Free chapter · Read without an account

29

by Ramlat Abdulrahman Manga · SO da CIWO

*❤️‍🩹SO da CIWO❤️‍🩹*

®©Ramlat A Manga

Mai_Dambu

500₦

8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay

Shaida biya a turo ta wannan numbers din.

***

Or

***

Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76

Second to the last....

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

Dakata hajia💃💃💃💃💃 kin Dade kina Neman inda Zaki sai amintattun jaka, da takalma, sarkoki,masu kyau da quality cikin farashi Mai sauki❓

Ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,wannan gidan na RUMIEE UNIQUE BAG'S GALLARY na budeshi ne saboda na Baku damar siyan jaka,da takalma na Yara Dana manya masu kyau da quality da Kuma saukin kudi cikin aminci daga wajena.masu siyan daya da masu sari duk Muna mataba daku

Muna Kano Muna Tura kaya kowanne state da makotan Nigeria cikin yardar Allah,

Uhmm rigi-rigi ko kun san kayanmu sun iso like bags irin wanda Maamah take amfani da shi, Veils, Shoe's, more and more suna nan dasu...... Let go ❤️‍🩹💃🏻🐾

29

anin yadda Labibah take kwance da taimakon na'urar, haka yasa shi jin kowa damuwa da kullatar Innar Ayuba a ranshi, koda suka tawo a motar nan yayi mugun fata ya kai sau goma, domin yaso motar ta kwace Innar Ayuba ta musu yaga yadda za ayi idan Ibrahim bai aure Yar shi ba shege yake, xan yace dama motar ta kama da wuta idan suka isa. Kai mugun abu dai bai yi ba. Da ace ba iya Allah ke duba zukatar bayi ba, tow wallahi da an mutu a duniyar nan domin wani ya ga yadda kake mishi mugun fata ba zai muku dad'i.

Sun iso lafiya, da yake Dalhatu ya musu bayani sai gasu Bintu, nan ta kara musu bani dama sun zo ne tare da Baba Isuhu, baba Bashir sai Baba Hassan. Jikinsu ne yayi sanyi jin zunzurutun kudin da Yaran Bello suka biya sai wani irin kunya take dawainiyya da su, saka hannu Baba Bashir yake son yayi amma ya kasa sai diriricewa yayi Mijin Bintu Mustapha ya amsa ya ce masa. "Kawo Baba!" Ya saka hannun sannan aka zo aka fita da ita. Kallon fuskarta suka yi tayi wani fayau. "Yanzu Labibah ce ta koma haka?" "Eh Malam ai zuciya ce ta tab'u." "Zuciya!!!" Suka kara bin masu tura da idanu. Hawaye Laraba ta share tana faɗin. "Ciwon zuciya aikin da za'ayi mata ma na zuciyar ce, damuwa ta mata yawa ta rasa waye zai dubata. Yarinya ce da nayi imani da Allah bata da laifin kome, laifin namu ne" ta juya tana kallon Innar Ayuba da take juyayin maganar zuciyar. "Boddo!" Hadiye yawu tayi tana kallonta kafin ta ce mata. "Na'am Laraba!" "Labibah Ibrahim take so, kin sani na sani ita kanta ta san tana sonshi me tayi da Allah zai daura mata laifin da ba nata ba, Ni ce na cancanci haka ni ce na cancanci wannan kyautar." "Tow Laraba ban gane me kike nufi ba?" Cikin kuka ta ce mata. "Son Ibrahim ne ya janyo mata haka." Murmushi Innar ayuba tayi tana faɗin. "Ikon Allah ciwon zuciya kuma? Kuma sanadin Ibrahim? Haba sai dai Tatsuniya!" Rike hannunta Bintu tayi tana girgixa mata kai, idanunta cike da kwalla. "Innar ayuba kada ki ce haka." "Me nace? Haka suka fada ranar da aka kai mahaifinku cewa suka yi ciwon zuciya sai dai wani ciwon, bayan abinda suka yi yau sun tuno min abinda suka aikata ne, sun fama min ciwon da suka ji min ne." Ta zauna a kujeran da yake kallonsu. "Ni me zance? Na mishi dole ko me? Nace mishi yaso Labibah ko? Bayan Yaya Bashir abin da kuka aikata? Ni yanzu ban san me kuke so na fada mishi. Shi hali a jikin rai yake kuma gadonshi ake, zai yiwu ka samu wanda zai yarda da haka." Ta d'ago kanta tana kallon Baba Bashir da jikinshi yake rawa. "Yau ga abinda ya dawo maka, ban san yadda zan fada maka ciwon da naji lokaci guda ba, zafi biyu ka hada min na rasa mijina na rasa d'ana. Yau ga Labibah a cikin irin yanayin da na kasance Rayuwarta ko akasin haka." Tana gama fadar haka ta mike tana share hawayen da ya zubo mata. "Ba zan ja da ikon Allah ba, amma matukar ni ce na haife shi ba zai tab'a tsallake batuna ba." Daga haka ta mike tana me barin asibitin da sassarfa Bintu ta bita tana faɗin. "Kin koya mana yafiya da Afwa." Wani murmushi Innar Ayuba ta mata tana faɗin. "Tabbas Ayuba ya bude min idanuna amma bana jin zan iya yarda da wannan haɗin, Yar Bashir ce wanda a kullum burinsa ya ga bayanku sai na bar shi, ban san me Ubangiji ya shirya ba amma hada iri da Bashir jini ce tana bin zuria. Idan mutumin kirki ya samar da abu har abada abin yana tasiri ga al'umma idan mutumin banza, ana gadarshi!" "Innar Ayuba!" "Bari na tuna miki kissar Annabi Musa da Hijr, ko baki sani ba ne?" Hawaye ne ya zubowa Bintu. "Innar Ayuba damuwa ce ta nakasa jijiyar zuciyarta." "Ni damuwa da tashin hankali ya kashe min Mijina waye madadinsa? Bani da Uwa bani da Uba, bani da ahali shi din dai Ubanta kin san me ya faru bayan mutuwar Babanku?" Saka hannu tayi a bakinta tana faɗin. "Shiiii!" Ta fada tana me rike hannunta suka isa gaban Motar mijin Bintu yana bin bayansu. Bude mata balancy yayi ta shiga suka yi shiru domin kukan da Bintu take. Kauda kai tayi tana faɗin. "Shi Bashir idan yana da kunya bai isa ya kalli idanuna da sunan niman yarshi ta auri Ibrahim ba. ". Girgiza kai tayi tana jin hawaye na zuba mata. "Na miki wata misali?" Kura mata idanu Bintu tayi hawaye na zuba mata. "Idan yau Yayan Mustapha ya nime keta alfarmarki ya zaki yi?" Ba ita ba hatta Mustapha da yake gaban Motar sai da ya juyo yana kallon Innar Ayuba baki a sake. Murmushi tayi sannan ta cigaba da magana, duk da jikin Bintu na rawa saboda tashin hankali da kaduwa, wani irin yanayi take ji a ranta kamar zuciyarta zata buga. "Kina tsammanin haka bai zai faru ba ne? Ko kina ganin karya zan mishi?" Kifa kanta tayi a cinyar Innar Ayuba, tana jan numfashi dakyar. "Innar Ayuba! Bar maganar nan haka, ko mutuwa yarinyar zata yi a hakura da wannan abin. Indai Baba Bashir ne zai aikata. Nima na zare hannuna akan Yarinyar ba ke ba Innar Ayuba wanda kike tare da shi aka tab'a kimarshi sai inda karfinmu ya kare, har abada Uwa na dauke ki. Don haka nayi iya nawa sauran kuma su san yadda zasu yi My Lady idan kina da yadda zaki yi tow na gama nawa." Ya fada yana tsaki tare da kananan magana.

Haka Bintu da Innar Ayuba suka sha kuka, shi kan Mijin Bintu kudin mota ya bawa Balancy ya bawa Baba Isuhu su koma gida amma Inna ya barta anan zata huta. Bawan Allah nan baya son abinda zai tab'a Innar Ayuba, karfin dawowa da mahaifiyarshi innar Ayuba ce tace ya dawo da ita gefen Bintu ga girma ga kadaici, Yara suna shiga su ta damunta ita kuma taki barin Rano,.shine ya ce ya biya mata umara amma sai watan azumi da haka zai dawo da ita wurinsa.

Da yamma Innar Ayuba suka koma gida, shi kuma balancy ya tafi da motar babu kowa a hanya ya dibi fasinjoji abinsa, ina ruwansa yana da damarshi ba zai yi wasa da ita.

***

Yola.

Ranar da na cika kwana sha uku da maraici na farka, jin ance na farka kafin wani lokaci dakin ya cika wanka nayi na zauna a kasa na fara sallah, ina jin hawaye na zuba min naki magana da kowa domin gani nake kamar Baffanmu ya mutu, kasa fada min suka yi wurin karfe shida da wani abu ana fita sallah, na kifa kaina a tsakanin cinyoyina. Ina kuka a hankali. "Rahmah!" Da sauri na juya ina kallonshi, kallon Mama nayi ta galla min harara. "Ina cewa kin magana kika yi mana!" Turo shi Hamma Umar yayi yana washe baki, nace mishi. "Baffanmu!" "Na'am Baby gurl" da rarrafe na isa gabanshi na daura kaina a cinyarsa. "Baffana!" "Ke yar renin hankalin wani baffana!" "Ba zaka kyale min Yarinyata ba ko? Omar zan maka rashin kirki!" "Allah Baffanmu idan ka ga yarinyar nan tana shagwab'a ji nake kamar na hadiye zuciyata na huta yarinya sai tab'ara." "Allah ko? Tow kayi na kudinka!" Inji Mama tana hararanshi. "Hassanah taci abinci kuwa?" "Ina ta kalle ni balle ta nime Abincin ma!" "Mama Allah gani nake kamar wani abu ya faru kuke hide dinsa, ni kuma bana son naji mugun labari na Yaya ma da shi zan koma ga Allah." Jan kumatunta tayi, aka turo kofar Raheemah ce dauke da basket bayanta Sharahbil ne. Kura musu idanu nayi naga kamar na fasa ihu. "Princess zo ki ci abinci!" Ta fada tana rike hannuna na mike zuwa bakin gadon na zauna. "Mama ina kewar Innarmu, matar da muka hadu a Umara kullum sai ta saya min madara da dabino da apple!" "Kai Umar ungo je ka sayo mata Admiral da dabino yar Madina." "Baffa da kabar shi na sayo mata." "Na gode!" Ya fada yana kallon Mama tana zuba min abinci, "Mama abincin Addah Salaha ce tayi ko?" Murmushi tayi tana faɗin. "Eh!" Gyara zama nayi da kyau ina kallon abincin ta fara bani a baki. "Maamah ya jikinki?" "Alhamdulillahi!" Na fada ina amsar abincin. "Mama ya baki hada min da namar!" Da yake da hannu take bani, kallona tayi sannan ya yanko kazar ta saka min, "Hassanah kira Salim ya mai dani daki." "Tow na mai da ka mana Alhaji." "A'a ka barshi Hamma Salim zai zo!" Na fada da sauri domin tsoron shi nake kada wani abu ya faru ya kara saka min zuciya sukuni. "Tow ka barshi tunda tace a'a." Daga haka na cigaba da cin abincin a hankali. "Mama kin tuna ranar da nace zan yiwa Baffanmu abinci?" "Yawwa Princess muna komawa gida zaki fara min kafin ayi bikinki!" "Yes, Allah sarki Yayana zan yi girki bata nan." Duk sai wani abu ya tsaya a ranmu, domin tunawa da Yaya, Kallona Raheemah tayi tana faɗin. "Abinci zaki mana." "Hmm!" Na fada mata. "Twins na damu da ke ki tambayi Mama." Yadda tayi kalar tausayi sai naji ba zan iya dauka ba. Kallon Mama nayi ta gyada min kai tana faɗin. "Kada ki ga yadda ta damu kamar ta cire ciwon ta kara a kanta." Idanuna ne suka cika da kwalla. "I'm sorry Twins." Mika min hannu tayi na rike muna hira, har Hamma Umar da Salim suka shigo, nan muka ta hira suka manta da wani Sharahbil. "Ni kamar bai da lafiya?" "Who care ya mutu ko ya rayu?" Duka Mama ta kaiwa Hamma Umar. Haka suka raka Baffanmu, ni kuwa muka yi ta hira na manta da wani a wurin. Sai can da Sharahbil ya gaji yayi sallama yana faɗin. "Raheemah zo na ajiye ki a gida." "Twins zamu tafi bari mu baku wuri." Ta fito Mama itama ta fito, tunda suka zauna Mama take kallon yadda Raheemah take dame. "Akwai wani abu ne?" "A'a babu kome!" "Raheemah amana daya ce idan aka tab'ata Allah sai ya tab'aka, ki sani amana tana tsakanin siradi haka zumunci, idan ka tab'a kowanne ba zaka tab'a wuce su ba sai sun bukaci sanin me yasa baka rike su da kyau ba. Shiru tayi tana kallon kasa. Domin Mama ta daure ta da kalamanta. "Maamah ta yarda dake, kuma ta amince da ke ni ban tab'a ganin wacce aka bawa amanar rayuwa kamar ki ba.....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.