Free chapter · Read without an account

39

by Kansa'u Bello · ALLON ƘADDARA

✨✨✨✨✨✨✨✨  

 _*ALLON ƘADDARA*_

        _*By*_

   *_OUM FATIMA_* 

_*(Hakimar D. A. W. A)*_

✨✨✨✨✨✨✨✨ 


     _*DASHEN🌲ALLAH*_ 

_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_


            _*TEAM*_

_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_





 *PAGE 39* 


_*بسم الله الر حمن الر حيم*_





**** "Ƙaraso mana Habebty". Cewar Ammy ganin na tsaya na kasa ƙarasowa. A natse na ƙarasa na zauna saman kujera. Ɗagowa nayi da nufin gaishesa na tsinci idanunsa na min wannan kallon da na saba gani daga gare shi, baki na tsuke na tura shi gaba ina mitar 'ni me nayi masa to'. Kansa ya ɗauke yana kaɗa kai a ransa yake faɗin "rigimammiya". 


Cikin natsuwa da matuƙar girmamawa ya gaishe da Ammy da tambayarta ya mai jiki. Cike da kulawa ta amsa masa tana cewa "Jiki Alhamdulillah ai ta ware sai dai son jiki irin nata".


Kallonsa ya dawo dashi saman fuskarta irin wai hakan ɗin nan. Fuska na shagwaɓe kamar zan saka kuka yayi saurin kaɗa min kai alamar kar nayi.


"Kinga ni bani wuri in wuce, na rasa yaushe zaki san kin girma". Ammy ta faɗa tana mikewa ta nufi ƙofar da zata kaita ɗakin Baba Malam.


"Good morning Hammah". Na faɗa a hankali ina kallon fuskarsa da tayi wani shar da ita tana fitar da annuri kwarjininsa da haibarsa na cika min ido.


"Kin tashi lafiya Mamyn Little, ya jikin?". Ya tambaya yana tsare fuskata da kallo. Wani irin huruwa naji kaina yayi jin ya Kirani Mamyn Little. Lokaci ɗaya kuma na kwaɓe fuska zan saka masa kukan da baya so. "Menene?" Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya a hankali.


"Bayan an nuna min fin ƙarfi an kwace min ita!". Na faɗa har zuciyata hawaye na zubo min. A natsensa ya taso ya zo kusa dani ya zauna, hannu ya saka ya riko nawa ya sarƙe wuri ɗaya kafin ya fara magana cikin natsuwa da kamewarsa yace "Kinga ya isa haka kar kiyi kuka kinji, ba wanda zai ƙwace maki ƴarki ni da kaina zan kawo maki ita amma ba yanzu ba sai ta ƙara wayo, ai Kinga yanzu jaririyace bazaki iya kulawa da ita bako?". Ya ƙare maganar cikin lallashi da sigar tambaya.


Da sauri na gir-giza kaina ina cewa "A'a Ni dai a kawo min ita haka zan iya kula da ita".


"To shikenan naji amma sai kin daina rigima sannan, kuma sai kin koma Gidanki sannan, ai haka yayi ko?". Shiru nayi na ɗan wani lokaci sai kuma na ɗaga masa kai alamar na yarda.


"Ok to muje ki bani breakfast ana jirana Asibiti". Tashi nayi na ƙara sa table na haɗa masa breakfast muka yi tare kafin ya fice ya nufi Asibiti, ni kuma na shiga tattare kayan da muka ɓata na shiga wankewa a kiching mai taya Ammy aiki na gyaran kiching ɗin.





✨✨✨✨




Kamar wasa alaƙa mai ƙarfi ta fara shiga tsakanin Alhaji Bilal da Samha, sau biyu hanya na ƙara haɗa su bayan sauketan da yayi ranar da Motarta ta samu matsala. Haduwarsu ta biyu a Companynsa taje amsar wasu bayanai da aka turata daga Office ɗin maneger, har ta gama abinda ya kawota ta fito zata wuce suka haɗu dashi. Shigowarsa kenan ya ganta tana ƙoƙarin shiga Motarta.


Da kansa ya ƙarasa suka gaisa cike da mutunta juna, anan ne ya amshi Number wayarta da nufin su riƙa gaisawa. Tun wannan lokacin yake ɗan kiranta suna gaisawa kaɗan kaɗan har shaƙuwa mai ƙarfi ta fara shiga tsakanin su ba tare da sun farga ba.


Samha Mace ce mai kirki da iya mua'amala da Mutane, sannan tana da nuna kulawa akan wanda ke tare da ita. Da waɗannan ɗabi'un nata ne ta fara kama zuciyar Alhaji Bilal har yaji zai iya yin rayuwa da ita idan har zata amince masa.


Bai fito Ya faɗa mata cewar yana sonta ba amma duk wasu alamomi dake nuna hakan ya bayyana mata su. Itama har zuciyata taji yana burgeta kuma zata iya rayuwa da shi matuƙar ya bukaci hakan, don haka yau bayan ta tashi daga wurin aiki ta wuce Gidansu Hanan sabo da tana buƙatar yin magana da ita.



**** "Sai yau nake ganinki Samha anya kuwa da amana". Na faɗa ina hararar Samha wacce shigowarta kenan cikin parlourn Ammy da muke zaune ni da Aunty Ade da ta tsare ni sai na cinye dahuwa kazar da tayi min yau ga kuma ƙaton galan cike da tsimin sassaƙen ɓaure da yaji zuma da mazarƙwaila sai tashin ƙamshin kanumfari yake yi.


Gaba ɗaya a kwanakin abinda take min kenan don yau cewa tayi sai na shanye wannan galan ɗin duka maganin sanyi ne da rana. To sauƙin dana samu ma shine abin zaƙi gare shi ga ƙamshi shi yasa nayi ta banka babu musu.


Zama tayi kusa dani tana gaishe da Aunty Ade dake kwaɓa wani haɗin dilkar da zata min amfani da dare. Cikin sakin fuska ta amsa tana tambayata aiki da kuma Mutanen Gida, Ammy dake kiching tana haɗa dinner ce ta fito suka gaisa kafin na miƙe muka nufi ɗakina don mu tattauna domin naga kamar da magana a bakinta.


"Aminiya wata magana mai muhimmanci da ta shafi rayuwata nake so mu tattauna dake". 



"To ina jinki, mai ke faruwa?". Na faɗa ina kallonta.


Tun daga haɗuwrsu ta farko da Alhaji Bilal, da alaƙar dake tsakaninsu har zuwa yanzu ta faɗa mata komai sannan ta ƙara da faɗin. "Shawara nake so ki bani tun kafin ya tare ni da maganar in rasa amsar bashi, don yace gobe zai zo min da magana mai muhimmanci. Harga Allah zuciyata ta samu natsuwa dashi naji zan iya rayuwa dashi ko ba komai zan rage masa raɗaɗin rashin da yayi tunda Kinga nima ba wanda na tsayar a matsayin Miji, dama kuma Abba yayi maganar na fito da wanda nake so, nayi addu'a na nemi zaɓin Allah sai gashi ya haɗani da wanda ban yi tsammani ba, amma yaya kike gani?". Ta ƙare maganar tana kallon ƙasa kamar mai jin kunyata.


Murmushi na saki nasaka hannu na ɗago fuskarta ina dafa kafaɗarta nace "Yau kuma surukarki na zama hala, kike wani sunkuyar da kai!". Na ƙare maganar cikin sigar tsokana. "Ba haka bane Hanan kawai sai naji ina jin kunyar ki ne, sai dai kin san bani da wacce zan iya yin wannan maganar bayan ke". Ta faɗa tana kallona.


Ajiyar zuciya na sauke kafin nace "Kar ki wani ji kunya ko nauyi na don kinso Alhaji Bilal, Allah ne bai ƙaddara aure na dashi ba. Don munyi soyayya dashi hakan ba zai hana ki soshi ba ko shima ya soki sabo da kina ƙawata ba, Zanyi matuƙar farin cikin kasancewar hakan Samha domin kuwa kun dace da juna keda Alhaji Bilal sabo da mutumin kirki ne da ya samu sheda a wurin mutane, samun sheda da karɓuwar da yayi a wurin Iyayena yasa na bashi dama na fara kulashi. A hankali yayi amfani da kyawawan halayensa da kyautatawa da nuna min kulawa har na amince zanyi rayuwa da shi, sai dai Allah bai nufi hakan ba. Ba zan ce maki banji komai ba lokacin da akace ya fasa aurena ba sabo da ban zaci hakan ba, sai dai daga baya mun fahimci juna mun kuma yima juna uzuri. Na amshi zaɓin da Allah yayi min na kuma gode masa, shi kuma na masa fatan alkairi kamar yanda yayi min. A halin yanzu babu komai a zuciyata game da shi, don haka ina tayaki farin cikin samun nagartaccen mutum, ina muku addu'ar Allah ya tabbatar da alkairi a cikin alaƙarku. Daga karshe ina baki shawara kiyi addu'a ki nemi zaɓin Allah matuƙar kika ji natsuwa a zuciyarki game da al'amarin kar kiyi wasa da damarki. Sannan don Allah ki kula da shi tsakaniki da Allah, duk da bai taɓa faɗa min matsalar da yake fuskanta a Gidansa ba ni da kaina na fuskanci wasu da kuma magan-ganun da suka yi ta yawo Lokacin neman aurena. Sabo da haka ki zame masa canjin alkairin da yake nema". Na ƙare maganar ina dafa kafaɗarta.



"Na gode sosai da shawarar da kika bani Hanan, kuma in sha Allah zan yi addu'a kamar yanda kika Allah ya saka da alkairi ya bar zumunci".


"Ameen ya Allah". Na faɗa mata muka shiga wata hirar. "Wai yaushe zaki tare ne?". Samha ta tambaya.


"Ke ba fa wani abu za'a ƙara yiba, naji dai ance ran Friday zai zo mu tafi". Na faɗa cikin sanyin jikin daya zo min na lokaci ɗaya da maganar tafiya na bar Gida.


Sai bayan magriba Na rako Samha har wurin Motarta ta wuce ni kuma na koma ciki.




★★★



Washe gari ya kama saura kwana biyu tafiyata kamar yanda aka faɗa min, tun da safe Aunty Ade tazo da mai lalle da kitso, bayan an gyara gashin an wanke sa da hadaɗun mayuka da turaruka. An yi min wanki ƙafa da gyaran farata aka yi zaman tsara min ƙananun kitso da ba'a taɓa min irinsu ba tunda nake sabo da ni dai Allahn da yayi ni bana son kitso, na fi son inje a wanke min shi in ɗaure. Sai kuma manyan Kalba da ake min wasu lokutan.


"Masha Allah!". Kowa ke faɗa lokacin da aka gama tsara min kitson ya sauko har saman bayana yana sheƙin mai da tashin ƙamshi.


Sallah da cin abinci mukayi aka yi zaman zana min hadaɗden lalle ja da baƙi da yayi matuƙar haska farar fatata yayi min masifar kyau, har bakin mutane ya kasa rufuwa. Jan yayi kamu sosai har maroon yake, ni kaina kasa ɗauke idanuna nayi akan lallen haka nayi ta safa shi ina murmushi.


Sai dai fa nasha zama don sai da na kusa kuka Aunty ta bari aka cire shi, don haka a gajiye nake ina sallar Isha'i naci abinci na kwanta barci ban ko bi ta kan tashin da Aunty ke min ba akan in tashi insha wanan in ci wancan nayi baccina na ƙyaleta tana ta mitarta.




★★★ 




Washe gari aka je Gidan Hamma Jabeer da yasha gyara kamar bashiba, gaba ɗaya aka fitar da komai aka zuba min haɗaɗdun furnitures ɗina da suka amsa sunansu. Duka ɗakunan dake sama da ƙasa sai da aka zuba min tsadaddun gadaje da duk abinda ake ƙawata ɗakin ƴargata dashi, haka ma duk parlourn aka ƙawatasu da duk wani nau'in kaya da ake ƙawata parlour dasu.


Kiching ɗin dake sama da ƙasa duk suma an zuba sabbin kayan amfani, lokaci ɗaya Gida ya ɗauki kala da wal-walin sabbin kaya sai tashin daddaɗan ƙamshin turarukana da aka baɗe ko ina dashi ke tashi.


Sosai Ammy ta zuba maƙudan kuɗaɗe wurin zuba min tsadaddun kayan da suka ƙara motsa hassadar masu haddasa. Iya kuɗin da ta kashe wurin haɗa min kayan ƙamshi irin su kumrah da turarukan wuta kaɗai ba kaɗan bane, duk wani abu da akewa ƴargatan da ta amsa sunan gata Ammy da Baba Malam sun yi min sai, ba abinda zance sai dai in tayi musu addu'a da fatan gamawa da duniya lafiya.


Lokacin da Companyn da aka ɗauka suka gama shirya gidan sai Masha Allah kawai ke tashi daga bakin su Aunty Ade da suka kula da aikin.


Lokacin da suka dawo Gida kuwa ana bada labarin haɗuwar da Gidan yayi sai baƙin ciki ya kusa halaka Momy da Hajiya Mama da a wannan karin ta kasa ɓoye hassadarta itama ta biyewa Momy suka riƙa yada magan-ganu, sabo da duka yaranta biyu da ta aurar babu wacce ta samu wanda ya ko kusa kama ƙafar Jabeer ne bare kamo shi. Ga maganar yanda aka yiwa Hanan kayan da ba wanda aka kwatanta yiwa su a Gidan gaba ɗaya.


Don haka suka riƙa yada magana cewar Ammy don tayi fariya ne tayi hakan kuma a banza da ba'a san asalin balbela bane shine zata ɗagawa mutane kai. Ai kowa ya san ubanta a matsiyacinsa ya shigo Kano dukiyar da take tutiya da alfaharin da ita a wurin masoyin da aka mata fin ƙarfi akaci amanarta aka sameta ba gadon iyaye bane.


Wannan karin maganar tayiwa Ammy matuƙar ciwon da ta kasa shanyewa har sai da ta maidawa Momy martani, kiran Iyayenta matsiyata da tayi yayi mata ciwo sosai har ta zubar da hayawe.


Abinda bata taɓa yiba shi tayi yau don har sashin Momy taje ta gasa mata baƙaƙen magan-ganun da Aunty Ade tayi mamakin fitowarsu daga bakin Ammy, kowa sai da yayi mamaki don tunda aka san rashin jituwar dake tsakaninsu a gidan ba'a taɓa ganin Ammy ta biyewa Momy koda maida maganar baki ne ba sai yau da ta ƙuere haƙurinta ta iskota har inda take ta maida mata zazzafan martanin da yasa ta raina kanta.


"Ke kin san duk abinda kike min nake ɗauke kai ba tsoronki nake jiba Habiba ina duba girman amintar da muka tashi da ita da kuma amincin dake tsakanin Iyayenmu, sannan ina yi maki uzuri da tunanin wata rana zaki san kin girma ki daina wannan dabbacin da kike, amma sai naga alamar kullum ƙara cin ƙasa kike yi har yanzu baki san Allah ɗaya bane, zan ja kunnenki ne da babbar murya duk iya irin rashin mutuncin da zaki ɗebo ki sauke shi iya ni da Habebty zan iya ɗaga maki ƙafa, amma Iyayena dake kwance cikin ƙasa koda wasa ƙar haukanki yasa ki ƙara ƙoƙarin faɗar bakar magana a kansu bare zagi, kika kuma abin ba zai mana kyauba, sannan duk abinda kike faɗar nayi maki to nayi ɗin kiyi duk abinda zaki iya, maganar ƙwacen saurayi da kike shi ya gani ya nace bani na tallata kaina ba, Macen da ta isa ita ke ƙwacen saurayi a hannun ballagazar Mace, duk abinda kike ji dashi dai-dai nake dashi domin kin isheni, baba don Allah wannan wace irin jarabace abu yaƙi wucewa a rayuwa!". Ammy ta ƙara sa cikin fusatar da ba'a taɓa gani daga gareta ba tayi gaba ita da ƴar'uwarta da take binta da kallon mamaki, nan suka bar Momy da sakakken baki ita da Hajiya Mama da sauran waɗanda aka yi abin a gabansu da Mamy Sakina dake ta kumfar baki.


"Caɓdi! Lallai Yaya ashe dama kin iya masifa kika bar matarcen take hawa maki kai?'. Aunty Ade ta faɗa cike da jin daɗin yau ƴar'uwarta ta ƙwatar wa kanta ƴanci.


Kin kulata Ammy tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya har yanzu ranta a ɓace yake. Duk abinnan dake faruwa ina ɗakina ina barci ban sani ba sai da na tashi Aunty ke bani labari.



 *Oum* *Fatima*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol