Free chapter · Read without an account
21&22
Follow the 💖 A'ISHA M.B✍️ HAUSA NOVELS 📚 WORLD 🌎 📚💗💖 channel on WhatsApp: ***
*🔥KUNDIN CINIKAYYA*🌎 *(Three siblings from different part in the world)*🪐🌎🪐.
Daji 🌲
Magarƙama🏢 da kuma
Birni🏙️
WRITTEN & DIRECTED BY ✍️ A'ISHA M.B 💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)
***
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*DIAMOND 💎 STAR⭐*
*LADIES 🧝♀️🧝🏼♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
بسم الله الرحمن الرحيم
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai!
*🔥KUNDIN CINIKAYYA* *🌎 PAGE 2️⃣1️⃣▶️2️⃣2️⃣
*_________________________________________________*
Nan take cikin Gov. Musa Muhammad ya ɗuri ruwa. Katse wayar ya yi yana mai faɗin.
"Tabbas in dai da gaske tana a raye ba za ta barni na cika ƙudiri na ba, ga shi zaɓe ya kusan gaba to wa, ya zama dole nayi wani abu".
Nan take wani dabara ya faɗo masa. Ɗaukar wayar sa ya yi tare da shiga cikin contact list, nan ya lalubo wata number wanda aka rubuta Aliyu a jiki.
Kiran wayar ya fara yi amma tana ba shi switch off. Wurgar da wayar Gov. Musa Muhammad ya yi ya ce. "Pick up Aliyu! Pick up. I need your help urgently please". Aka yake ta faman magana shi ɗaya.
********
Ɓangaren su Aliyu kuwa, har an shirya musu visa sun shiga jirgi sannan suka kashe wayoyin su. Kowa na cikin jirgin su suke kallo ganin Safeera a goye bayan Mom kamar ƙaramar yarinya.
Ganin cewa kowanen mutum a jirgin su yake kallo ya sa Aliyu faɗin. "We should all concentrate on something necessary please". Ya faɗa tare da ɗaura seat belt. Jin hakan ya sa kowa ya kawar da kansa. Nan take aka sannan cewa kowa ya kasance a shirye sannan kowa ya saka seat belt tare da kashe wayoyi domin jirgi zai tashi.
Saida kowa ya kammala sannan jirgin su ya tashi.
*************
"Wai ke ƴar gidan wace ce?, daga gani ma daga magarƙama ki ka fito domin kuwa wannan kayan ƴan magarƙama ne sanye a jikin ki".
Murmushi Zahra ta yi ta ce. "Wannan ba abin da ya shafe ka ba ne, idan ma hakan ne mene ne naka a ciki, kada ka ce za ka faɗa min magana wanda raina baya so".
Kallonta yariman ya yi ya ce. "Kada ki manta fa Kano ki ka shigo, kano ko da me ka zo an fika. Don aka ki ajiye wannan jiji da kan naki domin kuwa ba za ta yi miki amfani a nan Kano ba".
Kallonsa Zahra ta yi tare da sakin wani miskilin murmushi sannan ta ce. "Au aba da gaske?, kenen dai ko da hauka na zo an fini ko?. Ka sani cewa ni Zahra ce, kuma ba'a haifi wanda zanji tsoron sa ba, bayan ma'halicci na sai fiyayyen halitta. Don aka ka matsa domin bani da lokacin ɓata wa".
Zuwa ya yi daff da ita sannan ya ce. "Idan na ƙi fa?, me za ki yi?".
Kallon cikin idanuwansa Zahra ta yi sannan ta mayar masa da martani da cewa. "zan yi maka sambaɗe-baɗe, zan yi maka dukan da gaba ɗaya masarautar ku sai an gagara gane ka". Ta faɗa tana mai ƙoƙarin wuce wa ta gefen shi.
Babu zato ta ji ya janyo hannunta tare da janyo ta jikinsa.
Zaro idanuwa Zahra ta yi waje, nan take ta kurma ihuuu! tana mai faɗin. "Kai ɗan iska ne?, wato dama kai dan iska ne ko?, ni ƙanwar ka ce da za ka jawo ni jikin ka?, maza ka sake ni kafin nayi maka abin da ba za ka ji dad'i sa ba".
Matse hannunta yarima ya sake yi a karo na biyu sanann ya ce. "Ba zan saki ba".
Duk abin da ke faruwa a gaban idanuwan jama'an da ke wajan.
Nan take fadawa suka shigo tare da ƙwace Zahra daga hannun yarima sannan ɗaya daga cikin su ya ce. "Ranka shi daɗe, mai maryaba ya umarci da mu dawo da kai gida yanzu, ya kamata ka tawo mu bar nan wajan".
Ɗaga musu hannu ya yi ya ce. "Naji shi ke nen". Maida kallonsa ya yi kan Zahra ya ce. "Ke kuma, muddin ki ka bari muka sake haɗuwa saina hukunta ki bisa raina ni da ki ka yi".
Gwalo Zahra ta yi masa ta ce. "Kaje ka ji da abin da ke damun ka malam yarima mai ɗagaggen wando". Ta faɗa tana mai kwashe wa da dariya.
Kare shi fadawan suka dinga yi har suka isa bakin mota. Shiga ciki gaba ɗaya suka yi tare da barin harabar wajan.
Murmushi Zahra ta yi ganin cewar ta yi nasaran zaran wasu kuɗaɗe a aljihun yarima tare da wani ɗan ƙaramin maƙulli. Saka maƙullin ta yi a cikin aljihun ta. Maida kallonta zahra ta yi kan ma'aikata tare da jama'ar wajan sannan ta ce. "To ku ta shi mana, kun wani durƙusa ƙasa kamar masu bara. Shi da mutum ne kamar kowa amma shi ne ku ke ba shi wani girmama wa har kuna durƙusawa ƙasa saboda mutum ɗan adam irin ku, tirr gaskiya kun bani kunya".
Miƙe wa gaba ɗaya suka yi yayin da ɗaya daga cikin ma'aikatan wajan ya kalle ta ya ce. "Yarima Junaid kenen, mutum ne mara tausayi, mara imani. Baya tausayin talakawa sannan baya da mutunta wa, duk in da ya samu ƙusa kai yake ba tare da yana jin tsoron kowa ba, an sha kai ƙarar sa gidan mai martaba sarki. Kuma sarki yana ɗaukar mataki hakan abin da yake yi sai dai kuma muddin ya fito sai ya je har gidan wanda ya kawo ƙararsa sannan ya tozarta shi ya sa shi ya bar gari gaba ɗaya. Sai dai yana da yahya wanda yake matuƙar tsoro, tun da yahyansa ya bar ƙasar nan ya je ƙasar waje aiki shi ke nen ya ƙara iskancin sa a kan na da. Amma da a ce yana nan ba za ka taɓa ganin koda inuwar sa ba".
Girgiza kai Zahra ta yi sannan ta ce. "Ni dai karya sake ya gwada min wanann shashanci don ba zan rabu da shi ba.". Ta faɗa tana mai ɗaukar lemo da biscuit sannan ta miƙa wa ma'aikacin kuɗin da ta zara a aljihun Yarima Junaid. Karɓa ma'aikacin ya yi tare da yi mata godiya.
Fice wa ta yi daga cikin wajan yayin da ta samu bakin hanya ta fara kurɓan lemo. Nan take mutane suka fara binta da kallo.
Ɓangaren asibiti kuwa su DPO na shiga ɗaki suka tarar Zahra ba ta ciki. Nan take suka bazama neman Zahra yayin da suka fara patrol a cikin wajan fita suka yi daga cikin asibitin sannan suka fara bibiyar Zahra.
**********************
*JIGAWA*
Yallaɓai tun ɗazu muke ce mata ta sauko amma ta ƙi sauko wa.
Ajiyan zuciya Umar ya sauke!, sannan ya ce. "Yanzu tana ina?".
Amsa Nurse ɗin ta ba shi da cewa tana cikin room 6. Jin hakan ya sa shi nufar in da ɗakin take. Baiyi wata-wata ba ya shiga cikin ɗakin.
Duba ko ina ya yi ya ga babu Amrah a cikin ɗakin. Hankalin sa ba ƙaramin tashi ya yi ba. Duban nurse ɗin da ke tare da shi ya yi ya ce. "Ina mara lafiyar da na kawo?".
Amsa nurse ɗin ta bashi da cewa. "Ka duba saman silin yallaɓai. Jin hakan ya sa Umar ya maida kallonsa sama.
Abin da ya gani ba ƙaramin firgita shi ya yi ba. Saurin ja da baya ya yi ganin Amrah zaune kan fankan ɗakin ta rirriƙe shi gamm tamkar bishiya.
Maida kallonsa ya yi kan nurse ya ce. "Garin ya ya ku ka bari ta au kan fanka?, ita ɗin fa mara lafiya ce, ya kamata a ce kuna kusa da ita domin ku dinga kula da lafiyar ta".
Kallonsa Nurse ɗin ta yi ta ce. "Munyi hakan yallaɓai, amma kwatsam sai mu ka ga ta firgita ta miƙe tsaye, bamu yi aune ba kawai muka ga ta buga tsalle tare da aye wa saman fanka tamkar buri, Allah ma ya sa babu wuta a jikin fankan da shi ke nen mun rasa ta".
Ajiyan zuciya Umar ya sauke jin abin da nurse ɗin ta ce. Sannan ya dube ta ya ce. "Wace ce special nurse ɗin da aka aje a nan domin ta dinga kula da ita?".
Amsa nurse ɗin ta bashi da cewa. "Nurse Nadiya ce, ita ce take kula da ita kafin ka zo".
"To ki je ki ce mata ta zo ina da buƙatar ganinta". Cewar Umar.
"Shi ke nen". Nurse ɗin ta faɗa tare da fice wa daga cikin ɗakin.
*******
Ɓangaren su Aliyu kuwa, hawanni ƙalilan ya yi musu suka iso Nigeria. Yayin da suka sauka a airport. Fito wa suka yi tare da neman taxi suka hau kai tsaye suka nufi hanyar asibiti.
******
Mitin ƙalilan nurse Nadiya ta isa ɗakin da su Umar suke. Da sallama ta shiga ɗakin Umar ya amsa. Dubansa ta yi ta ce. "Naji an ce kana kira na lafiya dai ko?".
Amsa Umar ya bata da cewa. "Lafiya ƙalau, ina neman taimakon ki ne, yanzu zanje gida ne na ɗauki abun da zai sa ta sauko ƙasa. Ina so ne ki jire min ita dan Allah kinji?, bana son ta fita ko ina please".
Murmushi Nurse Nadiya ta yi ta ce. "Aiki na ne yin hakan, don aka kada ka samu damuwa za ka iya tafiya ni zan zauna na kular maka da ita".
Godiya Umar ya yi mata sannan ya fice daga cikin ɗakin.
Zama nurse Nadiya ta yi tana mai maida kallonta sama sannan ta girgiza kai ta ce. "Allah mai iko, ko ta ya ya na aka yi ta ɗane kan fanka oho. Kina jina ƴar lele, maza sauko ƙasa kinji kyakyawa, zan siya miki alewa".
Ganin Amrah ba ta kula ta ba saima ƙara zama da ta yi kan fankan. Furzar da iska nurse Nadiya ta yi sanann ta ce. "Shi ke nen tun da ba za ki sauko ba". Ta faɗa tare da ɗaukar lemon ɓawo da ke cikin plate ta fara ƙoƙarin kai bakin ta.
Hango lemon ɓawo da Amrah ta yi ya sa ta dira ƙasa tare da wafce lemon, sannan ta fara haɗa wa da bawon jikin sa tana sha.
Zaro idanuwa Nurse Nadiya ta yi ganin irin launin idanuwanta. Cikin ranta ta ce. "Wannan green eyes ne da ita, sakk kalar idanun ɗaya daga cikin yaran Mrs Laila. Allah sarki". Ta faɗa yayin da hawaye suka fara bin kan ƙuncin ta.
*************
Bayan isar Yarima Junaid fada ya shiga cikin part ɗin sa ba tare da ya kula kowa ba. Shiga wani ɓangare ya yi a gidan sannan ta duba aljihun shi domin ya ɗauki maƙulli. Zaro idanuwa ya yi waje gani cewar babu muƙullin ɗakin sa a aljihun shi.
"Ta ya ya hakan za ta faru?, ina maƙullin ya shiga kuma?, na shiga uku!, muddin banga maƙullin nan ba sai Yahya ya hukunta ni, yanzu me zan yi kenen?".
Nan take ya tuna da cewar ɗazu ya riƙe Zahra. "Kodai ita ce ta ɗauka?". Ya tambayi kanshi.
Da sauri ya fita daga cikin part ɗin sa. Tare da fita hanyar waje. nan take ya ci karo da mai martaba.
Sunkuyar da kansa Junaid ya yi sannan ya ce. "Allah ya ƙara maka nisan kwana ranka shi daɗe".
Dubansa mai martaba sarki ya yi sannan ya ce. "Junaid me ya sa ka fita daga cikin masarautar nan bayan na hana ka fita?".
Nan take cikin Junaid ya ɗuri ruwa.
***************
Ɓangaren su Safeera kuwa, shigar da Safeera aka yi cikin room 8, yayin da likitoci suka rufa a kanta. Babu abin da Mom ke yi in banda addu'a yayin da take ta kai kawo a cikin reception ɗin.
Saida suka ɗau lokaci sosai a kanta kafin daga bisani suka samu numfashin ta ya dawo. Nan take suka yi mata allurar bacci.
Fito wa likitocin suka yi suna sharfe zufa. Ganin sun fito ya sa su Mom suka nufi in da suke tare da tambayar ya lafiyar Safeera.
Ɗaya daga cikin doctor's ɗin ne ya dube su ya ce. "Alhamdulillah, mun samu numfashin ta ya dawo yanzu kuma ta samu bacci. Zamu saka ɗaya daga cikin nurse ɗin mu ta je ta duba ta.
"Shi ke nen". Daddy ya furta.
Shiga cikin room ɗin da nurse Nadiya take likitan ya yi sannan ya dube ta ya ce. "Nurse ina son ki je ki dinga kula da wata mara lafiya tana room 8".
Kallonsa Nurse Nadiya ta yi ta ce. "Am sorry to say sir, but ba zan iya rabu wa da wannan mara lafiyar sannan na koma kan wata ba, wannan an bani amanar ta ne. Kuma nayi alƙawarin zan kula da ita, kuma yana da kyau idan mutum ya ɗau alƙawari ya yi ƙoƙarin cika wa. Ka saka wata nurse ɗin ta je ta kula da ita Please sir ". Ta faɗa cikin ƙasa da murya.
Kallonta doctor ɗin ya yi sannan ya ce. "Ina mara lafiyar da ki ke kula da ita take?".
Amsa nurse Nadiya ta bashi da cewa. "gata chan a sama".
Maida kallonsa Doctor ɗin ya yi sama. Zaro idanuwa waje ya yi domin abin da ya gani ya yi matuƙar bashi mamaki. "I can't believe this, how can this be possible". Ya faɗa. Maida kallonsa ya yi kan nurse Nadiya sannan ya ce. "Ina so yanzu kiyi maza-maza kije ki duba patient ɗin ke cikin room 8 yanzu". Ya faɗa hankalin shi a matuƙar tashe.
Kallonsa nurse Nadiya ta yi ta ce. "Lafiya dai Doctor, naga kamar hankalin ka a tashe".
Doctor ɗin ya dube ta ya ce. "Dole hankali na ya kasance a tashe domin naga abin da ya firgita ni, kije ki duba ɗakin ko mara lafiyar mu tana wajan, ni zan wuce office".
"As you wish sir". Ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye tsreda fice wa daga ɗakin.
Zama Doctor ɗin ya yi yana mai kallon Du'a wanda ke a kan fanka. "Abin mamaki baya ƙare wa, yanzun nan da na fito daga ɗakin ɗayar yarinyar amma kuma yanzu na zo nan, na tarar da mai kama da ita sakk. Wai ko dai na sha maye ne yau?". Ya tambayi kansa.
******
"Shi ya san abin da ya gani hankalin sa ya tashi, koma dai mene ne zan je ɗakin na gani". Cewar nurse Nadiya. Tana isa ƙofar ɗakin ta murɗa handle ɗin ƙofan.
Chan ta hango Safeera a kwance. Riƙe haɓar ta nurse Nadiya ta yi ta ce. "Lahaula, Amrah wato har kin riga ni zuwa nan ɗin ma. Ta ina ki ka bi har ki ka riga ni zuwa?". Dube-dube ta fara yi.
"To wai ina mara lafiyar take ne?, wato dai wannan likitan so yake kawai ya bani wahala shi ya sa ya ce min wai akwai mara lafiya a nan". Ta faɗa tana mai maida kallonta kan safeera wacce ke kwance kan gado idanuwanta a lumshe.
Mamaki ne ya kama nurse Nadiya ganin cewar tufafin da ke jikin Safeera ba irin shi ne a jikin Amrah ba. "Ta ya ya Amrah ta iya sauya kaya cikin ƙanƙanin lokaci aka?". Nurse Nadiya ta tambayi kanta.
Furzar da iska ta yi sannan ta ce. "Mybe ni ce
ban duba ba sosai . Amrah ina zuwa bara naje na faɗa wa Doctor ɗin cewa banga mara lafiyar da ya faɗa ba". Ta faɗa tare da fice wa daga cikin ɗakin.
Nufar ɗakin da Amrah take ta yi. Tana isa ƙofar ɗakin ta buɗe tare da shiga cik. Yayin da idanuwanta suka sauka a kan Amrah. Nan take gabanta ya yi mummunar faɗuwa!, yayin da gabanta ya shiga dukan uku-uku. Babu zato ta ji kanta ya yi mugun sara mata. baki na rawa ta ce.
" Amrah!, kenen ba Amrah na gani a wan can ɗakin ba?, to in dai da gaske ba Amrah bace a wannan ɗakin ita kuma ta cikin ɗakin wace ce?".
💃💃💃🌹🌹💃💃💃
*TASHIN KAI, NURSE NADIYA FA TA SHIGA RUƊANI KOMAI ZAI FARU IDAN TA GANO CEWAR SU BIYU NE A ASIBITIN, SANNAN KUMA YARAN LAILAH ABDULLAHI NE?. MUJE DAI ZUWA*
*WAYYO LOW BATTERY 🔅 🔋, MUNA FAMA DA RASHIN WUTA BANI DA CHARJI🥺, JIYA MA NASO NAYI MUKU AMMA RASHIN WUTA YA HANA. KUYI HAƘURI DA WANNAN PAGE PLEASE 🙏*.
KARKU MANTA DA SHARING, COMMENTS, AND LIKES FISABILULLAH 🙏🙏🙏🙏.
ALƘALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️Jajirtattu)