Free chapter · Read without an account
45
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*ALLON ƘADDARA*_
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*PAGE 45*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
***** Kamar yanda Hajjo ta umarci Abba yaje ya maido Momy yau yayi hakan, da farko da ya samu Mahaifinta yayi masa bayanin yanda sukayi da Hajjo cewa yayi "Ai da an barta tukun ta ƙara sanin rayuwa duk da dai jiya da kanta tazo ta bani haƙuri ta roƙeni akan in baka haƙuri, da alama tayi nadama kamar yanda ta faɗa ta kuma yi alƙawarin bazata sake mai-maita wannan kuskuren ba, shikenan zaku iya tafiya Allah ya tsare gaba in sha Allah da kaina zan zo Gidan in haɗa su da ƴar'uwar tata in yi musu nasiha". Babansu ya faɗa.
"Bi komai Baba Allah ya taimaka".
"Ameen bari in kirata". Ya faɗa yana miƙewa ya nufi cikin Gidan, Mamansu yace taje ta kirawo masa ita. Nasiha sosai ya ƙara mata da ƙwaƙwƙwaran gargaɗi kafin ya sallame ta suka wuce ita da Abba da tunda ya amsa gaisuwarta bai sake kallon inda take ba, hakan kuwa ba ƙaramin damunta yayi ba, don sai kallonsa take tana ƙara wa har suka isa Gida.
Suna zuwa ya fice ya barta a Motar yayi shigewarsa, haka ta fito jiki a sanyaye tabi bayansa ko zarafin amsa gaisuwar da ma'aikatan Gidan keyi mata bata tsaya ba ta shige.
Har ɗakinsa ta bishi ta bashi haƙuri cikin sauke kai abinda bata taɓa yiba tsawon zamansu tayi masa laifi ta amsa tayi har ta bashi haƙuri sai a wannan karon, wanda sosai hakan ya bashi mamaki ya taɓa shi.
Akace tsakanin Mata da Mijinta sai Allah nan take tausayinta ya kama shi ganin yanda take kuka ya. Rungumeta yayi yace "Ya isa haka komai ya wuce sai a kiyaye gaba". Godiya ta masa sosai daga nan komai ya wuce suka dai-daita tsakaninsu.
****** Satin Hamma Jabeer ɗaya a Gida bai fita aiki ba sai dai ko Asibiti idan ta kama dole ana nemansa yake zuwa, sai kuma Gida da yake zuwa gaishe da Iyayensa. A tsawon satin da mukayi tare bai sake zuwa gareni ba sai dai tsantsar kulawa da yake nuna min, gaba ɗaya ya gama lalatani da zama a jikinsa ko mai yake ina lafe a jikinsa kamar wata mage.
Har wata ƙiba na ƙara nayi wani Fresh dani, tare muke yin gyaran Gida da yake iya sama nake gyarawa ƙasa akwai mai zuwa tayi share-share da goge-goge. Compound kuma dama akwai ma'aikata dake kula da komai.
Ko girki tare muke yi zan iya cewa ban taɓa samun yanayin da naji daɗinsa sosai irin wannan da na samu ba. Don haka nayi wuri na aje shi a cikin sweet memoryna.
Samha tazo ta yinar min kamar yanda ta faɗa mun shirya tsare-tsaren da zamuyi, ni da ita duk bamu da wasu tarkacen ƙawaye don haka ba wata gayyata zamuyi ba iya abokan aikinmu ne sai waɗanda baza a rasa ba. Anisa na kira muka haɗu muka tsara duk abinda ya kamata, maganar kuɗi bamu da matsala da su don Angonnata ya buɗe mana bakin aljihu.
Don haka muka yi shiri sosai duk da dai ni bana fita iyaka mu tsara su fita ita da Anisa da Asiya da suka jone tun bikina na farko da akayi.
★★★
Yau Monday Hammah zai koma aiki don haka tunda asuba muna yin Sallah ban koma ba na shiga gyaran Gidan ko ina a sama sai da na gyara na baza ƙamshi kafin na faɗa kiching nayi mana lafiyayyen breakfast na jere a table na shiga wanka.
Wanka nayi sosai na wanke ko ina yanda ya kamata ta fito na tsara kwalliyata cikin wata dakakkiyar shadda ɗinkin Nijer irin wanda ake ɓuɗe rigar tun daga sama har ƙasa aka zuba mata aiki. Ɗauri na kashe ya zauna ɗas na saka ƙaramar sarkar zinari da ƴankunnenta da awarwaro na baza turare nan da nan ƙamshi ya baza ɗakin na fito a amaryata sak, ni kaina dana kalli madubi sai da na sake murmushi na ciro wayata na fara kashe selfie.
Ina cikin ɗaukar hoton ne azababben ƙamshinsa ya fara gauraye hancina don haka na dakata ina zubawa ƙafa ido, a hankali ya shiga takowa yana tsarkake sunan Allahan da yayi masa kyautar wannan tsadaddiyar halittar da ta kasance kyakykyawa gwanar iya tsara ado.
Rungumeta kawai yayi sosai yana sauke ajiyar zuciya ya furta "Barakallah, Masha Allah Sofy kinyi kyau kamar kar na fita na zauna nayi ta kallonki". Ya faɗa lokancin da ya ɗagota daga jikinsa yana kallon fuskarta.
"To kayi zamanka kawai Hammah nima nayi ta kallonka domin bana son kowacce Mace taga wannan kwalliyar!". Na faɗa ina tura baki gaba cikin shagwaɓar da ta kusa tsiyayar da man kansa.
Ai kuwa saƙon da ta tura ya je fiye da inda ta aika shi don sai da ya kusa loosing balance ya dafe mirror da kyar basu faɗi ba ta faɗo kansa yayi mata kyakykyawan riƙo.
"Kar ki karasa bawan Allah Iyalin Jabeer!!". Ya faɗa yana lumashe ido yana buɗewa.
"Muje na baka breakfast kar kayi letti". Na faɗa ina juya manyan idanuna da gayya nayi don jan magana. Ai kuwa abin ya taɓasa ba kaɗan ba don kasa jurewa sai da ya janyo ta ya haɗe bakinsu wuri ɗaya ya fara bata tsaftatsccen kis irin wanda ba'awa ƙazamai.
Luf nayi ina karɓar zazzafan darasin daya ke koyar dani. Dan kansa ya sakeni ya kama hannuna muka sauka ƙasa, saman table muka ƙarasa ina ta sunkuyar da kai sabo da kunyar da ya bani.
Yana ankare da yanda ta kasa haɗa ido da shi sai dai yayi murmushi a ransa ya furta 'Ashe da sauranki yarinya'.
Chips and eggs nayi mana sai lafiyayyen tea da na dafa yaji kayan ƙamshi sai bread mai laushi don haka nayi serving ɗinmu muka fara ci cikin natsuwa. Sai da muka kammala kafin na rakasa har ƙofa ya tafi bayan ya rungumeni ya sumbaci goshina. "Take very good care of your self". Ya faɗa yana min wani irin kallo. "Take care too". Na faɗa masa ina shagwaɓe fuska kamar zan yi kuka don Allah ya sani bana son ya tafi ya bar ni sai dai ba yanda zanyi dole ya fita aiki.
Yana tafiya na haye sama na kwanta don rama barcin safe da ban samu damar yi ba tunda ni sai wani satin zan koma aiki.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
An ɗaura auren Samha da Alhaji Bilal a ranar da aka saka shi wanda sai bayan ɗaura auren ne Alhaji Mahmud da sauran ƴan'uwansa suka je suka samu Mahaifiyarsu cikin hikima da rarrashi suka sanar da ita, da farko rikici tasa musu akan an raina ta an munafunceta don haka sai dai ya saketa yanzu tun kan Aliya taji azo a samu matsala.
Da ƙyar da nasiha da rarrashi suka nuna mata illar hakan ta haƙura da maganar sakin, Mahaifin Aliya da kansa yace zai sanar da ita. "Amma fa ka bita a hankali kar ka sake kace zaka matsa mata". Hajiya Asma'u ta faɗa tana kallon Mahaifin Aliya.
"In sha Allah Hajiya za'a yi kamar yanda kike so". Da wannan suka samu aka wuce wurin aka shiga hidimar biki da shirin tarbar Amarya.
**** A ɓangaren Amarya bikinmu mukayi abinmu cikin aji da wayewa ba wani shirme, bridal shower mukayi ranar Alhamis iya Mata a cikin Gidansu. Hamma Jabeer da kansa ya kaini duk da kuwa aikin da ya sha masa kai amma haka ya kaini da dare kuma yaje ya ɗauko ni.
Washegari mukayi ƙayatacciyar Walima wacce aka shirya a Gidan dai itama aka gudanar, manyan Malamai Mata aka gayyato suka ragargaji wa'azi aka raba kyautuka aka tashi cikin farin ciki.
A gajiye yau na koma Gida ina ta yi wa Hammah shagwaɓa da mitar gajiyar da nayi yana ta lallaɓani har mukaje Gida, da kansa ya shiga ya haɗa min ruwan ɗumi ya taimaka min na gasa jikina nayi wanka. Ina yin Sallah na ɓingire barci saman abin Sallar ko abinci da ƙyar ya samu ya naci kaɗan ina layi na kwanta.
★ washe gari Assabar ɗaurin aure da yake weekend ne Hamma Jabeer baya fita sai ta kama, don haka muka yi barci sosai kafin mu tashi. A gur-guje nayi mana breakfast muka karya na shiga shiri don miss Call rututu na Samha da su Anisa na tarar.
Shiryawa nayi cikin wata dakakkiyar shadda Coffee colour da taji ɗinkin da ya dace da ita, tsayawa faɗa muku kyan da nayi ma ɓata baki ne ku hango yanda Hanan ɗinku zata kasance kawai idan ta ɗauki wanka. Duk wani abinda zan buƙata na saka a jaka na fito na nufi ɗakinsa cikin sauri ina amsa wayar Anisa da ta kira ni.
Samunsa nayi shima ya gama shiri cikin wani tsadadden farin yadi daya masa kyau ya fitar da kwarjininsa, komai Hamma Jabeer ya saka kyau yake masa. Shi yasa a kwanakinnan in naga yayi kyau sosai ya fita sai inji ina baƙin cikin ƴan'mata su ganshi.
Kwalliyata ya yaba sosai kamar ko yaushe ya ɗora da sanar dani yana kishin wasu su ganni, nima yaba tasa nayi nace masa muje ya kaini ana jirana.
Tafiya muka yi bayan na yafa babban mayafina daya shiga da kayan jikina, muna tsayawa ya amshi jakata ya zuba min kuɗi masu yawa kafin ya wuce bayan ya shaida min cewar in kula da kaina.
Ciki na shige shi kuma ya nufi can Gidanmu. A compound na haɗu da Anisa ta fito tana amsa wayar saurayinta don haka tare muka ƙarasa tana ta min mitar wai ni daɗi Miji shine nayi ƙus a Gida naƙi fitowa.
"Ke da Allah bazaki gane bane kawai muje, ina amaryar?". Na faɗa ina mata murmushin tsokana. Ai kuwa ta hau don mita ta fara tana faɗar. "Iye! Wato bazan gane ba, kaga manya Matan aure to muma Allah kasamu daga cikin nan ko zamu gane". Ta faɗa tana kai min ƙaramin duka. Dariya mukayi gaba ɗaya muka ƙarasa part ɗin da Samha ke yini.
Itama ina zuwa mitar ta fara yi, haƙuri kawai na bata na fito na shiga can part ɗin Mahaifiyarta muka gaisa nayi mata barka na aje mata bundir ɗin 1k nace a sayawa amarya turaren wuta. Sosai taji daɗi tayi ta sa ma ƙawancenmu albarka, fita nayi na koma muka ci gaba da yinin binmu muna ta tarbar baƙi ƙawayenmu da abokan aikinmu.
Da azahar bayan munyi Sallah nayiwa amarya make up mai tsari da ta dace da fuskarta, sai su Anisa da suka dage sai da nayi musu kafin nima na tsara tawa kwalliyar daya tashi kawunansu na shirya cikin wani tsadadden Leshi muka fito ana kashe mana pictures kafin anguna su shigo aka riƙa yi musu tare da amare.
A lokacin muka haɗu da Alhaji Bilal tun bayan rabuwarmu, gaisawa muka yi na masa murna nayi gaba abina yana bina da kallo. Ciki na koma sabo da gargaɗin da Hammah yayi min.
Biki yaci gaba da tafiya cikin farin ciki da birgewa har aka yi Sallar magrib aka zo ɗaukar amarya, Hammanah na kira nace masa zamu raka amarya Gidanta yace in jira shi.
Ai kuwa ba'afi mintuna goma ba ya ƙara so ya ɗaukeni, su Anisa kuwa abokan ango suka ɗauke su muka rakata ƙaton Gidan Mijinta daya sha gyara, part ɗinta na kusa dana Matarsa wanda shima upstair ne. Tuni an shirya mata kayanta don haka amarya kawai muka saka sai muna gab da fitowa Matarsa ta dawo daga gantalinta ta fara mana hauka....
Kuyi haƙurin jina shiru ina fama da zazzaɓi ne ku sani cikin addu'oinku.
*Oum Fatima*