Free chapter · Read without an account
38
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*ALLON ƘADDARA*_
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*PAGE 38*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
A natsensa ya ƙarasa sashen bakinsa ɗauke da sallama saman laɓɓansa, Samha ce da ta fito ɗauko min ruwa ta amsa masa da girmamawa ta shiga gaishe sa kwarjininsa na mamayeta har tana kasa kallon fuskarsa da tayi niyar yin hakan da farko.
"Tana ciki Hanan ɗin Bismillah". Ta faɗa tana nuna masa hanyar bedroom ɗin da Hanan ɗin ke ciki. Kai kawai ya ɗaga mata bayan ya amsa gaisuwarta ya nufi ƙofar da zata kaishi inda take. A nutsensa ya buɗe ƙofar ya shigo bakinsa ɗauke da sallama yana dauke idanunsa fes akan fuskarta da ta lumshe ido kamar mai barci.
Anisa dake zaune gefen ta ce ta gaishesa tana miƙewa cike da taka tsan-tsan ta fice a ɗakin ta nufi inda su Asiya suke ɗakin yaran Aunty Mamy suna shiryawa.
A hankali ya zauna kusa sosai da ita yana zubama kyakykyawar fuskarta idanu, sosai gyaran da tasha ya amsheta sai sheki take tana glowing. Tsaftatsccen hannunsa yasa yana taɓa goshinta don jin tempretue ɗinta, har yanzu goshin nata da zafi.
Tunda ya shigo ɗakin azababben ƙamshinsa ya gama gauraye duka ƙofofin hancina musamman da muka samu kusanci sosai da juna, jin ɗumin tafin hannunsa daya sauka a saman goshina ya sakani motsa idanuna dake lumshe a hankali kafin na buɗe su gaba ɗaya na zube saman fuskarsa da ya ranƙwafo saman tawa. "Yaya jikin, me kike ji yanzu?". Naji nutsatstsiyar muryarsa ta sauka cikin kunnuwana.
"Fuska na kwaɓe zan saka kuka yayi saurin ɗora yatsansa saman laɓbana ya ce "Karki fara rigimar nan yanzu kinji, ba zan iya jurewa ba, yanzu faɗa min miye damuwar?". Ya faɗa yana ƙara narka idanunsa cikin nata idanun da suke wani maiƙo-maiƙon hawayen da ta fara tarawa.
"Nima ban sani ba Hammah sai nake ji kamar ina jin tsoro, zuciyata ta kasa zama wuri ɗaya kajima zazzaɓi nake ji kuma!". Na ƙare maganar a sakalce ina matse hawaye.
Tagumi kawai ya zabga yana kallon yanda take kassara natsuwarsa, take neman zubar masa da man kai tsakani da Allah bayan shima ba lafiyarnan gare shiba.
"To yanzu allurar za'a yi ko?". Ya tambaya yana ƙoƙarin ɓoye murmushinsa ganin yanda ta miƙe zunbur! Tana zazzaro ido.
Ƙwal-ƙwak nayi da ido hawaye na malalowa nace "Ni dai bana son allura don Allah!". Na faɗa ina ƙara marairaice wa ko zai ji taisayina. "To naji amma sai kinci abinci na baki magani ko kuma allura sai ki zaɓi ɗaya".
Fuska na kwaɓe don har ga Allah bana son ko ɗaya, sai dai gara min hakan da dai a huda min jiki ana zaman lafiya. Wayarsa ya ɗauka ya saka kiran Asiya, tana ɗagawa yace "Ki kawo min abinci mai sauƙin ci". Ya kashe wayar ya aje ya zuba mata ido yana kallon yanda take ta shagwaɓe fuska tana mimi da baki alamar halinne ya motsa.
Bai bar ɗakin ba sai da ya bani abinci da kansa ya bani magani ya sani na ɗan zauna kaɗan kafin ya barni na kwanta ya rufeni ya fice da gargaɗin banda rigima idan ba haka ba zai zo ya min allura.
Luf nayi ina sauke ajiyar zuciyar da ta maƙale min a wuya bayan fitarsa na lumshe ido wani nutsatstsen barci na ɗauke ni.
Da haka aka gama yinin biki kowa ya kama gabansa ya rage sai dangi kaɗai don ba yau za'a kai amarya ba sai bayan nan ya gama gyara inda zata zauna kuma itama ta ƙara samun natsuwa cewar Alhaji Babba.
Bai samu kansa ba sai bayan yayi Sallar Isha'i ya wuce Gida ba tare da ya koma Gidansu ba, wanka ya fara yi kafin ya shiga kiching ya sama wa kansa abinda ya samu ya sama cikinsa wanda tun break fast ɗin safe da yayi kafin ya fita bai sake saka wani abu a cikinsa ba sai yanzu da ya haɗa tea da milk Cake yaci ya kwanta cike da samun natsuwar zuciya bacci mai daɗi yayi gaba dashi bayan ya tura mata guntun text message na tambayar yanda take.
✨✨✨✨✨✨✨✨
Fitowarsa kenan daga wanka yana shirin fita Office, gaba ɗaya kwanakinnan haka yake fama da ƙuncin zuciya sabo da haka cikin rashi sukuni yake shirin sa cikin Suit ɗinsa mai kyau da tsada aka buɗe ɗakin aka shigo.
Kansa ya ɗaga ya sauke saman fuskarta da tasha uwar kwalliya sai sheƙi take, kallo ɗaya yayi mata ya maiyar da kansa ga abinda yake yi. Cikin yauƙi da iyayi ta shiga takowa tana juya ɗan shafal ɗin jijinta kasancewar ta mara jiki ko kaɗan, rungumesa tayi lokacin da ta ƙara so tana faɗin "Honey ashe baka fita ba, good morning dear". Ta faɗa tana wani narkewa a jikinsa.
"Da ƙyar ya iya danne kansa yace mata "Morning". Baki ta taɓe ganin yanda yake wani shareta. "Ka yi ka gaji aure ne dai ba za kayi shi ba, dani kaɗai zaka gama rayuwarka, don ko mutuwa nayi sai na hanaka auren wata Mace". Ta faɗa a ranta.
"I come to check on you ne dama, baye na wuce rurin aiki". Ta faɗa tana sumbatar goshinsa ta yi gaba abinta ba tare da damuwa da irin kallon takaicin da yabita da shi ba.
Yana gama shiryawa ya fito ya samu yaransa a saman table suna breakfast. Da gudu Noor ta taso ta rungumesa tana masa surutu. Ɗaya bayan ɗaya ya bisu ya rungumesu yana sumbatar goshinsu da tambayar yaya suke, cike da farin ciki yaran suka yi breakfast da Mahaifinsu kafin ya ɗauke su da kansa ya kaisu Makaranta da alƙawarin zai kaisu ShopRite da week end.
Duk da kasancewarsa na Miji mai uzurori da yawa a gabansa amma yaran sunfi samun lokacinsa fiye da na Mahaifiyarsu.
A hanyarsa ta zuwa wurin aikinsa bayan aje yara a Makaranta ya haɗu da Samha ƙawar Hanan a bakin hanya Motarta ta tsaya tana neman abin hawan da zai ƙarasata wurin aiki. Har zai wuce sai kuma ya fasa ya tsaya sabo da duk abin da ya shafi Hanan yana girmama shi koda kuwa bai aureta ba. Kashe Motar yayi ya fito sabo da ba da driver ya fito ba sabo da ya samu kai yaransa Makaranta da kansa.
Sallama yayi mata da ɗago tana amsawa, fuska ta saki sosai suka gaisa zuciyarta cike da tausayinsa sabo da ita shaida ce akan soyayyar da yayi wa Hanan, sai dai Allah bai kƙaddara aurensu ba. Tayin sauketa yayi mata ba musu ta amsa ya buɗe mata ta shiga, kamar wasa suke ɗan taɓa hira har ya sauketa tayi masa godiya ya wuce nasa gun aikin.
******
Barci nasha sosai ban tashi ba sai da magriba. Wanka na shiga nayi a nan naga baƙona yazo min duk da sai nan da kwana biyu nake sa ran ganinsa, kaina na kimtsa na fito na samu Anisa muka fice zuwa sashenmu don nayi kewar Ammy sosai duk yinin yau tun da safe da naje gaisheta ban sake ganinta ba. Itama fama da jama'a yasa bata samu zuwa dubani ba sai Aunty Ade ce ke kai-kawon zuwa dubani.
A bedroom dinta na sameta ta gama sallah tana zaune tana lazumi, kusa da ita naje na zauna ina ɗora kaina saman ƙafarta na sauke ajiyar zuciya. "Yaya jikin Habebty?". Ammy ta tambayeni cike da kulawa.
"Alhamdulillah". Na bata amsa ina zamewa na kwanta saman ƙafafunta. "Kinci abinci?". Ta kuma tambaya.
"Eh Ammy". Na bata amsa ina lumshe idona cikin samun natsuwar jina kusa da ita.
Da wannan damar Ammy tayi amfani ta riƙa min nasiha mai ratsa jiki cikin tattausar murya da kwantar min da hankali. Cikin nasihar ne tace min "Ki kasance mai karɓar duk abinda Allah ya zaba maki a rayuwa in sha Allah zaki kasance mai nasara matuƙar da zuciya ɗaya kika amsa kika gode masa, kar kiga an ɗaura maki aure da wanda ba zaɓinki ba kice zaki yi jayayya da zaɓin da Allah yayi miki, ki karɓa da hannu biyu kiyi godiya ga Allah sannan ki dage da addu'a Allah yasa haka yafi alkairi. A kullum addu'ata itace Allah ya baki Miji na gari wanda zai riƙe ki tsakani da Allah ya kula dake, sai gashi Allah ya maki sauyi da ɗan'uwanki kenan shine alkairi a gareki tunda shi muka roƙi Allah. Sai kiyi bakin ƙoƙarinki wurin ganin kin kyautata masa kin kuma riƙe amanar marainiyar da aka bar masa, in kika yi hakan sakamakonki na ga Allah. A karshe ina maki fatan alkairi ina kuma maki addu'ar Allah ya baki zaman lafiya ya tabbatar da farin ciki a rayuwarki!". Ta ƙare maganar cikin sanyin da jikinta yayi na kewar tilon ƴarta da ta fara tun yanzu.
Kuka sosai nake zuwa lokacin ina ƙara ƙanƙame Ammy, magan-ganunta sun matuƙar sanyaya min jiki, nan take nima tsoron rabuwa da ita ya mamayeni irin wanda ban jiba a lokaci na farko da za'a kaini Gidan Ya Nabeel. Cikin kukan da yaci ƙarfina nayi mata alƙawarin yin aiki da duk abinda ta umarceni.
Sai da nayi kuka mai isata kafin Amma ta rarrashe ni nayi shiru ina sauke ajiyar zuciya. A ranar dai a ɗakin Ammy na kwana tare da ita kamar wacce akace gobe za'a kaini kuma ba zan ƙara ganinta ba haka nake ji.
★★★ Washe gari na tashi jijina Alhamdulillah babu zazzaɓi sai dai rashin ƙwarin jikin da na tashi dashi, tun da safe Aunty Ade tazo ta sani gaba da kayan gyara don tace gyaran jiki zata min wan da ya amsa sunan gyara. Ba don ina so ba na barta ta ware ta darji fatata kamar zata sauya min wata, zuwa yanzu na gaji da wannan gyaran da ɗuren-ɗuren magungunan da take min tunda bikin ya matso. Ana gamawa nayi wanka na kwanta barcin gajiyar da aka tara min ya ɗauke ni ban tashi farkawa ba sai kusan 12:00am na tashi na karya.
Samha tun jiya ta wuce Gida sabo da zuwa wurin aiki daga ni sai Anisa da su Asiya muka wuni a ɗakina, sai fa sashen Hajjo da muka je da yamma don nace nifa na gaji da zaman wuri ɗaya.
Washe gari ƴan Katsina suka tashi da shirin komawa tunda kai amarya ba yanzu ba, sunce bayan nan zasu zo ganin ɗakin ko kuma in ta haihu suzo suna.
Haka aka haɗa musu sha tara ta arziƙi suka tafi cike da farin ciki ana sam barka.
Ƴan Yola ma wasu sun koma wasu kuma suna nan a sashen Hajjo since sai sun raka amarya ɗakinta sannan tun da Alhaji Babba yace ya gama duk abinda yake nan da sati biyu ya ɗauki Matarsa zuwa lokacin ta gama war-warewa.
**** Wasa-wasa Momy sai da ta yi kwana huɗu tana jinya a Asibiti kafin a sallamota ta dawo Gida. Sau biyu su Ammy na zuwa dubata kafin a sallamota amma ko kallon inda Ammy take bata yi bare ta amsa ya jikin da take mata. A wannan karon Hajjo kasa shiru tayi sai da ta faɗa wa Momy baƙaƙen magan-ganun da suka ƙara ƙone zuciyarta don tas Hajjo ta mata a gaban Matan Gida ta kuma ce inta sake sai ta kashe kanta a banza da wofi sabo da baƙin ciki da hassadar da tasa a zuciyarta na mutanen da ba abinda suka tare mata. "Haba don Allah! Ni tunda nake ban taɓa ganin baƙar zuciya mai azabar riƙo irin taki ba Habiba, ace abin duniya ba zai wuce a wurinki ba, sai kace a kanki aka fara rasa masoyi, gaba shekaru aru-aru ki riƙe ƴar'uwarki da abinda ya faru ba laifinta bane haka Allah ya tsara kuma wanda kike abin ma a kansa baya duniyar amma don masifa ki hana zuciyarki sakat, na ɗauka rashin Nabeel da kika yi zai zame maki darasi ashe ƙara busar miki da zuciya yayi, to Allah in baki sauƙakawa kanki ba ke zaki kashe kanki a banza kuma takwara zama daram a Gidan Mijinta mutu ka raba da yardar Allah!". Hajjo ce ke wannan maganar cikin jin haushin baƙin hali da hassadar da Habiba ke nunawa.
Wani irin tattauran hawayen baƙin ciki da kunyatar da ita da Hajjo tayi ne a gaban mutane suka zubo daga idon Momy, baya kawai ta juya musu tana fashewa da kuka mai raɗaɗi Aminatu na taya ta, yayin da Sakina keta hare-haren tana cika tana batsewa sai dai ba fuskar da zata kawowa Hajjo wargi domin kuwa Macece mai kame kanta da kuma kwarjinin da ba a kawo mata wargi.
Ficewa Hajjo tayi daga sashen dawowarsu kenan daga Asibiti ta shigo dubata ta same su suna maida magana akan abinda ya faru shine ta mata tas a gaban Matan Gidan da suka shigo dubata.
Tun daga waccen ranar da yazo ya sakani cin abinci da bani magani ban sake ganinsa ba har kwana huɗu sai dai kullum ina ganin text message dinsa na tambayar lafiyata, sai yau da yazo Gidan da safe ya shigo gaishe da Ammy ni kuma na fito daga ɗakina zuwa dining table yin breakfast da Ammy ta tasoni daga barci...
Oum Fatima