Free chapter · Read without an account
022
*BAYA DA ƘURA.*
Fitattubiyar2025
©️Nana Haleema.
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11
*BOOK 1*
*Page 022*
Bebi sai da yayi sallar i'sha sannan ya ƙarasa ƙofar gidan su Manal, Baba ya gani ya fito daga masallacin da yake farkon layin yana shigowa a ƙasa yana jan charbi, ganin sa sai ya fito daga motar Baba da ya hango shi sai yayi murmushi ya ƙaraso yace, "Adnan ka ƙaraso?."
"E Baba, barka da dare" ya faɗa yana duƙawa ya amsa yana cewa, "barka dai likita, ya aikin naku?."
"Alhamdulillah."
"To ma sha Allah. Muje ciki" Baba yayi gaba yana bin sa a baya.
Sai da suka shiga soron gidan su Manal ɗin sannan yace, "anyi sa'a ma yau ma da wuta, kasan da yake ni ban amince da wani taɗi a soro ko a mota ba gaskiya, nafi gane a shigo har cikin gida in ta kama a tsakar gida ma a zauna hakan yafi min kwanciyar hankali." Bebi ya girgiza kai cikin jin daɗi da gamsuwa yace, "haka ne Baba." Tare suka shiga gidan babu kowa a tsakar gidan a share tiles ɗin yayi tass sai ganyen bishiya da ya faɗo ƙasa, gidan shiru kamar babu kowa.
Ƙaramin falon da suka shiga jiya nan suka sake shiga an gyara shi sai khamshi yake kaɗan kaɗn Baba yace, "ka zauna a nan zan turo maka ita yanzu nan." Bebi yayi godiya ya zauna Baba ya fita dan ya kiran Manal.
Yana zaune yana danna wayar sa yaji sallamar ta ya amsa yana ɗago kai ya ganta cikin baƙin hijjabin da ya ganta a asibiti, shine lokacin da ya kasa mantawa ko yaushe tunawa fuskar ta yake a wannan lokacin. Shaf ya manta kallon ta yake yi, yaso yayi controlling emotion ɗin sa a kanta amma ya kasa ashe har ta ƙaraso ta zauna daga gefe a kan carpet ɗin da yake falon sai ji yayi tace, "ina yini."
A lokacin ya dawo hankalin sa ya dake kamar bashi ba dan ya shagala da kallon ta shi kansa ya sani yace, "kin yini Lafiya? Ya jikin ki?, I hope kin samu Lafiya sosai?."
Jin tambaya har uku da yayi mata lokaci ɗaya sai ta kalle shi suka haɗa ido ta shagwaɓe fuska tace, "to wacce zan fara amsawa?. Na yini Lafiya, naji sauƙi, eh sosai a samu Lafiya." Jin ta amsa masa duka a tare yadda ya tambaya sai yayi murmushi sosai yana jin wani nishaɗ a zuciyar sa, ya gama lura shagwaɓa a jinin ta take kowa ma yi amsa take yi.
Ganin yana murmushi abin ya bata mamaki tana kallon sa a ranta tana ayyana daman ya iya murmushi yake kullum fuska a ɗaure fuska.
Ya girgiza kai yace, "Adnan Mu'azzam shine sunana, nasan kin san aikina ni likitan zuciya ne." Ta girgiza kai bata ce komai ba ya kalle ta yace, "Baba ya sanar dake dalilin zuwana nasan da hakan, haka kawai Allah ya saka min ke a zuciyata na kasa mantawa dake har sai da nazo gidan nan jiya na samu Lafiya."
Bata ce komai ba yace, "Manal bana son ƙarya, duk wani abu da kika sani ya shafe ki ki sanar dani kar ki yi min ƙarya kat ki ɓoye min wani abu. Manal ƙarya tana sakawa naji mutum ya fita daga raina lokaci ɗaya, dan haka kar ki ɓoye min komai a kan ki. Bazan ce lallai sai kin so ni ba, in kina da ra'ayina daman haka nake fata, in bakya yi haka Allah yayi daman." Yayi shiru yana kallon ta dan yaga yanayin ta amma bai fahimci komai ba yadda take haka take yace, "meye a zuciyar ki?."
Ta girgiza kai tace, "babu komai. Amma ni masu aikin ku basa burge ni, likita bai taɓa burge ni ba, so bana tunanin...." Sai tayi shiru bata ƙarasa ba.
Yayi murmushi yace, "Kina da wanda kike so?." Ta kalle shi ya ɗaga mata kai yace, "na faɗa miki bana son ƙarya ko ɓoye-ɓoye, ina son magana kai tsaye."
Tayi ƴar dariya tace, "ƙarya ba halina bane, bazan kuma fara daga yau ba."
"Okay Answer me."
"Ni bana dashi, dan bani da wannan lokacin, kula da Mamana shi na saka a gaba." Ya girgiza kai cikin jin daɗin hakan yace, "Zaki iya saka Adnan zuciyar ki?."
"Sai na duba naga yuwar hakan" ta faɗa bata kalle shi ba. Yayi murmushi yace, "haka ne, amma nasan you most love him." Sai tayi dariya tace, "really? For what reason?."
"Saboda na yarda da kaina." Tayi murmushi bata sake magana ba yana kallon ta, Allah ya sani yana sonta matuƙar so, daga lokacin da ya fara sonta soyayyar ta tayi masa kamu sosai musamman yanzu da take gashi gata tana kuma murmushi tare da magana mai sanyi cikin muryar ta mai zaƙi.
Haɗa ido suka yi sai yace, "Ki bani phone number ki." Ta kalle shi ido cikin ido kamar zata yi magana sai ta fasa ya miƙa mata waya ta karɓa tana saaka number kira yana shigowa taga an rubuta Rumana.
Miƙa masa wayar tayi ya karɓa ganin wace take kiran sai ya ajjiye bai ɗauka ba suka yi shiru babu mai magana a cikin su. Kallon ta yake yi yana ji farin ciki sosai a zuciyar sa, Allah ya sani yana son Manal so mai yawa. Ƙara wayar ta yi ganin mai kiran sai ta ɗauka tace, "Yaya."
Bai ji me akace mata ba sai yaji tace, "subscription din ya ƙare." Cikin shagwaɓa yaji ta kuma cewa, "nidai Yaya kawai ka shigo yanzu, in kace sai gobe ni bana so na kai gobe ban gama ba" ta faɗa kamar zatayi kuka. Sai yaga tayi murmushi tace, "to ina jira." Ta yanke wayar ta ajjiye tana murmushi yana kallon ta sai suka haɗa ido ta sake faɗaɗa murmushin tace, "na tafi?."
Wani irin abu yake ji a zuciyar sa na tasowa yana game ilahirin jikin sa, ko ba'a faɗa ba yasan kishi ne hakan ya saka shi zuba mata ido kawai yana kallon ta. Allah ya sani yana da kishi shi kansa ya sani. Ya sauke numfashi domin ya san kishin Manal sosai, zuciyar sa zafi take yi jin tana waya da wani.
Ya sauke numfashi yace, "Manal you have to be careful ba komai nake iya controlling a kai ba lokacin. Kina waya a gabana hakan zai bai min daɗi ba."
Manal ita mamaki ma yake bata daga zuwa zance zuwan farko sai a dinga kafa mata sharaɗi kamar mijin ta?. Sai magana yake yi dan ita bata ɗauka ma yana da magana haka ba, wai ba komai yake controlling ba kamar wanda yake auren ta. Ta kalle tace, "Yayana ne." Bai bata amsa ba sai kallon ta da yake yi tana kallon sa kafin ya janye Idon sa yace, "Ban san kina da Yaya ba."
"Ynzu na sanar da kai." Ya kalli gefe ya kulle ido ya buɗe, in ba soyayya ba taya wannan yarinyar zata zauna a gaban sa yana faɗa tana faɗa?. Ya tabbatar ko Mimi zata iya girmar ta, amma itace yana faɗa tana mayar masa inda sune da yanzu zanen yatsun sa sun bayyana a fuskar su.
Sake kallon ta yayi ta sauke kai ƙasa tana wasa da wayar ta yace, "sai da safe."
"Allah ya tashe mu Lafiya" ya faɗa tana tashi itama ya ajjiye kuɗi a inda ya tashi baice komai ba ya fita ta bishi da kallo, ita dariya ma ya bata wallahi da mamaki, daga zuwa zance sai a fara mata zancen bana son kaza ba'a son kaza.
A haka ta koma cikin gidan Mama tace, "Manal ina fatan kin amince dashi?."
"Wanne irin na amince Mama? Kina ji yana kafa min sharaɗi daga zuwan farko?, shi baya son ƙarya kuma yana da kishi kamar wanda ya haife ni ko yake aurena."
Mama tayi dariya tasan halin Manal ɗin ta bata son rainin hankali sannan akwai faɗa duk da kuma akwai surutu kamar aku tace, "ai ya faɗa miki gaskiya ne Manal, gwara ku saba tun yanzu."
"Yaya Haroun ne fa kawai yayi min waya dan na ɗauka muna waya shine ya dinga kallona irin zai zane ɗin nan fa Mama, shine aka fara cemin ana da kishi" ta faɗa tana dariya.
Mama ma dariyar tayi tace, "kema da laifin ki meye na ɗaukar waya a gaban sa?."
"To Mama Yaya Haroun ne fa?."
"Na sani ai, amma ai baƙo ne dake sai ki bari ai kin fito sai ku gaisa."
Manal tayi dariya Mama tace, "kina jin a zuciyar ki zaki iya amincewa dashi?." Manal tace, "gashi nan dai Mama, bashi da fara'a ko kusa ni sai jiya da yau naga dariya, sannan yana da shariya da faɗa."
Mama tayi dariya sosai tace, "Manali ta kenan, Nidai ina miki sha'awar aure sa duk da bana ganin rashin fara'ar tasa." Tayi dariya itama tace, "to Mama zamu gani dai" ta faɗa tana tashi ta shiga ɗakin su ita da Mubeena tana dariya dan bata ɓoyewa Mama komai.
Shi kuwa farin ciki farin ciki, ɓacin rai ɓacin rai haka ya koma gida, bai yi niyar shiga wajan Mama bama ta window ta gano shi ta kira shi ya shiga ta bi shi da kallon tuhuma tace, "zance kaje ne Bebi?."
Ya kalli Maman alamun bashi da gaskiya zaiyi magana tace, "in ma can kaje na faɗa maka kayi ganganci, kana ɓatawa ko wacece lokaci ne domin kuwa kai mallakin Rumana ne, ya kamata ka san da wannan tun ba yanzu ba, babu wata mace da zata zama mallakin ta matuƙar Rumana tana da rai. Sannan gobe ba jibi, kaje ka samu Yayan mahaifin ka aje gidan su Rumana a nemo maka auren ta, kar kayi min bayani akan wata mace na riga na faɗa maka tun ba yau ba. Indai ina raye baka da mata sai Rumana ka jingine ko wacece a gefe, in kuma ban isa da kai ba dai zan gani" tana gama faɗa masa haka ta koma ciki. jikin sa yayi sanyi sosai, gashi soyayyar Manal tayi masa kamun da bazai iya haƙura da ita ba, gashi kuma dole yayi abinda Mama take so, to ya zai yi?.
Yana shiga ɗaki zama yayi a kan kujera ya zubawa waje ɗaya ido cikin rashin sanin abinda zai yi, tashi yayi ya shiga ɗaki ya canja kaya zuwa ƙananu ya fito ya hau mota ya wuce asibiti.
Yana shiga da Dr Hadiza suka haɗu zata fita tace, "barka da zuwa Dr." kai ya ɗaga mata kawai ya wuce ciki a reception ya tarar da Huzaifa yana niyar tafiya ganin ya wuce shi sai yabi bayan sa daman akwai abinda zai faɗa masa.
Haɗuwa suka yi da Hamza ya fito daga maternity yace, "Ga Bebi ɗin can yazo, muje muyi masa zancen ko?." Ya amsa suka wuce suka same shi a tsaye ya juya baya ya harɗe hannayen sa a ƙirji Hamza yace, "Yauwa Bebi kana ji, akwai machine ɗin nan da aka siyo to custom sun kama shi a jirgin ruwa, don Allah ka yiwa Abba magana bazai rasa sanin wani ba a sake su don Allah. In machine ɗin nan yazo mune asibitin farko da muka fara mallakar sa a kaf nigeria." Huzaifa yace, "Akwai sabbin ma'aikata da muke tunanin ɗauka this year, shima yana da kyau ka nutsu mu duba cv ɗin su mu gani, ni nan da wasu kwanaki zan je Qatar Daddy yana son ganina, kaima kace min akwai contract ɗin ku da india."
Sai a sannan Bebi ya juyo ya kalle su yace, "kuyi abinda ya dace kawai, zan samu Abba na sanar dashi zancen machine ɗin. Amma batun wani members kawai ku yi." Huzaifa ya kalle shi yace, "akwai damuwa ne?."
Kamar jira yake yace, "Na rasa ya zanyi, Mummy tana cewa in ma akwai wacce nake so na ajjiye ta a gefe indai tana raye bani da mata kamar Rumana. Na shiga tashin hankali sosai, na farko bazan iya tsallake maganar ta ba, na biyu bana son Rumana a yanzu, na uku yarinyar da nake faɗa muku Allah ya ɗora min ƙaunar ta fiye da tunanin ku. Gabaɗaya komai baya min daɗi."
Hamza yace, "to kayi haƙuri ka aure su duka su biyun." Ya kalle shi yace, "wallahi bana son Rumana, in na aure ta kamar tayi nasara a kaina ne, kullum gadarar ta sai na aure ta ko bana so."
"Haka zaka yi haƙuri kayi na dan ita na dan saboda Mama, ita kuma waccan ɗin ka haƙura da ita in da hali." Ya girgiza kai yace, "bazan iya ba wallahi, baku san abinda nake ji a kanta ba shiyasa ku ke cewa haka. Ban taɓa son wani abu lokaci ɗaya kamar yadda nake son ta ba, bana so na rasa ta. Bana son ɓatawa Mummy rai, in akwai mai son farin cikin Mummy ni ne, amma....!" Sai bai ƙarasa ba yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya.
Sun lura yayi rauni sosai, da alama abin ya taɓa shi har zuciyar sa yake maganar. Huzaifa yace, "Ka cigaba da addu'a kawai, kar ka daina sauraren ita sabuwar saboda kana sonta, in duka matan kane sai ka aure su. Ni a shawara ta in Mama ta matsa ka samu kuyi magana kace mata zaka auri Rumana amma ta bari ka fara auren ita wacce ka ke so ɗin daga baya sai ka aure ta, zata iya amincewa saboda tasan baka yi mata ƙarya sannan kuma itama Rumana an bata dama ta farko har ta auri wani bakai ba, duk da lokacin kana sonta ba'a matsa mata ba aka bari ta auri wani ba kai ba, kaima ya kamata a baka wannan damar."
"Anya Mummy zata amince kuwa? Bata da burin da ya wuce na auri Rumana."
"Zata iya amincewa mana ai ba ƙin auren nata kayi ba ka fahimta?."
Ya kalli Huzaifa yace, "to ƙarya nayi mata kenan ko da gasken zan aure ta ɗin?."
"Zaka aure ta mana, kaima ai baza yi mata ƙarya ba?." Ya girgiza kai yace, "wai kasan yadda na tsani batun aure akan yarinyar nan?." Hamza yace, '"mafita kake nema, zancen ka tsana duk bai tashi ba ai Bebi. Dan Mama zaka yi ba don ita ba." Ya sauke numfashi yayi shiru baice komai ba dan bai san abinda zaiyi din ba.
Mujahid yana tsaye a bayan su yana jin duk abinda suke faɗa,yazo ya yi masa albishir akan yayi nasarar fara soyayya da ƙanwar sa sai yaji abinda yafi soyayya da ƙanwar sa ma dadi, yana tsaye yana girgiza kai a zuciyar sa tana faɗa masa ba mutuncin ƙanwar sa ya kamata ya taɓa ba, wacce yake so ya kamata ya fara da ita domin shima abinda yake so ya raba shi dashi. Murmushi yayi daga bayan su yace, "Ina da Shawara...." Duk a tare suka juya suna kallon sa cike da mamaki.