Free chapter · Read without an account

029

by Halimatou Khabir · BAYA DA ƘURA

*BAYA DA ƘURA.*

Fitattubiyar2025


           ©️Nana Haleema.


Wattpad@Nanahaleema

Arewabooks@nanahaleema11


*BOOK 1*

*Page 029*



    Adnan yana zaune a gaban babban Yayan sa yana masa bayanin abin da ya faru a gidan su Manal da suka je nema masa auren ta, yace, "Ai suna da kirki sosai wallahi, na yaba da su sosai. Sun karɓe mu hannu biyu, na ji daɗin yadda suka yaba da kai sosai, nima na yaba da yarinyar. Duk wanda na tambaya wani abu game da gidan su babu wanda ya faɗi wata kalma mara daɗi, kowa yace in dai aure ne zai haɗa ku da mutanen gidan ku je kan ku tsaye."


Adnan yayi murmushi jin daɗin Yayan yace, "Kuma wanda yake riƙon nasu yana da faɗar gaskiya ya san mahimmacin faɗar gaskiya a ɓangaren neman aure, kasan harkar neman aure ba a so a ɓoye komai gaskiya ake faɗa. Shi ne yake sanar damu ma shi bashi da alaƙa dasu yarinyar, mijin mahaifiyar ta kawai amma shi ba ƙanin mahaifin su bane, ana faɗar cewa shi ƙanin mahaifin su ne kawai saboda wani dalili."


Adnan ya kalle shi tace, "Kamar ya kenan Yaya?."

"Eh, yace mana mahaifin ita yarinyar da babar ta rabuwa suka yi ba mutuwa yayi ba kamar yadda ake faɗa, kuma basu da tabbacin ya mutu kawai tana faɗar ya mutu ne saboda bata son ma tuna musu mahaifin su. Shi bashi da alaƙa dasu mijin mahaifiyar su ne kawai, sannan ya shaida mana yarinyar tana da ciwo diabetics wanda ka san dashi."


Adnan yayi shiru baice komai Yaya yace, "wannan ai ba wani abun damuwa bane ba, an tsayar da rana kamar yadda kace a saka. Itama Mimi an tsayar da lokaci daidai da naka lokacin, abinda muke jira su daga can gidan su matar taka sun ce zasu yi waya in sun yanke hukunci. in yanke hukunci daidai da lokacin mu shikenan, in sun ƙara ko sun rage duk ɗaya ne." Kafin yayi magana Yayan ce, "mun je da gwajin jinin ka yadda ka ke lafiya haka ta ke, genotype ɗin ku kai AA itama AA. Blood group ɗin ka kai O positive, ita kuma B positive. Sai dai naga tana da diabetics ai ka san dashi ko?." Bebi ya ɗaga kai yace, "eh na sani Yaya, Huzaifa ne likitan da take gani." 


Yaya ce, "ma sha Allah, sai mu jira lokaci."


Bebi yace, "haka ne, Allah ya kai mu lokacin." Yayan sa ya amsa da amin Bebi ya tashi ya fita zuciyar sa cike da tunanin meyasa Manal bata faɗa masa abinda yaji yanzu ba?.


Mota ya shiga zai ja kenan sai aka masa waya sai ya tsaya ya ɗauki wayar daga can ɓangaren aka ce, "Bebi kamar yadda ka ce na nemo maka na nemo, Yayar Manal Mubeena an jima da korar ta daga makaranta, yarinyar bata jin magana zan iya ce maka ma tana ɗan taɓa yawon banza. Sannan Haruna ɗan wanda yake riƙon su son Manal ɗin yake."


Ajiyar zuciya yayi yace, "na gode." Yana faɗa ya sauke wayar zuciyar da masa zafi akan ƙaryar da Manal tayi masa, meye in ta faɗa masa gaskiya ai ba wani abun bane tunda ba itace take yawon ba. A haka yaja motar zuwa asibiti ransa a ɓace sosai auren ma yana fitar masa daga rai.


     Mama tana zaune da glasses ɗin ta a ido tana gani amma ba sosai ba Baba yana zaune ya ajjiye mata kuɗin da aka kawo na aure da kuma na saka rana a haɗe yace, "Baki ce komai ba, ga kuɗi an kawo har naira dubu ɗari biyar na aure da na saka rana, kuma su suna so ayi auren ne nan da wata huɗu masu zuwa in Allah ya nuna mana."


Mama tace, "to ai shine ya saka na kasa magana, wata huɗu ai yayi kusa Baban Manal, ina laifin ma shekara ɗaya?."

"Ban da abin ki Fatima ko shekarar aka saka zai zo fa."

"Eh haka ne, amma wata huɗu me muka shirya?. Akwai aiki sosai fa, ko da kayan kitchen aka bar mu aiki ne mai yawa balle gasu gado da manyan abubuwa." Baba yace, "iya abinda za'a iya shi za'a yi ai, kuma kin manta akwai kuɗin ki a hannuna wanda ake juyawa?, sannan nima akwai nawa matsayina na mahaifi?.”


Mama tace, "ban manta ba, amma duka kuɗin zamu kashe muyi amfani dasu?." Baba yace, "A'a da wasu za'a yi amfani, kar ki damu wallahi Allah zai rufa asiri ayi komai a gama. Bikin ƴar gata za'a yi in sha Allah, ke kan ki sai bayan komai ya lafa zaki dinga tunanin a ina aka samu kuɗin da aka yi wannan aka yi wancan, ki miƙa lamarin ki ga Allah kawai." Mama tace, "haka ne wallahi, Allah ya nuna mana lokacin. Gwara a bar shi a hakan ma ayi a gama."


"Amin. Ina Mubeena take?." A lokacin Mubeena ta shigo tace, "gani." Baba ya kalle ta sai da zauna yace, "kin mayar da kan ki wata shiru-shiru saboda kawai an miki faɗa gaskiya Mubeena? So kike mu barkı kina abinda kike so da sunan wayewa?." Tayi shiru baba yace, "tunda haka kika zaɓarwa kan ki daidai ne, Tunda kin zaɓi ki janye jikin ki daga cikin mu saboda akwai an miki faɗa akan abinda kike yi ke kika sani. Kina gani an kawo kuɗin auren ƙanwar ki har an saka rana, ki yi ƙoƙari kawo naki mijin a haɗa ku duka biyun a aurar a huta."


Mubeena tace, "to." Baba yace, "tashi ki shiga ciki." Ba musu ta tashi ta shiga Mama ta kalle ta dan tana iya ganin ta bayan ta wuce tace, "Ni tunda idona ma ya buɗe nake mata wani kallo, wallahi gani nake kamar an canja ta, wayewa ta tayi yawa idanun ta cikin na mutane take magana bata jin kunya. Kaii!" Ta faɗa tana dafe kai akwai abinda ta tuna.


Baba yace, "ki cigaba da yi mata addu'a." Mama tace, "Allah ya shirya. Kuɗin fa, ka barsu a nan?."

"Ki bar su a hannun ki, ki fara siyan kayan kitchen


Mama tace, "to bara a na tura ta wajan Balaraba su yi lissafin abubuwan da zasu siyo." Baba ya amsa ya fita Mama tace, "Manal." Ta amsa tana fitowa ta zauna kusa da ita Mama tace, "ga kuɗin auren ki da na saka rana, abinda za'a yi kije ki samu Balaraba ku rubuta abubuwan da zaku siyo in yaso sai ku shiga kasuwa keda Surayya ku siyo a ajjiye a gidan su." 


Manal kallon kuɗin take yi abin mamaki yake bata wai kuɗin auren ta, har yaushe suka haɗu da shi gashi ana maganar aure har an kawo kuɗi, lallai in akace lokaci to tabbas in yazo baya jira.


Mama da take ganin ta dishi-dishi ta kalli ta tace, "ya naga kin yi shiru?." 

"Mama da gaske wata huɗun za'a bari?." 

"Eh mana Manal, ko shekara huɗu aka saka ai zata zo, gwara ayi a gama kawai a huta."


Idanun ta suka ciko da hawaye tace, "Mama wata huɗu yayi kaɗan, kwata-kwata yaushe muka haɗu dashi da za'a ce za'a yi biki nan da wata huɗu?."


 Mama tayi murmushi tace, "ƙarya kike, ki faɗi asalin abinda yake zuciyar ki Manal. Kina son Adnan, dan haka kina son kasancewa matar sa nan kusa, abinda yake ran ki na san bai huce zaki yi aure ki bar gidan nan ba." Sai kuwa ta fashe da kuka ta kwanta a cinyar Mama tana kuka kamar wacce akace gobe ne auren, Mama tana shafa bayan ta tace, "Manal aure ai ba mutuwa bane, zaki dinga zuwa kina gani na indai ina da rai, kuma bakya ganin yanzu na samu lafiyar idanu? Har girki zan iya yi da kaina ai ba abin damuwa bane wannan Manal." 


"Nidai Mama a'a, a bar shi nan da shekara don Allah."

"Baza'a ɗaga bafa Manal, aure ne sai anyi shi in sha Allah. Da kike wannan koke-koken wata rana mutuwa zanyi na bar ki." Manal tace, "ai sai na riga ki mutuwa Mama." Mama tayi dariya tace, "ni dai bana son wannan kukan naki Manali, aure fa zaki bautar Allah zaki je ki yi to meye na kuka?." Zatayi magana ta hana ta tace, "Kiyi addu'a kice Allah yasa hakan shine alkhairi a rayuwar ki."


Shiru tayi Mama ta ɗago ta ta share mata hawaye tace, "amarya! amarya!." Dariya ta bata ta ɗora kanta a kafaɗar Maman tana dariya Maman ma tayi dariya tace, "Ko kefa fa Manali na, yanzu kije wajan Maman su Surayya ki faɗa mata sai ku zauna ku rubuta duk abinda kike so, ko me kike so ki siya indai ya burge ki, daman ke mai son harkar kitchen. in kun gama rubutawa gobe sai ku shiga kasuwar ke da Surayya ku siyo duk abinda kika rubuta."


Manal tace, "har da Yaya Mubeena ko?." Mama ta kalli Mubeena da take zaune daga cikin ɗaki tana kallo su tace, "baza taje ba, ki ƙyale ta gaba take yi da mutanen gidan gabaɗaya." Mubeena da take gefe tace, "zan je." 


Mama tace, "babu ruwana sai kin tambayi baban ku, in ya barki to." Ta kalli Manal tace, "tashi kije ki same ta, baki da wata uwa kamar ta bayan ni." Ta amsa da to ta tashi zata fita Mama tace, "zo ki kai mata kuɗin ta ajjiye a wajan ta." Manal ta turo baki tace, "to kawai sai na kai mata kuɗi nace na kuɗin aurena na ne?." 


Mama ta kalle ta tace, "kunyar ta ki ke ji?." Manal tace, "eh." Mama tayi dariya tace, "ƙarya kike, yadda bakya jin kunya ta itama bakya kunyar ta." Manal tana dariya tace, "To Mama ai ke aminiya ta ce, ita kuma Maman su Surayya ce fa." Mama tana dariya tace, "zo ki ɗauka ki wuce, ina wata kunya a wajan ƴan matan yanzu?. Sai dai gulma da munafurci." Manal ta ɗauka ta fita tana dariya tana son dramar su da mahaifiyar ta sosai.


     ** Suna zaune a cikin mota ita dashi, gabaɗaya ya gama kashe mata jiki yadda yake faɗa mata yana sonta abin yana sake jefa zuciyar ta cikin kogon soyayyar sa. Ya iya kalmai, ya san ta kan iya tsara ƴan mata, yanzu zai miki murmushin da zai rikita zuciyar ki. Ya kalle ta ya ce, "yanzu Lubna haka zamu zauna kenan? Meye aibu na? Na taɓa ƙoƙarin koda taɓa jikin ki?." Ta girgiza kai alamun a'a kamar zaiyi kuka yace, "to meyasa baya so na Lubna?, meyasa yake so lallai sai ya raba mu dake?."


Kamar zata yi kuka saboda rauni tace, "ban sani ba, ni na rasa me na yiwa Yaya baya sona ma gabaɗaya." ya sauke numfashi yace, "ga Mimi an kawo kuɗin ta ko?."

"Har an saka rana ma, shima an kai kuɗi sa har an saka rana amma ni ya hana." Da sauri ya kalle ta kamar bai sani ba yace, "an saka rana?."


"Eh an saka ranar sa, kuma wata huɗu aka saka." Girgiza kai yake yi lallai Manal ta shammace shi, shi a tunanin sa tunda bata da wani ilimi mai zurfi ba wani wayo ne da ita ba, kasancewar ba wata babba bace zata yi sauri yarda da abinda zai ce sai gashi tayi watsi da abinda yace mata. Nan da nan ransa ya ɓaci, Bebi bai isa ya cigaba da yin nasara yana barin sa ba, ya zama dole yayi nasara a kansa ya cusa masa baƙin ciki da takaici kamar yadda yake ji a zuciyar sa.


"Tunanin me kake yi?." Kallon Lubna ɗin yayi yace, "ina tunanin yadda baya qauna ta ne, ina so na samo mana mafitar da zai amince dani." Tayi shiru cikin damuwa ya kuma yace, "Ko Abba na samu da maganar bazai kawo mana mafita ba?." Tace, "Abba sai ya kira Bebi ya faɗa masa kuma bazai amince ba tunda baya son ka."


Ya kalle ta sosai cikin taushin murya yace, "Sweetheart!." Ta kalle shi itama yace, "Kina sona?."

Ta kalle shi tace, "Wannan wacce irin tambaya ce?."

"Ki amsa min kawai." Ta girgiza kai tace, "ina son ka." Yayi ajiyar zuciya yace, "kin amince bazan cutar dake ba?." 


Tana kallon sa cikin soyayya da shauƙin da yake gani a idanun ta tace, "na amince baza ka cuce ni ba." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "Alhamdulillah! Sweetheart bazan cutar dake ba saboda ina son ki, mafita nake nemar mana da zamu kasance a inuwa ɗaya matsayin ma'aurata."


Ya gyara sosai yana kallon ta yace, "shawara zan kawo ko nace mafita, ban sani ba ko zaki amince ko baza ki amimce ba, sannan ban san da wacce fuska zaki kalle ta ba." Ta kalle shi a raunane tace, "na amince ka faɗi ko meye zan amince da kai, na tabbatar baza ka cutar dani ba." 


Ya sauke numfashi yayi shiru yana kallon ta kamar ba zai magana ba kafin yace, "ban san ta ya zaki ɗauki abun ba, amma dai ina so na taimaki junan mu ne dan na tabbatar in muka rasa junan mu zamu faɗa wani hali." 


Lubna tace, "ka faɗa kawai, ni na amince da kai nasan baza ka taɓa cutar dani ba." Ya girgiza kai cikin gamsuwa a zuciyar sa kuwa tausayin ta yake ji amma ya zaiyi bazai bari tausayi ya rinjaye shi akan fansar sa ba, saboda fansar sa yake komai har soyayyar da yake nuna mata duk ta ƙarya ce. yace, "ina so ki bani dama ki amince dani har zuciyar ki, ki yarda bazan cuce ki ba, ina so mu kusanci junan mu...." Kafin ya kai ƙarshe ta kalle shi da sauri, sai ya tari numfashin ta yace, "ki jira na gama faɗar abinda yake bakina kafin ki yanke min hukunci please."


Kallon sa take yi hakan ya saka yace, "so nake hakan ya faru,in ya faru babu wanda zai hana ni auren ki. Wallahi Lubna zamu yi hakan ne saboda a bani ke na aura ba dan wani abun ba Allah ya sani kema kin sani. Amma in kina ganin hakan bai dace ba shikenan sai mu haƙura da junan mu tunda Bebi bazai bari mu auri juna ba." 


Shiru tayi alamun tunani, shi kuma yana sake karyar da murya yana yi mata bayanin yadda abin zai kasance har yaga ta fara aminta da maganar sa ta kalle shi tace, "in na amince baza ka guje ni ba? Baza ka manta dani ba in hakan ta kasance?. Kaga ni ba ƴar iska bace ba, wallahi ko hugging wani namiji ban taɓa yi ba har yanzu, zan amince da abinda kace ne saboda ina sonka, na amince da kai baza ka cutar dani ba domin kana sona kuma kamar ƙanwar ka nake. Kayi min alqawarin baza ka guje ni ba?."


Kalaman ta sun saka yaji wani iri a zuciyar sa ya sauke numfashi yace, "bazan guje ki ba Lubna, ina son ki bazan taɓa abinda zai cutar da ke ko rayuwar ki ba." Ta sauke numfashi tace, "Allah yana kallon ka in ka cutar dani, Allah bazai bar ka ba domin kaci amanar ƙaunar da nake maka."


"Lubna ina wannan abun ne dan neman mafita ba dan ina so na kasance dake ba, inda ni mutumin banza ne da yanzu kin fi kowa fahimtar hakan Lubna." Ta girgiza kai cikin amincewa da maganar sa tace, "nima ban ce kai na banza bane, kawai ina so ka riƙe min alƙawari ne kar ka guje ni bayan ka raba ni da abinda nake dashi." Mujahid yace, "indai alƙawari ne nayi miki." 

"Shikenan, na amince da abinda kace" tana faɗa sai ga hawaye sharrrr suna sakkowa daga idon ta. sai jikin sa yayi bala'in sanyi ya kalle ta murya a raunane yace, "meye na kukan?."


Murya na rawa tace, "Daga zuciyata yake zuwa, ban san dalilin zuwan sa ba." Yayi murmushi yace, "kar ki damu, zan nema mana wata mafitar in bamu samu ba sai muyi amfani da wannan ɗin. Hakan yafi miki ko?." 


Ta sauke Ajiyar zuciya ta ɗaga kai tace, "to." Ya kalle ta yace, "to ki yi murmushi mana, haba Sweetheart." Murmushi tayi shima yayi yana kallon ta kafin yaja motar su tafi zuciyar sa nayi masa saƙa da warwara akan lamarin Lubna, Anya yayi mata adalci? Anya in yayi hakan bai cuce ta ba?. Amma Itace hanyar da yake da ita wacce zai sakawa Bebi baƙin ciki a zuciyar sa, babu yadda zaiyi dole yaci amanar qaunar da take masa.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol