Free chapter · Read without an account
Free page 2
KIRJIN MAI HANKALI*_
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳✈️🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_FREE PAGE: TWO/SHAFI NA BIYU NA KYAUTA_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
"Aameen Yaa Rabbi" yan wajen suka sa baki gaba daya..
"Malam ba zaku shigo ku duba su ba?" Cewar wata mata dattijuwa . Tana rike da katon baho a hannuwanta... Tana mai nuni da inda masu jegon su ke..
"A'ah" suka hada baki wajen amsa ta, hadi da saurin barin wajen suka fashe da daria.
Aka cigaba da hidima. Abinci da abun sha da alawa haka aka fito dasu anata rarrabawa yara.
Wajensu malam di ma an kai zobo da aka daddaure a ledoji.. Sai wanda malam Nata'ala ya saya ya kakkara musu...
Suka doddara akan abinci nan suka shiga ci. Anaci ana sanyawa yaran da aka haifa albarka. Da shiwa iyayen su alkhairi...
Haka mutane akayita hidima. Har dare yaja ainun duk suka tattafi. Gidah ya zama sai yan cikin sa da masu gidan...
Saboda kunya irinta mutanen maraya. Da Kuma dattako na ahalin. Sai da dare yaja ainun sosai koina yayi duhu. Tukun sannan su malam Nata'ala da malam idi suka shiga gidan nasu.
Kana cikin babban gidah ne harda sukuntumi. Gefe daya daga can baya bandaki ne babba a tsaftace. Sai daga bayan sa kuma dakin girki ne duk kuwa da awajen tsakar gidah matan gidan ke aiyukan girkunan su da sauran hidindimu na yau da kullum...
Daga can gefe Kuma dakuna ne har biyu a jere. Kowanne da katifar sa ta akwatinan karfe masu kyau da kuma asaberi a sakale.
Sai wasu dakunan biyu dake daga bayan sa shima. Guda biyu manya kaman wadancan. Komai da iri daya gwanin ban shaawa.
Gidah dai mai kyau a karkara, Kai ko cikin birnin ne irin unguwar nan ta masu karamin karfi, ka samu gidah irin nasu malam Nata'ala to Kai din ka mallaki matsugini mai kyau. Lamarin sai dai ace Alhamdulillah ala kullu halin kawai.
°°°°°°
Asaberin ya daga a hankali ya shiga bakinsa dauke da sallama ya Saka Kai ya shiga ciki....
Tana daga zaune akan tabarma. Kullin yar acikin zani na daga gefenta akan katifa.
Fitilar kwai ce mai ci ta haske dakin, amman ba haske mai dallare idanu ba. Dai dai gwargwado dai.
Ta Saka hannu ta sake matse hasken ya ragu. Kana tana kokarin gyara zamanta. Malam Idi yayi azamar karasawa wajenta. Ya na girgiza Kai hadi da zare hular kansa ya ajiye a gefe..
Ya dauki diyar tasa acikin zani yana dubanta. Bakinsa na motsawa da alama adduoi yakeyi . Ya duka ya tofa mata. Ya mayar da ita ya kwantar yana dubanta tamkar zai mayar da ita ciki.
"Sannu da zuwa malam.... Ya Kuma kokari? Allah yabada Iko da nasara ya Kara temakawa"
"Sannu da kokari zainabu... Ai ke zaaiwa sannu... Ubangiji Allah ya miki albarka zainbauu. Kinji? Allah ya karamiki lafiya. Ya baki lafiyar shayarwa ya Kuma rayabmiki wannan yarinya. Ya mata albarka. Ya bamu ikon Kula da su Amin"
Kanta a kasa cikeda kunya ta amsa da,
"Aameen malam"
"Mai kike bukata yanzu? Banason ki zauna da yunwa.. "
"A koshe nake malam"
"Yanzun lawujo zai aiko da sakon mu. Banason musu. Kici ki Sha kinji?"
"To malam inshaa Allahu"
Ya bude baki zai magana kuwa sai ga sallamar lawujo. Da yar fitilar sa a hannuh yanata rafka sallama dai dai misali yana haske tsakar gidan da cochilan din hannun sa.
"Wa'alaykum Salam sannu lawujo" malam Nata'ala. Ya fito da sauri daga dakin sa
Gaisawa sukayi da lawujo. Ya karbo ledojin yana masa godia. Da ma tuni sun bashi kudin.
Malam Idi ma yafito suka Kara gaisawa da dan uwan nasa. Kana ya karbu tasa ledar yayi masa sai da safe ya koma dakinsa ya shige.
Ledar ya bude.gasasshen tsire ne an zuge shi sai kamshi ne ke tashi. Gefe daya Kuma shayi ne mai kauri shima a leda mai kwari. Sai buredi, biredi bugun Kato babba a leda da Kuma wani daurin sukari
"Tashi kici zainabu .... Kinji ko?"
"To malam bakwa gajiya? To angode Allah yasa ka muku da alkhairi ya Kara arziki Amin"
"Aamin zainabu"
A gaba ya sakata. Sai daya tabbatar taci komai ta koshi. Tukun sannan yaji sanyi a ransa. Ya dauki yarinyar tamkar zai mayar da ita cikinsa yana dubanta sosai tun daga kan yan yatsun kafafunta dake cikin zani, zuwa gashin kanta da sumar ta fiffito an sinke Fe ta da hula tanata bacci tana fitar da numfashi ahankali.
"Zaytuna....... Allah ya miki albarka ..Allah ya miki albarka ya raya ku keda Rumana. Aamin"
Itadai tanada gefe tana amsashi tana Kuma sakin murmushi gwanin ban shaawa. Son mai gidan nata na dada ratsa magunar jini da tsokar ta .
To haka ma bangaren Malam Nata'ala. Shima sai daya Saka Mai dakin nasa a gaba ya tabbatar taci tukun sannan ya kyaleta.
Idanuwansa na kan yar jaririyar su Rumana daketa bacci gwanin ban shaawa.
Sun raba dare suna hirarra kin duniya. Kafin daga bisanj su daura alwala bacci Kuma ya kwashe su..
Hakan ce ta kasance ko da yaushe safe da rana mutane ne fam agidan .matan karkarar kullum suna hidima agidan.yayinda mazan kwa na waje suna daukar karatunbayan sun dawo daga noma. Wasu daga cikin na birni inda suke aiki a wajeje da kasuwanni. Da dare Kuma su shiga gidajen su..
A haka har akayi suna. Yara sukaci sunayen su. Taro kuma ya watse rayuwa ta dora daga inda ta tasaya. Yaran nata girman gwanin ban shaawa cikin ikon Allah da qudirar sa da Kuma buwayar sa. Domin shi din wahidin ne gagara misali....
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga ***_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
****.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*****
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*