Free chapter · Read without an account

04

by Fareeda Aliyu · Ba Ni Da Masaniyya

Bai ɓata lokaci ba ya hau zagaye da ni tare da gabatar da ni as an ardent listener that i am ga duk ma'akacin da muka haɗu da, wasu na san su ta dalilin jin radion. Tuni na mance wani iri da naji bayan zuwana ganin yanda kowa ke magana da ni cikin sakewa barin ma uban gayyar, kamar irin ya daɗe da sani na a fili. Har da manajan gidan sai muka gaisa kafin mu tafi kai tsaye zuwa studio bayan agogo ya nuna biyar saura minti goma. Kujera aka sa min kusa da tashi na zauna don ganin yanda ake yin shirin kai tsaye.

A duk lokacin da ya sanya kiɗa sai ya yi muting mic mu yi ta hira. Yayi min tayin ko ya gabatar da ni on air na yi magana, amma tsoron me zai wakana tsakanina da Umma da ba ta san ina naje ba ya sa nace a a. Ya rage bai fi saura minti sha biyar ya kammala shirin ba na tuna da camerar da na ɗauko gidan Yaya Muna, a bazata ɗaukar shi hoton da na yi ta zo masa. Murmushi kawai na yi na ƙara ɗaukar wasu hotunan. Daga dole ne su Yaya Muna, Minal, Hajjo da Ni'ima su ga bawan Allahn nan.

Sai kuma yanzu ne na gane dalilin da yasa nake jin daɗin turancinsa, yanayin karyewar harshensa da fulatanci ne ya sa turancin yake fita a haka sai kuma baiwar sanyin murya da Allah ya wadata shi da ita. Bayan kammaluwar shirin kuma sai muka ɗauki hotuna da dama har ma da wasu ma'aikatan da suke bakin aiki a lokacin.

Ganin magriba ta cimma ni sai na kirawo Malam Habu domin ya taimaka ya zo ya ɗauke ni, tsoron bin hanyar nake na tafi gida ni kaɗai. Mr. Jamz kam babu yanda bai yi da ni akan na bari ya sauke ni gida amma na ƙi yarda. Kar tsautsayi ya ja ana sauke ni a ƙofar gida mu yi karo da Alhajinmu. To na ce waye ya kawo ni gida kenan?"

Wurin sallah kawai ya nemar min na je nayi, wurin da ma'aikata mata suke yin sallah ne ma shi kuma ya ƙarasa masallacin da suke yin ta su sallar.

Tare muka zauna da wasu kaɗan daga ma'aikatan waɗanda abokansa ne da alama muna jiran Malam Habu ana kuma ɗan taɓa hira. Sai a wannan zaman na san sunansa Jamil ne. Har sai da na shiga mota sannan na tuna ashe ban ba shi turaren ba, sannan na miƙa masa, yana cikin wata leda ne sai ya buɗe zai ga menene a ciki.

Minal na iske zaune tana jiran na zo na ba ta labari, uwar gulma ba. Daɗina yau Umma aikin yamma take yi, da nasan yanzu haka tana ta faɗan daɗewata. Hotunan Minal take kalla ina yi mata bayanin ko su waye, kasancewar ta fi ni jin radiyo sai ya zama na tafi ni gane su ma.

Wayata ta ɗau ƙara, sai da gabana ya faɗi ganin sunan me kiran watau Jamil.

"Hello?"

"Ammm.... Zara kin isa gida? Ya hanya?"

"Lafiya lau Jamil, ya naka hanyan?"

"It was okay. I'm happy for seeing you today. Na ga turare. Nagode sosai. Ina son ƙamshin sosai da sosai."

Wani sanyin daɗi ya lulluɓeni jin ya yaba da turaren da nake ganin ba wani abu ba ne a wurinsa. Ya ɗan ci gaba da ja na da magana, ita kuma Minal sai zunguri na take yi akan na ba ta wayar su gaisa.

**************


Daga nan kuma na tattara hankalina gabaɗaya kan karatuna don so nake kawai na burge Alhajinmu. Idan kana son ka zama ɗan gaban goshinsa to ka yi bala'in saka himma a boko da islamiyya, don ba ya gajiya da bayar da kyauta in dai har mutuk ya zo na ɗaya a makaranta.

Gefe guda kuma ina haɗawa da karatun Jamb, don ma har mun yi jarabawar muna jiran sakamako. Sati ɗaya tsakani na je wani cafe a kusa da gidanmu dubo jarabawar Jamb ɗin. Jikina sai rawa yake yi duk da a gidanmu babu wanda na faɗawa nayi jarabawar ma bare. Tsoron faɗuwa nake yi don na ga yanzu nasarar karatu ta fara yi min gardama, abin da da ban san hakan ba.

Sakamakon ya nuna ina da 207. Saboda murna ban san lokacin da na fara tsalle a shagon cafe ɗin ba, su kuma sai dariya suke yi min, wasu kuma na faɗin congrats. 

Ko da na koma gida ban faɗawa kowa ba, bari nayi sai da daddare bayan Alhajinmu ya kammala cin abinci na je na kai masa.

Abu na farko da ya fara tambaya ta bai wuce a wurin da na samu kuɗin na siya form ɗin ba, na kuma faɗa masa. Fuskarsa kaɗai na kalla nasan ya ji daɗi ƙwarai amma sai ya ce "Kar saboda kin ci Jamb ki ƙi mayar da hankali a IJMB ɗinki fa."

Ganin yanda farin ciki ya mamaye fuskarshi, har da Umma da take zaune ɗan nesa kaɗan da mu sai na ji wani daɗi mai ratsa jiki. Da alama na goge baƙin fentin da na shafawa kaina a baya.

Sannan da jarabawar promotional ta P1 ta zo, wannan karon duka na cinye komai don ko resit ban ɗauke ba bare kuma a koreni. 11 points na samu ma. Tuni muka shirya da Alhajinmu, barin ma da ya ƙara ganin makin da na samo a post UME don ya wuce iya wurin da suke buƙata ma. A ƙarshe dai himmata ta biya buƙata don na samu matakin farko a Jami'ar Bayero da ke Kano, zan karanta Chemistry.

Duk wannan kujiba-kujiba da nake tayi muna tare da Jamil. Muna yawaita yin waya, a tsakaninmu ba ma jiran sai ɗaya daga cikinmu ya nemi ɗaya, duk lokacin da kowa ya so zai iya kiran ɗayan kuma ya amsa. Ya kawo min ziyara sau biyu ma amma ban bari ya zo gida ba, a gidan Yaya Muna muka haɗu.

Ranar da Yaya Muna ta zo gida muna maganar a tsakanimu sai aka yi rashin sa'a Umma ta jiyo mu. Ta yi min faɗa tare da cewa na tabbata duk me son haɗuwa da ni ya zo gidanmu ba wai gidan Yaya Muna ko wani gida ba.

Ganin na samu admission sai na watsar da CAS ɗin na daina zuwa duk da cewa yanzu ina P2 ne. Hajjo kuma ta samu mataki na biyu kai tsaye a nan bayeron, ni da Ni'ima ne muke level 1, ita za ta karanci kimiyyar tsirrai watau Botany.

**************


Yanzu ra'ayina akan samari ya sauya ƙwarai, domin daga fara jami'a na yi samari har uku da muke tare da su har zuwa yanzu kawai dai ban ba su mahimmanci ba ne. Idan ka ga na ɗaga waya na kira ɗaya daga cikinsu to tabbas wani abin nake son a yi min. Iyakarta kenan don ko hango kaina tare da su ba na yi bare na ji soyayyarsu a raina. An dai yi dace yanzu babu tsana.

Ba sa gajiya da sanya min katin waya sannan ba na bayar da fuskar da za su yi min ƙorafin rashin kiransu da ba na yi. Duk wannan na faruwa ne ta dalilin ƙwallafa raina da na yi akan Jamil, duk da ta ɓangarensa babu wata alamar abin da nake son ya farun. Ina da matsala guda ɗaya, ina da yawan raina watau low self-esteem, sai na dinga ganin ban isa ba ko ban kai ka kuma hakan yana rage min ƙwarin gwiwa a abubuwa da dama.

Na yanke shawarar yin nesa da shi ko hakan zai taimaka min wurin ganin gari da kyau. Sai dai yanayin da Jamil ɗin yake tafiyar da ni ya kan rushe min tsarina ya kuma mayar da himmata baya. Ga misali, idan na ci alwashin ba zan kira shi a waya ba, imma a fili ko a lokacin shirinsa sai kawai na ga kiran wayarshi kamar wanda yake sane da tsarina, yana tuhuma ta aka cewa na zubar da shi na bar shi yana ta kewa ta. Sai hakan ya narkar min da zuciya.

Ko kuma kawai na ji ya kira ni yana tambayata ko ina free zai zo gida ya ganni don ban ƙara zuwa gidan Radio ɗin ba. Kuma babu yanda za a yi ya zo gani na a gida hannu rabbana, sanin cewar ni ma'abociyar kayan zaƙi ce, ya kan taho min da alawoyi kala-kala har ma da chocolates. Sai dai ba ya rabo da cewa "Zara ki rinƙa rage shan zaƙin nan kar ki zama ɓakutu." Na kan yi dariya na ce "Daga baya kenan, sadaka da karuwa."


Wayata ba ta rabo da text messages ɗinsa (tunda lokaci su ake yayi). Idan na ce saƙonnin da yake turo min suna rikita to na yi ƙarya, na kasa gane me yake nufi da ni. A wasu sai ka ga kaman ya ɗaukeni ƙawarsa, a wasu kuma kamar na wuce wannan babin.


Ni'ima kam ta rantse ta kuma akan soyayyarmu muke yi kawai, sam ta ƙi yarda da bayanin da nake yi mata. Ta ce idan mun gaji da rainawa juna hankali za mu bayyana matsayarmu ne. Ni dai nasan matsayina na bahaushiya 'yar arewa idan za mu ƙare rayuwarmu a haka ni ba zan taɓa ɓararwa ba, in dai ba shine ya fito ya ce wani abu ba.

Idan kuwa na saurari shirinsa na ji irin 'yan matan nan masu kashe murya sun kira shi, to kuwa na dinga ƙunci da ɓacin rai akan yanda yake sake masu har yana biye masu on air. Sai na dinga tunanin yanzu haka su ma babu mamaki ya gayyace su zuwa gidan Radio yanda ya yi min. Ba mamaki su ma yana zuwa gidajensu yanda yake yi min. Duk irin waɗannan tunane-tunanen sai su yanke min duk wani jin daɗi.


Ranar wata Laraba muna zaune wurin azahar gaban twin theatres kusa da faculty of medicine, na zauna ne bayan na yo sallah a Mussa Mosque. Jiran Ni'ima nake yi tana cikin lectures, ita Hajjo kuma yanzun nan suka fito kuma ta tafi ta yi sallah ita ma. Na tsayar da me fan ice yoghurt na siya guda uku da zimmar zan sha biyu na ragewa Hajjo ɗayan.

A hankali hankalina ya ɗauku ga wata mota da take doso wurin, sai kuma na lura da kusan kowa na wurin hankalinsa ya karkata can, duk saboda dalilin kiɗan da motar take fitarwa kai ka ce gidan rawa aka zo ba makaranta ba. Ɗan gaba kaɗan da ni aka yi parking, kasancewar gilasan masu duhu ne watau tinted ban ga ko waye a ciki ba sai kuma aka kashe motar da kiɗan gabaɗaya. Daidai nan kuma Hajjo ta iso, ba ta tsaya tambayata ba kawai jan fan ice ɗaya tayi ta fara shan abin ta.

Kafin na kai ga magana sai na ga ƙofar motar ta buɗe, ai kuwa na baza ido ta gefe ina son ganin wanda zai fito daga motar. Khadija Uba ce! Don haka sai na juyo sosai ma fuskance ta don ina son ganin ko mai zai faru. Ashe ba ni kaɗai ce me kallon ƙwa-ƙwaf ɗin.

Har ta fara tafiya tana doso mu sai na hango am sauke gilashin an yi mata magana, ban ji me aka ce amma na ga ta juya ta koma wurin motar saitin buɗaɗɗen gilashin. Bayan ɗan daƙiƙai da suka nuna alamar tana sauraron magana ne sai na ga an buɗe motar, wannan saurayin nata ne da na san su a tare tun CAS, kuma babu kunya babu tsoron Allah ya rungumeta a wurin, irin rungumar nan ta sallama. Kasancewar bayanta ne ke fuskantar mu, hangame bakin da nayi shi ne ya gani, sai kawai na ga ya yi ƙaramin murmushi da kashe min ido ɗaya kafin ya sake ta ya koma motar. A gefena na ji wani yana cewa "Tirrrrrrrrr! Ka ji maza!" Wannan ya ƙara tabbatar min da cewa dukkanmu da muke wurin ke kallonsu.

Na juyo wurin Hajjo da ita ma kallonsu take yi hankalinta kwance irin ko a kanta ɗin nan. Na ce "Watau Hajjo yanzu kin daina mamakin ganin irin waɗannan abubuwan ko?"

Ta yi murmushi mai sauti ta ce "Ke ma Zara, yau kika fara ganin Khady da saurayinta ne? Rungumar ma ai kin taɓa gani a CAS."

Na waiga don ganin ko ta taho wurinmu amma sai ma hangota da wasu suna magana, na ce "Mu kam alhamdulillah, mun samu tarbiyya daga gidajenmu."

Wata 'yar ajinmu da har yanzu ban san sunanta ba, da ke zaune ta bayana ta juyo tare da dafa min kafaɗa domin jan hankalina zuwa gare ta ta ce"Zara ki daina faɗin haka. Ita rayuwa da kika ganta wata irin aba ce, irinsu addu'ar shiriya ake yi masu har ma da mu kanmu gabaɗaya. Idan ba haka ba sai abun ya juyo ya dawo gareka kai mai bakin tsattsagarsu, sai ma ka tsinci kanka kana aikata mafiyin wanda suka yi, sai ka yi sa'a ne ma za ka ƙare da yin daidai irin nasu....."

Da sauri na katse ta da cewa "Allah ma ya kiyaye!"

Su duka suka ce "Amin!"


Hakan kuma yayi daidai da isowarta tana cewa "Shegiya Alhuda-huda, ya kike?"

"Lafiya ƙalau. But wait! Ta ina kuka shigo school ɗin nan yau?"

Ta amsa "Kamar ya ya?"

Na ce "Iyakar sanina dai ba'a shigowa da mota mai tint cikin BUK in dai ta gate aka shigo."

Ta ƙyalƙyale da dariya ta amsa "Kamar ba ki san Amin ba? Sai da muka shigo ya liƙa su da salotif."

"Bala'i!"

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.