyarta sosai tace "kuma ma dai umma ni bana wani ganin so na a cikin idanunsa ko kallon cikin idanunsa nayi ban ganin shauki na so a cikinsu", Haj Aseeya ta ɗan harareta tace, "ke ni bana son sakarci, duk wannan lissafin da kike na menene?, Duk dai karshen so ai shine mutum ya ce zai aureka don haka ki bar wannan maganar, ki sani Allah ya yi Miki komai ya taimake ki, daga fara maganar aurenku cigaba nawa kika samu sannan abin alheri nawa kika samu to ki bar maganar nan kawai, ki tashi ki kwashi kayan abincin ki kai sasan Dada ".

  Ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta tashi ta kwashi kulolin abincin ta fita, dai dai lokacin Alh saluhu Malami ya shigo falon. 

   Yadan dakata yana.dubanta yace " ina zaki je da kulolin abincin ", kafin ta bada amsa Haj Aseeya tayi karaf tace "Abincin Bakil ne zata kai masa dakin Dada ". Daganan ya shigo falon ita kuma sajeeda ta wuce sasan Dada.

  Ya zauna akan daya daga cikin kujerun falon, da suka gama ganin rayuwa duk sun lamutse sun yage basu da ko kyan gani, tun kujerunta ne na lokacin da Allah ya ara musu dama , lokacin da suke fantamawa da kuɗi da daula, nagartattun kujeru ne masu tsada kila shi yasa suka kawo har yanzu ba tare da sun tashi aiki ba gaba ɗaya.

  " Ya naga fuskar sajeeda wani iri, ko wani abu ya faru ne?" Haj Aseeya ta ɗan gyara zamanta tace "shirmenta ne kawai, wai tana ganin Bakil kamar baya sonta , to ko ba ya sonta tunda ya yarda zai aureta ba shikenan ba a hankali ai zai so ta, balle nasan hasashen banza take yi, idan da baya sonta ai bazai yarda ya aureta ba". 

 Alh saluhu Malami ya numfasa yana dubanta yace "ba shirmen ta ba ne, Aseeya tun farko bana son na gaya Miki ne saboda bana son sajeeda ta sani".

 Cike da kaguwa Haj Aseeya ta dube shi tace "meye baka son ka gaya min?". Ya jinjina kai yace "Bakil ba sajeeda yake so ba akwai wacce yake so, dole kawai muka yi masa ya amince da auren sajeeda", ta dube shi sosai cike da damuwa tace "Dole?, Kana nufin baya son sajeeda ", ya gyada kai yace "kwarai kuwa, ni ma na amince da auren ne saboda shine rufin asiri na, kinfi kowa sanin kusan da Bakil duk muka dogara kuma mu muna jin tsoron ya je ya auri wata ne daban wacce zata iya raba mu da shi ba fata muke ba, amma yadda mata yanzu suka ɓaci da rashin imani tabbas yana iya auren wacce zata dinga jin haushin irin hidimar da yake yi da mu har ta nemi ta raba tsakaninmu, shine dalilin da yasa duk muka dage da sai ya auri sajeeda ".

    Haj Aseeya ta yi shiru tana nazarin maganganun nasa, ya cigaba da cewa "kuma ina son mu bar maganar a tsakanin mu , bana son sajeeda ta ji domin muna iya samun matsala da ga gare ta ". Ta girgiza kai tace "Babu yadda za'ayi ta ji, kuma ni ban ma ga wani abun tashin hankali ba, wahalar dai ayi auren da zaran anyi zai so ta zai kuma manta da waccan da yake so". Alh saluhu Malami ya yi shuru yana tunanin irin tashin hankalin da Bakil ya shiga a lokacin da suka gabatar da sajeeda a matsayin wacce zai aura, dimbin son da yake ma yarinyar, baya tunanin akwai ranar da Bakil zaice baya sonta, Haj Aseeya tana faɗan hakane kawai saboda bata ga halin da Bakil din ya shiga ba ne a lokacin. Ba kuma ya son ya gaya mata don haka ya ja bakinsa ya tsuke.

 Bakil kuwa na can dakin Mama, yana sauraron korafin da tunda ya shigo dakin take yi masa. Gaba ɗaya ya rasa in da Mama ta dosa, me take son ya yi ?. 

  Ta tsaida idonta a kansa ta cigaba da cewa, "Na rasa yadda za'a yi ka fahimci abinda nake so kuma kayi min, ina mamaki da duk abinda bana so shi kake yi", ya dago daka kallon da yake ma wayar hannunsa yace " me nake yi da bakya so Mama, zan bari saboda bana son wannan maganganun da kike yi, sai ina ganin kamar na gaza ne a kan abinda nake yi muku".

  Ta aje numfashi a hankali tace "Baka gaza da komai ba kana iya bakin kokarinka , a kanmu amma ni ina son komai zakayi ka dinga yin shawara da ni kafin kayi shi, ina kuma son duk abinda zaka ba wani a gidan nan ya dinga biyowa ta hannuna , yanzu meye abin wahala a wannan bukatar tawa?".

  Ya ɗan muskuta yace "shikenan Mama zan dinga yin hakan, in sha Allah".

 Ta ɗauke idonta akansa tace

    "Ka faɗi haka yafi a kirga"

Ya dan rausayar da kansa yace

   "Yanzu Zanyi ƙoƙarin tabbatar da hakan ".

Tace "Allah yasa, sai kuma magana ta biyu " cikin kosawa ya dubeta yace "To ta meye maganar ".

  Ta tamke fuska sosai tace"ka kiyayi Naja, bana so kana shiga harkar ta ko harkar ƴaƴan ta, ina sane da cewa kai ka turo kuɗin makarantar Hamza, to ka fita a ido na na mayar na rufe". Kan Bakil ya yi matuƙar daurewa, Allah ya sani baya son irin wannan halin na son raba kansu da yan'uwansa da take son yi tun ba yau ba, wani zubin irin maganganun da Mama ke yi suna matukar tayar masa da hankali. 

   "Ko baka jina ne"

Ta katse masa tunanin da yake 

  "Ina jinki Mama, kawai dai ina ganin kamar hakan ba dai dai ba ne, idan kince na daina kula Anti Amarya ko na daina yi ma ƴaƴanta hidimar makaranta ai ba zai yuwu ba , saboda hidimar makarantar su kan Alh take idan kuma har baida halin yi Kinga dole kenan ni Zanyi ". Ta zuba masa harara tace "Basai ka barshi ya nemi yadda zaiyi ba, ba ya'yan sa ba ne , don me zaka karbi hidimar su bayan ba kai ne ya zamar ma dole kayi ba, na dai gaya maka". Yasan mitar Haj Hadeeza yasan idan yace zai cigaba da yi mata musu to zasu kwana suna tafkawa ne.shi kuma gaba ɗaya ya gaji da sauraron maganganun da yake ganin basu da wani amfani a gare shi. Tun bai kai haka ba kullum hudubar ta kenan a gare shi .


   Ya dubeta yace "shikenan zan kiyaye Mama ". Ta gyada kai alamar ya dai fi, sannan tace "Ita kuma sajeeda da kake ta aikin yo mata aike na menene? Ka dai fi kowa sanin duk kayan dakinta kanka yake nasan ba abinda iyayenku maza zasu iya tsinana mata kaine bawa komai kanka yake don haka ka daina wannan barnar kuɗin idan sunyi maka yawa ne ka kawo su akwai abinda za'a yi da su, amma ba kayi ta narkawa sajeeda ba babu gaira babu dalili". Tab Mama ho, wato ita dai idan akan abin duniya ne kowa ma bata so Bakil ya hidimta ma, duk son sajeeda da take da son ya aureta ba zata iya jurar ya dinga kashe mata kudi ba. Nan ma to ya bita da shi domin su rabu lafiya. Haka dai Mama tayi ta gittawa Bakil sharuda ya na amsa duk domin dai a zauna lafiya.

   

  A wannan zuwan su Alh Bello Malami sun ɗauke ma Bakil yin kayan lefe, domin hidimar da yake yi a gidan ta yi yawa, Kuma ko yanzu kusan shi zai yi komai na bikin , don haka suka yafe masa lefe sadaki kawai zai bayar shima ba mai tsanani ba irin sadakin da Addini ya tanadar . Wannan hukunci da suka yanke sosai ya yi ma Haj Aseeya da sajeeda zafi, sai dai babu yadda zasu yi domin ba zasu iya tada bore ba don anfi karfinsu.

   Hakan yasa Haj Aseeya tace zasu fanshe,dama ba sa so a yi auren a lokacin don haka sai biki ya zama baifi wata ɗaya ba sai Sajeeda ta kwanta ciwo kamar me aljanu, haka Bakil ya zai dinga turo kuɗi ana yi mata hidimar magani na Karya, domin kuwa Haj Aseeya ke kaita wajen maganin na bogi, dole take sawa a daga auren, 



   Ba kananan kudi Haj Aseeya da Sajeeda su ka tara ba, domin bikin da akasa wata hudu sai da akayi shekara kafin Sajeeda ta samu lafiya sannan aka tsaida wata ranar bikin 


   Sai dai shi ma a dai dai wannan gaɓar Bakil ya fara wani training da office din su su ka tura shi, na tsawon watanni shida , ya nemi alfarmar a daga bikin har zuwa lokacin da zai kammala training din.

   Ba zasu ce a'a ba tunda lokaci dai an riga an ja shi a sanadiyyar ciwon sajeeda. Don haka su ka amince masa 

  Duk wannan tsawon lokacin da aka ɗauka, wani abu da ke ba Bakil mamaki shi ne yadda ko kaɗan Jawaheer ba ta taɓa nuna masa wai zai ƙara aure ba, domin tun daga ranar da aka yi maganar a gidansu to tsawon wannan lokacin ba ta taɓa ta da maganar ba, kai ko shi ne ya dakko maganar ta kan yi sauri ta canja hirar.


  Hakan yasa dole shi ma ya daina yi mata maganar aurensa, tunda ya fahimci ba ta so, soyayyar su ko kaɗan ba ta canja da komai ba.

  Duk da Jawaheer ta damu sosai abin kuma ya na cin zuciyarta amma ta danne ba ta nunawa ko a gidansu ta bar komai a cikin zuciyarta.


   A haka har Bakil ya kammala training din sa, makonni uku kacal a ka diba na daurin auren.

    Amma Bakil bai zo Ɗandume ba sai ana saura kwana biyu daurin auren sa da sajeeda. Kafin tahowarsa bai boyewa jawaheer komai ba ya sanar da ita daurin aurensa zai tafi. Sai dai ya yi mamakin yadda ya ga dauriyar Jawaheer domin bata nuna masa komai na damuwa ba illa fatan alheri da tayi masa, sai dai bayan rabuwar su jawaheer boye kanta tayi a daki ba tare da sanin kowa ba ta yi ta kuka me motsa zuciya, daga bisani ta yi addu'ar Allah yasa hakan shine mafi alheri a gareta. 

  Alh Nuraddeen canji kuwa ya so ya je daurin auren Bakil abu biyu suka taka masa burki, na farko jahar Katsina da Bakil ya ambata a matsayin nan ne jaharsa domin ba ya kaunar duk wani dalili da zaisa ya je Katsina, baya ko son jin kalmar Katsina, na biyu kuma baya gari akwai taron su na yan canji da za'a yi a Ghana dole zai halarta. Abubuwa da yawa sun tsaya ma Alh Nuraddeen canji a zuciya, me yasa tun farko bai tambayi Bakil dan wace jaha ba ne shi?, Hakika da tun farko yasan ɗan jahar Katsina ne da bai sakar masa jiki ba, sai dai kuma laifin wani baya shafar wani ba don haka ba da ya goge duk wata alaka da ke tsakanin sa da duk wanda ya fito daga jahar Katsina.

  Ranar juma'a bayan sakkowa daga sallar juma'a aka daura auren sajeeda da Bakil, wanda da yawa jama'ar office dinsa sun yi masa kara sun zo daurin auren ciki harda ogan su da kuma Mustapha. 

    Rana ta farko kenan da Mustapha ya zo Ɗandume mahaifar Bakil, ya ga iyayen Bakil sun gaisa, katon gidansu Bakil me sasa sasa ya ba Mustapha sha'awa yana son irin wannan rayuwar ta zama tare a waje ɗaya a matsayin su na yan'uwa.ko da yake gayama Bakil sha'awar hakan, kallonsa kawai ya yi gami da murmushi domin baisan tarin kalubalen da ke tattare da irin rayuwar da yake sha'awa ba, shi da ya rayu a irin rayuwar yasan daɗin ta ya kuma san wuyarta.

  Bayan daurin aure ,nan Bakil yabar sajeeda, da nufin sai ya samu sabon gidan da ya dace da zaman ma'aurata sannan zai dawo ya tafi da ita.

  Amma saboda matsawa da sajeeda ta yi , kullum kiran waya ta gaji da zama a gida, hakan yasa Bakil ya dawo ya dauketa, da farko sun fara zama a gidan da ya ke, daga bisani da ya samu wani gidan suka tattara suka koma.

 Ga dai zama nan da dad'i ba dad'i ana tayi, kowa na hakuri da juna. A lokacin Bakil ya so sajeeda ta koma makaranta tunda iyakarta Sakandire amma dad'i aure sai ta nuna masa bata bukatar yin wani karatu ta fi son ta zama full house wife. Bai matsa mata ba ya rabu da ita, duk da kullum banibaninta yana damunsa, ga rainuwa duk abinda zai mata saita raina, bai taɓa nuna mata damuwarsa ba, domin wani halin Bakil da kowa ya sani shine hakuri da kauda kai akan komai.

  Duk wannan abin Bakil da Jawaheer suna tare, shakuwa da kaunar junansu kullum ƙara yawa take. Haka zalika ya maida gidan Alh Nuraddeen canji tamkar gidansu bashi da shamaki a ko'ina. Wani abu kuma da ke ƙara dorama Bakil kaunar jawaheer shine yadda tunda ya yi aure, ta toshe duk wata kofa da zaisa Bakil ya yi mata maganar matarsa, so take ta manta ya yi aure kuma Allah ya taimaketa ta manta    domin ta yi yaki da zuciyarta ta cire ma kanta damuwar komai.

  Shekara ɗaya da rabi da aurensu , sajeeda ta yi barin ciki wata huɗu. Tasha wahala sosai, dalilin da yasa kenan da Haj Aseeya ta zo kawai sai ta kakkabe zani ta yi zamanta a Kaduna. Sai da Alh saluhu Malami ya yi tsaye tsaye Sannan Haj Aseeya ta dawo bayan ta kwashe watanni uku a Kaduna, sai kace bata da mafadi tsabar son hutu da son daula.

  Tun daga wannan cikin sajeeda bata ƙara samun ciki ba har zuwa wannan tsawon lokacin.

     Zaman auren dai kawai Sajeeda ke yi amma ba ta san me mijinta ke so ba me ye ba ya so, ga shegen son jikin tsiya wanda shi ne ya haifar mata da kazanta, muguwar kazamiya ce 

  Wanda da tasan halayen mijinta da tasan cewa duk duniya babu abinda ya tsana irin kazanta, 

  Amma bata damu da ta tsaya ta gane waye Bakil ba, duk da ya sha gaya mata cewa baya son irin dabi'unta, kuma a gabanta zata ga ya tashi ya na gyara inda ta bata har kicin baya kwanciya sai ya tabbatar ya gyara ya goge ko'ina, ita kam yar gogar ta na nan manne da waya ta shiga wannan group ta fita. 

   Ga shegen kishin tsiya babu damar ta ga Bakil ya na duba waya ta dinga lekawa kenan ta na son ta ga charting yake yi ko me, ko waya yake kunnanta na kai. Idan ko ta kira shi ta ji ya na waya da wani ta dinga cika da batsewa kenan ranar kuma sai yasha tambaya akan da wa yake waya.

  Fahimtar irin kishin Sajeeda yasa Bakil ya boye mata komai akan Jawaheer, don ya yi imani da cewa ba zata taɓa fahimtar sa ba 

     Sai dai kuma gaf da cikar lokacin da Alh Nuraddeen canji ya dibar masa Sajeeda ta fahimci akwai wata a cikin rayuwar mijinta bayan ita 

   Domin kuwa rana tsaka saboda yawan hawa social media da sajeeda take yi musamman facebook, ta ga yadda mata ke fadin sun duba wayar mijinsu sun ga yana neman mata, wata tace mijinta ustaz ne amma da ta duba wayarsa ta ga ya na neman mata. Irin waɗannan maganganun da matan Aure ke turowa a mafiyawan groups din su shine ya jefama sajeeda shakka da zargin ko shi ma Bakil ya na ɗaya daga cikin irin mazan , hakan ya yi sanadiyar da ta tsiri ɗaukar wayar Bakil tana bincike, da zaran ya fita yin sallar asubahi zata ɗauki wayar tasan yadda zata bi ta cire nambobin sirrin da ke wayar tasa, ta zauna ta bincike komai na wayar.

  To ananne ta ci karo da jawaheer, ta kuma tabbatar da budurwar mijinta ce. Tun daga wannan lokacin rashin zaman lafiya ya wadatu a gidan Bakil, kullum cikin tashin hankali suke da juna, duk wata shimfidar zaman lafiya da so da aka shimfida duk an nade ta. Har zuwa yanzu da maganar auren Bakil da jawaheer ya tashi.


  Bakil ya dawo daga duniyar tunanin da ya faɗa, ya muskuta ya gyara kwanciyarsa a kan doguwar kujera. Har yanzu ya na jiyo gunjin kukan sajeeda, ya aje wata nannauyar ajiyar zuciya, jawaheer itace jinin jikinsa, babu yadda za'a yi ya iya rayuwa ba tare da ita ba, saboda haka dole sajeeda ta yi hakuri ta rungumi irin ƙaddarar da jawaheer ta runguma shekarun baya, ruwanta ne ta natsu ta gane babu me hana masa ƙara auren nan sai Allah.

  Gaba ɗaya ya kosa gari ya waye ya bar Ɗandume. Duk yadda ya so ya yi bacci hakan ya faskara, a kunnansa a ka yi kiran farko, ya yunkura ya tashi ya shiga cikin dakin,kwance ya hango sajeeda a kasa bacci ya kwasheta, baya son ya yi wani kwakkwaran motsin da zai tashe ta don yasan yadda bai runtsa ba itama bata runtsa ba. Ya shiga banɗaki ya kama ruwa, sannan ya dauro alwalarsa ya fice zuwa Masallaci.

  Nan ya yi raka'atanul fajir dinsa da ya riga ya saba kullum bata wuce shi, ko ya je masallaci a makare ya kan yi kokarin ya ramata bayan ya idar da sallar asubahi kasancewar ita ana iya ramata saboda tsabar falalarta.

  Bayan idar da sallar asubahi, ya zauna a masallacin har ya kammala azkar dinsa , sannan ya fito ya shiga gida lokacin gari ya fara haske.

 Dakin Dada ya fara shiga, ya gaisheta, ta dan dube shi tace "Amma jiya baka samu bacci ba ko, don ga idon ka nan ya nuna". Ya numfasa yace "Hakane ", ta aje casbahar hannunta a gefenta tace"Kace zakayi sammako yau ka koma, haka zaka tafi kana tuki kana bacci a mota, meye ya hanaka yin baccin?, Bayan kowa ya karbi maganar karin auren naka, har zasu je su nemo maka , to damuwar da rashin baccin kuma na meye?". 

  Ya kara numfasawa yace "Hmmm Dada idan kowa ya amince da kara aurena, ita sajeeda har yanzu bata amince ba, kwana tayi kuka, shi yasa na kasa runtsawa, kinsan dai ni ko motsi ne hanani bacci yake balle kuka, na rasa yadda zanyi na fahimtar da sajeeda muhimmancin jawaheer a rayuwata, da kuma irin sadaukarwar da nayi na auranta alhalin bana sonta, duk kuma da haka na yi ta tursasawa kaina na so ta na kuma yi mata adalci tunda ta riga ta zama wani bangare na rayuwata".

  Dada ta runtse ido ta buɗe tana cewa "lalle idan sajeeda tayi wasa zata zama yar kallo a gidan ka, don idan ta cigaba da wannan zubar da girman tabbas za'a shigo gidanta kuma a ci ta da yaƙi, kuma lalle wannan tashin hankalin da take Sanyaka ciki bazan dauke shi ba, don ba zata hanaka ƙara aure ba". Ya jinjina kai yace "Ina fatan sajeeda ta fahimci hakan da gaggawa". Ya juya tsintsiyar hannunsa yana kallon lokaci a jikin kyakkyawan agogonsa, yace "Bari naje na kimtsa Dada lokaci ya na kurewa " lokaci ɗaya ya mike Dada tace"To jeka ka shirya". Ya fice da sauri.

  Yana shiga falon, sajeeda ya tadda zaune kan sallayarta da alama tunda ta idar da sallar asubahi bata tashi ba. Ta ɗora kanta a saman cinyoyinta. Karo da dama ya ji tausayinta ya kama shi, domin dai kishi masifa ne yasan ba ta da yadda zata yi ta hana kanta kishi,laifinta ɗaya ne da ta kasa hana kanta yin mugun kishi ta kasa yaƙi da zuciyarta ta fita daga turbar shaidan ta rungumi kaddarar da Allah ya ɗora mata, maimakon haka ta zauna ta na wahalar da kanta a banza.

   Dubanta ya yi yace ''Ki shirya da safen nan nake son mu wuce Kaduna'', bata yi magana ba har ya wuce cikin dakin.

  Lokaci daya ya shiga wanka, har ya fito ya gama shiryawa Sajeeda bata shigo ba, kuma bata tashi daga inda take ba.

  Ya fito rike da jakarsa, ya tsaya kusa da ita yana kallon ta sosai ya kira sunanta, ''Sajeeda'', ta dago kai da idanu jajir ta dube shi lokaci ɗaya ta dauke kanta daga gare shi ba tare da ta amsa ba.

   Ya nisa gami da gyara tsaiwarsa ya cigaba da cewa ''ya har yanzu baki tashi kin shirya ba, bayan na gaya Miki yanzu zamu tafi''. Ta girgiza kai tace ''Ba ni da karfin guiwar binka yanzu'', ya lalubi kujera ya zauna yace ''Saboda me?'', Ta yi ƙasa da kanta tace "Saboda bansan matsayi ne a wajena da ya wuce na matata uwargidana'', ta girgiza kai tace ''idan har hakane me yasa kake son jefa rayuwata cikin kunci da kangi, me yasa ba zaka iya hakurin zama da ni, ni kaɗai ba, ko don ban haihuwa ba ne yasa kake son Ka kara aure........?

   Nan da nan Bakil ya haɗe rai yace ''kada ki fara kawo wannan maganar, ko kaɗan ba ni da wannan tunanin, don me zanyi haka, ko na taɓa yi miki maganar me yasa baki haihu ba? Ko kuma nace Miki ina son na haihu ne? ( Ya girgiza kai) Ko ɗaya zan kara aure ne don ina da ra'ayin yin hakan, na dauka kin fahimci kuka tace ''ba gaskiya bane kawai dai ka daina so na, kuma ........'' Da sauri ya mike tsaye yace ''Ki shirya ki zo mu tafi'', ta dube shi ido cikin ido tace ''Bazan bika ba'', tana rufe baki ya juya ya yi ficewarsa ba tare da ya kara yi mata magana ba. Gaban Sajeeda ya fadi da ta tabbatar da Bakil ya tafi, tayi zaton zai nace ya na lallashinta akan ta zo su tafi, amma kawai sai ya tafi ya barta, ba tayi zaton hakan ba, da tayin farko ta sallama ta bi shi. Cike da tashin hankali ta tashi ta shiga banɗaki domin tayi wanka ta yi saurin shiryawa kila su Baba Bello su sa baki ya tafi da ita, da sun kirata kuwa ba zata ja aji ba zata tattara ta bi shi.

   Bakil ya yi sallama ya shiga falon Haj Hadeezar, tana uwar daki, jin Muryar Bakil yasa ta fito sanye da hijabi, yana gaisheta tana dubansa ''yau din dai zaka koman'', ya gyada kai yace ''Eh saboda office ba su ba ni izinin zama ba shi yasa gara na tafi''. Ta zauna a kujerar da take fuskartasa tace ''To ita sajeedan fa, na dauka tare zaku koma don banga amfanin zamanta ba anan'', yace ''Na so yin hakan, amma ta nuna bata da ra'ayin bina yanzu, na kuma fahimci har yanzu bata sakko ba, ni ma daga bisani nagane tafiya da ita baida wani amfani'' tayi masa kallon tsaf tace ''Kamar ya ya baida amfani'', yace ''saboda ko mun koma ba zamu sami jituwa ba gara ta zauna idan ta huce ta dawo''. Ta zuba masa ido tace ''saboda dole ka auri wannan kaddararriyar yarinyar wacce wannan mugun son da kake mata yasa na ji na tsane ta, har cikin zuciyata bana son yarinyar, ka hakura da auren nan ka dauki matarka ku tafi, kabar maganar nan'', ya mike cikin rashin son jin maganar yace ''Don Allah Mama ki daina fadan haka, kuma ya na da kyau ki sa ma kanki son Jawaheer domin itama surukar ki ce''. Ta watsa masa harara tace ''Na ki na sa ma kaina kaunar ta ta, kuma sai ka jira kaga ka aurenta kafin ka fara kiranta da surukuta, don ni banda wata suruka da ta wuce Sajeeda''.

  Yace" Mama na makara, tafiyar ba ƙarama ba ce, zan kama hanya", yasa hannu a aljihunsa ya ciro kuɗi masu yawa ya aje mata a gaba, ta dube shi tace "Allah ya yi maka albarka", ya wuce yana ''Amin, dakin Anti Amarya ya wuce can ya tadda Alh Bello Malami nan ma sun dan yi magana, shi ma ya so ya tafi da Sajeeda amma ya bashi irin dalilin da ya ba Mama, ya kuma gamsu da a barta har sai bayan anje anyi magana an gama komai saita koma kila zuwa wannan lokacin ta huce, tunda tasan babu fashi. Nan ma ya bashi kuɗi itama Anti Amarya ya bata duk sunyi masa addu'a. A sasan Dada ma bai zauna ba, duk da Dada ta na ta godo da shi akan ya tsaya ya karya amma ya nuna mata sauri ya ke domin ya riga ya makara nan dai ya bata nata kudin ya kama kan shi.

  Shi kadai a mota ya dauki hanyar Kaduna. Ya samu natsuwa da kwanciyar hankali tunda an amshi maganar aurensa da Jawaheer. Sai fatan zuwa ranar Alhamis da rai da lafiya babanninsa su taho Kaduna domin nema masa auren Jawaheer. In da gaba ɗaya nan burinsa ya tsaya .



Ku dakace ni 


Daga taskar ✍


Yar Gidan Imam

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol