Free chapter · Read without an account
52
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*ALLON ƘADDARA*_
_*By*_
*_OUM FATIMA_*
_*(Hakimar D. A. W. A)*_
✨✨✨✨✨✨✨✨
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S📚ASSOCIATION*_
_*TEAM*_
_*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*_
*PAGE 52*
_*بسم الله الر حمن الر حيم*_
**** Kamar yanda tayi niyya yau da dare da yake ita ke da turaka bayan ta gama shirya masa abincin dare ya kammala ci ta sako masa zancen da tun ɗazu ta rasa ta inda zata fara.
"Dama Alhaji nace..." Shiru tayi ta kasa ƙarasawa ta sadda kai. Ɗagowa yayi a natse ya zuba mata ido yana nazarinta.
"Uhum ina sauraron ki Maman yara". Ya faɗa yana tsare fuskarta da kallo.
"Cewa nayi baka ganin ya kamata ayiwa wannan yaron magana ya ƙara aure, kaga Asabe ta takura akan maganar Fa'iza tun kafin aurensa da Hanan, nace mata ba zan kuma masa dole ba idan shi ya buƙata da kansa to ba matsala, amma a yanzu sai nake ganin ya kamata ya ƙara ɗin tunda yana da halin hakan ko don a haifa masa zuri'ar da zasu masa addu'a ko bayan ransa".
Ta ƙare maganar tana sunkuyar da kanta ƙasa ganin irin kallon da yake binta da shi, numfashi ya sauke kafin ya fara magana. "Kin bani mamaki Fatima ban taɓa zaton haka daga gareki ba".
Saurarawa yayi kafin yaci gaba da cewa"Yanzu ashe kema kin yarda da surutun mutane mara tushe, ya kamata ya ƙara aure sabo da a haifa masa zuri'a? To ita Maman nawa cewa aka yi baza ta haihu ba ko me? Me yasa ku Mata duk girmanku idan kuka aikata wani abin sai kace wasu ƙananan yara, to kin ga matuƙar akan wannan dalilin mara tushe zaki ta kura shi ban amince ba, ki bari duk san da yaji yana son ƙara aure a karan kansa ya ƙara ba wan da zai hana shi".
Haƙuri ta bashi ganin ransa ya ɓaci ba dan abin ya fita a ranta ba.
**** Koda yazo mata da maganar tafiyarsu Lagos fatan alkairi tayi musu, sai da taji kamar ta masa maganar Faiza amma gargaɗin Alhaji Babba yasa ta fasa.
Sosai na warke na samu lafiya har ina maganar komawa aiki Hammah ya dakatar dani akan zamu koma Lagos mu zauna na wani lokaci, ban tambaye shi dalili ba na amince sabo da duk abinda yake so nima ina amincewa da shi kamar yanda ako yaushe yake goyon bayan nawa ra'ayin.
Ba'a wani ɗauki lokaci ba muka gama shiri, da kansa yaje Makarantar su Little ya amso mata transfer, mun wuce Lagos bayan mun yi sallama da Iyayenmu da abokan arziki.
Naso zuwa Katsina kafin mu wuce amma Allah bai yi ba don haka na haƙura zuwa wani lokaci.
Mun sauka lafiya in da aka zo ɗaukar mu a cikin Motocinsa dake can, haɗaɗɗen gida aka kai mu wanda ya gaji da ƙayatuwa, komai da muke buƙata nida yarinyata an tanadar mana hakan ya nuna cewa tuni ya gama shirin sa dama.
Sabuwar rayuwa muka fara a Lagos cikin farin ciki Hammah yana bani duk kulawar da ta dace, yana nuna min soyayya da kulawar da nake jin kamar nafi ko wata Mace sa'a a rayuwa, tuni aka samawa Little Makaranta mai kyau aka ɗaukar mata driver dake kaita ya dawo da ita. Wataran kuma ni nake kaita a cikin sabuwar motar da Hammah ya saya min wacce ta gaji da haɗuwa.
Tun da nazo ba inda nake zuwa sai dai inci in kwanta in yi barci don masu aiki ya zuba min sosai ya hana ni ko wane irin aiki, ko da na masa magana cewa yayi hutu nake buƙata don haka ba abinda zan yi kawai in huta.
Ai kuwa na samu hutun fiye da yanda nake buƙata domin tsananin kulawarsa a gareni yasa na rage damuwar dake raina sosai wannan yasa hankalina ya kwanta na ƙara kyau nayi wani Fresh da in ka kalle ni sai ka ƙara.
Watanmu uku a Lagos zaman wuri ɗaya ya isheni kasancewar na saba fita aiki don haka yau da dare muna zaune da Hammmanah yana aiki a system ɗinsa ni kuma ina yiwa Little Kalba a kanta sabo da gobe Monday akwai Makaranta, anan na sako masa zancen da nake son masa.
"Dama Hammah akwai abinda nake son yi ne shine nace bari in nemi shawararka".
"Ina sauraronki, mai iyalin Jabeer ke buƙata ne?". Ya faɗa yana min murmushinsa mai birgewa.
Nima murmushin na masa ina jin daɗin duk sanda ya kira ni da Iyalinsa, sai dai duk sanda ya faɗi hakan yana tuna min da Ya Nabeel ne, sabo shi ke kira na da hakan. Duk sanda na tuna shi kuwa ina masa addu'a da nema masa rahamar Allah.
"Dama ina son cika ɗayan burina ne na rayuwa, so nake in buɗe shagon make up da salon da gyaran jiki kaga zan ɗan riƙa fita tunda yanzu bana zuwa aiki". Na faɗa ina kallon sa.
"Kin san ako da yaushe ina baki goyon baya akan duk abin da kike so matuƙar bai sauka daga kan hanya ba, don haka a wannan karon ma ina baki goyon baya ɗari bisa ɗari wannan tunani ne mai kyau Allah ya taimaka". Ya ƙare maganar yana dafa kafaɗata.
Wani irin farin ciki nake ji a duk sanda Hammah ya nuna min yana bayana ako da yaushe yana bani ƙwarin gwiwa akan burikana, don haka murmushi na saki cikin farin ciki nace "Na gode sosai Hammana Allah ya cika maka burikanka ya kare ka daga dukkanin sharri".
"Ameen ya Allah Farhaty" Ya faɗa cikin jin daɗi.
"Akwai kuɗaɗen dana tanada don aiwatar da hakan, yanzu ta ina za'a fara". Na faɗa ina kallonsa.
"Ki bar komai a hannu na kawai".
Hira mukaci gaba da yi har ya kammala aikinsa muka haura sama, Little na fara kaiwa ɗakinta na canza mata kaya na kwantar nayi mata addu'a na fito na nufi ɗakina don shirin barci.
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
Zaune take a cikin ɗakinta tayi nisa a cikin tunanin da yake damuta na irin yanda ake yada mata habaici akan yanda Allah ya tsaro musu rayuwa ita da ƴarta.
Idan ban da son zuciya irin na mutane da ƙin gaskiya ƙuru-ƙiru, sun san ƴa'ƴa biyar ta haifa Allah ne bai bar mata ba amma ake cewa ai rashin haihuwar gadon su ne a gurinta Hanan ta gada, ita ba lallai ta samu ko ɗayan da Ammy ta samu ba.
Ta lura rigima Asabe ke nemanta da ita shi yasa yanzu da Hanan bata kusa take sauke wa Ammy abin da suke yiwa Hanan da, "to wai ma duka yaushe aka yi auren da za'a taso mu gaba? Har yanzu fa bata cike shekara uku ba!". Ta faɗa cikin damuwar da ta isheta.
"Allah na gode maka da yanda ka tsara min rayuwata ka bani ikon juriya in cinye duk jarabawar da kayi min!". Ta faɗa hawaye na silalowa saman fuskar ta.
"Tausayinta ya kama Baba Malam dake tsaye a ƙofa yana kallonta yana jin mai take faɗa ba tare da ta san ya shigo ba, sosai ya fuskanci tana cikin damuwa a kwanakin nan kuma ya san duk akan Hanan ne.
Ƙarasowa yayi ya zauna kusa da ita sai a sannan ta san da shigowarsa tayi maza ta share hawayen tana masa sannu da zuwa.
Cikin kulawa ya amsa mata kafin ya ɗora da mata nasiha ta sigar rarrashi ya kuma bata shawarar dagewa da addu'a ta faɗawa Allah buƙatunta shi mai karɓar kukan bayinsa ne a ko da yaushe, sannan ya ɗora da faɗa mata cewar muminai su Allah yake jarabta don ya auna ƙarfin imaninsu, taci gaba da addu'a komai zai wuce.
Da waɗannan kalaman na mijinta ta samu natsuwa ta ƙara zage dantse ta daina barci take faɗawa Allah damuwarta ba dare ba rana, sannan duk lokacin da da suka yi waya da Hanan abinda take jaddada mata kenan ta rage barci ta kusanta kanta da Allah shine maganin damuwarsu.
★★★
Tun maganar da muka yi da Hammah bai sake min maganar ba nima kuma ban masa ba, ashe tuni yasa aka fara aikin ba tare da ya faɗa min ba ko ya nemi kuɗin da nace masa na tanada domin hakan ba.
Cikin ƙanƙanen lokaci aka kammala komai aka zuba duk abinda ake buƙata domin kwararru ta fanni yaba wa kwangilar aikin, har ma'aikata an ɗaukar min.
Yau bayan ya dawo daga Asibitin da aka neme shi akan wani case da yake da ƙwarewa akai, bayan yaci abinci ya huta yace mu shirya mu raka shi wani wuri.
Ba tare da musu ko tabayarsa inda zamu je ba muka shirya muka fita, tafiya muka ɗan yi ya tsaya ya bani wani farin ƙyalle yace in rufe fuskata. Kallonsa nayi zan yi magana ya ɗora yatsarsa saman bakinsa alamar kar in tambaye shi.
Yi nayi kamar yanda ya buƙata kafin ya tada Motar muka ci gaba da tafiya, tafiya kaɗan muka ƙara muka tsaya ya buɗe motar ya fice ya zagayo ya buɗe ya fito dani bayan ya fito da Little. Hannuna ya kama muka ɗan yi tafiya kaɗan kafin ya bani damar buɗe ido.
A hankali na ɗago na kalle shi ya nuna min gabana alamar can zan kalla, sanƙamewa nayi kawai tsabar mamaki na ɗago na kallesa kafin na maida idona saman katafaren shagon da naga an rubuta sunana da manyan baƙi.
*HANAN'S PARLOUR*
an yiwa rubutun kwalliya mai birgewa, rungumesa kawai nayi a hankali na furta kalmar "I love you Hammmanah, kai na musamman ne"...
*Oum Fatima*