Free chapter 路 Read without an account
Eleven
馃挃RANAR YABO馃挃
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
By
Mom muhsen
&Asaad
Eleven
Daddy na bacci yaji kamar ana danna karaurawar main kofar sa dake can waje,tashi yayi idanunsa suna masa nauyi sosai ya duba wayarsa yaga karfe shad'ayan safe, saiga kiran security d'insa yai picking yana mgn cikin muryar bacci, "What's happening john"
D'an shiru yayi yana sauraren John d'in kafin yace masa "Allow her"
Ya sauke wayar yana sauke numfashi,zai bata wata damar yagani inhar da neman sulhu tazo sai yarda,amma in har da sab'anin hakan tazo anan ne zata san waye Naseer zahraddeen.
Koma wa yai ya kwanta cikin faffad'en gadonsa yana jiran shigowarta, aikuwa sai fata ta fad'o kamar daga sama babu ko sallama bakinta, d'an tashi yai yana jingina da gadon yana kallonta kamar yadda take kallon shi cikin fushi sosai tace masa,
"Miye ma'anar abunda kake yi Naseer?shin ashe akwai abunda zai iya nisanta ka damu a rayuwa irin wannan nisan da kai damu?ka mance irin yadda muke ada Naseer?ka mance yadda gidanmu yake cike da soyayya da kaunar juna, kai a wajenka akwai lokacin da yafi maka dad'i irin wannan lokacin? Miyasa ka kasa fahintar cewar zaman yarinyar nan ba alkairi bane a wajenmu?Sbd nayi wancen furucin kake wannan abun,har ya shafi y'ay'anmu to ga fadeel can kwance ba lafia sbd kewarka da yake,Idan har baka sauko dan kowa ba ai shi ka sauko domin shi"
Kallon ta kawai yake tunda tafara mgn har takawo aya,ya gyara kishingid'arsa yana dubanta sosai kafin yace "Ai ni na dauka kin sadudu ne da har kika tako k'afarki zuwa nan, na dauka kin damu dani da halin da nake ciki yasa kika biyoni,na dauka zuwa kikai kibani hkr ki nemi sulhu tsakaninmu mu gyara barakar data balle,ashe duka tunanina babu ko guda Hussaina?shin ke wace irin macece a duniyar nan iye?kin zauna kinyi tunani mai kyau kuwa?akwai ranar da wani naki yazo gidana na nuna masa wani hali marar kyau?ko kuwa akwai ranar da sukazo suka zauna na koresu ko kuma na canza musu fuska,ko kuma naci musu mutunci irin yadda kikai ma d'iyar k'anena,ki auna abun akanki Idan kece kika had'u da dan uwanki bayan tsawon shekaru fiye da ashirin da biyar kuma ya zamana shi kadai gareki gaba da baya, Kika dauko yarsa kina rik'o domin inganta rayuwarta da kuma faranta masa,sai kizo da ita gidanmu ince miki bazata zauna ba don Allah don son Annabi ya zakiji?"
Shiru Mami tayi tana kallonsa, bai barta tace wani abuba yaci gaba, "na barki da wannan kadai kije kiyi tunani mai zirfi akai,sannan last warning zan miki daga yau karki sake zuwarmu office idan bani nakiraki ba,sannan mgnr Fadeel kuma karki tunanin son da nake masa zai canza ra'ayina, ko cutar mutuwa yake inhar bake kika sauko daga naki ra'ayin ba bazai sake ganina ba a rayuwarsa,inda rabo mun had'u a lahira ni ba irin zuciyarki ce dani ba, ni tawa zuciyar akwai tausayi akwai soyayyar zumunta cikinta, sannan akwai kawaici da kauda kai, pls workout"
Jitayi hawaye zasu zubo mata tayi saurin maidasu kafin ta juya ta fice da sauri,hawayen na zubowa bata samu sararinyin kukan ba sai data shiga motarta,tayi mai isarta ta share hawayen sosai sannan tace "Mu zuba mugani, shege ka fasa Naseer Zahradden.
******
Ahankali na soma sabawa da yana yin da nake ciki tun daga ranar farko zuwa yanxu,na fahinci ita rayuwa duk yadda tazo maka ansarta kake hannu biyu ka godema Allah,sai na sanya ma zuciyata hkr da dangana koda muna waya da Baba ban yadda na sanar dashi wata kalma da zata nuna masa ina cikin damuwa ba,sai ma kara kwantar masa da hankali da nayi kan cewar ina nan tafe da mun kammala jarabawa.
Yan dakinmu sunyi iyakar kokarinsu wajen ganin sun hanani tunani,damun zauna inba karatu muke ba to zasuyi ta takalo abun da zai sani dariya da nishad'i,in weekend ne Fareed ke shirya mana fita ta musamman muje yawo cikin gari inda ma ban tab'a zuwa ba naje,wuraren shak'atawa da wajenjen cinye cinye da lashe lashe ba inda bama zuwa, tun safe mun muka fita sai isha'i muke dawowa kuma tare dashi da jamil muke tafiya duka dai yan grp dinmu, wannan abun yasa dolena na sake na cire komi na aje gefe muna rayuwarmu cikin farin ciki,wajen karatu ma ba kama hannun yaro Fareed saida ya tabbatar bamu da matsala akan kowane course da zamuyi exam akanshi, yayi kokari sosai muma kuma munyi sbd kusan tare mukeyi saidai abubuwan da suka shige mana duhu saiya bata lokacinsa wajen warware mana su,kuma bazai dakata ba har sai kowa da kowa ya fahinta kuma ya gane,daga nan sai muka ringa presentation d'aya bayan d'aya inda mutum keda gyara a gyara masa, ranar da zanyi nawa duk naji kamar banda lafia, sbd akwana biyun nan har zullumin mu hadu da Faa nake, lamarinsa ya soma dagula d'an lissafin da nake dashi, kallon da yake bina dashi kad'ai ya isa ya sakwarkwarce mun kwakwalwata, wannan dalilin yasa duk nakejina a kasalance, karfe takwas ranar muka fito Ina sanye da coffee abaya nayi Rolling da gyalenta,fuskata kamar kullin babu komi jikinta sai kwalli da lipstick,Turaren jikina saika matsoni sosai zakaji sa har muka iso class na kasa cewa komi, saida muka jira mazan suka iso sannan muka fara abunda zamuyi, Jennifer ta gama nata daman idashe ne jiyan bata gama ba lokaci yai muka tashi, tunda ya shigo nakejin kallon sa yana huda mun fatar jikina,saida ya gama abunda zai cikin system dinsa sannan ya dago yana cemun, "Madam Bismilla"
Na kalli sakeena dake danne dariyarta na d'an b'ata fuska sosai nace masa, "Wai don Allah sai nayi ne?"
D'an sosa kanshi yai kadan yana kallona yace, "Yes madam,yanda kowa yayi kema sai kinyi oya come out"
Jinake kamar zanyi kuka,kamar wacce zata kama fara na tashi na fara sand'o, gashi up head zakayi tunda on ready duk abunda zakai bayanin kanshi ka sansu kuma sun zauna maka,amma zaman Fareed class din nan yana bina da mayen kallonsa zaisa in kwafsa,kokarin natsar da kaina nake ina nuna dakewa sannan yace mun, "Start"
Cikin kyakkyawan turancina na soma gabatar da presentation din nawa, amma inayi Ina duburcewa sbd ji nake idanun Faa suna harde mun halshena, runtse idona nayi na bude akanshi ina cewa, "pls karka cinyeni wlh ka hanani nayi abunda ya kamata"
Aiko su Sakeena me zasuyi ba dariya ba,Jamil yace "Aa Bia karki ma Aboki sharri mana,kedai kawae tsoron mu kikeji bakya iya mgn haka gaban mutane"
Na dalla masa harara Ina cewa, "Ai gashinan sai ka tambayesa inba idanun sa ke addabata ba nake in Ina"
Dariya kawae suke mun,na koma na zauna ina cewa "Ni anan zan tsaya Allah ko"
"Kedai kawae kice kin kasa idawa zaki wani fake da ana kallonki,"
"Laaa abunda zakace kenan?"
Ya dage kafadarsa yace, "Koba gaskiya ba Jamil?"
"Sosai ma aboki,tsoro taji kawae"
Su sakeena suka shigarmun a haka dai aka b'ige da wasa da dariya,har lokacin tashinmu yayi sannan muka fito domin tafiya Hostel, kafin na had'a kan tarkacena har su Sakeena sun fita class din sun barni, daman kuma ba yau suka fara mun hakan ba kullin indai zamuyi karatun dare sai sun gudu sun barni,in nayi complain suce taya zasu tsaya su hanamu sakewa, mamaki ma mgnr ke bani su a tunaninsu soyayya muke da Faa, duk yadda zan musu bayani ba zasu gane ba shiyasa ma na daina bata bakina, wurin sauri na saki wayana k'asa nazo duk'awa in dauko shima ya sanyo kai ya dauko mun aiku kawunan mu suka had'u, cikin sauri na mik'e ina cewa, "Asshhh"
Cikin sauri ya rik'o hannuna yana duba inda mukai Karon,idanun mu suka sark'e cikin na juna cikin yan second zuciyata ta soma bugawa, yayinda na gaza cire idona daga nashi haka shima ya kasa kamar dai yauce rana tafarko da muka san juna, vibrating din wayata dake hannunsa ya dawo damu daga duniyar da muka tafi, kunya tayi kamar zata kasheni nai saurin juyawa zan fice daga ajin,saurin rik'e mun hannun jikkata yayi na kasa jiyowa jikina har rawa yake, "ur phone,ko kin barmun"
Hannu na mik'a masa ta baya bance komi ba,inajin murmushin sa lokacin saya samun wayar yana cewa, "Goodnight RABEE'ATU"
Kamar zan tashi sama haka nabar ajin har ina tun tub'e
Ina koma wa daki na iske harsuyi shirin bacci,na sha murr sbd nasan zasu tsokaneni nak'i bada fuska,amma duk da haka inajin Merry na cewa "Ana so ana kaiwa kasuwa"
Ban ma kulata ba ni nayi shirin baccina na kwanta, ina ganin kiransa nak'i dauka sai ma na kashe wayar kurin, har sannan zuciyata dokawa take sosai, na rasa taka maimai abunda ya sameni yau irin abunda ya faru dazun dole akwai abunda ke shirin faruwa dani,na dafe saitin zuciyata na lumshe idona ina adduar bacci, daker da sidin goshi nayi baccin.
Daga ranar sai na soma d'ari d'ari dashi duk yadda nake d'an sakin jikina dashi in muna tare yanzu ba haka ba,sannan ada nike jansa da mgn amma yanzu sai yai mun mgn nawa bance masa komi ba, mun rage ma keb'ewa inhar ba in group zamu hadu ba bana yadda,a haka muka fara jarabawa cikin sa'a ranar farko da zamu shiga ya kirani a waya, "Kin mance something a mota"
Da yake mun d'an fita dazun nidashi da su Sakeena, siyayyar kayan kwalama kawae ya mana shi duk a son Samun sa na daina dari darin da nake dashi, na tashi daga sit d'ina na fito da yake da sauran time na shiga jarabawar, can nesa na hango motarsa yau shid'aya ne ba guards din nashi, Ina zuwa wurin motar ya bud'e mun yana kallona ni kuma na b'ata rai, "Faa..."
Shiru nayi sbd yadda ya dora hannusa a baki,na bata rai sosai ya wani koma ya jingina da kujera yana cewa, "come in"
"Fa....pls ni wai nace miki zan cinyeki ne?"
Dole na shiga amma na matse can jikin k'ofa, Ina kallon sa kasa-kasa abu ya ciro daga aljihun jeans d'insa yana b'arewa, wani d'an mininin abune saida ya gama b'arewa kawae naga yaa matsoni nai saurin jaa baya idona warwaje, "Fareed"
Murmushi ya saki yana d'an lumshe idonsa yace, "ke wai mike damunki ne? Taya kike tunanin abunda ba shine ba?"
Zuciyata kamar zata fito,kuma naji kunyar kalaman shi sbd ya fahinci minake mawa, "duk kin addabi kanki nima kin takura rayuwata, nifa Yayanki ne ko bashi bane?"
Kaina nake jinjina masa naki mgn,yaja numfashi a hankali mai cike da kamshin turarensa mai sani jin wani kala, "kawo kunnenki kiga"
Kallon da nake masa yasa yai yar dariya wacce tayi masifar fidda ainahin kyansa, "Don Allah ki fiddo na saka miki time na tafiya"
Kamar zan masa kuka nace, "To.....to minene wannan d'in ka fada mun first"
Cikin bazata kawae naji ya zare abunda na mak'ale veil d'ina dashi,aiko gashina kamar jira yake ya warware ya sauko, Shi kanshi yadda zuciyarsa ta buga saida yaji tsoro, ya had'iye miyau daker muna kallon juna nida shi, kamar zan kuka nace "miyasa zaka cire mun abu,"
Jiyai babu kalma d'aya da zai iya furtawa, nai saurin daukar veil din zan maida,ya rik'e mun hannu ya matso sosai baice mun komi ba, ya sanyo dayan hannunsa ta bayan wuyana ya d'an sanya na duk'o,janye gashina yai naji yana lik'a mun abun dai dai saitin ramin kunnena,kaina kusan zan iya cewa yana dangane da kirjinsa,har bugawar zuciyarsa inaji duk na rud'e yana sakina nai saurin koma wa na zauna, na fizge veil dina na yafa zan fita, yai saurin danna lock ina ja taki budewa idona harda kwalla a ciki na kallesa, idanun sa sun lumshe sosai muryarsa ta kara sanyi kawarai "Ki gyara gashin karki fita haka"
Harararsa nayi yai d'an murmushi yana had'e hannuwan sa alamun ban hkr, "Afuwan,na sa miki ne yadda zamuyi communicating,in wani abun ya shige miki"
Gyara gashina nayi sannan na maida veil d'ina ina kallonsa, kamar zai cinyeni d'anya nace ina b'ata fuskana, "Karka sake cire mun abu"
"Afuwan Rankiyadad'e"
Na sake hararar sa sannan na bud'e na fice na kyalesa,nazo dai-dai shiga Hall d'in mukai karo dashi dagani har shi ba wanda yai tsammanin ganin d'aya,saurin jaa baya nayi ina kallonsa shima kallona yake sosai, Ina ganin shine bance komi ba kuma banyi komi ba na rab'a ta gefensa na shige Hall d'in.
Wannan abun da Faa ya samun yayi mun rana sbd last question din tazo mun a bazata sbd kaina ya rikice na gaza fahinta question din, bansan ya akai yasan halin da nake ciki ba sai naji muryarsa cikin abun yana tambayana, "Kina son karin bayani ne?ko na karanto miki ki rubuta?"
A hankali nace "No kamun in brief bayanin zanyi da kaina"
Sai gashi nice second d'in fita daga Hall din yana submitting tashi ba jima wa na bayar da tawa na fito, yana ganin na fito yai saurin zuwa wajena "kin tabbata kin ansa duka question din lafia lau?"
Murmushi nayi kad'an nace, "Yes sir"
Ya b'ata rai yace "I don't like sir pls karki kara"
Na juya idona Ina cewa, "aiko daga yau sir zanta kiranka"
"Nace fa banaso"
Dariya nayi ganin yadda ya b'ata rai ala dole shi bayaso, sai yai kamar dan yaro karami kuma yai kyau, "look at u,like are baby boy"
Zaro idanunsa yayi masha Allah yai kamar zai kamoni na matsa da sauri ina dariya,dai-dai nan Fadeel ya fito daga Hall d'in, saurin kawar da kaina nayi har ya wuce sannan na jiyo, kallona kawai yake kafin yace mun "Mi kika fad'a yanzu?"
Na b'ata fuskana nace "ni I'm not saying anything fa,kunnen ka ne yajiyo"
Jinjina kai yayi yace "zan kama ki,kuma zakiyi bayani sosai"
Su sakina suka fito cikin farin ciki alamun exam d'in tayi dad'i sosai, muka tab'a fira yaka junan mu kafin muka wuce Hostel.
Haka muka cigaba da exam d'inmu cikin kwanciyar hankali babu wata damuwa,kuma duk dare zamu fita karatu babu fashi abunda Faa ya ban duk sadda xamu shiga exam nake sawa,koda na ansa duka question dinsa saiya tambayeni in sake duba wa ko akwai inda nayi kuskure,wani lokacin yace na karanto masa yaji,a haka har muka ci sati guda.
Rannan mun fito exam karfe shidda ranar ma na riga Faa fitowa bansan kiya zaunar dashi ba, Ina zama wani d'an department dinmu Ibraham muna gaisawa dashi sosai d'an Nigeria ne shima kuma dan maiduguri shiyasa Muke mutunci sosai, yazo wajena muka zauna muna fira yake cewa ai zanje gida wannan hutun ko nace masa eh zanje,yace idan na sanya rana inyi masa mgn sai mutafi tare nace masa ba damuwa, muna a haka ya fito daga Hall din,mun had'a ido dashi amma sai ya juya ya canxa hanya.
Bayan yasan shi nake zaman jira,ganin danai karna tashi Ibrahim yaji ba dad'i sai ban bisa ba na zauna munata fira har su Jennifer suka fito sannan ya tafi, na duba ko ina banga Fareed ba har na kasa hkr na tambayi Jamil, "Ina abokin ka yaje"
Murmushi yai yace "Tofa,yau ke kike nemansa bacin kodayaushe kuna tare?"
Na b'ata rai nace "karka wani yimun boye-boye kasan inda ya tafi ai"
Ya shafa kanshi yace "Dagaske ban san ina yaje ba,tunda ya rigani fitowa ai"
Wasa wasa har muka tafi Hostel bansa shi idona ba,duk sai naji ba dad'i inajin wani kala, "Halan ma ba zaki iya cin abinci ba sbd shi?"
Cewar Sakeena tana kai lomar abinci bakinta da spoon,na dalla mata harara nace "Sbd ubana ne shi ko?Sakeey banaso kidaina"
Suka kwashe da dariya Jennifer tace, "Madam kibar wannan kwane-kwanen keda That guy u in love"
Jinai kamar anyi daka cikin zuciyata sbd yadda ta buga dakarfi, nace cikin karyayyar murya kamar zan kuka, "Jenny kinga bana tsokanarki,ki daina bana so Ni bansan wani love ba kidaina anbata mun shi,Fareed Friend dina ne kamar yadda kuke friend Dina"
Suka sake kwashewa da dariya,sai na tashi na shige toilet na kyalesu, har dare ban Samu wayarsa ba ko ince bai picking ba,nai ta maza na danne abunda ke damuna sbd idan nace rashin sa tare dani a lokacin bai tab'a raina ba karya nake,amma inata pretending karsuce dagaske soyayyar muke bacin babu abu mai kama da hakan tsakaninmu, Wajen karfe takwas saida na gama shirina zamu fita karatu sai naji ya kira Sakeena, bayan sun gama wayar na zuba mata ido ina kallonta nace "Miyace miki?"
Tace"Baya cikin school ma yaje gida wai sai monday zai shigo school,"
Da yake mun samu interval na kwana uku,wani d'aci yazo mun ga mak'oshina amma na had'iye nace, "shikenan sai mu ringa karatun a daki ba sai mun fita ba ko?"
Kallona take tayi tana son ganin wani canji daga fuskata, na hana hakan faruwa na dauki system d'ina na sauko k'asan capet ina karatuna,na aje copcon inaci a hankali.
Saida na daina jin idanunta akaina sannan na ja numfashi sosai,wannan daren yazo mun a wahalce tunda naji ya kira Sakeena dazun nasan cewar yana sane yak'i daukar wayana, to da akai masa mi? Tunda iya tunanina banyi masa laifin komi ba lafia muka shiga exam har yake tambayata idan na gama nace masa eh,shine ma yace na taso inzo in bada.
Wani abu yazo mun a wuya ban sake kiransa ba,wayarma bayan na kira Baba mun gaisa saina kashe banza,saidai in juya nan in juya nan na gaji da kwanciyar na tashi na tada salla nayi adduoi sosai sannan nayi karatun qur'ani na koma na kwanta, sai baccin ya daukan daker ma nayi sallar asuba.
Mom muhsen鉁嶏笍