Free chapter · Read without an account
{73..}
Kafin yamma tini gida ya kuma cika fiye da jiya don yan uwa ma na kusa duk sun hallara, Hajjaju Hajiya ma ta iso tana can ɓangarensa tare da ta ta bataliyar, yau Monday kuma yau ne za ai ladies party or bridal shower oho dai toh dai yau za ai a can garden da akay ma decoration, friends din Noor duk sun zo kuma a room dinta sukay branching hkan yasa Hajar ta gudu ɓangaren Hajiya, Hajiya kam na ganinta ta jawota gefenta tace tay zamanta kar ta shiga hayaniya, sai lokacin da za a fara ladies party Aysha wacca suka zo tare da Hajiya ta shigo, tasha gown dinta mai kyau da nude make up a fuskarta, kallon Hajar dake kwance rigingine tayi tace "Laa baki shirya ba Hajar..?", Hajar ta tashi zaune ta gyaɗa kai, Aysha tace "ai kam dai ki tashi ki shirya, ga masu make up can kije a miki", tare da Aysha suka je room din Noor ta saka kayanta na bridal shower din, make up kam cewa tayi bata so da kyar Aysha tayi convincing dinta ta shafa simple powder da lipgloss, she look cute with her natural beauty, ita dai Hajar tinda aka je wajen bridal shower din ta samu kujera tayi zamanta, duk wajen babu namiji ko ɗaya daga Amarya sai friends dinta ne suke shoshalewa, masu distributing drink ma da masu kiɗa duk mata ne, Khausar duk tafi zaƙewa a filin rawa sai wani rapping waƙa take ga gown dinta duk yafi ɗameta, irin dai ƴan matan Amaryar nan masu fiffiƙalewa da giggiwa. wata friend din Noor ce tazo ta zauna kusa da Hajar tace "Hi", Hajar tace "Hi", tace "Am Banafsha and you are..?", Hajar tace "Hajar", Banafsha tace "it is nice meeting you Hajar", Hajar tace "same", Banafsha tayi murmushi tace "i like your dress", Hajar ta mayar mata da murmushi tace "thank you", Banafsha ta tashi ta bar wajen, Hajar ta ɗan ƙalli wajen gami da tattare girarta don ji take kamar ana kallonta saidai ba taga me kallon nata ba, Aysha ce ta zauna kujerar kusa da ita daman position dinta ne, time to time take tashi ta ɗan zaga sai kuma ta dawo ta zauna, Hajar tace "ni kam zan koma ciki gsky", Aysha tace "har kin gaji..?", Hajar ta gyaɗa kai tace "kai na kamar zai min ciwo nake ji", Aysha tace "Ohk toh sai mun shigo", Hajar ta tashi walking gently ta nufi cikin gida har lokacin tana jin kaifin idanu a kanta da haka ta doshi main building tana jin wani iri, irin feeling din nan na arwa, kamar ance ta ɗaga kanta ai kam ta gansa tsaye a balcony din ɗakinsa ya riƙe railer yana kallonta, sosai fitilun da suke gaban gidan suka haska masa fuskarta tare da dressing dinta, hular turban din data saka anyi pushing dinta back wnda hakan ya fito da kwantaccen sajenta, da sauri ta saukar da kanta bayan zuciyarta ta buga ta shige ciki, room din Noor ta shiga ta cire kayan jikinta ta saka na barci bayan tayi wanka, saida tayi sallar isha'i snn ta koma ɓangaren Hajiya don yau tasan bbu space a ɗakin Noor, ta tarar da Hajiya da Sumayyah yar wajen Mama Mardiyya, bata daɗe da zuwa gidan bikin ba don a Kaduna take aure, gaisheta Hajar tayi, Sumayyah ta amsa da sakakkiyar fuska, Hajiya tace "Matar Usuman ce nasan baki santa ba", Sumayyah tace "Okay Allah sarki ai kam ban santa ba", Hajiya tace "ai shiyasa na gaya miki da wuri don karki zata bare ce", Sumayyah tace "zanje mu gaisa da Mami", Hajiya tace "Au toh idan kun gaisa ki biya ta kitchen kice da Asabe ta kawomin tuwan haka nan kar yunwa ta halakani, bazan ci wnn bushasshiyar shinkafar da aka dafa ba", Sumayyah tace "toh Hajiya" da haka ta nufi door, tana bude door din taga Nurain da eyebrows dinsa suke a haɗe shima zai shigo, tace "Ya Uthman ina yini", Nurain ya amsa yana shigowa ciki, Sumayyah ta wuce ta fita snn ta rufe ƙofa, Hajiya ta kallesa ta saman kantamemen glasses dinta tace "Au Usuman dman kana gidan tinda nazo ban ganka ba", a taƙaice Nurain yace "A'a bana nan", ya fakaici kallon Hajar bayan ya zauna kan Sofa, Hajar ta saukar da kanta a hankali tace "ina yini", bai amsa ba kawai kallonta yake sai kuma ya dubi Hajiya yace "na siyo miki man zafi iron lady idan kika gwada ya miki kyau sai a ringa siyosa", Hajiya tace "Ah to Madallah kamar kwa kasan kwalin nawa ya ƙare kwalbar ƙarshe ce na fiddo", Hajar ya kalla da wutsiyar ido, ta ɗago kanta sukay ido huɗu, turo baki tayi ta haɗe fuska lokaci guda ta miƙe sum sum sum ta shige bedroom din Hajiya, ya bita da kallo yyi slight smirk. washe gari da yamma Sakeena ta shigo part din Hajiya, kallon Hajar dake zaune tayi tace "ya ba kije an miki henna din ba Hajar..? kije a miki mna", Hajar tace "Tom", tin safe da taje ta gaida Mami har part dinta ta dawo wajen Hajiya, box din kayanta ma ta ɗakko daga room din Noor ta dawo dasu nan, a nan tayi wankanta ta shirya cikin sabuwar atamfar da aka dinka mata, Hajiya tace "Ah ƴar nan kema kije a miki filawar mana in kuma ba kya so sai a maki irin nawa yafi sauƙi", Hajar ta kalli dungulmin ƙafa da hannun Hajiya ta girgiza kai, Hajiya tace "Allah kuwa kyau zai miki sosai tinda gaki nan jajir", Sakeena tace "A'a iron lady wnn ai saiku tsofaffi, ina ita ina wani dungulmi", Hajiya tace "Au toh daman sauƙi nake nema mata", har ɗakin da ake ƙunshi Sakeena ta kai Hajar tasa wata cikin professional masu ƙunshin da suka zo tace ta mata, duk gasu Aysha nan da sauran friends din Noor an musu red henna, ita kanta Amaryar ynxu ake zana mata, Hajar ta zauna aka fara mata ƙunshin, ana cikin zana mata na hannu sai ga Khausar nan ta shigo, ta zaro ido tana kallon mai ƙunshin tace "what the heck mai lalle ba nice next da zaki yiwa ba, daga bari inje in dawo sai kuma ki kama wata", ita dai mai lalle ba tace komai ba ta cigaba da zanawa Hajar flowers masu shegen kyau, Banafsha da ita ta cire nata tace "c'mon girl ynxu fa za a gama a maki kema", mai lalle tace "ai na kusa gama mata", Khausar bata sake cewa komai ba ta zauna kusa da mai lalle fuska a haɗe, da gangan ta ringa tankwaɓar hannun mai lallen ƙunshin Hajar ya ringa caɓewa, ita dai mai lalle har ta gaji da gyarawa da shiru ta yiwa Khausar mgana tace tana tankwaɓarta, Khausar na latsa wayarta tace "Ohh sorry", Hajar dai ƙunshinta na kamawa tasa aka cire mata ta fita, za a mata baƙi tace bata so jan is okay, After 20mins Hajar ta sake dawowa ɗakin da ake ƙunshin da wayar Aysha a hannunta, miƙawa Aysha wayar tayi tace "Ana ta kiranki ne", Aysha ta amshi wayar tace "thank you", Hajar ta kalli Khausar da ake yarfawa black henna a hannu, ba ƙaramin kyau ƙunshin yayi ba, Khausar sai wani video take yiwa hannun nata, walking gently Hajar ta tashi ta fita, babu jimawa ta dawo da hijab dinta har yana jan ƙasa, da gangan ta baza hijab din kamar zata wuce wajen Noor ta damule ƙunshin Khausar tass, tayi gaba abinta kamar bata sani ɗin nan ba, Khausar tayi ƙara ganin baƙin henna duk ya damule mata hannu, sai a lokacin Hajar ta juyo, kamar gaske ta wani zaro ido tana kallon mai lallen tace "Ohh sorry", har wani huci Khausar take tsabar takaici tace "what have you done.. ke ba kya kallon gabanki ne...", Noor ta katseta da faɗin "plxx sorry sisto tana sane ai bazata caɓe miki ba", da sauri Khausar ta tashi ta shiga toilet, duk da wankewar da tayi amma ina duk ya caɓe kuma lallen ya kama sosai sbd mai kyau ne, haka nan dai ta haƙura da baƙin henna sbd hannunta duk sun ɓaci, haka nan da takaici Khausar ta ƙarashe Henna day din nan, gashi kowa taje ta shirya an fita compound ana kiɗan kwarya, Khausar daga ta kalli hannunta sai baƙin ciki ya turnuƙeta sai kace ta shafa gawayi. washe gari da za ai Mother's eve kam tin bayan sallar azahar ake ta shiri, wnda zasu make up duk sun tafi inda za a musu, ita dai Amarya tana gida tinda professional makeup artist aka kira don yi mata kwalliya, Ƙarfe bakwai na dare gidan duk ya daɗe sai tsirarun jama'um da bazasu event din ba irinsu Hajjaju Hajiya, kana ganin event din kasan na iyaye ne, ba saina ɓata lokaci na wajen gaya muku ydda abin ya kasance ba ko kuma abinda aka ci, kawai dai nasan anyi kulu washrabu tare da hani'an, Table ɗaya Hajar da Aysha da Sumayyah sai wasu ƴaƴan friend din Mami biyu suka zauna, Khausar kam tana can high table da sauran friends dinsu, bayan an gama serving Abinci Hajar ta hango Khausar sai ɓoɓɓoye hannunta take, ba tasan lokacin da ta tuntsire da dariya ba, Aysha da take sipping drink ta kalleta tace "what's funny...?", Hajar ta girgiza kai tace "nothing kawai na tuna wani abu ne", Aysha tace "Ohk", Saida aka kusa tashi daga event din saiga Nurain ya shigo shi da Farooq, dman tin jiya Nurain ya bar gidansu ya wuce gidansu Farooq, da gidansa yayi niyyar zuwa amma yasan gidan empty zai masa without her, bazai ji daɗin gidan bbu ita aciki ba shiyasa kawai ya tafi gidansu Farooq, direct table din da Mami da friends dinta dasu Ummin Farooq suke suka wuce, gaisawa sukay dasu Mami, Mami tace "Amma dai kar ku tafi zaku mayar da mutane gida", Farooq yace "Toh Mami", shi kam Nurain tini idonsa ya kyallaro Silly girl dinsa wacca bata ma lura dashi ba, saida ya kusa melting a inda yke after seeing her dressing, she look very gorgeous with natural beauty, habawa sai Nurain ya fara kalle kallen wajen wai ko zai ga akwai maza, and he saw them, ai kam tini wani zafi ya yanko masa a zuciya, sai ya fara tunanin hanyar da zai fitar da ita daga nan ɗin, Nurain ya kalli stage yaga lil sis dinsa na kallonsa, bai yi niyyar zuwa stage din ba amma sbd yadda take kallonsa kawai ya tafi wajenta, aka musu hotuna snn ya manna mata money bana wasa ba, tini ms ya cika mic yana ƙawata moment din na brotherly love, Nurain na sauka stage din ya kalli position din Hajar, ido huɗu sukay tayi sauri ta ɗauke kanta, da haka ya fita daga hall din tare da Farooq, bayan an tashi daga event Hajar na tsaye tare da Aysha a bakin hall din a inda Sakeena tace su tsaya, ganin sun fito Nurain da Farooq dake zaune can wajen da ake parking mota suka taso dman jiran fitowarsu suke, Hajar na ganin Nurain coming towards them ta shige hall din, Nurain ya dakata ya bita da kallo snn ya haɗe gira, gyaɗa kai yayi ya cije lower lip dinsa painlessly, ta bari idan suka haɗu ya koya mata hankali saita fara gudun nasa, ai ynxu ba komai take ba face wasa, mistake din da zatay shine ta bari ta shigo hannunsa, Khausar ce ta fito daga hall din holding her small handbag, da sauri ta matsa kusa da Nurain tace "Ya Nurain daman baka tafi ba", ba tare da ya dubeta ba yana kallon ƙofar hall din yace "yeah", tace "Ohk zan bika mu wuce gida tare", yace "Ohk", murmushi tayi tace "where is the car..?", parking space ya nuna mata sai kuma ya juya ya nufi motar tabi bayansa, yana unlocking motar tayi sauri ta buɗe front seat ta shiga, shi dai baice mata komai ba ya shiga driver seat ya kunna motar ya fito da ita sarari, ta glass ya hango fitowar Hajar daga hall din ta ja gefe ta tsaya don ba taga Aysha ba ta koma hall din nemanta, Calmly Nurain yace "koma back seat Khausar", kasaƙe Khausar tayi without making any move, ganin bata motsa ba ya kalleta, tayi saurin cewa "Okay" ta bude motar ta sauka, bata shiga bayan ba saita bar wajen, Nurain ya fito ba tare da ya kashe motar ba kuma ya bar door a buɗe, ai kamar wanda aka wurgo daga sama hka Hajar ta gansa a gabanta, ita bata ma san ta ina ya taho ba kawai ganinsa tayi, tana shirin ja da baya yayi sauri ya figi hannunta, yana riƙe da hannunta har gaban motarsa ya buɗe front seat with stern voice yace "get in..", turo baki tayi ta haɗe fuska ta shiga zuciyarta na lugude, Nurain yayi ajiyar zuciya ya zaga driver seat ya shiga, Khausar da komai ya faru akan idonta ta saukar da kanta ta koma jikin motar Farooq ta jingina, Nurain ya ringa kallonta bbu ko ƙiftawa kafin yayi kwafa, Ita dai Hajar tama kasa haɗa ido dashi zuciyarta sai bugawa take ta wani shige cikin kujera, in banda scent dinsa bbu abinda take shaƙa a motar, ta lumshe idonta gami da resting jikin kujera, wayarsa ya ɗauka yayi dialing numbern Sakeena, tana picking yace "Sister where are the rest nifa zan wuce", suna gama waya da Sakeena ya katse kiran sai kuma ya dubi Hajar, after a while yace "Hajar wollah nanda kwana biyu akace kimin pouting lips baza kiyi ba", da gefen ido ta ɗan kallesa ta murguɗa masa baki, yace "hmmm kiyi iya iyawarki Silly girl", Aysha da Sumayyah sai ƴar Haj Sadiya ne suka shiga motar Nurain, ragowar da suka rage da kuma Khausar suka bi bayansu a motar Farooq, Nurain na parking bayan sun isa gida Hajar ce ta fara buɗe motar ta fita, bayanta yabi da kallo harta shige ciki. washe gari da safe Hajar suna zaune palourn Hajiya suna breakfast da aka kawo, suna gama cin abincin Aysha tace "let me check on Khausar jiya da muka dawo mother's eve batada lfy", Hajiya tace "wace kuma ba lfy..?", Aysha tace "Khausar..", Hajiya ta gwalo idanu tace "Au Kaushi..", dariya Aysha tayi tace "Khausar din Anty Zulaihah..", Hajiya tace "Auho wnn ƴar ta Zulaihah..?", Aysha tace "Eh ita", Hajiya tace "toh ki mata sannu", Aysha tace "tom" sai kuma ta dubi Hajar tace "kema zaki dubatan..?", Hajar ta girgiza kai tace "No.. kawai kice ina mata sannu". Aysha na zuwa room din Noor ta tarar da Khausar din ma sai lodar abinci take, kamar ba ita bace ta ringa rusa kuka jiya ba wai cikinta ke ciwo, Aysha dai ta mata sannu da jiki ta gaya mata saƙon Hajiya da Hajar snn ta fita. wajen ƙarfe tara na dare Nurain ya shiga part din Maminsa, gaisawa sukay dasu Haj Fati da suke zaune palour snn ya wuce bedroom don yasan Maminsa na ciki, A kan prayer mat ya tarar da ita tana jan counter, ya zaune gefenta ya gaisheta, Mami ta amsa kafin tace "wai gida ka wuce ne, da safe na tura a kiraka baka nan..?", ya shafa kansa yace "Eh Mami ina wajen Farooq", Mami tace "ohh okay, kuna zuwa dai ku amshi abinci ko..?", yace "yeah we are fine alhmdllh", tace "Good", yace "Amm yau ma akwai wani program din ne..?", Mami tace "sure yau suke Dinner", wani irin zimm Nurain yaji don yasan definitely Hajar na can, snn kuma Dinner nan dole akwai maza wnda suka linka na event din jiya, Nurain yace "Mami ku bazaku ba..?", Mami tace "yeah am not going wnn fa harda Ango da abokansa ina naga ta zuwa, can dai suje su sha shagalinsu", Nurain ya haɗiyi wani yawu don har zuciyarsa tayi zafi, da kyar yace "har Sister Sakeena sun tafi can din..?", Mami tace "Eh duk sun tafi fa, nace dai kar suyi dare", yayi ajiyar zuciya yace "zan duba iron lady", Mami tace "Ohk", tini Nurain ya fita daga part din Mami ya shiga na Hajiya, Farooq dake palourn Hajiya suna taɗi da Amaryar tasa ya ɗaga kai ya dubi Nurain, hannu Nurain ya mika masa yace "Car key", Farooq ya ciro key ɗin motarsa ya basa yace "are you going out..?", Nurain ya amshi key din ya gyaɗa kai ya juya ya fita with speed, Hajiya tace "kaga dai wulaƙancin da Usuman yayi min ko, ƙiri ƙiri ya shigomin ɗaki amma ko ci kanki bazai cemin ba..?", Farooq yace "Ya haƙuri Amarsu ai ynxu zai dawo sai ya miki gaisuwan ta nutsuwa kinga sauri yake", Hajiya ta rausayar da kai ba tace komai ba. With speed Nurain ya fita compound ya buɗe motar Farooq da suka zo gidan ya shiga, wayarsa ya ciro yana tunanin wa zai kira ya gaya masa location din wajen Dinner din, duk waɗanda ya kira basa responding saida ya kira Khausar, tana picking bbu wani wala wala ya tambayeta location din, sunan event center din ta gaya masa tare da Address din wnda saida ta tmbaya itama, tana gama gaya masa ya katse kiran, duk da nisan Event center din amma da wuri Nurain ya isa sbd uban gudun da ya falfala, da Google map a wayarsa yayi amfani har yaje. Tin kafin ma Dinner ta fara ɗaukan harami Hajar taji gaba ɗaya ta gaji, kiɗan da ta sha kwana biyu duk ya isheta kanta har ya fara mata ciwo, gashi a duk event din da akay kwalliyarta ta yau tafi kyau da jan hankali, A hankali Hajar ta tashi ta kama hanyar fita daga hall din don sosai kiɗan ya hau mata kai so take ta ɗan sarara, wani daga cikin Abokan Ango da tinda ya kyallarota ya kasa ɗauke idonsa a kanta, tana fita daga hall din shima ya tashi yabi bayanta, daga can gefe kan wani dakali ta zauna ta dafe kanta, kawai taji ance "Aslm beauty..", Hajar ta ɗaga kanta gami da zuba masa lulu eyes dinta, after a while ta saukar da kanta ba tace komai ba, yace "baki amsa sallama beauty", a taƙaice tace "wslm", yayi murmushi yace "thank you", tini Hajar ta miƙe don ta gane take takensa zata bar wajen, yayi saurin riƙo veil dinta yace "Please listen to me", a daidai lokacin motar Nurain ta kunno kai, sosai fitilar motar ta haskesu kuma har lokacin bai sakar mata veil ba, Nurain bai san lokacin da ya saki steering din motar ba don abinda yaji bazai misaltu ba, da kyar ya iya danne birki ya tsaida motar.....✍️