Free chapter · Read without an account

38

by Fareeda Aliyu · Taƙaitaccen Tunani

Garam! Na ban ka ƙofar banɗakin, a yayin da na samu nan take kukan ya zo mun. Yanda kasan na kashe kaina haka nake ji. Sai yanzu na tuna ashe ana cewa INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN idan musiba ta same ka........ (Kamar yanda kuka karanta a can farkon littafin). Na cigaba da ba wa Abba labarin abinda ya wanzu har zuwa lokacin da na dawo Zaria da zama.

 

 

Abba ya yi ajiyar zuciya tare da sake gyara zamansa ya ce "Kayan lefen da aka kawo maki ya aka yi da shi?"

 

"Riƙewa nayi mana, ai na cancance su ko don wahalar da na shiga. Har yanzu ko rabi ban ɗinka a ciki ba kasancewar ina da kaya sannan kuma idan ma gansu suna sosa mun zuciya. Suna can gidan Gwaggo Safiya na kai mata ajiyar su."

 

Ya ɗan nisa kaɗan kafin ya ce "Ɗan dakata mana, ba kin san gidanshi ba? Shin kin je kin bincika ko wani abun ne ya faru?"

 

Na yi murmushin taƙaici na ce "Na je. Wani mutumi na tarar, ya kuma tabbatar mun satinsa huɗu da siyan gidan kenan sannan kuma kwanansa biyu kacal da tarewa ranar da naje gidan. Duk da ina ganin zahiri amma kasancewar zuciyata ta ƙi yarda akan cewa yaudara ta ya yi, har shagunan da muke zuwa tare da shi kasuwa naje, na kuma samu amsar cewa wai kayan da ya kawo masu na ƙarshe ya shaida masu wani ne zai ci gaba da kawo masu kayan. Tun daga wannan lokacin nasan cewa da gaske guduwar yayi. Ba mamaki ma shirye-shiryen nan ya yi su ne don na zaci wani abun ne ya same shi ba wai guduwa ya so yi ya bar ni ba."

 

Abba ya yi ajiyar zuciya ya ce "Gaskiya sai Allah ya saka maki."

 

Da sauri na karɓe maganar tasa da cewa "Haba Abba! Ai magana ɗaya ce kawai, Ya Buhari Allah ya sakawa kawai. Wace irin shawara ce da hannunka mai sanda da ba'a yi mun ba? Mai rabon shan duka ai sai ya sha shi. Na dage, na zaƙe akan Yallaɓai saboda ina tunanin so na yake yi da gaske, don wauta ma har ɗauka nayi ni ce nale juya shi."

 

"Yanzu kina nufin tun rabuwar ku da su Ya Buharin a waccan lokacin ba ki ƙara jin zancensu ko ganinsu ba? Shi dai na tuna kin ce ranar da za ki taho Zaria kun haɗu da shi a tasha kaman ko?"

 

Na amsa masa da cewa, Eh to! Ganinsu ne kawai ban yi ba amma na ɗan samu labarin abin da ya faru da su musamman Ya Buhari. Na ji labarin kayan kamfanonin da Daddy yake shirin buɗewa gab da rasuwarsa, custom sun kama kayan ba su saki ba. Don haka ginin kamfani na nan amma ba wani abu abu da zai iya wanzuwa a ciki saboda kowacce hanya aka bi don samun kayan an kasa samu. Kuma abin da ya yi saura na kasuwancin Daddy, 'yan uwansa sun babbake komai domin har lokacin suna kan bakansu na cewa Buhari yaro ne, bai kamata a sakar masa ragamar kasuwanci ba. Sun rufe idon su sun manta cewa idan Daddy ya yi tafiya shine ya ke kula da abubuwan, bayan nunnuna masa komai da Daddy yake yi ma tunda sun sha yin tafiya tare akan kasuwancin ai. Abinda kuma ya jawo rigima tsakanin 'yan uwan Daddy da su Ya Buhari shine abin da suke zaton samu bai kai ko rabin zatonsu ba, ba su da masaniyyar ya kwashe kusan komai ya yi ginin kamfani da kuɗin na shi tare da odar injinan da za'a yi amfani da su a kamfanonin. Don haka abin da ke ƙasa suka riƙe suka hana su Ya Buharin da 'yan uwansa. Na kuma san shi ya ƙarasa biyawa kansa karatun da yake yi a lokacin. Sai dai yanzu ban san ya suka ƙare ba, shin sun ji tausayinsu sun mayar masu fa haƙƙinsu ko sun riƙe? Allahu a'alam. Gidansu na layinmu har yau a rufe yake, shi na ji maganar cewa wai 'yan uwan Daddy sun so sanya gidan a kasuwa su siyar, amma Ya Buhari ya kafe ya jajirce akan babu wanda zai siyar masu da gida, ya ce su riƙe kasuwancin Daddy amma gida kam babu wanda ya isa! Ba irin zagin da basu yi masa ba amma ya ƙi yarda, na kuma san da sun san wurin da takardun gidan nan suke sai dai su Ya Buhari su ji labarin siyar da gidan. Sai dai ta ɓangaren su Anty Aysha ban ji komai ba har yau, tun ina tunanin za mu haɗu da su har na cire rai.

 

Shi yasa ranar da zan taho Zaria ban yi mamakin ganin Ya Buhari a tasha ba, don babu mamaki 'yan uwan Daddy ba su bar masu komai ba. Mamaki ɗaya naji, nasan Daddy lokacin da yana raye ba ya rabo da ba mu kuɗi mu mata ma kenan, balle kuma Ya Buhari, to ko ba shi da tattali ne?

 

Shiru muka yi ni da Abba kowa da saƙe-saƙen da yake yi a zuciyarsa. Wayarsa da ke tsakanin mu na jawo domin ganin ko ƙarfe nawa, da sauri na miƙe tsaye domin har sha ɗaya ta gota. Cikin gaggawa na ce "Bari na wuce gida, ashe dare ya yi haka sosai. Sai dai kar ka manta duka labarin nan da na ba ka ya riga ya wuce. Wallahi ban ƙara kwatanta abin da nayi a baya ba, ƙaddarata ce haka duk da dai naji ana cewa mu ne muke ɗorawa kanmu bala'i mu kuma fake da faɗin haka. Ni kuma a wauta irin tawa, tun kafin mu zo duniya an riga an rubuta rayuwar da za mu yi a lauhul_mahfuz. Sai da safe Abba. Ka gaida gida. Allah ba mu alkhairi."

 

Baban Zaria ya yi ta faɗan daɗewata a waje bayan na shiga gidan, kaina a ƙasa har ya gama faɗansa sannan naje na yi alwala domin yin sallar ishan da ban yi ba. Da yake kuma bana jin bacci, sai na ɗora da karatun Alqur'ani bayan na idar. Farkawa na yi naji an kusa sallame sallar asuba a masallaci, ga Alƙur'ani a gefe, Allah ma ya sa ban kwanta a kan shi ba. Ina kuma idar da asubar na haye kan gado saboda irin yajin da idona yake yi na bacci, don ko azkhar kasa yi nayi.

 

Da yake babu makaranta a ranar sai ƙarfe sha biyu na farka, a lokacin ne kuma na samu na yi wanka na ci abinci ina ta ƙoƙarin kwantarwa da kaina hankali domin babu amfani ɗagawa kaina hankali d9n babu abin da zai canza. Idan ma ina damuwa bai wuce ta ganin Ya Buhari ba game da zancen neman yafiyarsa tunda zuwa yanzu kam nasan ban kyauta ba duk wasu halayensa suka tura ni nayi abinda nake ganin shine daidai da ni a lokacin ba tare da hango me zai je ya zo ba. Ga shi Rukky da za ta mun jagora ba ta samu sararin zuwa ba, ga ƙarin ni ma yanzu na ɗaukantu da son ganin nayi aure ko domin haka ba na fatan Faruƙ ya ji zancen nan balle ya yi mun wata fassarar da ba zan iya ɗauka ba.

 

Sallamar Abba ce ta katse min tababar da nake yi da zuciyata. Gwaggo na kicin a lokacin, ta leƙo suka gaisa ta koma abin ta. Ya kuma yi ƙasa da murya yana faɗa min cewa ya zo ya raka ni wurin Buhari ne saboda na damu akan sai nemi gafararsa, amma shi a ganinsa lamuran rayuwa ne, da ba wai dole sai na je ba. Amma idan neman yafiyar ce za ta sa hankalina ya kwanta, so be it. Sannan kuma ya ƙara tabbatar mun da cewa duk abin da na faɗa masa na sani cewa sirrina nawa ne, daga ɓangarensa babu mai ji in shaa Allah.

 

Sai da muka yi sallah sannan muka doshi gidansu Faruƙ. Abba ya san gidan saboda Fahd Badamasi na ajin mu. A mota ya bar ni ya shiga gidan, kuma bai daɗe na sai ga shi ya fito kirana. Gabana sai faɗuwa yake yi na doshi gidan, sanye nake zumbulelen hijabin Gwaggo da na ɗauka aro, sai a lokacin ma nake jin da ma na ɗauko niƙabin da take sawa idan zasu je islamiyya na sakaye fuskata da shi.

 

Kafin mu ƙarasa wurin da Buharin yake ne, Abba ya ke faɗa min cewa Faruƙ baya nan ya fita, Buhari ne kaɗai. Na ji wani sanyi ya ratsani don ba ni da buƙatar Faruƙ ya san akwai sanayya tsakanina da Ya Buhari. Shi ma wayo ya yi wa Fahd akan cewa mun zo neman Faruƙ ne, shi ne yace masa baya nan sai dai anokinsa. Sai Abba ya ce babu matsala duk ɗaya ne ai. Muka kuma ci sa'a yana can bayan wani gini, ya kishingiɗa akan darduma yana karanta jarida, wurin da ƙarancin mutane ko zan iya cewa babu kowa a wurin. Kafin mu ƙarasa kasancewar hankalinsa bai zo kanmu ba, sai na samu sararin ƙare masa kallo, ashe kallon tsoro nayi masa da na gan shi a makarantar mu, don kam ya ƙara girma, fari da kuma kwarjini.

 

Tunda ya ɗaga ido ya hango mu muna doso wurin da yake, sai ya mayar da idanunsa kan jaridar da yake nazari kamar bai gan mu ba. Sallamar Abba kaɗai ya amsa, kuma hakan bai sa ya ɗago ya sake kallonmu ba balle ya gyara zamansa. Gabansa lemuna ne birkij zube da wasu chocolates da nasan yana son su tun ba yanzu ba.

 

Ganin mun zauna akan dardumar da yake kai ne yasa ya ɗago ido yana mana kallon ya aka yi? Amm dai bai furta haka ba sai ma tayin lemun da ke gabansa da ya yi Abba, don ko kallona bai sake yi ba. 

 

Abba ma bai karɓi tayin lemun ba sai ma magana da ya fara da "Ya Buhari mun zo wajenka akan dalilin da zan iya cewa kai da Halimatu kun san shi. Ta damu ƙwarai akan ta yi maka abu na rashin kyautatawa, butulci ko abu makamancin haka. Mun zo nan ne domin ta neman ka yi haƙuri ka yafe mata. Ni ma ina taya ta roƙonka don girman Allah da son Annabi Muhammad (SAW) ka yi mata afuwa ko da a idonka ba ta cancanci haka ba." Ya yi shiru tare da zubawa Ya Buhari ido yana jiran ya ga me zai yi ko zai ce.

 

Jaridarshiya sake dubawa sannan ya ajiye tare da zama sosai, fuskarshi ta ƙi bayyana komai. Ya ce "Ammmm.... Malam...."

 

"Abba" Abban ya faɗi masa sunan shi.

 

Ya Buhari ya ci gaba da magana "Yeah, Malam Abba. Ina son tabbatar maka da cewa duk abin da Sadiya tayi zaɓinta ne, don haka hakan ba damu na ya yi ba. Kuma da kake zancen yafiya, ai ni ban riƙeta da komai ba. Idan ma ta ɓata mun rai a baya ne kuma ya daɗe da wucewa, domin daga ita har laifin na daɗe da mancewa da su..." Ƙarar wayarshi ta katse abin da yake faɗa.

 

Ya juya tare da kallon fuskar wayar, a take kuma wani murmushi mai sanyi ya mamaye fuskarsa ya ɗaga wayar, "My dear, My love. Ya ya muke? Idan ba ki fara missing ɗina ba to ba zan dawo ba." Sai da gabana ya faɗi ras jin yanda ya kwantar da muryar shi yana magana. Daga ni har Abba muka yi tsuru-tsuru tare da sauke kawunanmu ƙasa muna sauraren maganarda yake yi ta dole har ya kammala wayar. Irin kalmomin da yake faɗi a yayin wayar ne suka ɗaga mun hankali, (ku ɗan dakata please i know I don't have such right) irin nishaɗin da yake yi a wayar kaɗai ya isa ya faɗa maka ko ma wace wallahi ba ƙaramin son ta yake yi ba don gabaɗaya babu alamar ya tuna muna zaune a wurin.

 

Da ya katse wayar ma sai da ya kalle mu da irin kallon 'are you still here?' , ya haɗe rai sannan ya ce "Ina fatan kun gamsu ko? Ni ban riƙeta da komai ba, infact na manta komai. Ji nake yi kaman mafarki ne. Above all, her disappointment is a blessing in disguise for me." Ya kalli wayar shi, sai na ga kaman mai shirin yin murmushi, da alama shauƙin wayar ne bai sake shi ba.

 

Tunda ya fara magana bayan ya kammala wayarsa raina ke mun zafi. Wai yaushe Ya Buhari ya zama mai wulaƙanci? Kunya duk ta rufe ni, kunyar Abba matuƙa nake ji da gaske. Tuni na miƙe tsaye ina ƙoƙarin danne tururin da zuciyata take yi na ce "Well, tunda haka ne, that's good. Na ji daɗi da hakan ya zama kaman mafarki, ina kuma fatan nan gaba kaɗan zai daina kasancewa mafarkin ma gabaɗaya. Mun gode. Allah ya jiƙansu Daddy, Ya kuma yi masu Rahma... (hawaye suka fara tarar mun a ido)." Da sauri na juya na sa takalmana na kama hanyar fita saboda na ga kaman Abba ba sauri yake yi ba. Ko kallon Ya Buhari ban ƙara ba bare nasan a wani yanayi yake. Na kuma ƙulla a raina cewa wannan ce haɗuwar mu ta ƙarshe bi'izinillah. Kai ina ga ma har Faruƙ ɗin ma ya kamata na daina gani don kar mu'amala ta shiga tsakanina da Ya Buhari da kuma wannan banzar da yake wani washe baki over the phone yana wani kiranta 'My love'. Mts!

 

Na yi baƙin cikin rashin ɗauko makullan motar Abba, don har sai da na jira shi na kusan minti uku, ga shi bana fatab Faruƙ ya dawo ya iske ni tsaye ƙofar gidansu don babu wata ƙaryar da za ta suturta zuwa na gidansu. A ƙarshe dai sai ga Abbab ya fito, muna zama cikin motar ya ce "Me yasa Sadiya ba kya danne zuciyarki ne? Ke da kika je neman a yafe maki me ye na fushi? Ko ma me yace ba sai ki ƙyale shi ba?"

 

Na ce "Haba Abba? Ai na ɗauka na fi ƙarfin wulaƙanci a wurin Ya Buhari, ko da wani ne ya wulaƙanta ni kamata ya yi a ce shi kansa bai ji daɗi ba bare shi da kansa ya yi min. Abun haushin ma shine tunda nake da shi ban taɓa ganin ya wulaƙanta wani ba bare ni."

 

Abba ya ce "Ya kamata ki gane cewa yanzu an ɓata masa ne fa, maimakon da muka zo ki buɗe bakinki ki roƙe shi yafiya sai ki ka yi shiru ki ka bar ni nayi magana ni kaɗai, kamar irin ni na matsa maki neman gafarshi saɓanin ra'ayinki."

 

A zafafe na ce "Ka ga dakata Abba, komai ya faɗa maka mtsalarku ce! Ka bar ni naji da zafin wulaƙancin da aka yi mun!"

 

Sai ga mu faɗa baran-baran da Abba a mota. Gida ya mayar da ni yana ta kumburi ya kama gabansa ko ƙala bai ƙara ce mun ba. Ni ma haka na fice daga motar shi ban yi masa sallama ba, ya bule ni da ƙura saboda yanda ya ja motar a fusace, na ƙara ƙulewa, na shiga gida raina a ƙoluluwar ɓaci.

 

Tunda na koma gida a kwance na ƙarasa yinin don komai yayi mun zafi, sallah kaɗai ke tashina. Gwaggo ta yi tambayar ko akwai abinda ke damu na har ta gaji ta kawo ido ya zuba mun don na dage mata cewa babu abinda yake damu na.

 

A daren ranar na kira Rukky tare da faɗa mata dukkanin abin da ya faru a ranar. Ko kaɗan ba ta goyi bayana ba, don har cewa tayi na kashe wayar da muke yi da ita a lokacin na kira Abba na ba shi haƙuri. Saboda dukkanin abinda yayi, ya yi shi domin ni, don me zan watsa masa ƙasa a ido? Har tana daɗa tuna mun sai ya tafi sannan zan gane ko yana da amfani a gare ni ba shi da shi. Hakan duk sai ya sauƙar mun da makaman yaƙin da na ɗauko, na koma tunanin ta wace hanyar zan ba wa Abba haƙuri ni Halima? Abba ba ya fushi, amma duk ranar da ya yi kuma an shiga tara ba uku ba ma.

 

Ina gama waya da ita na dinga kiran shi amma wayar har ta gama ɓurarinta bai ɗaga ba. Na kira ya fi sau biyar. Gaba na sai da ya faɗi, iyakar sanina Abba ba zai yi min fushin da zai ƙi ɗaga wayata ba a tunanina. Ni kam yau abu goma da ashirin ya haɗe mun, bacci dai sai da ƙarfe uku ta gota yayi nasarar ɗaukata.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol