Free chapter · Read without an account

4

by Ameera Adam · SHU'UMAR MASARAUTA 2

*SHU'UMAR MASARAUTA*

        *BOOK 2*


      ©AMEERA ADAM


 *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

  (_Home of qualities and trusted writers of the nation_)


Tsokaci: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a wata kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

  

 SHAFI NA HUƊU


GIDAN SARIN KAYA🥳🔥

Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada.


   Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi.


 Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa.


 Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰


  Akwai cotton material da lesuka da atamfofi siyan ɗaya ko sari.

    Tuntuɓe ni a wannn lambar ***



 Bamaguje ya share hawayen da ke kwarmin idonsa sannan ya dafa kafaɗar Boka Jassu ya ce.


 "Na yarda da kai ɗari bisa ɗari Boka Jassu, don haka ma ba ni da haufi a kanka aikinka." 

 Amsa masa Boka Jassu ya yi, sannan ya ƙarasa bakin gefen wata murtukekiyar jijiyar bishiyar kukar, ya ɗauko wani baƙin garin magani ya damƙa wa Bamaguje haɗe da faɗin.


 "Wannan magani na wani ɗan Kasuwa ne da zan yi wa aiki amma na fasa yi masa, domin wata kusan ta fi wata in ji masu iya magana." 

 Da sauri Bamaguje ya karba da hannunsa jiki na karkarwa.


 "Shekara ɗaya kenan ina haɗa laƙanin wannan maganin, babu wata hidima ko ɗawaini da za ka yi wa maganin domin na gama yi masa komai. Abu ɗaya za ka aiwatar, wato ka turarawa jikanka da shi. A take zai rikiɗe zuwa surar baƙin kare, an binne laƙabinsa a cikin kabarin Sarkin Gabas. Ragowar laƙanin kuma yana cikin kogin Buzzar, idan har ka aiwatar da haka har abada ba zai dawo surarsa ta ainahi ba. Domin laƙanin yana cikin hatsabibin kogin da na sanar da kai, tun da na fara sauke numfashi a doron ƙasa; mutum biyu ne na ji labarin sun taɓa shiga cikinsa sun fito a raye." 


 Bamaguje na jin jawabin Boka Jassu ya bushe da dariyar ƙeta, ganin haka ya sa shima Boka Jassu ya fara ƙyaƙyata dariya. Sai da suka yi mai isarsu sannan ya ci gaba da cewa.


 "Sai kuma Masarautar Huddam! Idan na fahimci labarin da ka ba ni. Dattijo Maharaz babban jigo ne a masarautar tun da yana ba su taimako da kulawa?" 

 Bamaguje ya gyaɗa masa kai.


 "Lamarin Dattijo Maharaz ka bar mini komai a hannuna, domun ta bayan gida zan ɓullo masa, ka san an ce da ɗan gari akan ci gari har a kai shi ƙasa. Na yi maka rantsuwa da girman hatsabibiyar bishiyar kukar nan da buɗe idanuwana a cikinta, sai na karya alƙadarin Maharaz. Sai kuma na nuna masa bakin rijiya, ba wurin wasan makaho ba ne. Ka zuba ido ka ga yadda za ta kaya tsakanina da su." 

 Boka Jassu ya ƙarasa kalamansa cikin cin alwashi, Bamaguje ya saki murmushin farinciki.


 "Sai kuma Umaima..." Boka Jassu ya furta.


 "Ka bar mini lamarin Umaima a hannuna Jassu, ni na san yadda zan yi da ita." 

 Boka Jassu ya jinjina kai, sannan suka ci gaba da ƙulla makirci cikin bushewar zuciya irin ta marasa imani. Daga ƙarshe Boka Jassu ya ƙara wa Bamaguje ƙarfin tsafi da sihiri sannan suka yi sallama zuciyarsa fal farinciki.


 Cikin kogon da Bamaguje ya kafe Basiru can ya koma, yana shiga ya same shi a ƙandare kamar yadda ya bar shi.

 Sai da ya zagaye shi kusan sau uku sannan ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya, ya jima yana yi sannan ya furta.


 "Yaro man kaza, ai na faɗa maka ta yaro kyau take ba ta ƙarko. Yanzu wa gari ya waya ɗan samari?" Basiru da yake jin sa a ƙandare ransa ya yi mugun ɓaci, sai dai ko yatsansa ya gagara motsawa.


Yawu Bamaguje ya tofar a ƙasa lokaci ɗaya wuta ta kama, ya ɗebo waɗansu itace ya zuba har sai da suka cinye suka zama gawayi. Ya ambaci sunan hatsabibin kogin Buzzar sau uku sannan ya zuba garin ya fara hura wa Basiru. Wata irin azaba yake ji tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa, a zabure ya taƙarƙare ya kwara wani irin azababben ihun azaba har sai da Bamaguje ya sa hannu ya toshe kunnensa. 


 Baƙin hayaki ne ya turnuƙe wurin da Basiru yake yana wata irin hajijiya, sai da aka ɗauki kusan minti biyar kamar ƙurar ba za ta lafa ba sai kuma komai ya washe.


 Bamaguje ne ya kai kallonsa kan tafkeken baƙin karen da ke sunkuye a gabansa, ya saka hannu ya fara shafa kansa yana murmushi ƙeta da zalinci.

 Da hannu Baaguje ya nuna masa hanyar wani ƙungurmin daji sannan ya ce.


 "Duk kiwon da za ka yi kada ka sake ka wuce dajin nan, idan ba haka ba a haɗuwarmu ta gaba hallakaka zan yi." 


 Bamaguje ya ɗauko garin Maganin da niyyar sake zubawa a cikin wutar, ganin haka ya sa Basiru da ke cikin surar Kare ya fita a guje saboda gudun azaba. Bamaguje ya saki dariyar ƙeta sannan ya daki ƙasa ya ɓace daga cikin kogon dutsen.


 Ƙauyen Sara


 Sallamar da Malam Bukar ya ji a ƙofar gida ya sa shi rife kwanan abincin da ke gabansa, sai da ya saka hularsa sannan ya nufi ƙofar gida. Turus ya yi ganin mai yin sallamar, sai kuma ya saki murnushi.


 "Yau a gari in ji maƙi baƙo Malam Bala? Ashe talaka na ganinku?" 

 Malam Bala ya saki murmushi ya ce.


 "Ga dai talakan ya kawo ziyara wurin masu yatsun zinare." 

 Miƙa masa hannu Malam Bukar ya yi suka gaisa sannan ya yi masa iso har cikin ɗakinsa da ke soron gidan.


 "Gaskiya ba ka da zumunci Malam Bala, rabonka da garin na ka fi shekara uku!" 

 "To ya za a yi Malam Bukar sabgogin ne sai a hankali." Malam Bala ya furta.


 Malam Bukar da Malam Bala abokai ne tun na yarinta, silar abokantakarsu ta samo asalin a makarantar allon da suka yi a wani gari mai suna Dile. Sun shaƙu sosai domin duk wata gwagwarmaya ta karatu tare suka sha, bayan sun yi sauka sai kowannensu ya kama gabansa. A haka suka ci gaba da ziyartar juna har girma ya cim musu. 


 Hirar yaushe gamo suka ɓalle da ita, suna cikin haka suka ji hayaniya a ƙofar gida. Da sauri malam Bukar ya fita, shi ma Malam Bala ya rufa masa baya.


 Matasa ne tsaye mutum biyu riƙe da da wata mata da ke kuka jini yana fita a ƙafarta, ganin haka ya sa gaban Malam Bukar ya faɗi.


 "Sani me ya faru da Faɗime?" 


 "Wallahi titi ta zo tsallakawa kawai wani mai mota ya bige ta, mun yi yinƙurin tsayar da shi amma ya gudu." 

 Ganin ƙwallar da ke fita daga idonta ya sa Malam Bukar ya girgiza kai cikin damuwa, yana riƙo hannunta ta fashe da kuka tana yi masa nuni da ƙafarta. A hankali ya riƙe ta suka shiga gida, hankali a tashe Inna ta riƙo ta tana rambayar abin da ya faru.


 "Ke Zainaba saka hijabinki maza ki kira mini Isa mai kemis." 

 Wacce aka kira da Zainab ta miƙe da sauri ta fice daga cikin gidan.


 "Ya aka yi kuka bari Faɗime ta fita daga gidan nan?" 

 Malam ya yi maganar rai a ɓace.

"Wallahi Malam ban ankara ba, fitowa ta daga banɗaki kenan."


 Suna nan tsaye Isa ya ƙaraso bayan ya ga ciwon da ta ji, ya koma Kemis ɗinsa ya taho da kayan aiki. Ba a ɗauki lokaci ba ya yi mata diresin, sannan Malam ya biya shi kuɗinsa ya yi masa sallama ya wuce.


 Malam ne ya yi wa Malam Bala iso ya shigo suka gaisa da Inna sannan suka koma turakarsa.

 "Waɗansu mutanen ba sa tsoron Allah, yanzu ka saka mota ka bige mutum kuma ka yi gaba, ta ya ya za mu zauna lafiya a ƙasar nan." Malam Bala ya faɗa cikin takaici.


 "Wallahi ka bari Malam Bala, yanzu wanda ya yi mata wannan abin haƙƙinta kaɗai ya ishe shi. Ko don yana ganin tana da rangwamen hankali oho?" 

 Cikin tausayawa Malam Bala ya ce.


 Malam Bala ya gurgiza kai cikin tausaya ya ce. "Abin kam babu daɗi sam, kuma da alama kamar tana jin jiki."

 Malam Bukar ya gyaɗa kai.

 "Lamarin baiwar Allahr nan akwai tausayawa, taɓin hankali gare ta ga shi kurma ce ba ta magana!" 

 Malam Bala ya jinjina kai ya ce.

 "Allah sarki, har ta ba ni tausayi. Allah Ya ba ta lafiya kuma ta jima da wannan lalurar?" 


"Labarinta yana da tsayi kuma cike yake da ban al'ajabi, kar dai na cikaka da magana fara da wannan." 

 Malam Bukar ya miƙa masa kwanon abincin da Inna ta kawo masa. Sun jima suna hira sannan Malam Bala ya ce zai yi masa sallama, suna tafe suna hira har cikin tasha ya raka shi.


 "Yanzu kuma idan ka tafi sai yaushe? Yau ma na tabbata gaisuwar mutuwa ce ta kawo ka, shi ya sa ka biyo ta gidana." 

 Malam Bala yana shirin yin magana, wata Dattijuwa ta katse su da yin sallama. Bayan sun amsa mata ta gaishe su, Malam Bukar ya kai dubansa kan wata matashiyar budurwa ya ce.


 "Na'imatu ya jikin?" 

 Wacce aka kira da Na'imatu ta ɗago ƙafarta ta ce. "Da sauƙi malam."


 "Malam jiki fa kullum ƙara kyau yake yi, Allah Ya saka da alheri. Bari mu ƙarasa gida mu jira ka." 

 Sai da suka wuce Malam Bala ya ce.


 "Abokina wai har yanzu kana bayar da taimakon ne?"


 Malam Bukar ya ce.

 "Muna ɗan taɓawa Malam Bukar, wannan yarinyar da kake gani Saurayi ne ya yi mata sihiri ƙafafuwanta suka shanye. Ka san wasu iyayen da ƙwadayi, sun gama cin kuɗinsa suka hana shi ita, to cikin ikon Allah kuma sai aka samu ƙafar da miƙe." 

 Malam Bala ya ce.

 "Allah Ya rufa asiri, ni kuwa ba don kar na yi karanbani ba ai da na samu Sarkin garinmu na kwaɗaita masa ko zai amince. Na jima da jin raɗe-raɗin makantar yaronsa Yarima sihiri aka yi masa, tun da shi ma lafiya ƙalau aka haife shi. Idan ka ga idanunsa fa ba za ka taɓa cewa makaho ba ne sai an faɗa maka, don a buɗe suke ras." 


 Malam Bukar ya yi jim sannan ya ce.

 "Komai fa zai iya faruwa ka san gidan Sarauta ya sha bambam da ragowar gidaje, ballantana masarautar garinku ka san ba kamar kowacce gidan sarauta ba ce." 

 Lokaci ɗaya suka saka dariya, Malam Bala ya ce.


 "Yau kuma tsiya za ka yi mana?" 


 "Yoo masarautar da jinsin Aljanu da mutane suke mulkarta ai ko me aka ce, ko aka gani a cikinta ba za a yi mamaki ba." Gabaɗaya suka saka dariya sannan suka yi sallama.


           ***

 Hawayen da ke gangarowa daga idanunta ta share, ta durƙusa a kan gwiwoyinta tana faɗin.

 "Don Allah Hajiya ki taimaka mini kamar yadda Allah ya taimake ki, Hajiya ko wanki ne ku ɗauke ni na dinga yi muku. Wallahi ni marainiya ce mahaifiya ba ta da ƙarfi yanzu haka ƙannena ne suke jinyarta." 

 Shiru Mami ta yi tana nazari sannan ta ce. 

 "Ban ƙi ɗaukarki aiki saboda komai ba, sai don ƙarancin shekarunki. Gani nake aikin da za a ba ki zai iya yi miki yawa..."

 Yarinyar ta share ƙwalla tana shirin magana Papa ya furta.


 "Ina ganin ko ba ta yi wanki ba, sai ta dinga ba wa flowers ruwa. Na lura tana buƙatar taimako." 

 Papa ya furta yana zama a kan kujerar da ke fuskantar yarinyar.


 "Alhaji ku fa kuke ganin yarinyar nan ba za ta iya ba, mu fa yaranmu na karkara ƙarfi gare su kamar shari'a, duk sa'o'inta tuni an kai su ɗaki har da masu haihuwa biyu."

 Dillaliya ta yi karaf ta fara yi wa Papa jawabi cikin jin daɗi, don ta san idan suka ɗauke ta ba ƙaramin alkairi za ta samu ba.

 "Shi kenan Papan yara yadda ka ce haka za a yi."

Mami ta amsawa Papa.

 Kallon da Papa yake yi wa yarinyar ya sa ta sunkuyar da kai ƙasa, tana cikin wasa da yatsun hannunta. Haka kawai ta ji tsikar jikinta na tashi, tana cikin haka ta ji muryarsa yana faɗin.


 "Ya sunanki!"

"Sunana Nafi!" 

 Yarinyar ta furta a sanyaye.

 Miƙewa Papa ya yi ya kira Mami ta bi bayansa, suna shiga ƙaramin falo ya ce.


 "Ki buɗe drowerta ki ba wa Dillaliyar nan dubu ɗari, ita kuma yarinyar sai mu dinga ba ta dubu hamsin duk wata." 

 Da mamaki Mami take bin Papa, don a sanin da ta yi masa duk 'yan aikin da take ɗauka ba ya shiga sabgarsu. Saboda shi ba shi da ra'ayin haka, musamman da ya kasance masu aikin da take ɗauka ba sa daɗewa suke guduwa ba tare da ta san dalili ba.


 "Lallai wannan yarinyar mai sa'a ce ta shigo da ƙafar dama."

 Mami ta faɗa tana murmushi, Daddy ya saki murmushin da shi kaɗai ya san dalilin yin sa sannan ya ce.

 "Na ji ta ce ita marainiya ce, sannan mahaifiyata tana jinya to kin ga tana buƙatar taimako ne." Cike da gamsuwa Mami ta jinjina kai, tana ta zabga masa godiya.

 Kamar yadda Papa ya ce haka Mami ta damƙa wa Dillaliya kuɗinta, ta kuma shaida mata duk wata za su dinga biyan Nafi dubu hamsin. Dillaliya tun da ta fara safarar 'yan aiki tsawon shekara goma, ba a taɓa yi mata alkairi irin wannan ba. Don haka ta zube ƙasa har da dafa ƙafar Mami tana zabga mata godiya, da za ta tafi ta gargaɗi Nafi da ko kaɗan ta kuskura ta yi laifin da suka kore ta idan wahala za ta kashe su, ba za ta sake nema musu gidan aiki ba. Kuma duk inda ta ji labarin za a nema musu gidan aiki sai ta soke shi, wannan tsoratarwar da Dillaliya ta yi wa Nafi ya sa ta shiga hankalinta sosai. Ta kuma ci alwashin yin aikin da za ta yi kan jiki kan ƙarfi.


 Yanayin da Rawiya take ji ne ya sa suna shiga babban falo ta wuce ɗakinsa, sanyi take ji sosai ga wani irin sara da kanta yake yi mata. Tana shiga ɗakinsu ta faɗa kan gado ta ja bargo ta kwanta, bacci ne ya fara fisgarta duk yadda ta so gudanar da sallar la'asar don dole ta haƙura ta kwanta.


 Daddy na komawa ɗakinsa ya zuba hannuwa biyu ya yi tugumi cikin damuwa. Babban tashin hankalinsa bai wuce shigar Rawiya cikin ƙungiya ba, a baya ya yi tsammanin bayan shigarsa cikin ƙungiya idan ya tara abin da ya samu zai rabu da ita. Ashe lissafin ba haka yake ba? Yana cikin haka ya ji wayarsa ta fara ƙara. Lambar ƙaninsa Mustafa ya gani, bayan ya ɗauka daga can ɓangaren a gaggauce aka furta.


 "Yaya dama jikin Baffa ne ya rikice yanzu haka mun wuce asibiti." 

A hargitse Papa ya furta.

 "Wanne asibitin ne?" 


 "Muna Al-Nur." 

 Papa yana jin haka ya katse wayar tare da shiryawa a gurguje, don dama kwana biyu kenan yana mafarkin mahaifinsa nasa. 


 Lokacin da ya ƙarasa asibitin an yi wa Baffa allurar bacci don jikin ya yi sauƙi sosai, ciwon sugarsa ne ya tashi amma cikin ikon Allah bayan taimakon likitoci sai jikin nasa ya yi kyau. Don haka bayan wani lokacin Papa da su Mami suka dawo gida.


Ranar Talata

 Ƙarfe biyun dare 2:00am


 Farfajiyar ƙungiyar cike take da mutane waɗanda suka haɗa farare da baƙaƙen fata. Sai da mafi yawa daga cikin ƙungiyar baƙaƙen fata ne daga mabambamtan ƙasashe, sai turawa suke bin bayansu sai kuma tsiraru daga cikin larabawa. Gabaɗaya sanye suke da dogayen riguna jajaye da baƙaƙen huluna, a jere suke sun yi sahu-sahu suna tafiya a hankali suka tunkari wata ƙorama. Ruwan ƙoramar Jawur yake kamar jini, suna zuwa gabansa suka kanfata suka yi kurɓa uku, sannan suka bi ta cikinta suka tunkari wata sassaƙaƙƙiya kuma tsafaffiyar gunki mai munin gaske. Ta baki da kunnuwanta take dalalar da jini mai yauƙi, jinin suka lakata suka shafa a goshinsu cikin haɗin baki suka furta.


 "Madogara!"


 Shugaba ne ya fito gabansu, sai da ya zagaye kowannesu sannan ya janyo hannun Papa ya zagaye gunkin da shi. Shugaba ya saka hannu ta saitin al'aurar gunkin haɗe da faɗin.


 "Ya ke madogarar wannan ƙungiya, a yau muna durƙushe gabanki da kuma yardarki domin naɗin zaƙaƙuran mambobinki zuwa mataki na gaba. Ƙungiya ta yi baƙin mambobi da za ta gabatar a gare ki, ya ke madogara mai rabon tarin arziki." Shugaba yana gama magana Gunkin ta ɓarke da wata irin dariya jini yana cigaba da dalala da yawa tamkar an buɗe famfo. Lokaci ɗaya ta yi shiru ta fara yin magana da murya marar daɗi cikin yarirrika daban-daban, daga haka har ta gangaro zuwa harshen hausa.


 Duk yaren da gunkin ta yi idan waɗanda suke jin yaren suna wurin sai su ƙarasa gabanta su yi gaisuwa, sannan su dangwali jinin gabanta su shafa a tsakiyar kansu.


 "Muna yi wa sababbin mambobi barka da zuwa, da fatan za a sanar da su dokokin ƙungiyarmu. Waɗanda suka samu ci gaba muna taya su murna, da fatan za su ci gaba da yi wa ƙungiya biyayya." Gunkin ta yi maganar da murya mara daɗin sauraro.


Tamkar gawa haka Rawiya ta yi tsaye tana bin mutanen wurin da kallo, domin tun da ta zo duniya wannan ne karo na farko da haka ya fara faruwa da ita. Abin da ya sake ɗaure mata kai, babu fuskar mutum ɗaya da ta sani a wurin. Abu ɗaya ta sani jini da ta gani ta kuma tabbatar da shi, musamman yadda karninsa ya cika mata hanci.


 Shugaba ne ya saka hannunsa a saitin al'aurar gunkin, ya zaro wata sihirtacciyar hular jini guda biyu. Kowacce da suna da lambar matsayin mutum, sai da su Papa suka hau kan waɗansu ƙasaitattun kujeru sannan Shugaba ya kafa musu hulunan a kansu. Lokacin ɗaya mutanen da suke wurin suka ɗauki tafi da sowa, suka shiga taya su Papa murna da fatan suma su samu irin wannan matsayin.


 Shugaba ya kamo hannun Rawiya da ke tsaye tana bin su da kallo, sai da ya kai ta gaban madogara sannan ya saluɓe mata kayan jikinta gaaɗaya, ya ɗauki wani ruwa mai yauƙi ya kwara mata. Tana tsaye kamar gunki ta gagara motsi ko kaɗan, Shugaba ya bata umarnin ta yi gaisuwa ga Madogara. Tamkar raƙumi da akala haka Rawiya take biye da duk abin da Shugaba ya ba ta umarni,bayan an gama yi mata wankan shiga ƙungiya Shugaba ya ɗauko wurin da Papa ya kai masa ya damƙa mata a hannu sannan ya yi mata raɗa a kunne. Yana ɗagowa Rawiya ya gyaɗa masa kai, ta ɗauki wata jar doguwar riga ta saka a jikinta. Haka kawai ta ji ta fara tafiya a saman iska, kamar wacce ta tashi sama. Ba a ɗauki lokaci ba ta isa Masarautar Huddam, kai tsaye ɗakin Yarima ta tunkara, a lokacin yana kwance yana bacci hankali kwance. A gefensa ta zauna ta ɗora hannunta na hagu a saman ƙirjinsa tana shafawa, jin haka ya sa Yarima Ramadan ya tashi a hankali haɗe da bin ta da kallon mamaki. Domin tun da lalurar makanta ta same shi ko hasken rana bai sake gani da ƙwayar idonsa ba, sai wannan matashiyar da ya ci karo da ita.


 "Wace ce ke?" 

 Yarima ya furta yana tsare ta manyan idanunsa.


 "Sunana Umaima."

 Rawiya ta furta tana sakin shu'umin murmushi, ganin kamar Yarima bai gane ba ya sa ta shafi gefen goshinsa da hannunta mai jini ta ce.

"Idan ba ka fahimci wace ce ni ba, ka tambayi tsohon Sarki Kamaludeen da mai ɗakinsa Jawahir." 

 Rawiya ta yi magana ita ma tana tsare shi da idanunta.



***

Ummou Aslam Bint Adam🌚

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol