Free chapter · Read without an account
017
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
*BOOK 1*
*Page 017.*
Kai tsaye gidan Yayan sa ya wuce kamar yadda yace yana neman sa, kafin ya shiga sai da yayi sallar magriba sannan ya shiga cikin gidan ya samu matar sa da suke kira Anty Khadija tana zaune a falo, ya shiga da sallama sai ga yara guda uku sun tawo a guje ana masa oyoyo. Shi fuska babu fara'a sannan ga ɓacin rai hakan ya saka ɗan yayi murmushin da babu wanda ya lura ya riƙe hannayen su yace, "baku zo gida ba ba ko?." Zama yayi sai ya kalli matar Yayan nasa suka gaisa tace, "wato dai Bebi ba'a ganin ka a gidan nan ko da ziyara sai da dalili."
Yace, "kin san aikin namu, ko yaushe tasowa yake babu excuse."
"Haka ne kam, Allah ya taimaka ya bada nasara. Ai tunda yaran nan suka ji zaka zo shikenan ake murnar ganin ka." Yayi dariya yana kallon su yace, "gashi yau ban zo da chocolate ba ko?." Babbar ciki tace, "zamu je a siyo ko?." Ya ɗan saka sakin fuska yace, "to sai a siyo." Matar Yayan nawa ya sake kallo yace, "Ina Ummi?."
"Tana ciki tana aikin karatu wai debate zasu yi Monday a school tun yau take ta practice."
"Ta kyauta."
"Khalifa kira Yaya" ta faɗa tana kallon ɗaya daga cikim yaran, ai kuwa ya shiga a guje sai gasu tare da matashiyar budurwa wacce zatayi shekara sha huɗu zuwa sha biyar sun fito tace, "Lah Yaya Adnan."
Kallon ta yayi tace, "ina wuni."
"Lafiya lau, ya school?."
"Lafiya lau yaya."
"Yayi kyau" ya amsa kawai tana tsaye a wajan mahaifin nasu ya shigo. Ganin Bebi sai yace, "A'a Alhaji Adnan ko nace Bebin Mummy, ashe kazo?." Anty Maimuna tace, "ya kamata ku ajjiye Bebim nan don Allah, haka zai aure kuna ce masa Bebi kamar wata ƴar tsana?" Ta faɗa tana dariya. Bebi yace, "sun kasa ajjiye suna, tun ina jin haushi har na gaji da magana."
Yaya yayi dariya yace, "zo muje mu tattauna. A kawo mana abinci." Tare suka fita zuwa nasa falon suka zauna ya kalli Bebi yace, "yarinyar nan ce tazo min da maganar wani yaro Mujahid ɗazu, sai nace ai kai zata samu da maganar sai take cemin wai kace baza ta aure shi ba bayan ita kuma tana son sa. Nasan kana da hujja shiyasa nace bara na kira ka naji meye dalilin ka."
Bebi yace, "Yaya in wanda muka haɗa kai dashi aka buɗe asibitin nan namu dashi?." Yaya yace, "wanda ku ka raba hanya daga baya kenan."
"Yauwa, shine to yake sonta. Ba kuma dan komai ba sai dan ya ɓata min rai kamar yadda yake ganin nayi masa." Yaya yace, "Wai wannan wanda yaso ɓata muku sunan asibitin?."
"Shifa Yaya, inda da gaske yana son tane sai a bashi auren ta amma wallahi ba sonta yake ba, ya nemi Mimi taƙi sauraron sa shine ya dawo kan Lubna kawai dan ya samu damar da zai rama abinda na saka aka yi masa."
Yaya yace, "Ai ko yana sonta ai ba mijin aure bane, wanda aka kama yana neman marasa lafiya ta hanyar banza meye amfanin bashi aure?." Bebi baice komai ba Yaya yace, "ai an soke wannan maganar gaskiya, abinda akayi kayi daidai in ka sake ganin su tare kayi mata dukan tsiya."
A lokacin Ummi ta kawo musu abinci ta ajjiye ta fita Bebi yace, "ni na kai Kamal ƙara hisba fa Yaya, yaƙi rabuwa da Maryam ko yaushe yana zuwa wajan ta da rashin dalili, taƙi fahimta, yaƙi fahimta. Na kai shi hisba anyi mana iyaka dashi, abin mamakin a gabana yake cewa shi babu niyar mayar da ita auren ta koda an samu damar hakan."
Yaya ya girgiza kai yace, "Wannan fa laifin maryam ne Adnan itace ta bashi dama wallahi, da bata bashi dama ba da bazai yi ba itace take biye masa har yake zuwa wajan ta. Da yazo ta kore shi, ya sake zuwa bata je ba, bazai sake zuwa ba saboda ta riƙe mutuncin ta, amma da yake bata da hankali wai har shiga motar sa take yi. Hakan da kayi shima daidai ne Adnan Allah ya cigaba da baka ikon yin abinda kake yi."
Ya amsa da amin yace, "Daman ɓacin rai bai barni naci abinci ba" ya yana buɗe abincin yaga dambun shinkafa ne sai farfesun nama a gefe. Rufe naman yayi ya zuba dambun ya fara ci Yaya ya kalle shi yace, "ashe fa kai baka cin nama, gaskiya ka bar daɗi." Murmushi yayi kaɗan yaci dambun sosai, dan ya masa daɗi suna hira da Yayan nasa kafin ya gama ya fita yaje mota ya tafi gida dan ya gaji sosai.
****** Su Manal bayan sun shiga gidan ana ta kiran sallah hakan ya saka Mama zama a tsakar gidan tace, "bani ruwa nayi alwala Manal." Manal tace, "Mama tsakar gidan yayi dauɗa kika zauna."
"Ke bani ni, abinda a cikin ƙasar za'a saka mu wata rana." Manal ta ɗauko buta zuba ruwan ta kaiwa Mama ta fara alwala Baba yace, "nima zanje sallah na dawo" ya faɗa yana fita Manal ma ta fara alwala duk da tana jin ciwon kai.
Bayan Mama ta kammala tace, "ɗauko min sallaya nayi a nan kawai, babu wuta ciki zafi zaiyi." Da to ta amsa ta ɗauko ta shimfiɗa mata ta itama ta saka tata ta yayar da sallar. Bayan ta idar Maman ma ta idar Manal tace, "Mama me za'a dafa miki?." Mama tace, "basai muna da abincin ba, duba ki gani in akwai ɗin dan yunwa nake ji kamar ban ci abinci ba ɗazu." Tana niyar tashi Baba ya shigo bai ƙarasa shigowa ba sai ga Maman Surayya a bayan sa da Surayyan riƙe da babban kula suka shigo.
Maman Surayya tace, "Maman Manal Sannu, kin sha jiki." Mama jin muryar ta sai tace, "bari kawai, sai dai muce alhamdulillah." Manal tace, "Mama, Baba, kullum Mama ce take bawa Surayya abinci kai mun mai yawa. Wani lokacin in Surayya ta tafi makaranta aika min take dashi, abincin na dinga ci har kawo yanzu." Baba sai yaji wani iri cikin takaicin halin mata sa yana da abinci ba babu ba amma matar sa na kwance asibiti babu wanda ya je inda take balle yayi tunanin basu abinci yace, "Allah ya saka da alkhairi." Mama tace, "Haba dai, babu komai wallahi da Manal da Surayya duk ɗaya ne a wajena."
Mama da take zaune tace, "Godiya ta zama dole ai, Allah ya saka da alkhairi. Ni daman na san ko babu raina Manal tana uwa." Maman Surayya tace, "haba don Allah ki bari, Kamar yadda kika ce ni uwa ce a wajan Manal, babu godiya a tsakanin mu ya kamata ace mun wuce wajan nan tun ba yau ba." Surayya ta ajjiye abincin tace, "Milky ga abinci nan kin huta girki." Manal zatayi magana Maman Surayya tace, "ke bana son ki ce min komai. Surayya tashi muje Allah ya ƙara lafiya yasa kaffara ce." Mama ta amsa da amin tana mata godiya sosai sanma suka fita.
Manal ta tashi ta ɗauko plate ta buɗe abincin sai kuwa taga tuwon alkama ne da miyar ganye ta zubawa Maana tace, "Mama kinga tuwon alkama suka kawo mana, kuma kin san Mama daman ko za'a kai min abincin a can har salad sai an saka saboda lalura ta." Mama tace, "Ai Balaraba mutum ce wallahi, tun kuna yara muke tare har yanzu bata ƴar dani ba. Kaf unguwar nan bani da kamar ta, jin ta nake kamar Yayata komai abu ya taso min ita nake faɗawa." Manal ta fara cin na Maman tace, "kuma Mama akwai wani ma, Baba ma zai iya ci har mu ajjiye da safe mu ci."
Mama tace, "Allah Sarki, da yawa haka suka kawo?."
"Wallahi" ta faɗa tana cin tuwon itama Maman tana ci. Ganin duhu yayi sai Manal ta tashi ta ɗauko fitili ta kunna a tsakar gidan ta dawo suka cigaba da ci har suka gama suka wanke hannu suna nan zaune har akayi i'sha.
Bayan i'sha ne sauro ya dame su a tsakar gidan dole suka koma cikin falon a lokaci. matan Baba suka shigo da sallanma, a ciki Mama da Manal suka amsa suka zauna Umma tace, "Ya jikin?." Mama tace, "da sauƙi."
"Allah ya ƙara Lafiya" Inna ta faɗa Manal ta amsa da amin daga haka suka tashi suka fita.
Mama tayi murmushi bayan ta fita bata ce komai ba Manal da take kallon ta tace, "Umma da Inna basa son mu Mama. Ranar da baki da lafiya da naje wajan su na faɗa baki ga abinda suka min ba, ni wallahi duk na tsane su." Mama bata ce komai ba Baba ya shigo da sallama Manal ta amsa bayan ya zauna tace, "Mama akwai tuwo da aka kawo na ɗauko maka?." Baba yace, "A'a kuci, su Umman ki sun shigo?." Manal tace, "eh sun zo."
"Su suka kawo tuwon?."
"A'a maman Surayya ce." Yayi tsaki zai tashi Mama tace, "Alhaji ka ƙyale su don Allah, mu mun ƙoshi ma munci tuwon alkama da aka kawo mana ka barsu kar rai ya ɓacı."
Kafin ya bada amsa Mama ta ace, "Mubeena a ina take kwana ne?." Baba yace, "dana dawo nayi mata waya bana samun ta, Manal ke kina samun ta?." Manal ta girgiza kai alamun a'a Mama tace, "me yarinyar nan take son zama ne? Ko asibiti bata je bafa inda nake, me take so ta zama? kashe ni take so tayi?." Baba yace, "kiyi haƙuri, ƙuruciya ce amma ki cigaba da mata addu'a."
"Yayar Manal ce fa, meyasa ita bata yi abinda take yi?. Wallahi na mutu a yanzu na tabbatar da baƙin cikin ta na tafi lahira. Yarinya kamar mai kunnen ƙashi? Tsakani da Allah a ina take kwana? Tana da inda ya wuce gidan ka ko gidan su Surayya ne?."
Baba yace, "Haba Zahra! Wannan maganar bata kamace ki ba, addu'ar da kike mata ko yaushe ita zaki sake dagewa a kai, wannan kalaman da kike babu abinda zasu gyara sai dai su ɓata, don Allah ki kwantar da hankalin ki kina jin abinda likita yace akan saka damuwa a zuciyar ki. In dai kina yi mata addu'a nan da lokaci kaɗan zaki ga canji a rayuwar ta."
"Damuwa da ita zan mutu ai indai akan Mubeena ne, yanzu tana ina? A ina take kwana don girman Allah?."
Baba ya kalli Manal da ta fara hawaye yace, "kira wayar ta." Manal hannu na rawa ya ɗauki wayar ta sai kuma tace, "bani da kati" ta faɗa murya na rawa. Baba ya ɗauko naira ɗari biyu ya bata yace, "siyo a kanti Bala kizo ki saka, in baya nan kar kije ko ina ki dawo wayata na bayar chaji." Karɓa tayi ta ɗauki Hijjabai ta fita.
Ba jimawa ta dawo ta shiga da sallama tace, "Baba na saka katin."
"To maza ki kira ta." Ba Musu ta kira ta amma bata ɗauka ba ta sake kira ba'a ɗauka ba sai tace, "bata ɗauka, gashi bani da number Bily ƙawar ta na tabbatar daƙyar in basa tare."
Mama ta girgiza kai tace, "kace kuma kar na damu?, in ban damu ba me zanyi?. Sati ɗaya bana gida ban san a inda yarinya take kwana ba ba dole na damu ba. Mubeena! Mubeena!! Hmmmm" ta faɗa kawa bata ce komai ba ganin hakan sao Manal tace, "Baba bara naje gidan su Surayya na dawo" ya amsa mata ta fita dan tana so ta basu waje ne ya rarrashi Mama.
Tana fita Baba yace, "Kiyi haƙuri mana, ki cigaa dayi mata addu'a zata yi hankali in sha Allah."
"Halin uban ta tayi ne kawai, bazata taɓa gyaruwa ba kamar yadda nasan bai gyara ba har kawo gobe in dai yana da rai. Ya cuce ni, ya saka ƴata tayi gadon halin sa tsiya."
"Wai ba magana nake miki ba? ina miki magana kina sake karkacewa, Meyasa baza ki haƙuri kiyi abinda nace ba?, yanzu wannan maganar itace zata gyara Mubeena ko ita zata saka ta dawo? Meyasa baza kice Allah ya shirye ta bane?."
Mama tace, "Allah ya shirye ta." Ta faɗa tana Jan numfashi Baba ya dinga rarrashin ya har ya samu ta ɗan sauka amma shi Kansa zuciyar sa cike yake da son sanin inda Mubeena take.
Manal a gidan su Surayya ta zauna suna hira sai da tara na dare tayi sannan ta dawo gida ta tarar Mama har tayi bacci Baba ma yana falon sa na tsakar gida.
Zama tayi bayan ta cire kaya ta ɗauki wayar ta tana sake kiran number Mubeena amma bata ɗauka. Katin da Baba ya saka mata ta siyi datar naira ɗari ta shiga WhatsApp rabon ta dashi har ta manta kasancewar babu wani abu a kai babu messages ɗin kirki duk yawanci groups ɗin makaranta ne, duba lambar Mubeena ta ganta online.
Magana tayi mata ta zauna jiran amsa shiru bata amsa ba kuma tana ganin ta online sai ta tura mata voice note tana cewa, "Duk abinda ya samu Mama akan tunanin ki Yaya Allah bazai barki ba nima bazan yafe miki ba wallahi, kwanan Mama bakwai a asibiti amma sau ɗaya kika je, inda babar su Bily ce da kullum kina can dan ki faranta mata rai. Bakya kwana ma a gida baki san halin da take ciki ba, wallahi ki kiyayi duniya domin tana gab da kai ki ta baro ki" tana gama faɗa ta tura mata ta kashe datar tayi lamooo tana tunani.
Mama na jin ta duk abinda take cewa tayi murmushi ta share hawayen idanun ta cikin so da ƙaunar ta, babu yadda zata iya haɗa matsayim Manal da Mubeena a zuciyar ta, ta ko wanne ɓangare ita ɗin ta daban ce. Abinda yake tayar mata da hankali yanzu a ina Mubeena take kwana?.
Mubeena kuwa duk kiran da ake mata tana gani kawai bata yi niyar ɗauka bane, lokacin da Manal take mata message tana kan yin waya da Baby shiyasa ma bata bi ta kanta ba hankalin ya yana ga soyayyar sa da ta gama mamaye mata jikin ta cikin lokaci kaɗan. Bata iya tsallake duk abinda tace saboda kar ransa ya ɓaci kamar yadda shima a nasa ɓangaren yake jin ta a jikin sa har ya ƙagu ya dawo kawai saboda ya ganta.
Daga can ɓangaren yace, "Baby." Ta amsa da cewa, "Na'am Baby."
"Gobe zan dawo me zaki tanadar min?." Tayi murmushi tace, "abinda ka ke sl." Yana kallon ta tana kallon sa kasancewa video call yace, "ni ke kawai nake so."
"Ni ai taka ce Baby."
"Ina so goben ya kasance na musamman, da fatan a ɓangaren ki hakan zai kasance ko?." Tayi murmushi tace, "sosai ma kuwa."
Murmushi ya mata tace, "Wai kuwa Baby matan ka nawa? A ina kake da zama?." Yayi ƴar dariya yace, "sai yau kika tambaya?."
"Sai yau naji ina so na sani."
"Mata na biyu, yarana takwas. Maza uku mata biyar."
"A ina suke zaune?." Yace, "mu bar zancen nan Baby, ni yanzu ki ji dani kawai." Tayi dariya tace, "to me kake so?."
"Ke mana. Da zan zamu abinda nake so gobe ina sauka daga lagos na ganki a gidana a zaune da nayi farin ciki."
"Kar ka damu zanyi abinda ka ke so."
"Da gaske zaki zo?." Ta amsa masa da Uhum ya dinga murna yana farin ciki a haka suka raba dare suna waya kafin ta kashe ta tashi daga falon ta koma ɗakin Bily tana zaune tana karatu, ta wuce ta kwanta bata ce mata komai ba itama bata ce mata ba.
Nana Haleema❤️🫶🏻