Free chapter · Read without an account

7-8

by Fadila Lamido · HAWAYEN ZARGI

HAWAYEN ZARGI

         By

Fadila Lamido

                         Page 7-8

      "Bazafa ki takura min da rakin nan naki ba"

   "Rakinmu dai dan kaima cewa kake ba a wasa da ciki..."

Bakin shi da ta ji cikin nata ya sata dole tayi shiru bayan minti biyar ya sarara mata, don haka Asma'u ta lashi lebenta tare da cewa "Abin da ka iya kenan"

  "Ashe kin fahimci hakan" Ya fada cikin murmushi sannan ya tashi zaune tare da cewa "Mu je mu kwanta."

   Yau a dakinta suka kwana suna manne da juna duk da cewa be nema wani abu ba amma suna manne da juna.

Bayan kwana biyu Habibullah ya yi sallama ya tafi, har gida Saminu ya zo suka wuce, Lokacin da aka dawo da su Khalil daga makaranta ji ta yi daban su kan su yaran duk jikin su a sanyaye suka dawo.

   Da wuri ta raka yaran dakin su tare da yi masu addu'a, sannan ta fito ta koma dakinta ta yi shirin kwanciya ta kwanta, sai dai bacci yaki daukanta har sha biyu da rabi ta yi amma idonta babu bacci kwata kwata, Habibullah keta fadu mata arai juyi kawai take babu alamar bacci a idonta ganin daya ta yi ta dauki waya ta danna kira...

  Kamar me jira, bugu daya ya daga tare da cewa "Ba ki yi bacci ba?"

  "Ya Habibi na kasa bacci kwata kwata wallahi gidan babu dadi."

  "Hmmm, Habibty ai dama nina san bazan iya bacci ba.

  "Me yasa baka kirani ba?"

 "Banson in hanaki bacci ne, ni fa gaskiya bana son tafiye tafiyen nan."

  "To ya zamu yi Ya Habibi amma dai fa gaskiya gidan babu dadi."

  "Hmmmm, ina yarana?"

  "Yau da wuri suka kwanta duk basu da walwala ita Najma ma zatonta gobe zaka dawo tana ta cewa daga mun yi bacci mun tashi Daddy mu zai dawo."

  "Allah sarki, amma kin mu su addu'a ko?".

  "Eh na mu su."

 'Kin kyauta, Allah yayi mu ku albarka."

 "Amin, Ya Habibi!"

 "Na'am Habibty"

 "Yanzu idan ka mutu ka barmu yaya za mu yi?"

 "Habibty bazan mutu yanzu ba, in sha Allah sai mun tsofa da yaranmu, kinga lokacin duk sun girma sun samu abokan rayuwa, ni da ke kuma ina fatan mu mutu rana daya, don ina kishin wani ya shiga gonata ko bayan raina gaskiya, ina ji ajikina don ni kadai aka yi ki, idan kuma ta Allah ta kasance na rigaki mutuwa don darajan Annabi karki yi aure Habibty, ki zauna ki kula da yaranmu ko baza ki iya ba?"

  "Zan iya mana, wai kai har yanzu baka gama karantata ba ne, ta yaya zan iya rayuwa da wanin ka, kaifa da kanka kana cewa samun miji kamarka sai an tuna, da gaske ne fa ya Habibi, kana kokarin sauke duk wani hakki dake kanka, sannan shekaranmu shidda da aure baka taba nuna gajiyawar ka ba, ko amaren da aka daura musu aure yau bazasu nuna mana son juna ba, jin dadin zama da kai Ya Habibi shi ya hana min bacci yau, dumin ina ji a jiki na ma rana daya za mu mutu, dan zuciyar Habiba bazata iya rayuwa cikin Duniyar nan ba tare da Habibullah ba, idan har zan samu labarin mutuwar ka mawiyacin abu ne na sake numfashi.

  Lumshe ido Habibullah ya yi tare da cewa "Allah yai miki albarka Habibty, yadda kika shaidai ni nima zan miki kyakyawan shaida, domin nasan soyayyar mu daga Allah take ko kadan bana tantama akan son da kike min, duk duniya nafi kowa sanin halin ki kuma nafi kowa karantar abin da zai bata miki rai haka kema ina da tabbacin kinfi kowa sanin halina da kuma abin da ke bata min rai, soyayya tasa mun karantaci juna domin mu zauna lafiya, kuma mun zauna babu me jin kan mu"

   "Yanzu ya Habibi kana nufin kasan abin da ke bata min rai"

"Eh harma da abin da zaki iya aikatawa idan ranki ya baci, kinga ko ranar da nawa Najma fada da Asuba ai ranki ya baci."

  Cikin jin kunya kamar yana gabanta ta ce "To ya Habibi me yasa zaka ce raina ya bacci bayan bance maka komai a kai ba?"

  "A duk lokacin da raina ya bacci kina kokarin kiga na huce kafin in fita, amma ranar kika ki sani dariya haka kika barni na wuni ina masifa."

   Dariya Habiba ta yi sannan tace "Ni ai ba laifi bane don ka mata fada, amma kanata fada wa karamar yariya kamar kanawa babba."

   "Baki fini sonta ba dai."

  "Haka ne" Ta fada tana me luumshe ido, hira sukaita yi basu an karaba suka farajin kiran sallah.

 Zaro ido Habiba ta yi tare da cewa "Ya Habibi kaga har an kira sallah."'

  "Umm kitashi ki yi idan kin gama sallaman yara sai ki dan kwanta Zan kira sadam zaizo anjima."

                               *****

 Misalin karfe shadaya taji ana buga kofa don haka ta fito da sauri, Sadam ta gani tsaye bayan ta bude kofar don haka ta juya ya biyo bayanta.

  "Ina kwana Anty" Sadam ya fada yana kokarin zama.

  Lafiya lau Sadam ya mutam gida.

 Duk suna lafiya.

Shiru suka yi tsawon lokaci zuwa can Sadam yace "Kin shirya ne muje? Kinsan yau Juma'a gajeruwan rana ce."

  "Mu je ina?" Habiba ta fada tana bin sadam da ido.

 "A'a be gaya miki bane, da Asuba fa ya kira ni ya ce in kai masa ke yau."

  Cikin zare ido ta ce "Ka kai masa ni sai kace kayan wanki Sadam, Ka kai ni ina?"

  "Abuja mana Anty, be gaya miki bane wai?"

 "Wai da gaske kake Sadam?"

"Cikin dariya ya ce "To Anty ki kirashi ki ji, ko yanzu ma uzzura min ya yi, naso sai na yi sallah ne nazo."

 "Cafdi, ni fa be gaya min ba, to yaran fa ta kare maganar da cewa bari dai na kira shi."

   Wayarta ta daga yana dauka yace "Sadam ya iso?"

"Eh, gashi zaune, yanzu Ya Habibi yaran fa? ko muje mu dauko su.?"

  "A'a ki kai musu kayansu gidan Anty yafi kusa da makaranta, na kira Abba zai dauko su da yamma."

 Amsawa ta yi kawai da to badan hakan ya mata ba, kayan yaran ta hada sannan taje hada nata nan Habibullah ya kirata yana tambayan sun taho.

  "A'a ina hada kayana ne nagama hada na yaran." Habiba ta fada cikin wayar tana me jiran abin da zaice kuma

 Cikin daga murya dake nuna ya fara fusata yace, "Badai kin hada na yaran ba?"

 "Eh na gama."

"Kibar nakin ku taho kawai, banson yamma ta muku a hanya fa."

  Amsawa ta yi tare da kashe wayar cikin sauri ta dauki mayafinta dake kan gado ta yafa sannan ta jawo akwatin ta fito.

  Sadam ne ya amsa akwatin yasa a mota cikin kankanin lokaci suka isa gidan Anty Saratu, Habiba ce ta shiga ciki a daidai lokacin Anty saratun na zaune da bakuwa, da alama kawarta ce bayan sun gaisa ta dire akwatin tare da cewa "Anty ga kayan yara nan Abba zai kawo su anjima."

  "Ina zaki?" Anty ta tambaya cikin tsareta da ido, "Abuja wallahi, yanzu kawai Sadam yazo daukata, ni kuma be fada min ba dasai na shirya da wuri kinganni duk a hargitse."

  Baki Anty Saratu ta kama tare da cewa "Amma wannan miji naki akwai jarababbe Habiba, jiya fa na hado dasu a hanya, Umar nata mai tsiya nan kofar gidanmu shine kwana daya da tafiya zaice a dauko ki? tab lallai" Anty Saratu ta fada cike da mamaki.

   Juyawa Habiba ta yi tana mata sallama cikin yanayin dake nuna tsoron sabawa umarnin mijin ta take.

   Tana fita matar tace "Wannan kanwar taki da alama mijinta na da kudi, ke kiga hannu da wuya duk gwalagwalai, gaskiya kudi sun yi dole ta guji sabawa umarnin sa"

  Murmushi Anty Saratu ta yi sannan tace "To Alhamdulillah zamu ce yana da rufin asiri"

   "Gata kyakyawa da ita kamar ita ta yi kanta amma fa wannan mijinta yaji dadi, don zai huta wurin nan, kinga fatanta sai shike take, to tana tsan mu ku dai ko?"

  Wannan karon ma Alhamdulillah Anty Saratu ta sake cewa sannan ta kara da cewa bantaba neman abu wajen Habiba na narasaba daga ita har mijin nata basu da rowa, da kannenta da nashi kannen duk suna kyautata mu su, tun da nake banta ganin ma'aurata irin su ba"

    Ma sha Allah kudi sun yi kinga yariya kamar ba jinin ku ba, ke kyace balarabiya ce, dole mijin ya guje yin nisa da ita, ko dan wannan uban kamshin da take zubawa."

 Wannan karon Dariya kawai Anty ta yi ta dauko wani zancen.

                         ABUJA

Bayan sun isa tankasheshen gidan raba ido Habiba ta fara yi, babu abin da take son gani illa Habibullah kokarin bude motar ta fara tare da cewa "Wai halan baya gidan ne ya fito mana nifa na kosa na ganshi."

  Kin bude motar Sadam ya yi yana kallon Habiba yana dariya tare da cewa "Haba Aunty jiya fa ku ka rabu amma ji abin da kike kamar kun yi shekara ba ku hadu ba"

  "In dai yana gidan ka bude min idan kuma baya nan in kira shi a waya"

   Bude motar Sadam yayi tare da cewa "Hmmm amma da kike ta wani basarwa kamar irin bakya son zuwa gun shi dinan"

     Saukowa Habiba ta yi batare da ta tanka wa Sadam ba

Sadam na gaba tana binshi a baya har suka shiga falon dake gidan, tana kokarin zama Habibullah ya fito sanye da jallabiya, hannu ya ware mata don haka ta yi saurin fasa zaman ta nufesa.

   Ta gefen ido sadam ke kallon su sun wani kwakume juna yayin da Habibullah ke sumbatarta kamar waddan suka shekara basu hadu ba, zuwa can suka karaso falon, sallah mangariba da aka kira ya hana su zama dole Habibullah da Sadam suka wuce masallaci

     Bayan sun dawo sallah suka samu Habiba ma ta idar da sallah, Habibullah ne yace baki shiga ciki ba taso muje, wani daki ya kaita sannan ya ce ki yi wanka ki huta ina zuwa, fita yayi zuwa can ya dawo ya aje mata abinci.

Wanka ta yi taci abincin, har ta gama bata jin motsin kowa ba, ganin har goma ta yi be sake shigowa ba ta sakko ta nufi dakin dake kusa da wadda take cikin.

    Kwankwasawa ta yi a hankali jin babu amsa ta tura kofar da nufin lekawa ko yana bayi ne, gabanta taji ya fadi hangoshi saman gado, sai dai abin da take hangowa yana kokarin hautsuna kwakwalwarta.

    Kara ware ido ta yi taga tabbas Habibullah ne kwance yayin da mace ke saman shi kwance suna bacci.

   Ji ta yi kafarta bazata iya daukanta don haka ta dafa bango tare da kara kallon hannun Habibullah dake kan gashin macen dake jikinsa, ji tayi kamar wani ruwa na gudu cikin kanta, don haka ta fice da gudu ta koma falo, wayar Sadam ta fara kira sai dai wayar sa kashe take don haka ta fashe da kuka tare da rasa abin yi.

Gaba daya tashiga cikin wanni irin tashin hankali wadda bata taba shiga ba, cikin matsanancin kuka ta ce "To yasan yana da wadda zai kawo ta debe mishi kewa yasa a dauko ni? Kodai ya shirya yimin cin fuska ne yasa a dauko ni? wannan tunanin ya kara fusata ta ta mike a fusace ta nufi dakin

   Tura kofar ta yi da karfi har yanzu suna nan in da ta bar su fuskarta face face hawaye dunkule hannyenta ta yi biyun sannan ta yi tsalle ta fada kan su tana meji aranta saidai a yi duk wacce za'a

    

  

  

 

   

   

 

   

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol