Free chapter 路 Read without an account
Two
*_馃挃RANAR YABO馃挃_*
*ADANI WRITERS ASSOCIATION*
By
Mom muhsen
&Asaad
Two
Ten thirty muka fito daga test d'in kasancewar department d'inmu d'aya dashi kuma departmental ce mukayi, jinai kawae an jawoni da d'an karfi nai saurin jiyowa muka hada ido da ita, "miye haka kikeyi?"
Fadeel da Bilal suka jiyo sbd suna gabana kad'an, ganin wacce rik'e da rigata yasa suma suka tsaya suna kallonmu, cikin bacin rai na fizge ina ce mata "karki sake min wannan abun,nadai gaya miki akan meye?"
"Nihal miyasa zaki jaking dinta?wannan ba daidai bane"
Cewar Bilal yana kallonta, ta wani ya mutsa fuska tana tauna cingam, "Ita ta zabi hakan,har ta isa nayi mata mgn tak'i kulani"
"Yaushe kika mata mgnr taki kulaki,kuma ai ke kinfi kowa wannan halin cikin makarantar nan,.........kamar diyar shugaban kasa ba"
Cewar Fadeel yana mata kallon wulakanci irin wanda ya saba, zaro ido tayi tana kallon shi shi kuma ya watsar da ita yana danna wayarsa, "Ayya wai akan rokon da kike min akan in baki no. Dinsa kina son ku tattauna kike tada jijiyar wuya,ohhh ai na dauka ba ke bace kikai mgnr,sai yanzu na tabbatar Gaki gashi saiki ansa ai"
Nayi gaba nabarsu anan,inajin Bilal na cewa "Rabibi ki tsaya don Allah"
Can wurin wani block na tsaya ina kallon wani gurin daban,mamaki nake da har Fadeel ya iya tsayawa da Nihal suna magana, sun dade tsayen kafin suka rabu kuma ina kallon sadda ya anshi wayarta ya sanya no. Din tashi sannan suka nufo inda nake,jinjina kai kurin nayi kuma ko ga fuska ban nuna hakan ya bata min rai ba,bcos nasan kadan daga halin Fadeel ne inhar akan mace ne.
"Bia yunwa nakeji sosai fa"
Mota naje na dauko mana breakfast din sannan suka bini xuwa rumfar da muke yawan zama don karya wa ko kuma tattauna abunda ya shafi karatun mu,na zuba mishi shida Bilal na zuba nawa na koma wata kujerar a can wani table daban inaci,Ina duba hand out d'ina wacce zamu koma lecture yanzu,karad'in Safna najiyo saida na runtse idona sbd rashin class din ta yayi yawa,ga bata jin kunyar kowa tana diyar musulmai haka zata ringa nanik'e namiji, "Wow fadeel,u look so good and nice kayan sun maka kyau kamar kasan kullin cewa nake zanso ace na ganka da black din kaya,sai gashi kamar kaga abunda ke raina,pls lemme take a picture together kaji"
Cheeps dinsa yake ci a natse yana kallonta,Bilal dai bai tanka ba shima cin dankalin kawae yake kamar baisan da zuwanta ba, shima karadinta haushi yake bashi, "please fadeel"
"Bi kiga Ina cin abu ba"
Ta turo baki kad'an, "to pls hurry up"
Haka yaita yanga har ta samu wuri ta zauna sbd tagaji da tsayuwa,zuwa can ta jiyo tana kallona "Hey ba mgn"
Murmushi na mata nace, "Hey ya kike"
Kafad'a ta d'age batace komi ba,ta cigaba da danna wayarta ashe pictures take ta mishi ina lura da ita, saida ya gama sannan ta shige jikinsa ta soma musu hotuna,ta ba Bilal ya dauke su haka ya ansa yana ta daukar su, Dana gama sai na tashi na wuce nabar su.
Inda friend d'ina ke zama na wuce sbd idan na tsaya kallon su Fadeel takaici ne zai isheni, saida lokacin koma wa aji yayi sannan na baro wurinsu na dawo class,sit na samu a gaba kad'an nai zamana ina sake duba hand out d'ina,zuwa can naji ance mun "pls can i sit"
Dago kaina nayi na kalleshi na d'an sakar masa fuska kad'an ina matsa mishi, "Bismillah"
Babu jimawa su Sakeena suka shigo suma suka zauna bayanmu tana zungurino ta baya,nai vanza da ita sbd nasan gulmar da take son yi mun, Fadeel da Bilal suna shigowa Malamin ya shigo muna gaidashi ya rubuta test ga blackboard, ai gaba d'aya class ya dauki hayaniya da surutu sbd babu wanda ya shirya ma test d'insa, hasalima shi sai daf exam sosai yake yin test Dinsa, surutun bai hanashi fara karato questions din ba,baida alamar rubutawa ga board din, dan danan na maida hankali wajen rubuta question din sbd hannuna har rawa yake, "take it easy,na riga na rubuta ki kwafa a hankali"
Na dago kaina ina kallon shi da mamaki, duk da ba abun mamakin bane kam makarantar ba wanda baisan *Fareed wazeer* ba indai wajen kwalwa ne da kokari,don shine overall dinmu tun aji daya har zuwa yanzu da muke aji uku first semester.
Na hadiye abunda ya tsaya mun na kwafi question din na gama kenan naji Dr sama yace "Five minutes only,and all questions over 10 ne" kenan duk question daya five mark Kai wannan mutumin mugun macuci ne wlh,ni daman ban tab'a cin course dinsa ba kuma test ce ke kadani kodayaushe, kallon questions din nai tayi ina mamakin yadda zaka gama su cikin minty biyar, don kowanne yana dauke da uban bayanai,nai bismilla na soma rubutun abunda nasani a cikin question one........ko layi uku banyi ba naji kurin ya anshe takaddar tawa ya soma Rubutu cikin kwarewa da wani irin sauri zaka dauka kamar computer ke typing rubutun,kuma kowane kalma tana fitowa ras gwanin kyau da burgewa, atakaice cikin minty hudu nidashi kaf ya gama mana test d'in, wata zufa naji ta karyo mun sbd mamakin Fareed, tunda zama irin haka bai tab'a hadamu ba Kai mgn ma bata tab'a hadamu ba sai yau, ya aje mun tawa yana cewa silently "ki duba sosai saikije ki bada"
Ya tashi ya nufi wurin Dr sama yai Submitting kamar kodayaushe shine farkon gama test ko exam, "Bia don Allah ki dago mun nayi,wlh ba abunda na iya rubutawa mutumin nan mugun macuci ne"
Sakina ke mgnr daga bayana,kunshe dariyata nayi ina cewa kasa-kasa "kiyi sauri kinsan halinsa inya ganmu zai yagata duka"
Cikin sauri take kwafa inajin sakeena bata iya koda layi biyar ba yace "time is over,kar inganka da pen kana rubutu"
"Shikenan burinsa ya cika daman ban taba cin CA dinsa ba, Dr sama kaida Allah"
Cewar sakeena daga bayana dariya nake kasa-kasa har yazo ya ansa na mik'e ba fice daga class d'in, can gefe da Hall dinmu na zauna ina duba wayata, naji ance mun "Hey"
Na jiyo na ganshi tsaye bayana ya rungume hannunsa a kirji,jakarsa rataye ga kafadarsa guda kasancewar ta goyoce, Fareed dogone amma ba irin tsawon da ya wuce kima ba, amma akaina shidin dogone saida na cire kaina sama na kallai, murmushi na masa kafin ya karaso gurina yana cewa "I'm Fareed Waxeer"
Hannu ya bani sai nabi hannun da kallo ina girgiza Kai nace, "Iam Rabi'atu Ridwan"
Jinjina kai yayi yace "pls lemme see ur phone"
Na kalli wayata kafin na kallai shima din idonsa akaina,sannan na mik'a mishi da yake bud'e take daddannawa yai kafin naji tashi wayar na kara, ya ciro yana nuna mun "ur no."
Murmushi nayi nace "Why?"
Saida yai saving kafin ya bani tawa ya na cewa, "I want be ur friend that's why"
Jinjina kaina nayi ina mamakinsa, kafin na hango Sakeena suna tahowa inda nake shina su din ya kalla yana ce mun, "I will call u in nakoma gida,na gama lecture dina sai gobe kuma"
Jinjina kaina nayi,har ya juya na tuna van masa godiya ba na kira sunan sa yadda zaiji, "Fareed" saurin jiyowa yai yana kallona kafin na masa murmushi nace, "thank you for the test"
Lunshe ido yai yana wucewa kurin,dai dai isowar su Sakeena "Bia yau keda Overall kuma?"
Ajiyar zuciya na sauke nace, "Nima mamaki nake,Fareed din da baya mgn da kowa vaya hudda da kowa dole nayi mamaki"
"Koba komi dai yau ya ceceki test din azzalumin can,kai wlh duk cikin lectures dinmu ba kamar Dr sama wajen k'eta"
Dariya nayi ina cewa, "Anya kuwa, kin mance sadda Dr Samuel yana tashe kenan?"
Zaro ido tayi "Kai Kai,yo na mance wlh amma duk da haka shi baya bada five minutes,suna Kai ten wlh amma wannan dan bakin munafukin.........Kuturuuuu!Bia kamar Nihal nake gani tare da Fadeel?"
Kallon inda take kallo nayi,kafin na dauke kaina ina cewa "banga Marry ba"
"Ke dalla ina miki mgn kina mun mgnr wata Merry can,kale su fa yaushe aka k'ulla wannan alakar ban sani ba?"
Shiru nayi bance komi ba inata duba hand out din da zamu shiga yanzu wacce daga ita zamu tashi, ganin naki kulata yasa ta zauna gefena tana aje jikkarta tace, "Duk course mate dinmu banga sakarai irin Fadeel ba,duk irin iskancin yarinyar can amma yake tsayawa da ita,kodayake ido ga yan mata da ta mashi farrrrr da idanu shikenan"
"Wai sai mgn nake kinyi banza dani, ke ko Haushi bakyaji ne Bia?"
Ciro kaina nayi ina kallonta nace ahankali, "mizance miki?in tayaki mu zagi d'an uwana dake?Aa bazai yuwu ba ki kyalesa yayi abunda yake ganin yafi mishi,rayuwarsa ce fa batawa ba kuma ni hakan bai daman ba"
Murmushi tayi tace"uhmm naga alama kam,"
******
Biyar da rabi muka tashi Sakeena tace zamu sauketa gida sbd batazo da mota ba,Merry kuma ta gudu bamu tashi da ita ba,muna fitowa na wuce mota kurin sakeena ta shiga baya sbd tasan halin Fadeel da dizgi zai iya mata rashin mutunci, munata fira da ita kan bikin da za'ai gidansu na yayarta next week sai gashi shida Yusra girlfriend d'insa da duk kowa ya shaida soyayyarsu a mkrntar, hannunsu cikin na juna, kallona yai daga bakin kofar da zai shigo ya zauna, ya na cewa fuskarsa ba walwala sosai "Ga Yussy zaku gaisa"
Ta d'an lek'o tana murmushinta data saba mai kyau harda dumful dinsa guda biyu masu kara mata kyau tace, "Hey Bia how are u"
Na ansa mata kadaran kadahan, "I'm fine"
"Ki gaida mun Mami da Anti zee"
Kai na jinjina mata kurin,sakeena na baya tana jan tsaki ya juya yana fuskantar Yusra data shagwab'e masa,matsawa yai gabanta yana kissing forehead din ta murya can kasa yace, "good by baby,zamuyi waya anjima"
Sannan ya shigo motar ya rufe,saida na tada motar na hangi wucewar ta wurin driver tadake jiranta, tafiyar shiru kamar ba kowa cikin motar Sakeena ke mun mgn ina bata ansa time to time,har muka iso unguwarsu na ajeta bakin titi da yake ba nisa saita gangara, na juya na dauki hanyar gida har sannan baice mun ba nima bance masa ba,muna isowa nayi parking na kashe motar zan fita naji ya rik'e mun hannuna, na jiyo fuskata a daure tamau nace "cika mun hannu"
Kamar jirana yake yace "bazan cika ba,ki kwata in kina da karfi"
Gwada kwatar nayi na kasa raina ya baci sosai nace, "karka bari muyi rigimar da ban shirya mata ba Fadeel ka sakemun hannuna"
"Miyasa zaki ba wannan katon banzai ya miki test?sbd kawae ki zubda mun darajata muna tare dake har zaki je ki zauna wuri guda dashi,har yana miki test sbd ke din kwalwaki bata jaa ta kifi ce bazaki iya rubutawa ba?"
Jinai kamar ya kwad'amun mari wannan mgnr, idanuna a warwaje nake kallon shi nace cikin rawar murya, "ni kake gaya ma wannan mgnr?.,........to inhar zaki iya akan me zaki bari har ya miki test?wace irin mace ce ke marar aji?"
Ban san sadda hawaye na suka silalo ba sharrrr akan fuskata, mgnr ta shigeni ta ratsa zuciyata ta kuma karya mun ita, lallai na yarda rashin mutuncin Fadeel bai kyale kowa ba, cikin zafin zuciya na fizge hannuna na fito daga motar, bai kyaleni ba ya zagayo yana cewa "wallahi muddin kina son zaman lafia dani karki sake mashi mgn,karki sake zama inda yake inba haka ba.........inba haka ba kuma me?zaka dakile karatuna ne?zaka hanani rubuta jarabawa?ko kuma zaka sanya amaidani kauyenmu kamar yadda kake mun barazana akodayaushe?idan ka fasa Fadeel baka haihu ba"
"Kaiiiii!!,ni kike cewa ban haihu ba?"
Raina yana hasala zuciyata na zillo a kirjina nace, "Ehy na fad'a Fadeel inbaka sanya anyi mun daya daga cikin abunda kake mun barazana dasu ba baka haihu ba.........."
Na ruga cikin gida ina kuka kasa-kasa ba mai hayaniya ba,Ina shigowa naci karo da Yaya zee idona ma baya gani sosai falon akwai mutane amma ita na iya gani, na wuce hanyar dakinmu amma sai mi? Kafin na iya bude kofar harya cinmani cikin zafin rai irin wanda yakan jima bai taso masa ba,ya na zuwa kawai naji ya wanke ni da wani mashahurin mari da saida na kifa k'asa nida jaka ta, wuta ta tadauke d'afff jina da ganina sun dauke na wucin gadi, kafin na fara jin mgnr g
Yaya zee cikin hargowa "Fadeel!,ashe baka da hankali ashe wannan zafin ran naka yana nan?Rabibin ka mara haka?macucin Ina ne Kai?"
"Karki sake zagina,babu ruwanki cikin mgnr nan nan,ke baki isa nayi miki bayanin abunda tai mun ba,kuma wlh wannan kadanne duk ranar da ta sake furta mun cewar in banyi kaza ba ban haihu ba"
Ya wuce yai tafiyarsa yabarmu nida ita,daman ai ita kadai ce sai Haleem da Daddy suke nuna damuwarsu in wani abu ya faru irin wannan,tunda ba yanzu ya fara mun ba tun kafin nayi wayau sosai yake mun wannan halin nashi, Yaya zee ta kamani muka shiga cikin daki har bedroom,lallashina take Sosai tana bani hkr tare da cewa Daddy zai dawo zai dauki mataki akan abun,sbd dagani har ita mun san cewar Mami komi Fadeel zaiyyi bata daukar sa laifi,kullin Fadeel shine mai gaskiya in wani abun yafaru ba gani ba ba ga sauran kannansa ba,yayyen nashi ma Anty Fadeela da yaya zee bai raga musu ba balle kannensa.
Ruwa ta hada mun nayi wanka sadda na fito ta kawo mun abincina har daki, tana ta sake bani hkr tace, "Nasan ba zaaki gaya ma Baba ba,kiyi hkr kinji ko Rabibi"
Murmushi nayi idanuna sun kumbura sbd kukan dana sha,don har a bayi ma saida nayi inajin zuciyata tana nauyi, abubuwa da dama suna zuwar mun amma banda karfin aiwatar dasu, hkr shine kawae abunda zan iyayi.
"Yaya zee ban tab'a sanar da Baba wani abu makamancin wannan ba,sbd babu anfanin hakan ranshi zai ba dad'i karshe kuma mgnr ta dawo ga Daddy zaiga kamar na hadashi da d'an uwansa ne"
Jinjina Kai tayi tana cemun, "ya kama ta ki dauki mataki tsakaninki da Fadeel Rabibi, idan ba haka ba bakida ranar da zaki wuce wulakancin sa"
Bance komi ba haka naita tsakurar abincin har aka kira magriba na tashi na gabatar da sallar, saiga Hidaya ta shigo ko sallama babu cikin isarta tace, "Mami na kiranki"
Bata jira nace komi ba ta juya ta fice,linke abun salar nayi sannan na dauki wayata daga chagy nabi bayanta.
Mom muhseen