Free chapter · Read without an account

{82..}

by Feenerh Feeche Studios · HAJAR


Ana idar da sallar juma'a aka sallaci gawar Baba, abinda yasa aka jinkirta jana'izar sbd ƴan uwansa na Yola da suka roƙa a ɗaga musu ƙafa suma su samu jana'izar dan uwansu, jana'iza kamila aka yiwa Baba kuma ya samu ɗumbin mutane, daga nan aka wuce dashi gidansa na gsky, Sosai mutuwar Baba ta wujijjiga mutune musamman ma dai iyalansa, Hajar na kwance ɗakin Umma bata ma san inda kanta yake ba tin bayan da aka fitar da gawar mahaifinta, suman da tayi na farko bata farfaɗo ba saida aka yi ta yayyafa mata ruwa ana mata fifita, tini fashin watanta yaxo bayan ɗaurewar da mararta tayi don it was behind the corner, ta samu dai taga fuskar mahaifinta kafin a fita dashi, kawai Allahumma ajirni fi musibati wa aklufuli khairan minha take furtawa, don bakinta ya kama addu'ar tin a mota da yace ta ringa faɗa, addu'ar ce tasa ta ɗan ji sassauci amma hakan baisa ta dena rusa kuka ba har saida ta fita daga hayyacinta, Umma kam har aka fita da gawar Baba ba ta san inda kanta yake ba, Nabilah kam wni lungu ta shige ta ringa kukan rashin mahaifinta kamar ranta zai fita, gaba ɗaya ta tsani ganin Maama da Maimuna da ita kanta Sa'adatu don gani take su suka kashe Baba, shiyasa ma taƙi zama a ɗakin Maama don bata son ganinsu, wajen ƙarfe biyu ana cikin jimamin mutuwa sai ga Balaraba ta shigo da wasu mata police biye da ita, fuskar nan ta Balaraba ta suntuma suntum kamar an buga mata iska da ƙatuwar bandage a goshi, idonta ɗaya saida ya nutse tsabar yacca fuskarta ta kumbura, tini Balaraba ta ringa kallon mutanen dake tsakar gida tana neman Maama, da bata ganta ba ta wuce ɗakinta da police women din biye da ita, ɗakin Maaman bbu wasu mutane sosai don ba tada wasu shaƙiƙan ƴan uwa duk karume karume ne, Balaraba ta kyallaro idonta da ya nutse ciki ta kalli Maama wcca tayi wni wujiga wujiga don sosai mutuwar Baba ta taɓata, shekaru talatin da wni abu sune tare da bawan Allahn nan, Balaraba tayi nuni da Maama tace "gata can..", ɗaya daga cikin ƴan sandan tace "Baiwar Allah zamu tafi dake can police station sbd muna tuhumarki da ƙoƙarin kisan kai", wata daga cikin karumen ƴan uwan Maama mai suna Jummai tace "ku kam ba ku san gidan mutuwa ba, baiwar Allahn nan fa mijinta ne ya rasu ko dawowa daga kaisa...", ƴar sandar ta ɗaga mata hannu tace "mu hukuma kawai aikinmu muke, an bamu umarnin kamota daga sama dole mu wanzar da aikinmu", haka nan ƴan sandar nan suka kaɗo Maama daga ɗaki tana rusu kuka kamar ba gobe tace "Dan girman Allah karku gwadamin wnn rashin imamin, ku barni da jimamin rashin mijina mna..", Balaraba tace "Ni imamin kika gwada min da kika tsiyayarmin da ruwan ido..", kuka wiwi Maama take tana turjewa don tini ƴan sandan suka fara janta, gashi jama'a bbu wnda yace uffan kawai kallon Maama suke suna taɓe baki, toh daman wa zai ce wni abun halinta ne yaja mata, gashi bata zauna lfy da maƙota ba bare su dubeta, da kyar Maimuna ta rarrafo daga ɗaki ta maƙale jikin ƙofa, ilahirin jikinta shatin belt ne da Huzaifa ya lakaɗa mata duka, ga kuma cikinta dake azabar ciwo kamar zai tsinke, lokaci zuwa lokaci kuma tana yin bleeding kuma shima tin jiya, Sa'adatu ma maƙalewa tayi daga jikin window tana kallon yadda ake jan Maama sai kace Akuya, Balaraba na cewa "Ni kaɗai nasan irin nakasta ni da kika yi, saida na zubar da jini yafi gwangwani huɗu ga uban ɗinkin da akay min ruɓi shida a goshi..", haka nan ƴan sandar suka tisa ƙeyar Maama daga gidan tana kuka Wiwi, hijabinta ya wani waskace ya koma gefen kunne sai haɗa gumi take tamkar tsohuwar kuturwa, Maama ta haɗa hannayenta tana kallon Balaraba tace "ki duba irin halin da nake ciki Balaraba kar kisa a kaini chaji Ofis da ɗanyen mutuwar mijina..", Balaraba ta taɓe baki ta kalli yan sandan tace "Ofisa ku kaɗata du Allah" don so take a kai Maama police station a sakata a cell, kuɗi sosai Balaraba ta biya domin a zane Maama idan an kaita cell. Sai yamma liƙis snn Naseer yayo bailing Maama, ko da yaje police station din sai ya tarar sun jibgi Maama sai kace jaka, da yayi mgana akan dukan sai suka ce ai gardama ta musu, saida Naseer ya biya dubu ashirin don Balaraba cewa tayi sai an bata kuɗin da ta kashe na magani, Balaraba dadi har cikin ranta don ta sami kuɗin da zata biya bashin da ta ciyo ta bawa ƴan sanda don su nakaɗawa Maama duka, ranta washar tinda an jibgi Maama. Sai a washe gari snn Umma ta fara watsakewa, ynxu kam har tana iya amsa gaisuwar wnda suka zo mata ta'aziyya ba kamar jiya ba, Hajar ta ɗan samu kuzari amma ba wni sosai ba, bata iya jimawa a zaune saita kwanta, manyan idanunta duk sun ƙanƙance kuma still bata dena kuka ba, gsky ta amshi tsumangiyar mutuwar mahaifinta, da yammacin ranar saiga Mami tare da Sakeena, a ɗakin Umma Anty ta saukesu, bayan sun gaisa da Umma suka mata ta'aziyya, Hajar dake zaune ɗakin ta gaida Mami, Mami ta amsa with care snn ta mata ta'aziyyar mahaifinta, Hajar suka gaisa da Sakeena snn ta mata ya dadin haƙuri, sosai Sakeeena taji wni mugun tausayin Umma da Hajar don saura ƙiris kukan da take dannewa ya taho mata, bayan wni lokaci Sakeena ta dubi Mami tace "Mami su shigo ynxu..?", Mami na kallon Anty da ta kawo musu ruwa ta zauna gefen Umma bayan sun gaisa tace "Za'a shigo a muku gaisuwa", After few minutes Nurain ya shigo shi da Farooq, suna gaisawa dasu Umma snn suka musu ta'aziyya, Farooq ya dubi Hajar ya mata gaisuwa, ta amsa kanta a ƙasa don ita ko gaisuwar ma aka mta sai ta fara kuka, ynxun ma dai kukan ne ya taho, Nurain ya sauke numfashi yana kallonta da wutsiyar ido, gaba ɗaya jiya bai samu ya ganta ba don tinda akai jana'iza suka wuce gida tare da Abba, da yamma ma dai da ya dawo bai samu ya ganta ba har ya tafi after magrib, gashi wayarta na wajensa though yasan ma ko tana wajenta bazata ɗauka ba, Farooq ne ya fara tashi snn Nurain ya bisa suka fita, su Mami basu wni jima ba suka tashi zasu wuce, Umma tace "Toh mun gode sosai..", Mami tace "Allah ya kara muku hƙuri shi kuma ya masa rahama yasa can tafi nan..", Umma tace "Ameen..", Sakeena ta matsa kusa da Hajar tana mata mgana a hankali, kawai gyaɗa kai Hajar take tana share hawayen dake zuba cheeks dinta, Umma ta ringa kallonsu hakama Anty, Sakeena ta saki hannun Hajar da ta riƙe tace "sai munxo gobe dear... Allah ya ƙara haƙuri..", Hajar ta gyaɗa kai sai kuma ta miƙe, Mami tace "yi zamanki daughter kinji..", Hajar ta saukar da kanta ta koma ta zauna, zaune kan tabarma su Mami suka tarar da Nurain da Farooq a soro, Farooq yabi bayan Mami da har ta fita, Nurain ya rage murya yana biye da Sakeena yace "Sister please how is she...?", Sakeena ta juyo ta kallesa tace "Toh partially..", ya sauke numfashi ya ciro wayarta da yake ta yawo da ita a pocket ya miƙawa Sakeena yace "please ki bata kafin mu wuce..", Sakeena ta amshi wayar ta juya ta koma cikin gida, bbu jimawa ta fito bayan ta kaiwa Hajar wayar. Da daddare wajen ƙarfe takwas Anty ta shigo ɗakin Umma, direct gado ta nufa inda Hajar ta duƙunƙune waje ɗaya, tapping dinta Anty tayi don tasan ba bacci take ba, Hajar ta miƙe zaune sai kuma ta kai hannu ta goge hawayen cheeks dinta, Anty ta girgiza kai tace "kinci Abincin kuwa Hajar...?", Hajar ta gyaɗa kai tace "Na ci", Anty ta duƙa ta bude plate din abincin sai kuma ta ɗago ta dubi Hajar, Hajar ta saukar da kanta ba tace komai ba, Anty ta sauke ajiyar zuciya tace "tinda kin ƙi cin wnn toh me zaki ci..?", Hajar tace "na ƙoshi ne..", Anty ta ɗan haɗe gira tace "A'a wne irin kin ƙoshi Hajar, na kawo miki kunun gyaɗa da Umma ta rage...?", Hajar ta saukar da kanta sai kuma tace "Toh..", Anty tace "yauwa bari na kawo miki tare da maganinki..", Anty na fita Hajar ta juya tana kallon wayarta da ta fara ringing, da fitilar wayar ta haska ɗakin don bbu Nepa, gashi kuma ana zafi shiyasa duk su Umma suka fita tsakar gida sai ita kaɗaice a ɗakin, tana ɗaukar wayar kiran ya katse, bbu jimawa wni kiran ya sake shigowa, a hankali tayi picking ta kara a kunne, da dasasshiyar muryanta tayi sallama, Nurain ya lumshe idonsa don he can feel the bitterness in her voice da sanyin murya yace "Baby wife...", ta saukar da kanta ta amsa a hankali, yace "please can you come out..?", ta gyaɗa kai a hankali sai kuma ta ajiye wayar bayan ta katse, saukowa tayi dga gadon ta gyara hijab dinta, Anty ta shigo da cup din kunu ganinta a tsaye tace "Ina zaki...?", Hajar tace "shine yaxo..", Anty tace "Ohk.. idan kin dawo sai kisha kunun kinji...", gyaɗa kai Hajar tayi walking slowly ta fita tsakar gida, ta duƙa gaban Umma da ke zaune kan tabarma, ga Sabrah kusa da ita tayi bacci, ta gayawa Umma zata fita ƙofar gida, Umma ta jinjina kai a takaice, Hajar ta tashi ta nufi soro tana tafiya a hankali, bbu kowa a soron don tin bayan sallar magrib masu zama a nan din suke watsewa, su Naseer kuma ta gansu a cikin gida, ta saukar da kanta ta shiga soron da ya gama cika da pure scent dinsa, Nurain dake riƙe da wayarsa ya haska soron ya ringa kallonta without blinking, ta ɗan tsaya nesa dashi, with cracking voice tace "Ina yini...", ya juya ya kalli waje sai kuma ya ƙarewa soron kallo, lokaci guda ya janyo hannunta ta tafi gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa, a hankali ya shiga patting bayanta yace "Ya haƙuri Baby wife..", ta kwantar da kanta hawaye na zarya cheeks dinta, ai kam tini ta jiƙa masa gaban riga da ruwan hawaye, haka ya cigaba da consoling wife dinsa har saida ya tabbatar nauyin zuciyarta ya ragu, tana jin bbu wanda ya mata rarrashin da ya shigeta kamar na mijinta, surely ta rarrasu don more than 60 percent na raɗaɗin da take ji ya ragu, ya kai soft palm dinsa ya goge mata ragowar tears din yace "please stop crying Allah ya jiƙan Abba..", sai wajen takwas da rabi Hajar ta shiga gida da bag din kayanta da ya taho mata dasu, other hand din nata kuma ledar kayan ciye ciye ce. Washe gari akay sadakar uku tinda kwanan keso Baba yayi, wajen sha daya na safe sai ga su Mami harda Hajjaju Hajiya da Noor da kuma Umminsu Farooq da Aysha, suka zo da uban abinci kala kala na sadaka, Anty da Umma ba ƙaramin mamaki suka sha ba ganin yacca surkan Hajar suke sonta, ga Iron Lady da suka ga tana mata wni tarairaya na musamman, Umma har cikin ranta take jin daɗi da Allah ya kai ƴarta gidan da ake sonta, yoh toh so mna idan dangin miji basa yi da kai ta ina zasu ringa maka irin wnn mutuncin, bayan 20mins da zuwansu Mami Anty Zulaihah ma tazo don tasan gidan tinda tare da ita aka zo ɗaukan Hajar, Khausar dake biye da mahaifiyarta ta ringa bin gidan da kallo tana yamutse fuska, tinda taji cewa gidansu Hajar Anty Zulaihah zata zo shine tace itama zata zo, Hajar ta duƙa ta gaida Anty Zulaihah wcca ta amsa mata da sakakkiyar fuska snn ta mata ta'aziyya, Khausar dai bata ko kalli Hajar ba bare ta mata gaisuwa, Hajar na lura da yacca ta ɗauke kai da ta ganta, ita kam bata damu ba don duk wnda ya wanko ƙafa yaxo gidansu sbd mutuwar Babanta ya gama mata komai, Hajar na kallon Khausar tace "Sannu Khausar", Khausar ta ɗan kalleta tace "Ya ƙarin haƙuri, Allah ya jiƙansa..", Hajar tace "Ameen..", ko 10mins su Anty Zulaihah basu ƙara ba suka tashi zasu tafi, zuwa lokacin har Khausar ta fara fifita da handbag dinta tana yamutsa fuska, kafin sallar Azahar su Mami ma suka tafi. Da yamma lokacin jama'a sun rage tururuwar zuwa Mu'azzam ya shigo gidan, kwaraɓaɓɓen kitchen din gidan da basa amfani dashi duk ya mutu sai uban shirgi ya buɗe, girgiza kai yayi ya bar bakin kitchen din, ɗakin Baba ya buɗe ya shiga bayan wni lokaci ya fito, wajen Naseer dake tsaye bakin titi tare da Huzaifa ya wuce, Mu'azzam na kallon Naseer yace "Yaya saidai a ajiye a ɗakin Baba a ynxu dai kafin a gyara kitchen din", Naseer yace "Tom.. ku shiga dasu", tini Huzaifa da Mu'azzam suka ringa ɗaukar Foodstuffs din da suke shaƙure a ƴar ƙurƙura suna shiga gida dasu, bayan sun gama kwashe uban kayan Abincin tare da ƴan tayi Naseer ya bisu gidan shima, duba yadda suka ajiye kayan yayi snn ya rufe ɗakin Baban ya bawa Sabrah muƙullin yace ta kaiwa Umma, Maama da akan idonta aka ringa jibgi Foodstuffs din don tana tsakar gida ta dubi Naseer da wni irin yanayi bayan taga ya bawa Sabrah key yace ta kaiwa Umma, Maama tace "Nasiru..", Naseer ya dubeta a karo na farko tin shigowarsa gidan, tace "Zo nan ina son ganinka" da haka ta tashi ta shiga ɗakinta tana ɗingishi, har ynxu ƙashin cinyarta ciwo yake sbd bugun da ta sha a hannun police, Naseer da zuciyarsa take zafi don har cikin ransa ya tsani halin mahaifiyarsa, da ƙyar ya tausashi kansa ya bita ɗakin, kallo ɗaya ya yiwa Maimuna dake malelekuwa a ƙasan leda tana murƙususun ciwon ciki, Sa'adatu ta cusa wayarta da take dannawa ƙarƙashin pillow ta hau baccin ƙarya, haɗe fuska yayi don ya lura da ita, ya duƙa gaban Maama yace "Gani..", Maama ta ringa kallonsa jin yacca yayi mgnar a daƙile, ta girgiza kai tace "Nasiru na lura kai da Huzaifa da Nabilah kun ƙullaceni a cikin ranku, kar ku manta dai ni uwarku ce ko da kuwa tsince tsince nake a bola..", Naseer ya sauke numfashi yace "ba hka bane Maama..", tace "Ai ni ba mahaukaciya bace da za kace min ba hka bane Nasiru, toh ba dai a canzawa tuwo suna, idan ma gani kuke ni na kashe mahaifinku toh wllh ba ruwana, lokacinsa ne yyi snn kuma dukkanku na fiku sonsa don tare kuka ganni dashi..", shi dai Naseer yayi shiru baice komai ba, Maama ta gyaɗa kai tace "Wccan Uban kayan abincin tuli guda a ina ku ka samosa..?", yace "Abokin Baba ne ya kawo..", Maama ta micincina ido tace "Abokin Baba kuma...?, ina mal yaga Aboki mai arziƙin da zai nannago uban kayan abincin nan ya bamu..?", Naseer yace "Alhj Muktar fa", nan ma Maama ta ƙanƙance ido tace "waye hka..?", yace "Surkin Hajar", saida zuciyar Maama ta koma ciki tsabar ruɗu amma bata nuna ba ta rausayar da kai tace "ba shakka shiyasa ai ka damƙa mukulli hannun masu abincin", Naseer ya shafa kansa yace "zan koma soro kar azo ana nemana..", bai jira cewarta ba ya tashi ya fita with speed, takaici ma bazai barsa ya gaya mata sauran Alkhairyn da Abba ya musu ba, ga kuɗi masu yawa ya bayar yace su riƙe a hannunsu snn yace duk abinda ake buƙata a gidan Naseer yaje ya samesa ya gaya masa, a wnn lokacin ai da wuya a samu mutum irin Abba wnda zai waiwayi iyalan Abokinsa bayan rasuwa, kowa ta kansa yake nafsi nafsi. Hajar ta raka Zainab da tazo mata gaisuwa har soro, Hajar tace "Ngd sosai Zainab..", Zainab tayi murmushi tace "ba komai Hajar, Please karki manta ki kirani anjima sai nayi saving number dinki tinda bakya amfani da wncan..", Hajar tace "insha Allah.. ngd sosai Zainab ki gaida Ummi dan Allah..", Zainab tace "zata ji". Hajar na gida har saida akai bakwai, kullum Nurain sai yaxo to check on her, gashi kuma suna waya frequently, yau ne akay sadakar bakwai, da yamma bayan gida ya watse bbu kowa don da yawan mutane sunxo sunyi gaisuwarsu, Anty ce tare da Umma a ɗaki, tin ranar uku Anty ta tafi gidanta sai ranar biyar da ta kuma zuwa sai kuma yau bakwai da tazo, Anty tace "Yau gashi har Baba yayi kwana bakwai a ƙasa, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa yasa aljanna ce makomarsa..", Umma da Hajar suka amsa da Ameen, Anty tace "Addah saidai wni hanzari ba gudu ba, zaman gidan nan a gsky ba naki bane ya kamata mu fara tunanin inda zaki koma, baza ki cigaba da zama da waccar matar mai zuciyar kafurai ba..", Umma ta numfasa tace "gskyr ki Jamilah, tabbas bazan cigaba da zama da Rabi ba a gidan nan, zanyi tunani akan hakan..", Anty tace "Yauwa kar ki ja tunanin nan ya daɗe don ni ko sati biyu bana so ki ƙara nan gaba wllh, wccar matar abin tsoro ce tsakani ga Allah", Umma tayi shiru ba tace komai ba, Anty tace "idan gidan Iya zaki koma toh..", Umma tayi saurin girgiza kai tace "A'a bazan koma gidan Iya ba gwara na tafi Yola kawai..", Anty ta zaro ido tace "Yola kuma Addah, wajen wa zaki a Yola..?", Umma tayi murmushi tace "haba Jamilah ya kike mgana sai kace wasu marasa dangi, wajen Gwaggo Habiba zan tafi..", Anty ta sauke ajiyar zuciya tace "haka ne Addah, wllh Gwaggo Habiba tana son mu kuma na tabbata bazata ƙi zama dake ba, lalurar da take da itace ma tasa bata zirga zirga wajen zuwa inda muke wllh", Umma tace "zan dai yi tunani Jamilah", Anty tace "Toh", tini idanun Hajar suka ciko da ruwa jin Ummanta za tayi nesa da ita, Anty ta kalli Hajar tace "ke kuma yaushe zaki koma gidanki..?", Umma tace "Ni nasha ma yau zata koma wllh..", Hajar ta saukar da kanta ba tace komai ba, Anty tace "Ya kamata dai ki tafi tinda anyi bakwai kar kuma a shiga haƙƙin aure..", Hajar bata iya cewa komai ba sai gyaɗa kai, Anty tace "Hajar na jinjina miki Allah ya miki Albarka, yadda naga dangin mijinki na tarairayarki suna ji dake nasan cewa kinyi riƙo da tarbiyyan da mahaifanki suka baki, Allah yasa ki cigaba da ɗorewa a haka kuma kar kiyi sagegeduwar da soyayyar nan da suke nuna miki zata ƙare..", Hajar tace "Insha Allah..", Daf da magrib Hajar na zaune kan kujera gaban rariya tana alwala don ynxu she's clean jiya tayi wankanta, Nabilah tazo ta ɗebi ruwa a buta ta durƙusa nan kusa da Hajar itama za tayi alwalan, Hajar dai bata ko kalli inda take ba ta cigaba da alwalanta a hankali, a hankali Nabilah tace "Hajara..", Hajar ta ɗaga kai ta kalleta sai kuma ta cigaba da alwalanta, Nabilah ta sake kiran sunanta a karo a biyu, da mamaki Hajar ta kalleta sai kuma tace "Na'am..", Nabilah da idonta ya ciko da ruwa tace "ya haƙurin mahaifinmu..", Hajar tace "Mun gode Allah..", Nabilah ta ɗanyi jimm sai kuma tace "Toh ayi haƙuri da duk wni abu da ya faru a baya, irin saɓanin da muka samu a matsayinmu na ƴan uwa, dan Allah kiyi haƙuri komai ya wuce Hajara..", Hajar tace "Ni kam a cikinku bbu wnda na riƙe a raina Nabilah, nice ƙarama acikinku amma kuka nuna bakwa sona a koda yaushe cikin kyarata kuke, snn kuka ringa haɗemin kai samm ba kwa nuna cewa ni ƴar uwarku ce..." sai kuma tayi shiru kafin tace "bazan manta ba shegiya kuke kirana duk da cewa ubanmu ɗaya, bbu damuwa komai ya wuce ni bbu wnda na riƙe a cikinku Nabilah..", Nabilah ta goge hawayen da ya zubo mata tace "haƙiƙa ba mu yiwa mahaifinmu adalci ba, ke kam bbu ruwanki sbd mu muke fara janyo duk wata fitina, duk wata matsala mu muke janyota wllh, dan Allah Hajara kiyi haƙuri mu manta da komai ko don mahaifinmu..", Hajar tace "ba komai kema kiyi haƙuri don ƙarfe ɗaya baya amo" tana gama fadin haka ta wanke ƙafarta ta tashi ta shiga ɗaki. Washe gari Umma tace da Hajar ta shirya ta tafi da wuri ido na ganin ido ba sai dare ba, haka nan Hajar ta hau shirya ƴan kayanta a jaka jiki a sanyaye, wajen sha biyu Abdallah ya kawo saƙo yace inji Anty kuma saƙon na Hajar ne, ai kam Umma bata buɗe ledar ba haka ta miƙawa mai ita, ita dai Hajar ta amshi ledar tana tunanin mene ne a ciki, Abdallah ko zama beyi ba yace zai wuce don kasuwa zai tafi Anty ta bashi saƙon ya kawo, bbu jimawa da tafiyar Abdallah kiran Anty ya shigo wayar Hajar, bayan sun gaisa Anty tace "Abdallah ya kawo miki sako ko..?", Hajar tace "Eh..", Anty tace "Ohk.. akwai paper acikin ko wanne wcca aka rubuta ydda ake amfani dashi..", Hajar tace "Toh ngd Anty" duk da bata san mene ne abinda Anty take mgana akai ba, Anty tace "Yau din zaki tafi..?", Hajar tace "Eh insha Allah da yamma..", da haka sukay sallama. Hajar ta saka hijab dinta a hankali, duƙawa tayi ta saka wayarta cikin bag din kayanta, idanunta cike taff da ruwa ta juya ta kalli Umma, da sauri ta tafi ta faɗa jikin Umma ta fashe da kuka tace "Umma dan girman Allah karki tafi Yola ki barni..", Umma ta daure tace "A'a bazan tafi ba Hajara..", Hajar ta ringa rusa kuka don mikin mutuwar ne ya wani taso mata, ynxu shknn bazata sake ganin Babanta ba, indai tazo gida bazata ga Baba ba, Mu'azzam ne ya shigo ɗakin ya tsaya yana kallonsu, sai kuma yace "kin fa bar mutum yana jira Hajar..", Hajar ta zame jikinta daga na Umma tana jan zuciya, Mu'azzam ya ɗauki jakar kayanta ya fita da ita yana cewa "ki fito hka nan..", haka nan Hajar ta fito tsakar gida da ledar kayan da Anty ta bata a hannu, Umma na biye da ita tace "Allah ya kaiku gida lfy..", Hajar ta kalli Nabilah dake zaune a ƙasa bbu ko tabarma ta zabga uban tagumi sai kace me fama da cutar depression, walking gently Hajar ta isa inda take ta duƙa gabanta tace "Nabilah..", Nabilah tayi firgigit don tayi nisa a tunanin da take, Hajar tace "Ni zan tafi sai na sake zuwa kuma..", Nabilah ta numfasa tace "Toh Allah ya kaiki gida lfy, zan amshi lambarki a wajen Umma sai mu ringa gaisawa..", Hajar ta gyaɗa kai da haka ta miƙe, hannun Umma ta riƙe tace "Umma na tafi..", Umma tace "Allah ya miki albarka Hajara ya kaiku gida lfy..", Hajar tace "Ameen Ummanmu..", Nabilah ta ringa kallonsu tana jin dama ta ta uwar ce a hka. Har bakin mota Mu'azzam ya raka sister dinsa, sai a lokacin Nurain ya amshi bag din kayan daga hannun Mu'azzam ya saka a booth, kafin ma ya gama saka jakar tini Mu'azzam ya juya ya shige lungunsu, Nurain ya zagayo side din da Hajar ta tsaya, ta ɗan kallesa sukay ido huɗu, murmushi ya sakar mata sai kuma ya kai hannu ya buɗe mata front seat, saida ta shiga ya rufe snn ya zaga driver seat ya buɗe ya shiga, ya rufe murfin motar sai kuma yayi stretching kansa sosai yace "Alhmdllh..", bai kunna motar ba ya juya yana kallonta, sosai ya lura da kumburin da idanunta sukay, ya sauki wni boyayyen ajiyar zuciya, Calmly ya kamo hannunta yace "Baby wife..", ta kallesa a takaice tace "Ina yini..", yayi pecking hannun nata yace "Ni har ynxu ba nida suna", ta saukar da kanta ba tace komai ba, ya sake pecking hannun nata na almost 10secs har saida ta ɗago ta kallesa, yace "Uhmm ba nida suna a wajen matana har ynxu..", ta kalli hannunta dake cikin nasa, yasa other hand dinsa ya riƙe haɓarta ya ɗago kanta, kallon eye balls din juna kawai suke, ya lumshe idonsa ya sake buɗasu a kanta, kashe mata ido daya yayi yace "A taimaka min da suna..", yacca ya kashe idon sai kace wni abu ne ya faɗa masa da kuma yacca yayi mganar ne ya bata dariya, bata san lokacin da wni murmushi ya kufce mata ba, ta ɗora forehead dinta kan hannunsu dake maƙale tare still tana murmushi, yaushe rabonta da wni abu wai shi murmushi, shima murmushin yayi ya ɗago kanta ya haɗe forehead dinsu waje guda yana murza hannunta yace "I like it when you smile"......✍️


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol