Free chapter · Read without an account
{88..}
Noor ta ɗago Khausar ta temaka mata ta koma kan kujera, gefenta Mami ta zauna tana tmbyarta lfy, har lokacin Khausar kuka take kamar wacca uwarta ta mutu, Noor ta kalli Mami tace "ba gidan Yaya ta tafi ba..?", Mami tace "Eh can taje sbd karatunta..", Mami ta saukar da murya ta dafa kan Khausar tace "Tell me what happened dear..?", da kyar Khausar ta tsaida kukan tace "Matar Yaya ce..", shiru Mami da Noor sukay suna kallonta don basu fahimci me take nufi ba, Noor tace "wai Hajar..?", Khausar ta gyaɗa kai tace "Eh ita", Mami dai kawai kallon Khausar take kafin tace "me Hajar din ta miki..?", Khausar ta nuna bakinta da ya fara suntuma gashi yayi jajir tace "kunga fa abinda ta min" sai kuma ta sake rushewa da kuka, Noor ta kalli Mami don taga reaction dinta, Mami tayi ajiyar zuciya don bata gane me Khausar ke nufi ba amma dai taga bakinta ya kumbura alamar ya fashe, Mami tace "Khausar ki nutsu ki gayamin me ya faru", Khausar ta ɗan tsagaita kukan tace "hankaɗoni tayi daga sama shine na faɗo na fasa baki and my ankle is also paining me...", Mami ta zaro ido tace "innalillah... was it a coincidence or intensional..?", Noor dai kasaƙe tayi tana kallon Khausar da mamaki, kawai ji tayi bata yarda da mganar ba, Hajar ba zata turo Khausar daga stairs ba gsky saidai idan wni abun ne ya faru, Khausar ta girgiza kai tace "No Mami tana sane ta turoni sbd mun sami slight misunderstanding kuma na bata haƙuri ashe bata haƙura ba, gashi tinda naje gidan ta mayar dani house help, nice nake komai ita nata kawai girki kullum tana upstairs, bata bani abinci idan ta dafa saita kwashe ta kai room dinta, idan Yaya ya dawo ya tmbyi naci abinci sai tace Eh, shine ni kuma na fara shiga kitchen ina dafawa da kaina, da ta lura ina shiga kitchen din shine ta rufe store ta wuce da key din, most of the time saidai nasha tea ko kuma naci biscuit dina dana tafi dashi, shine yau ta manta bata rufe store ba ni kuma na samu chance na dafa Noodles, zan wuce sama da Noodles din na tarar da ita zata sauko, shine tace wai me yasa na shigar mata kitchen ni kuma na bata haƙuri, bayan na gama cin Noodles din ne zan kai plates din kitchen ashe tana bayana shine ta hankaɗoni ƙasa..." ta fashe da kuka tace "ban san me ya faru ba kawai Yaya yace na haɗa kayana na bar masa gidansa tinda matarsa nake yiwa wulaƙanci, am very sure itace ta haɗamin sharri a wajensa..", Mami tace "ya isa.. sorry ki dena kuka kinji", da haka Mami ta shiga share mata hawayen cheeks dinta, deep down her mind tana jujjuya mgnar Khausar, Noor dai tsabar shock ta kasa cewa komai, Mami ta shafa kan Khausar tace "kinyi breakfast ko a kawo miki..?", Khausar tace "A'a..", Mami ta ɗanyi shiru tana wni lissafi, ynxu fa tace mata ai ta dafa Noodles shine ma abinda yasa suka samu misunderstanding da Khausar, Mami tace "Ohk... bari a kawo miki kinji, wuce part dina ki zauna kafin a kawo miki..", Khausar tace "Toh" ta tashi a hankali ta wuce part din Mami, Mami ta bita da kallo hakama Noor, Noor ta ɗan kalli Mami sai kuma tace "Our Mami plxx karki yanke hukunci sai kinji ta bakin both parties..", Mami tayi ajiyar zuciya tace "ki haɗawa ƴar uwarki breakfast ki kai mata..", Noor tace "Sure", Mami ta tashi ta shiga great room din Abba, Noor kam kitchen ta shige, Laure ta saka tace ta jere mata breakfast a tray, tini Laure ta gama haɗa komai, Noor ta ɗauki trayn ta fita dashi, part din Mami ta shiga ta tarar da Khausar kwance kan doguwar kujera, Noor ta ajiye trayn tace "sister ga abincin..", Khausar ta miƙe zaune tace "Thank you", Noor tace "na haɗa miki shayin..?", gyaɗa kai Khausar tayi, tini Noor ta haɗa mata tea mai kauri ta miƙa mata, Khausar ta amshi mug din ba tare da ta sha ba tace "yaushe kika zo..?", Noor tace "ban daɗe da zuwa ba..", Khausar tace "Ohk.. ya husby naki..?", Noor tayi murmushi tana cire veil din Abayarta tace "fine Alhmdllh shi yayi dropping dina ma, bai daɗe da fita sun gaisa da Mami ba kika shigo", Khausar ta gyaɗa kai ba tace komai ba, Noor tace "sister kin dai ƙi yarda da Aliyu ko..?", Khausar ta yamutsa fuska tace "waye kuma Aliyu..?", Noor tace "Aliyu fa abokin Abdul dina..", sai a lokacin Khausar ta gane kuma har waya ma suna yi kwanaki amma dai ynxu tayi blocking contact dinsa, Noor tace "he is a good person sister", Khausar tace "Ohk i will think about it" da haka ta kai cup din shayin baki tayi sipping, habawa ai da sauri ta mayar dana bakin nata cikin cup din shayin tsabar azabar da taji, kamar fatar bakinta zata ɓaɓɓako haka taji, tini ta ajiye cup din idonta ya ciko da ruwa, Noor tace "ba zaki iya shan shayin ba..?", da sauri Khausar ta gyaɗa kai tace "it is paining me so much, I can't take the tea", Noor ta ringa kallonta, can dai tace "Sister are you sure about what you told Mami earlier..?", Khausar tace "Sure..", Noor ta gyara zama tace "Ni dman tintini nasan jininku bai haɗu da Hajar ba sister, a time din bikina dai kece me kawo problem kina mata abubuwa amma ban san this time around me ya faru ba..", Khausar ta ɗanyi tsam tace "Toh me na mata lokacin bikin naki..?", Noor ta juya hannu tace "Nope bance kin mata komai ba amma ke kinsan yacca kikai mata", a ɗan fusace Khausar tace "wai me kike nufi ne..?", Noor tace "A gsky sister baki kyauta ba, koda abinda kike faɗa gsky ne toh baki kyauta ba, Mami fa uwar Mijin Hajar ce me yasa za ki faɗi irin wnn maganganun akanta a gaban Mami, kin san irin fitinar da hakan zai kawo..", a bit pissed up Khausar tace "Ohh i see dman ko time din bikin naki na lura ita kike backing, ynxun ma kinaso kice laifina ne knn?", Noor tace "Not at All.. kawai dai you shouldn't have told Mami all this...", Khausar tayi tsaki tace "Enough sister, ni dai kawai ki barni, ki bari idan ke aka fasawa baki sai kice hakan nagani" tana gama faɗin hka ta miƙe ta fita, ba ta jima ba ta dawo da jakar kayanta ta shiga room din da take zaune a gidan. Sam Mami bata kira Nurain ta tmbyesa ba'asi ba, tasan definitely zai zo da yamma toh saita masa mganar, kuma dman ita bata yanke hukuncin cikin fishi saita huce, gashi kuma wnn abune da ya faru na farko don hka dole sai ta tabbatar kafin ta ɗauki wni action din, 6 months knn da Hajar ta kasance daughter in law dinta bata taɓa jin wata matsalar daga gareta ba sai wnn moment din, daga side din ƴan uwa ma ba taji an faɗi aibunta ba saima kirkinta da ake faɗa, Iron Lady ma kaɗai ta isa hujja don ita tamkar littafi take bata ɓoye komai, gashi dai tinda take da Hajiya ba ta taɓa kawo mata complain din Hajar ba, jikokinta kam kullum sai tace ga abinda wane yayi mata, Mami dai bata sake yiwa Khausar mgnar ba tana jiran yamma Nurain yaxo, ai kam biyar saura few minutes Nurain ya iso gidan, ko a fuska Mami ba ta nuna masa komai ba har suka gaisa kamar kullum, ta tmbyesa Hajar, yace mata tana lfy, bayan wni lokaci Mami ta nisa tace "Sai kuma baka kira kaji ya yarinyar mutane tazo gida ba", ya ɗan tattare gira cause bai gane ba, har ga Allah ya manta da wta halitta wai ita Khausar, Mami tace "Khausar da ka kora daga gidanka baka kira kaji lfy tazo ba..", Nurain ya sauke numfashi baice komai ba, Mami ta haɗe gira tace "ka taɓa jin ranar da Abbanku ya taɓa korar ɗan uwansa daga gidansa ko kuma ni ka taɓa jin nasa ya kori wni nasa...?", ya ajiye numfashi yace "A'a Our Mami..", tace "wato baka taɓa ji ba sai kai tattabara sarkin ƴan aure shine zaka kori ƴar uwarka a gidanka sbd matarka ko..?", yayi ajiyar zuciya yace "Mami please do you know what happened..?", tace "if i didn't know how will I asked you such question Uthman..", ya shafa kansa bai ce komai ba, nan Mami ta zayyana masa kaff ƙaryar da Khausar ta giggilla mata, tsabar mamaki saida wni murmushin gefen baki ya kufce masa, Mami ta murtuke fuska tace "You think it's a joke ba..?", ya girgiza kai yace "Ƙarya take... wllh ƙarya take Mami, store din nan kullum a buɗe yake infact ma bbu key a jikin door din, keys din na wajena, kuma ina shiga kitchen din anytime to make a coffee ban taɓa ganin store a rufe ba, mganar abinci kam ƙarya take da kanta take dafa abinda take so taci, mganar ma ta cillota daga stairs ƙarya take nine na bigeta, mganar ta zama house help ƙarya take shima sau ɗaya ta taɓa share kitchen da palour kuma shima nina sakata, All what she said is a lie", Mami ba tace komai ba kawai kallonsa take, tashi tayi ta shiga room din da Khausar take, tana tare da Noor a room din, Mami ta kalli Khausar tace "kin iya shan Oat din..?", Khausar tace "Eh na sha da ya huce..", Mami tace "Ohk come with me..", a bazata Khausar taji zuciyarta ta buga haka kurum, da kyar tace "Toh", Noor tace "Mami kamar naji muryan Ya Nurain shine yaxo..?", Mami tace "Eh", Noor tace "bari naje mu gaisa" da haka tabi bayan Mami suka fita, ita kam Khausar wani irin kullewa cikinta yayi da taji Mami tace Nurain yaxo, da kyar tayi shahada ta fita walking slowly, kanta a ƙasa ta shiga palourn ta zauna kan carpet kusa da kujerar Mami, a fakaice ta kalli Nurain da suke mgana da Noor tace "Yaya ina yini..", bai ko kalleta ba yace "lfy", After few minutes Mami na kallon Khausar tace "Dear ki faɗi duk abinda kika gayamin da safe, me ya faru da kike je gidan Nurain ki faɗa shima yaji don yace bai sani ba", daram zuciyar Khausar ta buga ta sunkuyar da kanta, Nurain kam tini ya zuba mata piercing eyes dinsa yana jiran tayi mgana, sam Khausar taƙi cewa komai sai murza hannu take, Mami tace "Uhmm talk now..", nan ma Khausar tayi ƙumus, Noor ta ɗan kalleta sai kuma ta tashi ta bar palourn ta koma ɗaki, ba yacca Mami ba tayi ba akan Khausar tayi mgana amma taƙi, shi dai Nurain kawai kallonta yke cike da mamaki, shiru palourn ya ɗauka, Mami kam tini ta rafko jirgin Khausar, Nurain yace "Ohk Mami since she won't talk let me tell you what exactly happened...", Mami was more than shock ta ringa kallon Khausar bayan Nurain ya gaya mata me ya faru, Khausar ta fashe da kuka tace "Yaya dan Allah kayi haƙuri wllh sharrin shaidan ne..", ta haɗe kanta da kujera tana cigaba da rusa kuka, Mami tayi wni nazari akan hkan da Khausar tayi, tabbas ta gano dalilin da yasa take yiwa Hajar hka, Mami ta sauke numfashi tace "you may leave", Khausar ta miƙe kanta a ƙasa ta shiga ɗaki, after few seconds Nurain yace "Mami dman nace miki ƙarya take..", Mami ta numfasa tace "Naji... Amma am not in support da dukanta da kayi akan matarka Uthman, yess bata kyauta ba bai kamata ta yi wnn furucin ba, and karka sake korar ɗan uwanka daga gidanka just like that, both of them are young kamata yyi ka yiwa Khausar din faɗa ka nuna mata kuskurenta ba wnn tough action din ba", ya shafa kansa don shima sai daga baya yaga bai kyauta ba, yace "insha Allah hkan bazai sake faruwa ba Mami", tace "ywwa itama Khausar din zan mata faɗa ba kyaleta nayi ba..", Nurain yayi ta attempting sanar da Mami cewa Hajar is pregnant amma kunya ya hanasa, hka dai ya tafi bai gaya mata ba, Ai kam da daddare Mami ta samu Khausar ta nuna mata kuskurenta, bai dace ba abinda tayi snn kuma worst part of it ƙarya, snn kuma ta gaya mata cewa ynxu Hajar is part of them tinda tayi aure cikin family nasu, ynxu Hajar kamar daughter dinta take, little sister din Noor, Mami taji daɗin yacca Khausar ta amshi laifinta kuma tace bazata sake ba sharrin shaidan ne, ita dai Mami tasan bbu wni sharrin shaidan sharrin kishi ne tinda yarinyar taso Nurain a baya kuma tana tunanin son nasa ne yaja abinda take yiwa matarsa.
★Hajar ta fito daga Kitchen da plate din gasasshiyar kazar da tayi warming a microwave, ga kuma fresh milk ta ciko glass cup da ita, ko good 2hours ba tayi da cin abinci ba gashi ynxu ma ta kwaso wni za taci, shima abincin ma kwaɗayi take ci, har mamakin kanta take, kan carpet ta zauna ta baje ta fara aika kazarta tana korawa da fresh milk, ita kwaɗayin nata ma sai ita, rannan ta haɗa Popcorn da Coffee yau kuma Kaza da madara, yanka uku taci taji har ta fara ƙoshi kuma, wayarta ta ɗauka ta buɗe data ta shiga whatsapp, message ne suka fara shigowa, chat dinta da Hafsah ta buɗe don taga ma ta turo mata wni saƙon kuma voicemail ne, Online ma Hafsahn take, Hajar ta kunna voicemail din tana ji, dariya tayi ta shiga kiran Hafsah video call, tini Hafsah ta ɗaga don dman Online take, Hajar tana ganin fuskar Hafsah a screen ta sake fashewa da dariya tace "sister nidae ban gane voicemail din nan ba ki gayamin ta nan..", Hafsah ta tashi daga palour da take zaune ta shiga ɗakinsu ta kulle da key, kallon Hajar tayi tace "Wllh duk ke kika ja min..", Hajar tace "wai me naja miki bayan ban gane me kike nufi ba..", Hafsah tace "ba kin sa nayi unblocking dinsa ba da naxo gidanki..?", Hajar tace "Toh wai shi wa..?", Hafsah tace "Ahmad mna..", Hajar tayi murmushi tace "Okay ngane", Hafsah tace "Wai ɗan mutumin nan dan yaga ina ɗan saurararsa muna gaisawa har wataran muyi fira, in gaya miki shine yayi min diren mikiya, ban san dai yacca akayi ba ɗan mutumin nan kawai ya wni turo uncles dinsa wajen Abba, ban san hawa ba ban san sauka ba jiya daddare Anty da Abba suka kirani suna tmbyata wai nasan wni Ahmad, ni dae nace musu na sansa shine suka ce in tashi in tafi, sai daga baya Anty take tmbyata wai ko nice na basa chance ya turo ni kuma nace A'a, toh dai in taƙaice miki zance Abba yace zaiyi bincike a kansa idan bashi da matsala sai magabatansa suxo da kuɗin aure..", Hajar tayi wni kyakkyawan murmushi tace "Alhmdllh wnn lamari yayi min daɗi..", Hafsah ta haɗe fuska tace "Toh ni cewa nayi ina sonsa da zai min hka..", sosai Hajar tayi dariya tace "ba sai kin faɗa ba mu mun gani..", Hafsah ta juya idanu tace "Ni shiyasa ma na kashe wayar tin jiya don kar ya kira don haushi nke ji..", Hajar tace "Ah a meye haka dan Allah.. Allah yasa ma Abba yace ya turo next week Friday, mu sha biki nan kusa wllh, nan gidana zaki taho inada Oum Sulthan wcca zata mayar dake kamar kwai, ƙamshi kam ko gonar flowers albarka", Hafsah tayi kasaƙe tana kallon Hajar sai kuma tace "Uhmm nidae ban yarda ba", sun ɗan jima suna fira kuma duk tsahon lokacin nan Hafsah taƙi yarda cewa tana son Ahmad, bayan sun gama wayar Hajar tayi murmushi tace "ƴar farka zama ki saukar da kai ne", sai kuma ta tashi ta nufi kitchen. Da daddare Hajar na tsaye gaban wardrobe zata fitar da kayan bacci ta saka don already tayi wnka kwanciya za tayi, Nurain ne ya shigo, ta juya ta kallesa, kananun kaya ta gani a jikinsa instead of pajamas, ta kalli agogo taga ƙarfe goma saura, ƙarasowa yayi ya tsaya daga bayanta yace "me zaki saka ne..?", tace "night wears..", ya buɗe section din manyan kayanta ya ciro Abaya ya miƙa mata yace "wear this..", ta kalli kayan tace "dasu zan kwanta..?", ya shafa cheek dinta yace "we are going out Baby wife..", tace "Ohk", tini ta zura Abayan ta koma gaban mirror tayi rolling veil, shi dai yana tsaye yana jiranta har ta gama shiryawa, ya riƙe hannunta suka fita ɗakin tare, ita dai tasha ƴar fitar daren da suka saba ce a siyo kayan maƙulashe, compound suke fita zuwa parking space, ya buɗe motar snn ya buɗe mata front seat ta shiga, ya zaga driver seat ya shiga, kallonsa ta ringa yi har saida ya juyo sukay ido huɗu, ya ɗage gira yace "why..?", ta girgiza kai tace "bkomae", ya kamo hannunta a hankali ya shiga mirzawa sai kuma yayi pecking, tayi murmushi tace "where are we going..?", ya mayar mata da murmushin yace "you will see", da haka ya fara driving slowly suka bar gidan, tafiyar almost 20mins sukay snn yayi parking gaban wni katafaren building, shi ya fara buɗe motar ya fita snn itama ta fita, ta ɗaga kai ta karanta sunan wajen wato Baby's World, kana ganin wajen kasan sabon buɗewa ne kuma wajene da ake siyar da kaya designers masu kyau da aminci haka zalika kuma wajen ƴan ƙarya ne masu aljihu da nauyi, yace "muje Baby wife..", siyayya sosai sukay ta kayan baby from infant size zuwa 6months, ita dai Hajar ba ita tayi zaɓen ba shine ya ringa kwasar kayan, kuma duk ɓangaren da yaje sai yace a bashi na baby girl maimakon unisex tinda har yau ba'a san gender din babyn ba, uban kayan kam sai kace na triple, saida suka je wajen cashier ya biya bill snn aka musu packaging kayan, har mota aka kai musu kayan, saida suka hau saman titi Hajar tace "Moon wai wne yace mka mace ne..?", ya ɗan kalleta yace "i have strong feeling about that..", almost 11:30 suka isa gida. Washe gari Nurain ya shiga room din Hajar bayan ya dawo daga mosque, kwance ya ganta kan gado, ya ƙarasa gaban gadon yana kallonta, scent dinsa da ta shaƙa ne yasa ta buɗe idonta, ya zauna side dinta ya kwaye duvet din da ta lulluɓa, rigarta ya ɗaga ya sunkuya yayi kissing flat tummy dinta yace "Good morning princess".......✍️