Free chapter · Read without an account

Chapter 10

by Maman Nusaiba · ZAWAJUL MUWADDA

*ZAWAJUL MUWADDA*





Daga alƙalamin


_Sarat Alƙasum (Mom Nusaiba)_



_(Labarin Sidra)_



*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*



*بسم الله الرحمن الرحيم*


*PAID BOOK ONLY N500*

_duk mai buƙata ya bi wannan number +966577675904_




*SHAFI NA* 🔟



_Legos_

Cike palon yake da mutane ana ta surutai wasu na dariya wasu kuma na danna waya. Cikin takunsa na isa yake saukowa daga samar bene ya sha dinkin wani ratsatstsan yadi Blue colour, sosai dinkin ya fito da ainahin kwarjini da zubin halittarsa, kamar kodayaushe gashinsa a ɗaure yake amma wannan karon sai ya sake shi ya yo baya sai shanin yake wani kalar ƙamshi mai daɗin shaƙa na fitowa daga cikin gashin, kai da gani kasan ba ƙaramar kulawa ake yi wa gashin ba, barimar kunnensa ya kai hannu ya taɓa yana gyara ta da haka ya sauko.

Miƙewa wata matashiyar budurwa ta yi da nufo shi da sauri fuskarta dauke da zallar farin ciki, a gaban shi ta tsaya ta ƙure shi da na mujiya sai murmushi take kamar sabuwar kamu. David ya wani basar yana shan ƙamshi duk da kuwa ya ji kewar ta a zuciyarsa, amma a zahiri kamar bai taɓa ganin ta ba, kawar da kai gefe ya yi dan ya tsani kallo ya yi yawa ya saka hannu a cikin aljihunsa.

Raurau budurwar ta yi da idanu ganin ba ma ita yake kallo ba ta juyo ta ga duk sun kawar da kai ba su suke kallo ba, a hankali ta miƙa hannu ta shafo kwantaccan sajensa cikin wani kalar yanayi har da lumshe ido, ƙara matsowa daf da shi ta yi murya ƙasa-ƙasa ta ce “My love I miss you very very much, please hugging me.” Ta yi maganar kamar mai shirin yin kuka, hakan ya sa David juyo da kanshi gareta ya sakar mata da wani nau'in murmushi wanda yake ƙara narkar da zuciyarta a kan so da ƙaunar da take mishi, hannunta ya kama ya ɗan sunkuyo kasancewar ya fita tsayi kamar mai raɗa ya ce “come down Baby ki bari na gama da su sai mu fita.”

Wani irin sanyi ta ji ya ratsa mata zuciya ta juyo suka haɗa ido da wata ta mata wani irin kallon, kwafa ta yi tana kallon David wanda kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai ya ja hannunta suka ƙaraso palon..

A kan kujera mai cin mutum ya zauna itama ta zauna a gefen shi, Mom ta yi murmushi ta ce “My son tun ɗazu muke jiran ka me ya zaunar da kai a ɗakina?”

Aje waya ya yi ya fuskanci Mom ya ce “Wani abu na yi.”

Ok Mom ta ce sannan Dad ya yi gyaran murya ya ce “My Son mun gaji da zaman ku babu aure kai da Daniel, shi ya sa Mom ɗinku da nemi a haɗa ku aure da 'ya'yan' yan'uwana, amma Daniel ya ce a cikin su babu wadda ta mishi a samo mishi wata, yanzu kai muke jira mu ji ra'ayinta ka zaɓi ɗaya daga cikinsu.”


Ta gefen David ta haɗe hannaye tana rufe idanuwanta zuciyarta na bugawa har sai da David ya lura da hakan, ba ta son ya ce waccan yake so ba ita ba, nan da nan zuciyarta ta yi rauni sai ga hawaye sun silalo daga ƙwarin idanuwanta. Tausayi ta ba wa David domin ya tabbatar tana son shi fiye da yadda yake tunani shi ne dai bai ba ta fuska sosai ba, da zarar ta fara mishi kalaman soyayya zai ji haushi ya kawar da kai, in kira ne ya katse idan kuma Mom ce ta aike shi wajen Mommynta sai ya dawo a fusace ko da kuwa bai amshi sakon ba, haka itama ɗayar da shi sam ba ta birge shi ko kaɗan, saboda yadda take gudanar da rayuwarta abin ya ƙazantar har ƙanƙami take ba shi..


janye idanunsa ya yi ya kalli Mom and Dad ya ce “Mom ai dama mun jima muna son juna ni da Mariam, kawai dai ba ni da time ne da zan tsaya faɗa muku, yau na yi niyar sanar da ku sai ga shi ma sun zo har gida, kuma zan aure ta ba na son bikin ya yi nisa ina son na tafi da ita America, yawwa sannan Mom ya kamata fa su Uncle su dawo gida tum da suna gari ba barin ƙasar suka yi ba.”


Wani irin zabura Mariam ta yi ta faɗa kan David ta ƙanƙame shi tamkar za a kwace mata shi, idanu rufe take faɗin “ Oh my god, Thank you my love.”


Dariya yan palon suka sa Meesha ta tashi tsaye tana taka rawa irin tasu ta yarbawa tana rera waƙa da yaren, sauran yan palon suna taya ta.


Bayan komai ya lafa Mom Leena wadda take mata ga ƙanen Dad ta ce “To babu komai tun da ya zaɓi Mariam duka ai ɗaya ne da ita da Leena, so dan haka sai a sa ranar biki lokaci kusa mu sha shagali.” Ta ƙarashe maganar suna tafawa da Mom ɗin Mariam.


Leena ta cika ta yi fom ji take kamar zuciyarta za ta tsaga ƙirjinta ta fito, ita da ta ci burin auren David tana faɗa wa ƙawayenta babu wani namiji da za ta iya aura sai shi, haka shima ba shi da mata sai ita duk da kuwa ba ta samun fuska a wajen shi, idan ma ta kira shi a waya ba ya ɗauka in ta ci sa'a ya ɗaga daga iya gaisuwa zai ce yana da aikin yi sai an jima, cikin wani irin yanayi na ruɗewa ta sunkuyar da kanta tana shanye kukan da yake son fallasa sirrin zuciyarta.

Ruƙo hannunta Mom ɗin ta yi ta yi ƙasa da murya ta ce “My daughter am so sorry kin ji, karki damu ba ga Daniel ba nan da Emmeka za ki samu ɗaya daga cikinsu ya ce yana sonki, ke da Mariam duk ɗaya ne a wajen mu tun da sister ɗin ki ce.”

Jinjina kai kawai ta yi ba ta iya cewa komai ba, domin in ta ce magana za ta yi kuka zai biyo baya..


Haka aka tattauna Mom ta ce za su chochi domin su yo addu'a ta musamman a kan Mariam da David, sannan domin a sa ranar aure, da haka suka aje maganar Dad brothers ɗinsa suka fita a tare, David ya ja Mariam a kan idanun Leena.


Can gadin ɗin gidan suka fita Mariam ta kasa daurewa ta rungume David tana dariya, ɗago ta ya yi yana murmushi ya ja hancinta ya ce “Wata zuciyarta za ta yi breaking up.”

Dariya ta yi ta ruƙo hannayensa ta ce “Na tsorata sosai da aka ce ka zaɓa tsakanin ni da Leena, shi ya sa na rufe ido na gode sosai da ka zaɓe ni a matsayin abokiyar rayuwarka, ni kuma na maka alƙawari zan zauna da kai a kowani hali za ka shiga.”

Murmushin gefen baki ya yi yana gyaɗa kai, kallon ta ya yi ya ce “Yanzu za ki iya son duk abin da nake so? Sannan ko me na kawo za ki amshe shi hannu bibbiyu?”

Cike da tabbatarwa za ta iya ta kwanto da kanta bisa ƙirjinsa cikin shauƙi ta ce “In dai ba sayar da ni za ka yi wa masu shan jini ba komai ka faɗa zan yi maka, da alama kana tantama a kan soyayyar da nake maka.”

Agogon da ke daure tsintsiyar hanunsa ya kalla sannan ya ce “Nasan ku mata kuna da kishi, yanzu fa duk soyayyar nan da kike mini idan na ce miki ina da wata a gefe wadda nake so sai ki tashi hankali ko ki nemi kashe ni.”

Dam ƙirjin Mariam ya buga amma ta dake ta ce “No problem dan kana da girlfriend a wani waje, ni dai fatana ka so ni ka zauna da ni har karshen rayuwata karka rabu da ni, kuma ko da ka auro ta karka fifita son da kake mata a kan nawa, ina so ka so mu daidai ni da ita kar ka bambanta mu.”

Da mamaki ya kalle ta dan ya tabbatar ya ce “Kin san wani abu?”

Girgiza kai ta yi tana sakar mishi da murmushin masoya, shi kuma ya ci gaba da magana, “Da farko ban ji sonki a zuciyata ba sai kwanan nan da na fuskanci irin kewar da mutum yake ji idan ba ya kusa da wanda yake so, a kan ta ne na fara jin tausayin ki yadda kike nuna min so shi ya sa yanzu na zaɓe ki domin na yaba halayenki ba kya yawon hotel da gidajen rawa, ina matuƙar son Didi fiye da yadda nake son kaina, ina matuƙar tausayawa rayuwarta domin ita ɗin marainiya ce ba ta da uwa, a wajen wadda take matar Dad ɗinta wahala take ba ta.”

Cikin nutsuwa ya kwashe komai na rayuwar Sidra da ya sani ya faɗa mata, domin ya ji a zuciyarsa Mariam ita ce kaɗai za ta fahimce shi a wannan yanayi da yake ciki.”

Duk da kishi mai zafi ya taso wa Mariam amma ta danne domin ganin ta faranta mishi rai ta ce “Gaskiya abar tausayi ce ya kamata ka yi wani abu a kai kafin ka auro ta, amma kana ganin Mom za ta amince da hakan? Sannan a ina yarinyar take? Ko Baturiya ce ?” Ta faɗa a sanyaye.

Tashi ya yi tsaye hannunsa cikin aljihu ya ce “Haka nake fata, ba Baturiya ba ce ina son ki riƙe mini wannan sirrin daga ni sai ke.”


Karaf a kunnen Leena da ta ƙaraso ta kasa kunne dan ta ji me suke faɗa.


“Karka damu babu wanda zai san da wannan sirrin daga ni sai kai, kuma ina son ka kaini na ganta da idona domin mu saba da juna.”

Ajiyar zuciya ya sauke ya dafa kafaɗunta, “Thank you Mariam.”

A hankali ya yi hugging ɗin ta ya wuce ya bar ta a nan, har zai wuce ya ji kamar akwai motsi a gefen flower ya kalli wajen, Leena ya gani duk da ta ɓoye amma ya ga hannunta, hmm kawai ya ce ya yi kamar bai ganta ba.


Tana ganin ya tafi ta fito da sauri ta nufi in da ya fito, a zaune ta samu Mariam tana daddana wayarta cikin nishaɗi, kwafa ta yi ta tsaya a gaban ta hakan ya sa ta ɗago da kai ta kalle ta, ganin ita ce sai ta basar ta ci gaba da abin da take. Wannan abu ba ƙaramin ƙona mata zuciya ya yi ta kai hannu za ta fincike wayar Mariam ta janye hannunta da sauri, kallon kin raina ni ta mata ta miƙe tsaye tana murmushi ta juya za ta bar wajen, domin ta ji ba za ta iya tanka mata magana ba ko da ta yi.

Taku biyu ta yi ta sha gaban ta tana bin ta da kallon wulaƙanci, tafa hannu ta yi ta ce “Sannu da ƙoƙari Mariam kin kwace mini saurayi, amma ki sani ko da kun yi auren ba za ki taɓa jin daɗin zama da shi ba, domin na tabbatar jikinki yake so ba ke, da a ce ke yake so me ya hana tun wuri bai ce yana sonki ba sai yau? Na faɗa miki kin taro Mach ki tsaya ki ga me zan yi.”

A wulaƙance Mariam ta bi ta da kallo ta matsa ta bi gefen ta ta wuce tana wata irin kwarkwasa, ciza yatsa Leena ta yi ta wuce fuu..


_Kano_


Ƙarfe takwas na safiyar Juma'a sai ga KB da abokansa sun dira a ƙofar gidan su Sidra, wai ya zo zance kuma a ba shi dama ya turo iyayensa. Tun da ya kira Inna ya faɗa mata abin da zai kawo shi ta dinga sintiri a tsakar gida, ɗakin su Sidra ta dinga bugawa amma ta ji shuru, a fusata ta buga da ƙarfi ƙofar ta buɗe sai ta ga babu kowa. Baki buɗe take kallon cikin ɗakin kan shinfiɗarsu, wayam babu kowa a ciki ta ƙarasa shiga ta dinga kiran sunanta amma ta ji shuru babu alamun suna a ɗakin. Suwaiba da take kuka ta gaji da jiran a kawo mata Sidra ta mata dukan mutuwa sai ta bi bayan Inna, za ta shiga suka ci karo ta ce “Yawwa ina shegiyar take? Wallahi yau sai na karya ki a gidan nan.”

Janyo hannunta Inna ta yi ta ce “Ba ki ga lokacin da suka fito daga ɗaki ba?”

Suwaiba ta ce ita ba ta gansu ba, sosai hankalin Inna ya tashi ta nufi banɗaki nan ma ta ga babu kowa ta fito ta tsaya ta rasa ina suka je.

Ɗaki ta ja Suwaiba suka shiga tana rarrashin ta suka ji sallama Inna ta fito tana ɗora zani ta amsa, yaron ya ce “Wai an ce ana kiran Sidra.”

Ƙanƙance idanu Inna ta yi ta ce “Uban waye yake kiran ta? To ka koma ka ce mishi muma nan neman su muke yi k...”

Ba ta ƙarasa ba ta ga Sidra ta shigo gidan hannunta ɗauke da leda ita da Safwan, Suwaiba da ke gefe tajanyo wani kalar ashar ta ƙunduma musu ta yo kansu da nufin ta dake su, sai dai kafin ta iso sai ganin mutum biyu ta yi tsaye a gaban ta. Wani irin kallo Audu ke bin Suwaiba da shi, ta juyo ta kalli KB shima kallon tsana yake mata sai ta ruɗe ta durƙusa har ƙasa ta fashe da kuka ta ce “Wannan wacce iriyar masifa ce haka? Ke yanzu ƙanwata kwacan saurayi za ki mini? Ni fa 'ƴar'uwarki ce kin kwace mini waccan mai kuɗin yanzu kuma shima KB kike son kwace min n..”

Tsawar da Audu ya daka mata ce ta sa ta haɗiye maganar, nuna ta Audu ya yi yana muzurai ya ce “Ke tsohuwa ba wani abu ba ne ya kawo ni gidan nan illa kashedi, na zo ne na gargaɗe ki ke da 'yarki idan na sake gani ko jin kun musguna wa yaran nan Wallahi in ban sassara ku ba Allah ya tsinan, ko dan kun ga ba su da kowa sai ku shi ne kuke cutar da su? Wannan zuwan da na yi ya zama na farko kuma na ƙarshe idan har na ji wani abu ya faru sai na tsatstsaga muku jiki da wuƙa.” Ya ƙarashe maganar yana nuna Inna.


Inna da tsoro ya dabaibaiye ta ganin Audu ta kasa cewa komai har ya kai aya a zancensa, Suwaiba ta tashi daga tsaye ta riƙe ƙugu cike da rashin kunya ta ce “Ashe dai kai ƙaramin ɗan iska ne, Wallahi idan ka kuskura ka taɓa ɗaya daga cikinmu sai na yo hayar 'yan daba sun maka dukan da ba za ka amfanu ba nan da shekaru ashirin.”


KB ya ɗaga mata hannu ya ce “Ke dakata malama! Dan na ce ba ke zan aura ba shi ne kike dukan ta? To idan kika sake mata ko da kallon banza ne sai na sa an daure ki ke da uwar taki, kuma kin san zan iya sawa a ɓatar da ku daga doran ƙasa babu wanda zai ce ya aka yi bare ku yi tunanin za a yiwani abu a kai, banza Shashasha ballagaza.”

Kallon Sidra ya yi da ta ƙanƙame Safwan tana kuka, karasowa ya yi gaban ta ya sa hannu zai share mata hawaye ta ja da baya, ɗagowa ya yi ya kalli Suwaiba ya ce “Kinga yarinya mai tarbiya ba ta so na taɓa ta ta san hakan ba daidai ba ne ga mace mai tarbiya da sanin darajar kanta.”

Wani irin baƙin ciki ne ya ƙara lulluɓe Suwaiba amma ba halin ta yi magana, KB ya dubi Audu ya ce “Abokina daga yau na damƙa komai na Sidra a hannunka ka kula da ita, ina sonta sosai tun haɗuwar farko, idan na aure ta zan ba ta farin ciki marar yankewa.”

Jinjina kai Audu ya yi burinsa bai wuce ya ga Sidra ta fita daga wannan kuncin rayuwar ba, jikinsa ya yi sanyi da jin kalaman KB sai dai bai nuna mishi ba, Sidra ya duba ya ce “Ku je ɗaki ƙanwata babu abin da za su ƙara muku, ko da zagin ku suka yi za su ga ɗanyan aikin da zan musu.”

A hankali ta kama hannun Safwan suka wuce ɗakinsu, sai da suka ga sun rufo ƙofa sannan suka bar gidan.


Inna ta ciza yatsa cike da mamakin yadda suka shigo musu gida ba tare da izininta ba, kallon Suwaiba ta yi ta ce “Kwantar da hankalinki 'yar lele in sun san wata ai ba su san wata ba, zan yi maganin su daga shi Audun har saurayin naki, zo mu je ɗaki zan faɗa miki wani abu da za mu yi.” Tana tirjewa haka ta ja ta suka shige ɗaki.


Audu bayan sun fita waje ya fuskanci KB ya ce “Bawan Allah idan har kasan ba son gaskiya kake yi wa Sidra ba ina haɗa ka da girman Allah karka shiga rayuwarta, ita ɗin ba ta kowa ni nake a zaman yayanta babanta ba mazauni ba ne, in dai birge ka take ba son gaskiya kake mata ba ka yi haƙuri ka nemi wata.” Ya faɗa yana tsare shi da idanu.


Dafe kai KB ya yi ya ce “Kasan daga Allah ba wani to ina son Sidra so na haƙiƙa, na maka alƙawari zan kula da rayuwarta har kaninta zan ɗauke su gabaɗaya su rayu a gidana, tun da ka ce mini marainiya ce naji ta ƙara samun mazauni a zuciyata.”

Ajiyar zuciya Audu ya sauke da kyar yake iya gani saboda yadda zuciyarsa ke mishi mugun ciwo na kishin Sidra, amma ya ƙudiri aniyar haƙura da ita matsawar shi zai kula da rayuwarta, baya ya yi KB ya yi saurin ruƙo shi yana faɗin “Subhanallahi! Me ya faru?”

Girgiza kai ya yi ya ce “Babu komai ba na jin daɗi ne, ka ba ni number ka idan babanta ya dawo zan sanar da kai sai ka zo ka nemi aurenta, amma ka taimaka in kun yi aure ka mayar da ita makaranta boko da Islamiya.”

Number ya ba shi sannan ya ƙara tabbatar mishi ba shi da matsala da hakan zai mata duk abin da take so, haka suka yi sallama Audu ya tafi cikin wani irin yanayi marar daɗi tamkar wanda zazzaɓi ya zubo wa haka yake tafiya, shi kuwa oga KB ransa fes zai mallaki abar ƙaunarsa.



Haka suka wuni a gidan suna ɗaki, Sidra saboda da tsoron kar su mata rufdugu ta kasa kunna wayar da ta amso daga wajen Maman Ummi za ta kira David.

Cikin dare Inna da Suwaiba suka lallaba suka lakaɗa mata shegen duka sai da suka sumar da ita, Safwan na gefe yana kuka yana rokon su su rabu da ita Suwaiba ta juyo ta zabga mishi mari ba shiri ya yi shuru, yana ji yana gani aka yi wa yayarta dukan mutuwa.

Bayan ta farfado Inna ta murɗe kunnenta har sai da ta yi ƙaran azaba ta ce “Idan kika kuskura kika faɗa wa Audu an dake ki sai na yanka ki na binne ki daga ke har shi.”

Kasa cewa komai ta yi har suka bar ɗakin, kukan kanshi ya ƙi zuwa sai na zuci take tana shafa kan Safwan da yake rera kuka, ɗago kai ya yi ya ce “Anty ki tashi mu gudu mu bar musu gidan.”

Girgiza kai ta yi ta ƙara rungume shi, so take ta yi kuka ko ta ji sanyi a ranta amma ta kasa sai huci mai zafi take yi, da kyar ta haɗiye yawu ta ce “Gidan wa za mu je Safwan in mun gudu a cikin daren nan? Kuma ka ga ba mu san kowa ba a cikin garin nan daga Maman Ummi sai Yaya Audu, ka yi haƙuri.” Ta ƙarashe maganar murya a shaƙe. Tsayar da kukan ya yi ya ce “Anty to mu gudu gidan wannan likitan da ya kawo ki ranar mana, ba kin ce kun haɗu a kasuwa ba? Kinga in muka je can Inna ba za ta gano in da muke ba.”

Girgiza kai ta yi ba ta ba shi amsa ba, ita kanta da tana da yadda za ta yi ta bar gidan nasu domin su samun sauƙin rayuwa da ta yi, amma babu damar hakan a gareta, hankali ta zame ta kwanta Safwan ta gyara wa kwanciya ta yi rigingine tana kallon silin ɗakin, bacci tuni ya ƙauracewa idanuwanta, nan da na zazzaɓi da ciwon kai suka mata rufdugu







_Maman Nusaiba ce🤙🏻_

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol