Free chapter · Read without an account
Chapter 11
*ZAWAJUL MUWADDA*
Daga alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Mom Nusaiba)_
_(Labarin Sidra)_
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PAID BOOK ONLY N500*
_Saura fage 3 mu gama free fage ɗin littafin ZAWAJUL MUWADDA, ga wadanda suke son ci gaba da karantu za su fara biya kudinsu ta wannan account ɗin_
Account number 0003187186
Name account, khadija Salisu
Name Bank, Ja'iz Bank
_My whatsapp +966577675904_
*SHAFI NA* 1️⃣1️⃣
Da kyar ta iya buɗe idanuwanta lokacin da aka fara kiraye kirayen Sallah, wani irin sanyi take ji mai shiga ɓarkon jiki, ta sake jan hijabinta ta lulluɓa sai ta ji kamar an tsoma ta a ruwa mai sanyin gaske. Tashi ta yi ta rarrafa ta buɗe cikin kayansu ta fito da sauran magungunanta da suka rage ta dinga bincikawa ko za ta ga na zazzaɓi ta sha, can ta hango shi hannu na rawa ta janyo ta ɓalli biyu ta iso gaban butarsu, har za ta afa a baki ta tuna da maganar Abubakar.
“Ƙanwata Sidra karki kuskura ki sha kowani irin magani matukar kina jin yunwa, ki fara cin shan ko da ruwan shayi ne kafin ki sha.”
Jimƙe maganin ta yi ta dawo ta tashi Safwan da kyar yana miƙa ta ce ya je ya yo alwala an kira Sallah, kasa miƙewa ya yi sai ma zubewa ya yi a jikinta ya ci gaba da bacci, jiki ba ƙwari ta bubbuga fuskarsa ta ce “Tashi mana Safwan kar a kabbara.”
Buɗe ido ya yi yana murza su ya zauna, fuskarsa ta taɓa ya ji zafi ya kalle ta da magagin bacci ya ce “Anty zafi hannunki ba ki da lafiya ne?”
Girgiza mishi kai ta yi ta ce ya tashi ya shiga ya ba ta banɗakin wanka take son yi, kallon ta kawai ya yi ya tashi.
Bayan sun gabatar da nafila suna cikin addu'a suka ji an tayar da iƙama, tashi suka yi Safwan ya shiga gaba ya ja su Sallah. Bayan sun gama Sidra ta sake kwanciya zuwa wannan lokacin zazzaɓin ya ƙara tsanani sai huci take, sannu Safwan ke jero mata yana zaune a gaban ta ta ɗora kanta a cinyarsa, ganin tana kyarma sai ya tashi ya ɗauko robar da suke cin abinci ya zuba ruwa, ɗankwalinta ya ɗauko ya saka a ciki ya aje a gaban ta duk ya fara ruɗewa ya ce “Anty bari na miki irin yadda abokina da ina zazzaɓi a school ya mini kuma naji sauƙi sosai.”
Hijabin ya ce ta cire ta kasa tashi sai daga kwance ta janye ya ƙarasa cire shi, matse ruwan ya yi sannan ya ɗora mata a goshi yana mata sannu, idan ya jima sai ya sake mayarwa ya matse ya dora mata, ganin hakan ba zai wadatar da shi ba ya koma ya cika robar ya isa bakin kofar ɗaki ya sa zaninta ya jiƙa shi da ruwan, bai matse ruwan ba yana zuba ya nufo ta da sauri, bai tsaya yin komai ba ya rufa mata.
Wata irin kyarma Sidra ta ɗauka haƙoranta na haɗuwa da yan'uwansu, murya can ƙasa ta ce “Safwan zan mutu ka cire min wannan zanin mai ruwa sanyi nake ji.”
Ƙara rufa mata ya yi yana faɗin “Za ki fasa ji wannan fa abokina ne ya koya mini, ki tsaya da an jima zazzaɓin zai sauka.”
So take ta zame amma ya dinga cewa ta tsaya idan ta jima ba ta daina jin sanyin ba zai cire mata, ba dan ta so ba ta haƙura jikinta na rawa, duk addu'ar da ta zo bakinta yi take, sai rokon Allah take a zuciyarta Allah ya sa ba ciwon ajali ba ne take, Allah kar ya ɗauki ranta har sai ta ga girman Safwan ta inganta mishi rayuwa.
Sun kai kusan minti talatin a haka tukun ta daina rawar sanyi, a hankali zafin zazzaɓin ke sauka tana jin kuzarinta yana ɗan dawowa, Safwan ya yaye mata zanin ya sake tsoma shi a ruwa ya ɗauko ya sake rufa mata. Zama ya gyara ya yi tagumi yana kallon ta, har sai da ta buɗe fuskarta ta ga ya zuma tagumi hannu bibbiyu, wani irin tausayin shi ne ya rufe ta ta tashi a hankali ta jingina da jikin bango, mamaki ya rufe ta ganin har yanzu yana nan a yadda yake ta kai hannu ta janye mishi tagumin. Firgigit ya yi ya kalle ta, ganin ta a zaune sai ya washe baki yana murmushin jin daɗi ya ce “Anty kin gani ko? Dama na faɗa miki za ki ji sauƙi.”
Ba ta ba shi amsa ba ta lallaɓa ta tashi, janyo hijabinta ta yi ta leƙo waje ta ga har yanzu Ƙofar ɗakin Inna a rufe, ajiyar zuciya ta sauke jin mararta ta fara mata ciwo ta sa hannu ta dafe.
A hankali ciwon ke ƙaruwa ta ja ƙafa ta dawo ta janyo jakarsu ta sa hannu can ƙasa ta fito da kuɗi, dubu uku ta zara ta mayar cikin zaninta da ta cukuikuye ta mayar can ƙasa, Safwan ya kalle ta cike da jin daɗin ganin kuɗin ya ce “Anty kuɗin ne da wannan likitan ya ba mu?”
Da kyar ta iya amsa mishi ta ce “Tashi mu tafi gidan Mama mu sayo wani abu mu ci yunwa nake ji, yanzu haka ma cikina ciwo yake.”
Da hanzari ya tashi tsaye ya tattare shinfiɗar ya mayar gefe, kama hannunta ya yi suka leƙa suka ji ba motsin kowa sannan suka fito, a hankali ta janyo kofar ta kulle ta zare key ɗin suka wuce.
Sun kusa isa gidan Maman Ummi mararta ta yi mata wata irin murɗawa babu shiri ta saki hannun Safwan ta durƙushe tana riƙe ciki, a ruɗe Safwan ya ce “Zazzaɓin ne Anty?”
Girgiza mishi kai ta yi domin ka kasa magana sai juya kai take, ganin hakan da ya yi sai ya ce mata zai je ya kira Ummi su zo ta taimaka a dauko ta, ba ta m san ya faɗa ba domin tuni hankalinta ya fara gushewa.
Da sallama ya faɗo gidan Maman Ummi da ke ƙoƙarin haɗa wa Baban Ummi kayan break ta ɗago, ganin Safwan sai da gabanta ya faɗi ta dafe ƙirji ta ce “Safwan lafiya dai?”
Girgiza kai ya yi ya ce “Mama Anty Sidra ce jiya da dare. Ransa a ɓace ya faɗa mata duk abin da ya faru har tahowar da suka yi.”
Salati suka ɗauka Baban Ummi ya ce “Maza don Allah hanzarta ki fita ke da Ummi ku ɗauko ta, gaskiya yaran nan kuna ganin rayuwa.”
A Ƙofar gida Maman Ummi ta sa Hijabi Safwan da Ummi tuni suka yi gaba.
A kwance suka same ta wani dattijo ya tsaya a gaban ta yana tambayar ta lafiya sai ga su, ɗago ta Ummi ta yi ta sunkuya Mamanta ta taya ta ta goya Sidra suka wuce, suna isowa ɗakin Ummi suka kaita aka ɗora ta a kan gado sai huci take, da kyar ta iya buɗe ido ta kalle su cikin wani irin yanayi ta ce “Mama ruwa zan sha.”
Da gudu Ummi ta je ta kawo ruwa ta tallafo ta kafa mata ruwan a baki, sai da ta sha sosai kaɗan ta rage sannan ta janye kai. Ko minti ɗaya ruwan bai yi ba a cikinta ta zabura ta tashi za su maida ta ta ce “Mama amai nake ji.”
Kama ta suka yi suka kai ta banɗaki kafin ma ta sunkuya ta dinga maido ruwan da ta sha, sai da ruwan ya ƙare tas ta dinga kakari cikinta babu komai, ruwa mai sanyi sosai Maman Ummi ta fita ta tsiyayo ta cire mata hijabin, sunkuyar da kanta ta yi ta dinga zuba mata ruwan a ka.
Sai da ta tabbatar ko'ina ya samu ruwan ya ratsa ta sannan ta janye, Sidra ta jima a tsugunne sosai ta ji daɗin ruwan da aka suba mata a ka, ta daina kakarin aman sai dai ciwon mara ya ƙi sauƙi sai ƙaruwa yake, da kyar ta tashi tsaye tana runtse ido. Kama ta Ummi ta yi suka fito lokacin baban Ummi ya gama shiri zai fita sai ya tsaya, sai da suka ƙaraso kusa da shi ya kalle ta cikin jimami ya ce “Sannu Sidra Allah ya ba ki lafiya.”
Kai kawai ta gyaɗa mishi suka yi gaba shima ya wuce, kwantar da ita suka yi suka lulluɓe ta Maman Ummi ta fita ta haɗo mata tea mai zafi ta dawo. Gabaɗaya ta shanye zufa ta dinga karyo mata Safwan na gefe yana mata fifita duk da fankar ɗakin a kunne take, sosai ta ji daɗin tea ɗin sai ajiyar zuciya take saukewa idanuwanta a lumshe, ganin hakan ya sa duk ta kora su waje itama ta fito aka bar mata ɗakin.
Bacci ya fara ɗaukan ta babu arziki ta farka sakamakon wata irin murɗawa da mararta ta yi, hannu ta dinga yarfawa ta tashi zaune ta ji zaman ba zai samu ba ta kwanta nan ma ba babu damar hakan, kamar mai naƙuda ta dinga nishi tana juyi da abin ya gagara sai ta yi goho sai a lokacin ta dan ji dama-dama, hannunta ne ya kai kan wani abu ta ji tauri sai ta janyo, wayar Maman Ummi ce da ta soke da za su taho ta miƙa ta samar kanta ta lumshe idanu. Tana nan a haka sai ji ta yi kamar ta yi fitsari, da sauri ta gyara kwanciya ta laliba kan gadon ta ji babu komai ta ja numfashi a wahalce, so take ta yi bacci amma duk sai ta ji jikinta wani iri kamar dai ta yi fitsari amma ta ji babu, dogon numfashi ta ja ta gyara kwanciya sai ga Maman Ummi ta leƙo.
“Sidra zan je gidan Kawuna ni da Ummi matarsa ta haihu, ki kwanta ki yi bacci har Safwan za mu tafi da an jima zan dawo ba zan zauna ba saboda jikin naki, ga abinci nan Ummi za ta kawo miki na dafa miki taliya da ruwa-ruwa da yaji ki daure ki ci.”
Murmushin yaƙe ta yi ta ce “To Mama sai kin dawo ki gaishe min da Siyama.”
To ta ce sannan ta fita Ummi ta kawo mata ta je a gefen gadon ta fita, kallon kular abincin ta yi tana haɗiye yawu sai ta tashi a hankali ta sauko, tsayawa ta yi sai ji ta yi wani abu yana bin ta Tun daga sama har ƙasa, a hankali da ɗan sunkuya ta kalli ƙafarta ta ɗago a tsorace. Murza ido ta yi dan ta tabbatar da gaske abin da ta gani haka ne, ta sake buɗe ido ta ga da gaske ne nan da nan hankalinta ya yi mugun tashi ta fashe da kuka hannunta duka biyu a ka, a kiɗime ta ɗan ja da baya jin yana kuma bin jikinta, ta durƙushe a ƙasa sai jin ringing wayar Maman Ummi ta yi.
Sai da aka kira sau uku tukun ta miƙe da kyar tana dafe ciki ta janyo wayar, ganin number ba suna sai ta yi shuru tana bin wayar da kallo har ta katse aka kuma kira, ɗagawa ta yi ta ƙara a kunne cikin muryar kuka ta ce “Assalam alaikum.”
David da ke kwance kan gado ba shiri ya tashi jin muryar sahibar tashi ba yadda ya saba ji ba, duk da yasan ta da saurin kuka amma sai ya ji hankalinsa ya tashi, da wani irin yanayi wanda kewarta ta cika mishi zuciya ya ce “My Didin Uncle.” Ya faɗa yana gyara zama.
Da kukan ta amsa, “Na'am Uncle.”
Lumshe ido ya yi ya kai hannunsa kan saitin zuciyarsa ya ce “Waye ya taɓa mini ke Didi?”
Ji ta yi kuka mai ƙarfi ya zo mata ta ɓare baki tana rera mishi, dafe kai ya yi ya janyo rigarsa ya saka duk ya rasa sukonin shi ya ce “Kina so na zo ne?”
Kamar tana gaban shi ta girgiza kai sai kuma ta ce “Uncle zan mutu don Allah ka kira mini Mama ta tafi gidan Kawu.”
Da wani irin mugun sauri ya ɗirko daga kan gado yana zare ido ya ce “Ban gane ba Didi me ya same ki haka da kike cewa za ki mutu?”
“zazzaɓi nake kuma cikina yana ciwo shi ne na..” Kasa ƙarasa maganar ta yi kuka ya ci ƙarfin ta.
A ruɗe ya ce “One minute Didi Yanzu zan kira friend ya zo ya duba ki.”
“A'a ni dai ku zo tare.” Ta faɗa tana narke fuskar yayin da ta tsayar da kukan.
Fita ya yi ya biyo ta palo Daniel na mishi magana amma bai ji ba ya wuce da sauri, harabar gidan ya nufa ya ɗauki mota Maigadi ya buɗe mishi ƙofa ya wuce. Sai da ya nufi airport sannan ya duba wayar ya ga tana kan kiran ya ce “Didi am so sorry kin ji gani nan zan taho Kano, dama na kira ne na faɗa miki zan zo Kano yau, ki daina kukan yana sukar heart ɗina.”
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “To Uncle na daina.”
“good girl, yanzu zan kira shi sai ya zo gidanku ya duba ki, baba ya dawo?” Ya faɗa yana hawa babban titi.
A'a kawai ta ce mishi ya kashe kiran ya ci gaba da tuƙi, ya ƙagara dama ya je ya ganta kafin ya wuce America, shi ya sa ya yi booking ɗin ticket na ƙarfe 10:00am na safiya dan ya faranta mata rai. Yana zuwa jirgin da zai hau bai sauka ba sai ya zauna a mota yana jin kamar ya tashi sama irin na tsintsaye ya ganshi a gaban ta. Sai da ya yi minti goma sha biyar tukun jirgin ya sauka, da yake akwai masinja dayawa da suke jira ba su jima ba jirginsu ya ɗaga zuwa Kano..
Suwaiba na farkawa ta fito ta wanke fuska kawai ta nufo ɗakin su Sidra, murɗawa ta yi ta ji a kulle ta buga ta ji ba kowa ta dinga ɗura musu ruwan ashar tana kiran Safwan, Inna ta fito daga ɗaki tana tambayar ta lafiya? A kufule ta ce “Waɗannan munafukan nake kira me take har yanzu ba ta fito ta ɗora mana abinci ba? Kalli fa har ƙarfe goma ta wuce.” Ta ƙarashe maganar tana buga ƙofar da ƙafa, Inna ta duba sai ta ga a kulle ɗakin ta yi kwafa ta ce “Yo ke kina ta faɗa ba sa ma gidan.”
“Kan uban can! Gidan wa suka tafi?”
Maƙe kafada Inna ta yi ta ce “Zai wuce gidan Maman Ummi ne, ai matar nan idan ba ta fita harkar gidana ba da Malam ya dawo zan haɗa ta da shi ya je gidan ubanta ya kai mata ƙara, ni ba na son shishigi kar ta sake shiga harkar yaran nan tun da ita ba ƙanwar uwarsu ba ce.”
Juyawa ta yi ta shiga ɗakinsu tana faɗa kamar za ta ari baki, Inna na tsaye ta ga ta fito mayafi a hannu da handbag ta wuce fu, tambayar ta take ina za ta je ta ce za ta je inda za ta kawo ƙarshen matsalar ta yi gaba.
Tana fita ta samu mai adaidaita ta faɗa mishi inda zan kaita, bayan sun isa ta ba shi kuɗin har da na komawa ta ce ya jira ta a nan tana zuwa,da to ya amsa ya koma gefe ya faka ita kuma ta tsallaka ta shige wani kango.
A bakin ƙofa ta haɗu da wani ganin ta da ya yi sai ya nufo ta suka rungume juna, cikin muryarsa irin ta 'yan kwaya ya ce “Yane Baby na ganki da safe haka?”
Tsaki ta ja tana hura hanci ta ce “Ina saƙona?”
Kira ya yi sai ga samari uku sun fito ya ce “Ga fa kayana ta zo amsar saƙon da ta ba mu.”
Dariyar suka sa ɗaya daga cikinsu ya koma ya ɗauko wata baƙar leda ya miƙa mata, murmushi ta yi ta ce “Kai amma ka faranta mini rai masoyi, yau ina so ka yi min maganin matsalar da ta jima tana damun rayuwata, na tsani Sidra ba na son ganin ta, dan ta fini kyau da fari shi kenan duk wanda ya ce yana sona sai ta kwace mini shi, kaima dan ba ka taɓa zuwa k'ofar gidanmu ba ne da ka ganta za ka ce ba ka sona ita kake so.”
“Hahaha! Haba dai yan mata ni ai naki ne iya wuya alƙur'an ana jone, yanzu yaushe kike so mu mata aika-aikar? Dan ni fa duk abin da zai ɓata miki rai Baby ba ƙaunar shi nake ba.”
Jinjina kai ta yi cike da jin dadi yau dai za ta ga uban da ya tsayawa Sidra da take kwace mata samari, miƙa mishi ledar ta yi ta ce “Yanzu ba ta nan kuma inda take ba zan tura ku ba ku je a kama ku kuce ni na sa ku, ku bari zuwa jibi za ta fita talla da yamma zan faɗa muku hanyar da take bi, kar kuma a samu matsala Ɗan'ado.”
“Ai karki ji komai kamar an yi an gama,.”
Murmushin jin daɗi ta yi ta ce “Ka shirya yau za mu je wajen partyn ƙawata.”
Ihu suka sa suna tafawa ta juya tana dariya ta wuce ya ce sai sun yi waya ta amsa da to, tana isowa mai adaidaita ya dauke ta har ya juya ta ce “Yawwa ka juya zan faɗa maka ka kaini gidan ƙawata zan ba ka dubu biyar ka ji.”
Mai Adaidaita da barin jiki ya ce “To Hajiya.”
_Maman Nusaiba ce_