Free chapter 路 Read without an account
Chapter three
~~~~馃憫馃憫Masarautar Badara 馃憫馃憫~~~~
Chapter 3
Written by
(marubuciya馃枈锔忦煐婏笍
ZAIMAR馃挄馃挄)
Hatred馃枻
Love鉂わ笍
Romance馃槏
Bismillahi Rahamanin Rahim
**************Anisa ta nufi Inda yarima yake da gudu,daman akwai sauran alelen ta Mai manja da tasaya a hanya, ta chakuda a hannun ta tana isowa Inda yake ta shafa mishi ajikin rigarsa kaf, ta juya kenan zata gudu, ya Kamo gashin kanta ya ja ta ya wanka mata Mari hagu da dama. Ni Karan kai na Sanda na tsorata da Marin saboda bazan ma iya kirga adadin Marin da ya mata bah, Har sai da bakin ta ya fara Jin,latif ne ya jashi Yana cewa 'are you in your sense what wrong with you, can't you see she is just a small girl, and everything that she did to you, you are the one that cause it. Nimran yace' enough latif in ba zaka bi bayana ba toh just keep your mouth shut Naka ido. Ya juya kenan yaga ba ita ba alaman ta sai ganin Bayan ta yayi tana gudu, tana zuwa dai dai gurin fita daga gurin ta juyawa tayi tace'Allah ya isa mugu azzalimi, ta sake sa gudu ta karasa fita, yace wa dogarai su bisu zuciyan shi sai ta fasa yakeyi Yana ji Inda za'a kawo mishi yarinyar nan zai iya kashe ta.
Anisa tana fita ta hange kawayen ta achan ta gurin restaurant ta karaso da gudu, tana isa sai ta tsaya tanata nishi, kwayenta suna cewa 'kiyi hakuri Anisa duk mu muka jawo Miki da bamu dage kizo bah, suna cikin magana kenan suka hango dogarai din yarima suna zuwa suka saka gudu, gudu sosai kaman police da barawo kasan barawo bazai bar police yakama shi ba saboda yasan in ya Kama shi Kashin sa ya bushe. Da yake ba zaka hada gudu manya da Yara matsa ba tuni sunyi musu Nisa, haka suka koma wajan yarima suna ce masa yaran sun gudu, yayi ta musu masifa kaman Wanda su suka mishi laifin.
Abokanan yarima suka ta bawa yarima Nimran din hakuri duk da sunsan abunda yayi Bai dace bah, saboda kuma sunsan halinsa zaice sai ya dauke mataki Akan yaran kuma Har iyayen su sai abun ya shafa. Baya ma Jin abunda Abokanan sa suke cewa zun zurutun ya hau dokin zuciya Yana tunanin yanda zai wulakanta yarinyar nan da iyayen ta kai harda dangin su saboda ta ja musu. ko sallama ma baiyi da Abokanan san bah nufi Inda Motan shi yake ya shiga suka ja suka tafi, haka ya koma gida rai abace yayi part dinshi Yana shiga ya wuce toilet direct ya sake ruwa Akan sa Sanda yajima ahaka tukunna yayi wanka ya Fito daure da towel, lokacin Ana kiran sallan magrib kawai yasa jallabiya ya wuce masallaci.
****Su Anisa kuma duk da sun fita Daga yankari Amman basu daina gudu ba Sanda suka isa garinsu fanti tukunna suka tsaya, su kayi sallama da junansu suka Dada bada hakuri wa Anisa, dun Saban ta bugu ma Ga Gara kuka tayi gashin sun manta kwanon tallen su agurin, Koda yake anata kai wake ta Kaya, anata kiraye kirayen sallan magrib Anisa tagama tsanin Kashin ta ya bushe in mamanta ta kamata. Tana zuwa tashiga gidan su cikin tsanda batasan mamanta tana bakin kofa tana jiran dawowan ta, kawai ji tayi kaman Daga sama aka zuba mata bulala mamanta tace'Daga ina kike? Yanzu ne yakamata ki dawo kuma ina kwanan tallen kin? Tace'aa mama wallahi yau ma talatu ne ta nimeni da tsokana na kuma ta tafi da kwanan talle na harda kukanta dun mamantan ta yarda. Mamanta tace barin malan yadawo yaje gidan Mai garin nan, wannan Karon kan bazan hakura bah ta dakamun ya kuma ta kwace mata kwanan ta kullum, gaskiya na gaji. Da sauri tace'aa mama kiyi hakuri,innallaha ma'assabirin, ki Bari in ta Kara sai baba yaje, Dan Allah mama kiyi hakuri Kibar maganan, mamanta tace'wuce Kibar mun nan kuma banga Miki dukanki bah. Anisa ta karasa ta dauka buta tayi alwala ta shiga tayi sallah agefen mamantan.
***Bayan sun idar da sallah mamanta ta Cigaba da mata fada kuma tace ko talatu ta nimeki da rigima ko fada ki Kyaleta kawai kizo ki fadamun sai anje Har gidansu. Sai Ga babanta ya dawo yace mamana ta dawo kuwa, tace'eh baba nadawo, yace'albishrinki tace'goro, Zaki fara zuwa makaranta boko Wata sati in sha Allah , habawa tazo da gudu ta rungume baban ta tana cewa nagode baba farincikin kam ba'asa mushing Rana, sarki Badara ne dattijon arziki yace ya dauka dawainiyar karatun duk wani da namiji da ya mace na garin fanti, yashi, mainamaji da Badara Wanda basu da karfi ko Hali, Anisa tanata farinciki, tace 'Allah ya biyashi da gidan Aljanna yasa yagama da duniya lafiya, acikin zuciyanta kuma tace' gaskiya albasa batayi halin ruwa bah, shi baban shi ba ruwansa dattijon arziki, Har taimaka wa talaka wa yakeyi, shi kuwa Dan shi tsohon munafiki ne kuma wallahi Sanna Rama marina ehe, sai ya hadu da mummunan jarabawan rayuwa. Haka ranan muka kwana muna farinciki, gefe guda kuma ina tsaka yanda zanyi mugunta wa wancan munafiki.