Free chapter · Read without an account
🌸7
💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝
*Written by Fateemah MG
....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)
🌸Page 7
A tsaye Irfaan yyi 5 hours yana lectures nonstop dan ko five minutes break ƙin yarda ya basu sae dae yana lectures yana shan shayin da Zaynoora ta haɗa masa, sosai yaga students ɗin kansu na ja sosai kuma sun burgeshi matuƙa amma cikin students ɗin wacce ta shigo late tafi su ilimi ko rawan kai zaece bae sani ba dae amma kanta yana kawo wuta sosai, lokacin sallah yana yi ya ɗaukar masu break ya wuce Masjid dake kusa, ana idarwa ya koma ya cigaba da surfa masu karatu, Irfaan nayi magana mae ɗan ban dariya sae matannan su bushe da dariya duk cikin iyayi amma shi ko gezau baya yi, bae tashi ƙarashe masu lectures ba sae kusan uku da rabi, yana fita aikuwa ƴan mata suka bishi rututu da cewar zasu yi hoto ciki harda wasu maza, ya yarda aka ɗan yi hotunan kafin ya wuce gurin motarsa har zae shige, wannan kyakkyawar ta ɗazu ta ƙaraso gurinsa ita da wata ƙawarta suka yi masa sannu, murmushi tayi masa tace, "I'm Zahra Sir!" Kansa ya ɗaga mata alamar yana jinta nan ta cigaba, "Inason ƙarin bayani game da cigaba da karatu so I was thinking ko zan samu phone numbern ka since ba'a gari kk ba!" Glasses ɗin idanunsa ya zare kafin yace, "You can contact me on email ***" yana faɗin haka ya buɗe murfin motarsa ya shige sosai yaji haushin kansa dan ko da Zahra ta kasance kyakkyawar mace bae san ya akayi ya fara haɗa kyawunta da Zaynoora ba, tabbas Zahra tana da kyau amma Zaynoora tafi kyau amma abunda yasa yake haɗa kyawun wasu mata da ƙanwarsa ne ya kasa ganewa. Duk cikin jin haushin kansa ya taka mota ya cillata kan titi.
Tun kusan ƙarfe biyar na yamma Dr Anwar yazo gidansu Dr Irfaan, bayan sun gaisa da Aunty ne Zaynoora ta zauna a parlour suka fara hira tun lokacin har aka kusa kiran Magrib, zaune take cikin ɗinkin rigar atampa straight gown amma ko kaɗan bae ɓoye haɗaɗɗen shape ɗin dake a ɓiye cikin rigarta ba, tun ɗazun kuwa idanun Irfaan suke a sarƙe da jikinta dan har wani tsuma yake jin yana yi ga wasu mugayen feelings dake taso masa. Lokaci ɗaya Anwar yasan cewar yana son Zaynoora kuma yana sha'awarta kuma ko da Irfaan zae ce ya fito toh tabbas zae fito a ɗaura musu aure saboda yarinya ta kai aure tunda ko ina yake a cike to ko aure tsab zata zauna. Yanda take tafe tana girgiza cikin sakarci da rashin sani Anwar ke kallo yana jin wata iriyar jaraba na taso masa, trayn ruwan ta ajiye masa a gabanshi kafin ta koma ta zauna a gajiye cikin son jiki, tana zama sae dan kwalin kanta ya zame tana sane dashi amma son jiki yasa tayi ajiyar zuciya ta rabu dashi ba tare da ta gyara ba, nan Anwar dake zaune ganin yanda kitson suke ƙananu a matse ya burgeshi ga gashin baƙi ƙirin. Juyawa yyi ya kalli ba kowa a kusa hakan yasa ya matsa kusa da Zaynoora, tana can tana shiririta sae jinsa tayi yana shafa gashin kanta gashi ya wani matsota sosai har tana jin saukar numfashinsa akan wuyanta, wani kalar zulumi yake yana son yaji jikinta akan nasa ba tare da ya damu da cewar a gidansu yarinyar yake ba. A daidai lokacin motar Irfaan ta shigo cikin gidan parking yyi cikin gajiya ya fito daga motar riƙe da rigar coat ɗinsa, da sallamarsa ya shiga cikin babban parlour amma sae mugun gani da yyi a parlourn yana jiransa. Wata muguwar faɗi gabansa yyi take ya fara sallallami, lokaci ɗaya yaji ƙafafunsa sun kasa ɗaukar nauyinsa da kyar ya samu yace, "ANWAAR?" a wani firgice ya juyo ya kalli Irfaan dake tsaye a bakin ƙofa, a tsorace Zaynoora ta miƙe tsaye tana jin wani ƙarfi yazo mata ai bbu shiri ta ɗaure dan kwalin kanta ta matsa daga gurin gaba ɗaya, wani mugun tsoron Yaayan nata ne ya kamata lokaci ɗaya hakan yasa ta kasa ɗaga kai ta haɗa ido dashi. Kamar walƙiya haka Irfaan ya ƙarasa gaban Anwar ya kamo wuyar rigarsa cikin zafin nama, lokaci ɗaya Irfaan ya chanza kamanni ya koma kamar wani mayunwacin zaki. Hayaniyar ce ta saka Salma da Aunty fitowa dama ƙiris suke jira, Irfaan ko kallan gurin bae yi ba bare yasan cewar akwai mutane a gurin, sosai jijiyoyin kansa suka fito ga idanunsa da suka yi wani ja dasu kamar garwashi, sakin wuyan rigar yyi ya shaƙo wuyan Anwar da ta faman mayar da numfashi, murya can ƙasa Irfaan yace, "Saboda rainin wayo shine ka biyo ta har gida zaka danneta? Kai ko kunya baka ji ba?" Shiru Anwar yyi ya fara kakarin mutuwa amma ko a jikin Irfaan, ganin haka ba ƙaramin bawa Aunty mamaki yyi ba saboda Anwar abokin Irfaan ne sosai ko kusan tace shi kaɗai ya taɓa zuwa gidan a matsayin aboki na Irfaan amma gashi kuma yau suna faɗa kuma a cikin gidansu, da kyar ta samu bakin magana tace, "Aah Irfaan ka sake shi haka mana!" Yana cikin ɓacin rai yajiyo muryar Aunty hakan yasa ya sake shi amma sae huci yakeyi, ƙarasowa tayi tace, "Haba Irfaan meye yyi zafi har haka da zaku yi faɗa?" Shiru yyi bae bata amsa ba hakan yasa Anwar cewa, "Aunty fah wai dan nace ina son Noor shine wani abu?" Shiru Aunty tayi tana nazarin abun kafin tace, "Toh ai Zaynoora kamar ƙanwa take a gurinka ai ina ganin bbu komai!" Cikin ɓacin rai Irfaan yace, "Na gaya maka bata kai aure ba sae ta gama school dan haka ka fice daga gidan nan!" Yana faɗin haka yyi hanyar part ɗinsa, ganin Irfaan zae shige ɗaki yasa Anwar bin bayansa, sarai Irfaan ya lura da cewar Anwar yana biye dashi hakan yasa ya tsaya kafin ya ƙarasa part ɗinsa, ganin Aunty, Zaynoora da Salma a tsaye yasa ya bi bayan Irfaan ganin ya tsaya kuma yasa ya ɗaura hannunsa akan kafaɗar Irfaan yana cewa, "Irfaan dan Allah kayi haƙuri ni zan iya jira ta gama school amma wallahi ina sonta dan Allah, ka bani damar zuwa ko da hira ne kawai!" Tunda Irfaan yaji nan sae ransa ya ƙara ɓaci sosai, yana juyowa kuwa wata mahaukaciyar naushi ya kaiwa Anwar a baki da hanci nan kuwa Anwar ya fara ɓarin jini, jini ta hanci da baki ya fara tsiyaya, sarai Anwar yasan abu kaɗan ke ɓatawa Irfaan rai amma bae san abun nasa ya kai haka ba dan zafin naman da ya gani yau na daban ne. Taune haƙora Irfaan yyi yace, "Wallahi idan ka bari na fito na same ka a gidan nan baza ka ji da daɗi ba!" Yana faɗin haka ya juya ya shige part ɗinsa, cikin mamaki Aunty da Salma ke kallon ƙofar part ɗin Irfaan daya buga ta bayan ya shiga, cikin sanyin jiki Anwar ya kalli Zaynoora amma ganin kanta a ƙasa sae neman janye jikinta ma da take bbu abunda takeyi wanda hakan ba ƙaramin ɓatawa Anwar rai yyi ba dan bae yi haushin abunda Irfaan yyi masa ba kamar yadda Zaynoora tayi shiru da ita. Juyawa Anwar yyi abunsa ya fice daga parlourn, yana shiga cikin motarsa ya jawo tissue ya goge bakinsa, wani hucin takaici yyi kafin ya taka motar ya bar gidan. Zaune Irfaan yyi akan gadonsa yana mayar da numfashi, hannunsa yakai cikin gashin kansa yana fusga cikin jin haushi. Ganin hakan yasa ya miƙe ya fara ɓalle buttons ɗin rigarsa yana gamawa ya cire rigar ya ajiye ta kan gado ya shige cikin bathroom, kasa cire wandon yyi haka ya kunna shower nan ruwa ya fara zuba a jikinsa, ajiyar zuciya kawai yake saukewa dan idan bae kwantar da zuciyarsa ba sae yyi ta fushi har ƙarshen week ɗin. Sosai yake jin wani ɓacin ciki idan ya tuna yanda yaga Anwar ya danne Zaynoora yana kissing wuyanta ga yanda yaga tayi shiru da ita ko struggling bata yi ba barw ta kwace kanta. Tsaki yyi ya kashe showern nan ya zame wandon ya ɗaura towel ya fice daga toilet ɗin, gyara jikinsa yyi kafin ya zaro wata jallabiya ya saka, bae ɓata wani lokaci ba ya wuce Masjid.
Sae bayan sallar Magrib Aysha ta shigo gidan a gajiye, ɗakinta ta wuce tayi wanka ta canza kaya, sae bayan da tayi sallar Ishaa ta fita zuwa dinning area, acan ta tarar da Salma da Aunty suna cin abinci abunsu, tana zama ba da jimawa ba Irfaan ya ƙaraso kujerarsa yaja ya zauna ya fara cin abincin a hankali, yana cikin ci ne Aysha tace, "Ina Zaynoora take ne?" Taɓe baki Aunty tayi tace, "Yoo toh wacce take soyayya mae zata yi da abinci?" Kallon gefen ido Aysha tabi Aunty dashi nan Aunty dae ta cigaba, "Ni kam da ɓata kuɗin makarantar ta da akeyi dama auren aka yi mata kowa ya huta da jaraba!" Irfaan dake cin abinci ne ya ajiye spoon ɗinsa, fuska a haɗe ya ɗago da kansa yace, "Aunty karatu zatayi kuma banason ta haɗa karatu da komai!" Ƙurɓar ruwa Salma tayi tace, "Yaya idan tana so kawai.." bata ƙarasa ba ya watsa mata wani kallon banza yace, "Waya tambayeki?" Gumm ta kame bakinta inda Aysha dake gefe ji tayi kamar zata shaƙe idan bata yi dariya ba da kyar dae ta samu ta ƙunshe dariyarta ba dan taso ba sae dan tasan halin Irfaan sarai yanzu ya yanka mata rashin mutunci. Ajiye spoon ɗin Aunty tayi tace, "Amma Irfaan ai da sae ka tambayeta idan tana son auren, idan tana so ai sae ta ƙarashe a gidansa!" Haɗe girar sama da ƙasa yyi ya miƙe tsaye yace, "Karatu zatayi banason distraction acikinsa!" Yana faɗi haka ya juya ya koma part ɗinsa, idanu Aunty da Salma suka bisa dashi har ya shige part ɗinsa, cikin takaici Salma tayi tsaki nan Aunty tace, "Toh meye nashi dan tayi aure, sae kace mae kishi?" Tsaye Aysha ta miƙe tace, "Kwa ji dashi dae, zakuyi amai ku lashe kuwa!" Da haka tayi tafiyarta zuwa part ɗinsu, ɗakin Zaynoora ta shiga nan ta tarar da ita a kwance tana bacci, wato bata ci abincin dare ba ma kenan akwai tashin dare kenan dan tasan Zaynoora bazata taɓa iya bacci bata ci abinci ba kuma gashi ko kaya bata canza ba, wutan ɗakin ta kashe kafin ta juya ta fice daga ɗakin zuwa nata ɗakin.
Comment🌸🤝🏻