Free chapter · Read without an account
🌸5
💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝
*Written by Fateemah MG
....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)
🌸Page 5
Gyara zama Irfaan yyi yace, "Mey suke faɗa?" Ƴar dariya Anwar yyi yana sake ƙurewa Irfaan kallo kafin yace, "Wai duk zubin surarkan nan ta ƙarfafan mutane shine wai har za'a ce.." dariya ce ta kubce masa aikuwa ya bushe da dariya, kallon banza Irfaan ya fara zuba masa kafin yace, "Ban son iskanci kazo kana wani dariyar banza idan bazaka faɗa min ba kar ka jamin rai malam!" Ganin yanda ran Irfaan ya ɓaci yasa Anwar ƙara bushewa da dariya yana mamakin yanda ransa zai ɓaci idan yaji asalin labarin, "Easy my man, abunne da ban dariya wallahi, wai cewa ake yi wai kai ɗinnan wai..." sosai ran Irfaan yyi mugun ɓaci da jin iskancin da Anwar yake yi masa, kicin kicin yyi da idanu yace, "Ka ga malam tashi ka fitar mani a office ina da abun yi!" Kafin kace mae sae Anwar yyi fuska ganin ya ɓatawa Irfaan rai, ajiyar zuciya ya sauke yana fatan kar ya sake dariya yayinda ya faɗa masa abunda ake cewa, in a serious tone yace, "Wai cewa ake yi you are impotent, ƙurungus kenan!" Shiru Irfaan yyi yana zulumi kafin ya bushe da dariya shima, Anwar ne ya zuba masa idanu yana kallon ikon Allah dan yyi mamakin ganin Irfaan yana dariya bayan abunda aka faɗa, nuna kansa ya fara yana dariya kafin ya fuske yace, "There is no way ni suke faɗa sae dae idan saɓa lamba suka yi. Namiji mae jini a jiki kamar ni zasu kira impotent?? No wayy!" Shiru Anwar yyi bae ce komai ba, gaban desk ɗinsa ya ƙarasa ya danna intercom kafin ya juya yace, "Let's talk later Anwar, I'll get real busy right now!" Kai Anwar ya ɗaga masa kafin ya juya ya fice daga office ɗin. Zama kan kujerarsa yyi yana mayarda numfashi yace, "Bil haƙƙi sunce sae mutum ya zama ɗan iska shknn muje zuwa!"
Akwai AC a ɗakin amma zafi kawai yake ji, necktie ɗin wuyansa ya fusge ya ajiyeshi akan table ɗinsa, ba'a ɗauki lokaci ba Asmah ta shigo cikin office ɗin tana wani rausaya kamar stripper a club, tana ƙarasawa gabanshi ta samu guri ta zauna rai a ɓace ya kalleta yace, "Waya baki damar zama?" Shiru tayi tana neman turo masa baki, clenching haƙoransa yyi yace, "WA YA BAKI DAMAR ZAMA???!" Jin yyi tambayar cikin ɓacin rai yasa ta miƙewa zumbur tana ɓata rai, miƙewa yyi daga kujerarsa ya zagayo gurinta yace, "Wanne rumour kike spreading game dani a asibitin nan?" Zaro ido tayi tace, "Ni... ni... ni kuma..me n..nayi?" Tunkarota ya fara yi kuma ga ransa a ɓace hakan yasa ta tsorata matuƙa, baya baya ta fara yi yana tunkaro ta yana faɗin, "Ba tambayar ki nake ba?" A tsorace take dashi sosai ga wani kwarjini da yyi mata tana jin da kyar take iya shaƙar numfashi, jin bayanta ya mannu da jikin bango yasa ta ƙara rikicewa, sarai ya kalli tsoro a idanunta amma idan ta fara baza iskanci sae mutum ya rantse ƴar hannu ce amma sam ba haka abun hake ba, neman ta inda zata gudu tayi amma ya riga ya ƙaraso gabanta, iskan huhunta tsab ta nema ta rasa ganin yyi caging ɗinta a ƙirjinsa, rau tayi da idanu ta zuba su cikin nasa jikinta na rawa amma bata ce komai ba, labcoat ɗin jikinsa ya zame yace, "Ki faɗa mun ko ba tambayarki nake ba?" A tsorace tace, "Ni... ni.. fah bance komai ba!" Hannu ya kai kan rigarta ya fara ɓalle buttons ɗin rigar yace, "You were saying something like I am impotent?" Cikin idanunsa ta kalla tarr tace, "Toh ai ba ƙarya nake ba!" Ɓata rai yyi ya kalle ta da idanunsa da suka fara ja yace, "Ke har kin isa ki kalle ni kice ban cika namiji ba? Kinyi kaɗan!" Farke rigar jikinta yyi sannan ya kamo hannunta ya ɗaura akan mararsa.
Gurin ƙarfe biyar da rabi na yamma ya fito daga asibiti riƙe da briefcase ɗinsa da laptop, har ya buɗe ƙofar motarsa Anwar ya ƙaraso gurinsa cikin sarfa yace, "Irfaan! Kai nake ta jira fah!" Kallonsa Irfaan yyi kafin ya ɗage masa gira yace, "Baka tafi gida ba?" Kai Anwar ya ɗaga masa yace, "Eh, ina son magana da kai ne ai!" Gyara tsayuwa Irfaan yyi yace, "Ina jinka!" Gyaran murya Anwar yyi yace, "Dama akan Noor ne! Ta burgeni sosai kuma naji ina sonta and idan akwai possibility ina son na fara zuwa hira, tunda ya ambaci sunan Noor zuciyar Irfaan ta fara bugawa da sauri sauri, ɓata rai yyi bae ɓoyewa Anwar ba yace, "Sae ta gama school zan yi mata aure kuma bana son wani zancen hira ni kaga tafiyata!" Murfin motar ya sake buɗewa ya shige kafin ya rufe Anwar ya riƙe murfin motar yace, "Meysa nake jin kamar baka ji daɗin zancen ba?" Harara Irfaan ya watsawa Anwar yace, "Eh mana kuma na faɗa maka ba yanzu ba ai!" Fusge murfin motarsa yyi ya rufe da ƙarfi abunsa, har ya kunna motar yaji Anwar yace, "Idan ka hanata aure sae muga idan kai zaka aureta ai!" Wani murmushi ne ya zo masa ƙiri ƙiri ya kalli Anwar yace, "Ka sani? Ai baka san gaibu ba!" Wani irin kallon mamaki Anwar yabi motar Irfaan dashi da ta riga ta kai bakin gate ɗin asibiti, hannunsa ya ciza a baki da fuska irin kutt ɗinnan, tuno kamanninta ya sake yi kafin yace, "Kai amma ta kwaso kaya kuma bazan yi ƙasa a gwiwa ba!" Yana faɗin haka ya shige cikin motarsa ya bar asibitin da doctors ɗin dake da night duty.
Salma ce ta bi Zaynoora da idanu tana ganin yanda duk hankalinta yyi gaba ko tunanin me take yi ma oho tana ƴar ƙaramarta da ita, cikin mamaki Salma ke kallon yadda Zaynoora ke faman cika masu maggi cikin abinci ganin da gaske bata cikin hayyacinta yasa ta daka mata tsawa, "Ke lafiyarki kuwa kike neman cika mana maggi?" A zabure Zaynoora ta dawo cikin hayyacinta tace, "Oh, bansan ya kai ba ma!" Wata ƴar dariya tayi saboda ta kawar da tunanin Salma daga kanta, taɓe baki Salma tayi kafin tace, "Ki ɗauko mun kayan haɗa coleslaw ɗin!" Kai Zaynoora ta ɗaga kafin ta wuce store ta kwaso kayan ta dawo kitchen ɗin, yankan cabbage Zaynoor amma tunaninta na kan abunda ya ɓata wa Yaaya rai, ita kanta bata dan mae tayi ba amma sae faɗa yake yi kuma ta rasa mae tayi masa, ko kaɗan bata son abunda zae ɓata wa Yaya rai, tunanin yadda zata bashi haƙuri ta fara yi amma kuma ta rasa ta wacce hanya.
Ko daya shigo cikin gida bbu kowa kuma bae fita ba, jin kansa na yi masa ciwo yasa bae fita zuwa Masjid ba, a ɗakinsa yyi sallar Magrib, yana idarwa ya fita zuwa dinning area sanye da sweatpants da rigar jersey, yana ƙarasawa Aunty ta yashe baki tace, "Likita bokan turawa!" Ƴar dariya yyi yana sosa kai kafin yace, "Aunty barka da dare!" Murmushi tayi amma kafin ta amsa yace, "Salma ki kawo mun abinci ɗakina!" Tsaye Zaynoora ta miƙe tana tunanin sunanta zae kira amma shiru bae ce mata komai ba kuma tunda ya shigo ta lura da cewar yaƙi kallon inda take bare ya yarda su haɗa ido, sosai taji zuciyarta nayi mata wani zafi tana jin duk bbu daɗi. Yana barin gurin Salma ta sake wani murmushi daya sake ƙawata fuskarta, a tray ta jera komai sannan tayi hanyar part ɗin nasa cikin doguwar rigarta fitted da ta kama jikinta sosai, tana da shape mae kyau abunta wanda yasa gown ɗin yyi mata ɗas a jiki. Kallon yadda Zaynoora ke cikin takaici Aunty tayi tace, "Ke wai meye tsakaninki da yayanku? Bangane wannan irin alaƙar taku ba!" Cikin razana Zaynoora ta ɗaga kai tana kallon Aunty da tayi mata, daga part ɗinsu Zaynoora Aysha ta fito tace, "Meye kuwa ke tsakaninsu, alaƙa ce irin ta yaya da ƙanwarsa ji wata tambaya ma fi sabililla!" Juyawa sukayi su biyun suka kalli Aysha nan Aunty tace, "Ashe kina gidan!" Ɗauke kai Aysha tayi yace, "Idan bana gidanmu ina zan je?" Sosai maganar Aysha ya sosawa Aunty rai amma ya zata yi tunda da sannu zatayi maganinsu a gidan.
Abinci Aysha ta fara ci amma kuma bata kula Zaynoora dake zaune a gefenta ba, tana gamawa ta miƙe tayi tafiyarta da sauri Zaynoora ta miƙe ta bi bayan yayar tata suna shiga ɗakin Aysha ta maƙale bakin ƙofa tace, "Ya Aysha ya lectures?" Taɓe baki tayi kafin tace, "Lafiya" jin ta amsa yasa Zaynoora tayi sauri ta ƙarasa gefen Aysha da ta kunna laptop ɗinta, zama tyi akan gadon tace, "Ya Aysha kinsan me ya faru yau?" A hankali Aysha ta ɗago manyan idanunta ta kafe Zaynoora dasu dan sosai tana son hira amma bata son nuna cewa tana so, can daga baya Zaynoora tace, "Ya Aysha idan kina da abun daɗi dan Allah ki bani!" Kallon banza Aysha ta watsa mata kafin ta jawo handbag ɗinta ta wullawa Zaynoora chocolate ɗin dake ciki, murmushi Zaynoora tayi ta fara sha tana zubo zance, "Dama yau nayi faɗa a school shine aka yi suspending ɗina na two weeks!" Zaro ido Aysha tayi tace, "Mey Yaya yyi miki?" Shiru tayi kafin tace, "Bbu abunda yyi mun!" Shiru Aysha tayi saboda a saninta dae Yaya Irfaan baya son shirme dan lokacin da ita window kawai suka fasa amma sae daya zane ta kuma ya saka ta kamun kunni na awa biyu amma yanzu yyi sanyi sosai surprisingly. Toh dan Zaynoora auta ce ko mae???
* Drop your votes and comments😉🥂
* Follow me on Wattpad @_khanoum_
©️Fateemah MG