Free chapter · Read without an account

The Father

by Azizat Hamza · AKWAI SO


                      *AKWAI SO*❤

                    Chapter Two                                     

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

                   KANO, 1990

                 

                    The Father.

"SAKINA, Sakina, ga mai kitson ta iso fa" Baaba Ladi ta ƙwalo sunana daga tsakar gida.

"Ina zuwa!" Na amsa ba tareda na yi yunƙurin tashi ba. Littafin da nake karantawa mai suna CHANGES ya ɗau daɗi, gaskiya Danielle Steel ta iya rubutu.

"SAKINA, kin fasa komawa makarantar gobe ne?" Wannan karan Ummana ce ta kira tana bankaɗo labulen ɗakin.

"Gani nan Umma" na yi saurin tura littafin ƙarƙashin pillow. Daga Makaranta na taho da shi, wata 'yar ɗakinmu 'yar Lagos mai suna Adefunke ke taho mana da litattafan Daniele Steel da na Nora Roberts idan ta je hutu gida. Umma bata so ina karance-karancen nan, a cewarta idan na samu karatu sai na kwana in wuni a waje ɗaya ba tareda na assasa komai ba.

Na yi saurin gyara ɗaurin zanina sannan na fito daga ɗaki. Allah Sarki! Baaba Ladi har ta shimfiɗawa mai kitson tabarma tana jirana.

Na zauna aka fara min kitso.

"Kitso da bakin Magariba" Inna da ta fito alwala ta faɗa ganin ko rabin kitson ba a yi ba. Dama akwai ni da cikan gashi ba tsayi, shi yasa idan ana min ƙananun kitso ya ke cin lokaci.

Na dinga mimmiƙe ƙafafuna saboda gajiya, ga hannun yarinyar akwai zafi. Idan ta tsaga kai sau ɗaya sai ta taje sau biyar wai saboda ta samu damar kitsa wajen da kyau kar ya riƙa yanka mata hannu.

Na tsani yadda suke cewa gashina na yanka musu hannu ɗinnan, sai kace wani reza. Shaɗo maƙociyarmu ke min kitso tun ina yarinya amma wannan karan dana zo hutu aka ce wai ta je wankan jego a can ƙauye. Ni duk wacce ta min kitso idan ba Shaɗo ba sai na ji banbanci. Wannan ma ba dan makaranta zan koma gobe ba da na haƙura da kitson.

Abin haushin shine ga ni da iyaye mata har uku amma duk ciki babu wacce ta iya kitso.

Kusan sallan Isha da waje ya fara duhu Inna ta fito da fitila tana haska wa makitsiyar ana yin kitso ina gyangyaɗi.

Innata ta kaina kenan. Matan Babana uku ne, amma ba dai haɗin kai ba. Babu wanda zai zo gidanmu ya ɗauka kishiyoyi ne.

Alhaji Sabo Shehu shine mahaifina. Yana da arziƙi dai dai gwargwado. Ya tara arziƙinsa ne ta hanyar dillancin gidaje da filaye da kuma noma.

Inna ce uwargidansa. Khadija sunanta amma Dije ake kiranta. Baba ya aureta tun yana shekara ishirin a duniya ita kuma tana shabiyar. Auren haɗin gida aka musu shiyasa suka rayu tamkar abokanan juna, har gobe Inna ce abokiyar shawarar Baba.

Shekara ɗaya, biyu, har takwas Inna bata taɓa samun ciki ba wannan ya sa da maganar mutane ya yi yawa ta cewa Baba ya ƙara aure ko za a dace, wataƙila ita ce bata haihuwa. Ai kuwa wata goma da auro Baaba Ladi ta haifi babban yayanmu Yusuf. Daga nan sai Khadija da aka yiwa Inna mai suna, sai Musa, Abdullahi da kuma Muhammadu. Bayan haihuwar Yaya Muhammadu Baba ya auro Ummana. Umma ta haifi Ibrahim, sai ni, Ahmadu, Sulaiman da Aliyu. Itama Baaba Ladi ta sake haifan Kabiru da Usman bayan Yaya Muhammadu.

Inna ba ta taɓa haihuwa ba amma kusan kaf yaran gidan ita take yaye su. Lokacin da Baaba Ladi ta haifi 'yarta Khadija mai sunan Inna halak malak ta damƙa mata ita. Har Khadija ta rasu Inna ta ke gani a matsayin uwar da ta haifeta ba Baaba Ladi ba.

Khadija ta rasu tana shekara goma tun kafin a haife ni. Shi yasa a yanzu nice kawai 'ya mace a gidanmu.

Mu goma shaɗaya ne yanzu a raye. Kasancewata mace ɗaya sukutum cikin maza goma ya sa kowa ke sona a gidan.

Duk da Allah bai bawa Inna haihuwa ba ba za ka taɓa zuwa gidanmu ka ce bata haihu ba saboda tarbiyan gidan Alhaji Sabo Shehu ba a banbanta masa 'ya'ya, shi yasa duk muka taso bamu san wani abu wai 'yan ubanci ba.

Akwai 'ya'yan 'yan'uwa da Baba ya ke riƙewa tun ma kafin ya haifi nasa. Kafin a haifeni akwai 'ya'yan ƙannensa mata biyu da ya aurar a gidan. Ko lokacin dana taso akwai yara kusan bakwai a gidanmu da Baba ke kula da su. A yanzu dai su biyu ne suka rage amma akwai dayawa da basa zama a gidanmu da Baba ke ɗaukan nauyinsu.

A yanzu haka yaya Yusuf ya yi aure shima gidansa babu nisa da gidanmu dan a ɗaya daga cikin gidajen Baba da ke saman layi ya ke zama.

Babanmu iya matakin aji uku na primary ya tsaya a karatu amma kuma shi mutum ne mai son ilimi, shi yasa ma kwata-kwata baya wasa da ilimin 'ya'yansa.

Yaya Yusuf ya yi Diploma kafin ya faɗa harkan filaye kamar Baba. Shi kuma yaya Musa yana bautar ƙasa a garin Oyo, Medicine ya karanta a Maiduguri. Yaya Abdullahi yana aji uku a BUK. Shi kuma yaya Muhammadu Islamic ya ke karantawa a Misau. Ya Ibrahim kam fafur ya ƙi karatun boko, tun yana aji biyu a sakandare ya ke zillewa ba ya zuwa makaranta, ƙarshe dai da Baba ya takura masa cewa ya yi shi ba zai yi karatun ba kasuwanci zai yi. Wannan ya sa ya zamo ɗan hannun daman Baba dan da shi ake shiga a fita a dukkan kasuwanci da Baba ya ke yi.

Ni kuma yanzu ina aji shida a sakandare kuma alamu sun nuna Baba zai barni nima na cigaba da karatu saboda kwanaki da Inna ta kawo maganar wani ɗan ƙaninta na ra'ayina Baba cewa ya yi yana so Sakina ta yi karatu koda kaɗan ne irin na Yusuf.

Kusan za ka ce Baba ya damu da ilimi ne saboda illar da rashin ilimin yai masa a baya. Lokacin da ya fara harkar filaye da gidaje akwai wani lokaci da aka damfare shi filayensa da dama. Wani mugun mutum dake kusa da gwamnati ne ya karɓi filayen da ƙarfi da faɗin cewa filayen an siyesu ne ba bisa ƙa'ida ba, aka sa Baba ya saka hannu a wasu takardu ba tareda ya san me takardun suka ƙunsa ba. Ƙarshe dai wani abokin harkarsa Bayarabe ne da ya nuna wa takardun ya faɗa masa cutarsa aka yi har ma ya bashi shawara akan ya shigar da ƙara kotu. Ƙarshe da aka fara shari'a abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa gashi sai kashe kuɗi ya ke ta yi sai haƙura yai da filayen ya ɗau alƙawarin duk rintsi sai 'ya'yansa sun yi karatu.

Lokacin da aka gama min kitso kaina kamar zai rabe biyu tsabar zafi. Ni dama in dai ba Shaɗo ce ta min kitso ba ba a rabani da ciwon kai.

Aka cewa Uwani mai kitso ta tsaya ta ci tuwo amma ta ƙi. Inna ta fito da kuɗi daga bakin zaninta ta bawa Uwani. Umma kuma ta miƙo mata ƙullin Omo. Uwani ta musu godiya ta tafi

Lokacin da na miƙe tsaye wani miƙa na yi tukun saboda yadda kunkumina ya riƙe.

"Je ki wanke hannunki maza ki zo mu ci tuwo" Baaba Ladi ta faɗa lokacin da na yi hanyar banɗaki.

Tun da na taso na ke ganin iyayena mata na haɗuwa su ci abinci a fanteka ko tray ɗaya. Haka abun yake kuwa har gobe.

Lokacin dana fito har Baaba Ladi ta zubo tuwo a tray. A ƙofar ɗakinta aka shimfiɗa tabarma saboda ita ce ke da girki. Na wanke hannuna bayan na fito daga banɗaki na zauna kusa da Inna dan itace za ta ƙara min nama idan muka fara cin abinci.

"Yau kukan ta ɗan yi ɗaci" Baaba Ladi ta faɗa tana suɗe hannu.

Inna ta ce " Ba a gidan Yelwa kika sayi kukan ba?"

"Na aika aka ce ba a kawo mata ba, shine na sa Aliyu ya siyo min a saman layi"

"Gaskiya kam da banbanci. Da kin ɗan sa mata kanwa ai"

"Wallahi na manta ne" Baaba Ladi ta faɗa tana tauna ƙashi.

"Ungo 'yata" na yi saurin miƙo hannu ina murmushi saboda na san ƙaton nama Inna za ta bani.

Umma ta ce "Yaya ga nama a gabanta fa kuma kike bata naki"

"Maryama ai bani da haƙorin tauna ƙashi yanzu"

"Ni kam Umma ko dai kishi kike dani ne, ba wani nama fa a gabana duk na cinye"

Umma ta yi shiru dan ta san babu mai shiga tsakanina da Inna.

Lokacin da muka gama cin abinci na shiga ɗaki dan na yi sallah. Da na idar Umma ta shigo ta ce na je na samu Baba a falo yana nemana.

Da sauri na miƙe dan na san maganar kuɗin zana WAEC da zai bani ne.

A falo na samu Baba yana sauraron labaran ƙarfe tara na dare a Radio.

Na gaishe shi sannan na zo na zauna kusa da shi.

"Baba an min kitso" na faɗa ina nuna masa kaina.

Shafa kaina ya yi ya ce Allah ya shi Albarka.

"Gobe za ki wuce makaranta ko?"

"Eh, Baba"

Ya miƙo min kuɗi ya ce kuɗin jarrabawar WAEC da zan biya ne. Ya sake miƙo min wani kuɗin ya ce na riƙe kafin lokacin da za a zo min visit, nan na washe baki na fara murmushi. Na tsugunna na masa godiya.

"Kwanaki na ji kin ce idan an gama wannan akwai wata jarrabawar a gaba ko?"

"Eh, akwai Jarrabawar JAMB da za mu yi, shine dama zan zaɓi makarantar da zan je"

"Ayyo! Hakan na da kyau"

Baba ya yi shiru yana sauraron abin da ake faɗa a rediyo.

Na fara tunanin ko in faɗa masa makarantar da na ke son zuwa ko kuma in bari sai lokacin ya yi.

"Ehm! Baba" na fara wasa da kuɗin hannuna.

"Na'am, Sakinatu"

"Dama ina so in ce maka na fasa yin NCE ɗin, Kasuwanci na ke son karantawa a ABU Zaria"

"Shi kike so?"

"Eh, Baba"

"Allah ya nuna mana lokacin. Idan Allah ya bani aron rai duk abinda kike so shi za ki karanta"

"Nagode Babana na kaina" na sake tsugunnawa na masa godiya ina murmushi.

"Allah ya miki Albarka" na amsa da Amin ina murmushi har na fita daga falon.

Dana shiga ɗaki na nunawa Umma kuɗin da Baba ya bani ta ce za ta masa godiya gobe da safe.

Lokacin dana kwanta a kan gado sai juyi na ke ina jin daɗin alƙawarin da Baba ya min. Dama kwanaki ne Yaya Yusuf ke faɗawa Baba wai idan jarrabawar WAEC ɗinmu ya fito zai nema min NCE Azare na yi Diploma dan shima a chan ya gama. Da har na yarda zan yi NCE ɗin daga baya kuma da na ji duk 'yan ajinmu ABU za su tafi sai na ji nima ina son zuwa nan ɗin.

Washegari da sassafe na tashi na fara shirin komawa makaranta. Su Inna sun gama haɗa min kayan tafiya, yaji, ƙanzo, da kayan shayi da cabin biscuit.

Lokacin da na je gaishe da Baba aka ce min ya fita da sassafe anyi rasuwa a anguwa ya tafi jana'iza.

Yaya Abdullahi ne ya rakani tasha na tafi ko gaisawa ban yi da Baba ba.

©AzizatHamza2024


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol