Free chapter · Read without an account

15-16

by Fadila Lamido · HAWAYEN ZARGI

HAWAYEN ZARGI

By

Fadila Lamido

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Page 14-15

Tushen Labarin

Habibullah shine da na biyu a gidan su, Anty saratu ita ce babba tazaran shekara biyu ne tsakanin su, Sadam Abba da Farida duk kannen sa ne, Malam Yusuf Ladan shine mahaifin su, wadda ya kasance shine tshon ladanin masallacin unguwar, tun unguwar be gama zama gari ba, don haka sunan ya bishi babu wadda zakacewa Malam Yusuf Ladan yace be sanshi ba, daga yara har manya, Mahafiyar su wadda suke kira da Inna jajirtaciyar mace ce da ta tsayu akan karatun yaranta, bangaren isalamiya dana bako, Ranar da Saratu ta yi sauka a ranar malam Yusuf ya aurar da ita, duk da cewa taso ta yi karatu sosai amma malam ya ki alokacin tana da shekara sha bakwai, kasancewar Habibullah na mijin ya samu damar ci gaba da karatu har ya haddace alkur'ani, a bangare boko kuma ya shiga makarantar gaba da sakandire, duk da cewa malam Yusuf karamin dan kasuwa ne baya wasa wajen karatun yaran shi, tunda Habibullah ya haddace alkur'ani alokacin anan cikin unguwan yan kaba Kano a makaratar madarasatul Usman bin Affan ya cigaba da zuwa yana karantar da yara.

*****

Alhaji Ibrahim shine Mahaifin Habiba, wadda ya kasance tsohon soja ne, Alhaji Ibrahin, Matan shi biyu, Uwar gidan shi wadda suke kira Mama ita ce mahaifiyar Habiba yaranta maza uku, Ya Mubarak ya Abdurrazak ya Isma'il Habiba ita ce autar ta, sai amarya Umma yaranta maza biyu mata biyu duk kannen Habiba ne, gidan Alhaji Ibrahin katon gaske ne kowa da gefenta sai falon da ya hada dukanin bangarorin gida, mahaifin su mutum ne kaifi daya wadda baya daukan raini ko wargi, baram ma idan alluran sa ta motsa.

Tun tasowan Habiba yariya ce me kwazo a makaranta, bata fiye son magana ba, sannan tana da matukar kunya daga islamiya har boko duk malaman sun santa sabo da kwazonta da son karatu, shekaran ta 14 tana aji biyar a boko kuma tana ss 1"

******

"A'a, ya haka, kika shigo ranki a bace?" Mama ke fadin haka ganin shigowan Habiba idonta cike da kwallah.

Kasa magana ta yi tana matse kwalla don haka mama ta sake cewa "Yau na ga ikon Allah da girman ki ina magana kin min shiru me ya faru?" Ganin Daddy daya tsaya yana kallonta ta fashe da kuka tare da cewa "Wani malam ne ya dake ni."

Mama ce tace "Me kika yi? Haka nan ai baza a dake ki ba."

Zama ta yi tare da cire Hijjabin ta rike hannu tare da cewa "Ban yi komai ba."

Juyawa Daddy yayi yana kokarin fita tare da cewa "Sai ki yi hakuri, koyo kike dole idan kin yi ba daidai ba a hukunta ki."

Su Umma ma duk haka suka ce, don haka ta mike ta koma daki cike da takaicin dukan.

Washegari misalin karfe biyu bayan ta dawo boko ko abinci bataci ba ta wuce islamiya, tana zama yana shigowa ajin, don haka taji gabanta ya fadi, jiya ta fara ganin shi a makarantar sai dai duk lokacin da zasu hada ido harara zataga yana zafga mata don haka da sun hada ido take yin kasa da kanta, kuma duk idan zai yi tambayan ita yake fara tasa, don haka da ya shigo take daburcewa. idan ya ga dama ko ta yi daidai zai dake ta yace bata fitar da harufan yadda suka dace ba, don haka duk ta daburce, tun mutane basa fahimta har sauran dalibai suka fara fahimta, yau ma kamar kullum yana fita dalibar dake kujerar gaba ta juyo ta kalli Habiba dake maida kwallah tace, "Wai ke me ki kawa Malam Habibullah naga sai ya yi ta hararan ki.?"

Da Hannu Habiba tabata amsa da oho yayin da hawayen da take makalewa suka zobo.

"Tab kuka? Aiko idan ni ce bazan yi kuka ba wallahi yana hararata zan rama, gaki da manyan ido wallahi ki dinga ramawa, kuma ni karatun ma bawani kuskure sai yace wai bakya karatu dakyau duk kin zama wani iri a aji bakya sakin jiki yanzu sam. idan mun yi sallah mun dawo shi zai kara shigowa yana haranki ki rama, idan yace baki yi karatu daidai ba kice ya nuna miki daidai wajen."

Kaya Habiba ta fara hadawa tare da cewa "Ni ana tashi sallah zan gudu gida bazan tsaya ya dake ni ba, tafin hannunta ta nunawa Zainab dake zaune ta ce "Kinga nan dina in da ya kunbura dazon daya kawo min duka na tare "

" Tsanar ki ya yi kawai Habiba, garama tun wuri ki nuna masa kin gane"

Habiba bata sake cewa komai ba ta tattara littatafanta tasa cikin jaka, ana tashi sallah kuwa ta koma gida kamar yadda tace.

" Habiba daga ina haka?"

Mama ta tambaya ganin a Habiba kwance a falon gidan.

Mama gudowa na yi wani malami ne zai shigo mana ban iya karatun ba kuma ya cika duka.

Cike da mamaki mama tace "Ikon Allah, banta jin irin wannan a bakin ki ba, idan an dake ki a makaranta dawowa gida kike ki dage da karatu har ki iya, me yasa kika bari har aka kawo lokacin da zaki fara guduwa makaranta? Sakacin ki ko nawa.?"

"A'a Mama, ba sakacin ki bane, ni ma ba nawa bane, amma bazan taba iyawa bane kona koya bazan iya ba."

Sosai Mama ta kalli Habiba sannan tace "Iko sai Allah."

Mikewa Habiba ta yi a wurin tare da cewa "Ni acire ni ma a makarantar kawai."

Wannan karon mama bata ce komai ba illa binta da kallo har ta shige daki, tun daga ranar bata sake zuwa islamiyya ba har aka dauki tsawon sati daya Mama bata sake mata magaba don haka ta sake mike kafa sai dai abin da ya bata mamaki gaba daya gidan babu me mata maganar islamiya, tana kallo yaran gidan zasu shirya su wuce ita tai kwanciyarta, ranar wata asabar karfe biyu saura Mama ta samu Habiba a daki, kayan makaranr islamiya ta ajiye mata tare da cewa "Shirya ki je makarata Habiba karatu nata wuce ki."

"Mama ai in naje yau korata za su yi nafi sati biyu fa banje ba."

" A'a baza su koreki ba in kinje kice baki da lafiya ne."

Kuka Habiba ta fara don haka mama ta kara shiga mamaki domin duk gidan babu wadda ya kai Habiba son zuwa makaranta.

"Yanzu don nace ki je makaranta ki ke kuka?"

"A'a Mama ki yi hakuri dukana za a yi idan naje shiyasa."

"Ko kashi ki za a yi ki tashi ki je, banda rashin hankali don mutum be iya karatu ba kawai sai ya daina zuwa makaranta, sai da dankoyo ake yin gwani, dagewa zakiyi ki koya."

Kara karfin kukanta ta yi tare da mikewa ta fara saka kaya, bayan ta kare ta kalli Mama da har lokacin take tsaye tace "To azo a raka ni don Allah"

"Waye zai raka ki ? Ai kinsan dai gidan babu kowa."

"Ko ke ko Umma.'

"Kinga Habiba ki kama hanya idan ba haka ba zan hadaki da Mubarak."

Cikin matsanancin kuka ta fara tafiya tare da cewa "Amma Mama kinsan ba cire ni za ku yi ba kuka barni na dade banje ba..."

Bata jira abin da mama zata ce ba ta fice a gidan har ta isa makarantar kuka take don haka tana shiga ajin ta kwantar da kanta kan bencin tare da tattaro nutsuwarta, bayan an fara karatu ta dan saki jikinta, ganin yau ko gilmar shi bata gani ba, misalin hudu da minti Ashirin wani yaron ajin ya kira sunan Habiba cikin faduwan gaba ta daga kai ta kalli in da yake kokarin zama yana me cewa "Ki je inji Malam Habibullah"

Tun kafin ya rufe baki ta mike yayin da duk daliban suka juyo suna kallonta, tuni idon Habiba ya cika da hawaye, shawara sauran daliban ke bata cewa ta daina jin tsoron shi, wasu kuwa cewa suke taku ce bata zo daya da malam ba wata kila aljanun ku basa shiri.

Mazan ajin kuwa dariya suka fara mata tare da cewa be wuce rashin zuwan ki kwana biyu ne, jin haka Zainab ta yi karab ta ce, "Ai don tsoron shi ta daina zuwa marantar."

Jin maganganun bazasu kare ba ,tai saurin daukan jakarta ta fice, kai tsaye ofishin malam ta shiga ta wuce can karshe inda tasan yana zama, yana zaune da qur'ani a bude a gaban sa, ahankali Habiba ta tsuguna tare da cewa "Gani."

Shugaban makarantar ne ya waigo ya kalli Habiba sannan ya juya ya kalli Habibullah yace, ,"Lefi ta yi ne?"

Jin Malam Haruna na magana yayi saurin dagowa tare da shafa gemon sa yace "Eh malam"

"Amata afuwa, yariyar na da kokari tana da son karatu kuma akwai dokokinmu da yawa wadda take kiyaye mana su, duk malam sun shaida haka."

Cikin girmamawa yace "Malam baku gama fahimtan ta bane bata ji, sannan yau kwanata goma sha shidda batazo makaranta ba" Bulalan gaban shi ya nunawa malam haruna tare da cewa "Don haka yau kashi zan bata."

Dan murmushi malam Haruna ya yi sannan ya sake cewa "Kanneta sunzo sun gaya cewa bata da lafiya ai."

"Lafiyarta kalau Malam, ai tana zuwa boko kullum" Habibullah ya fada cikin girmamawa.

Baki Malam Haruna ya bude sannan ya jefawa Habiba tambayan wai tana zuwa boko, sunkuyar da kai ta yi batare da tace komai ba don haka malam Haruna yace "Akwai kamshin gaskiya kenan Habiba kin fara wasa da karatu ko, har ki zauna a gida na wannan kwanakin baki zo makaranta ba, lallai ya cancanci a zane ki" Mikewa ya yi ya fice kamar jira Habibullah ke yi ya mike tare da bulala ya tsula mata tai saurin zabura tare da shafa gefen cikinta don tanan taji radadin bulalar, mikewa ta yi tsaye don haka ya shiga tsula mata a kyauri iya karfinsa tun tana iya gane adadin da ya yi harta kasa, zuwa can taga ya yarda bulala ya koma ya zauna tare da cewa, "Ko ciwo kike a gunguro ki ko a baro ne a kawo ki makaranta, karna sake zuwa ajin ku naga bakyanan."

Radadin da take ji baxai barta amsawa ba

Dan haka ta tsuguna tare da hada kai da guiwa ta fashe da kuka cikin tsawa yace "Tashi kibar nan."

Mikewa ta yi tana fita ana tashi don haka ta fice a makarantar.

****

"Yaushe makarantar ta ku ta lalace haka, akan me za a ma yariya mace irin wannan dukan haka?" Dadddy ke fadin haka cikin bacin rai.

Yaye riga Habiba ta yi ta nunawa Daddy shatin dukan dake cikinta, fada Daddy ke ta yi yayin da Mubarak da Abdurrazak na tsaye gefen sa.

Mama dake gefe ne ta fada musu laifin Habiba ne don haka Daddy ya sausauta fushin shi tare da kara yi mata fada karta kara fashin makaranta.

Gadon ta koma ta kwanta tana rawan sanki yayin da ta ke kara jin tsanar makarantar cikin ranta, har washegari da Daddy yazo dubata jikinta zafi rau don haka Daddy ya cewa Abdurrazak kukai yariyar nan Asibiti ta ji jiki sosai, wai wanne azzalumun malami ne wannan ne, shi bashi da yara ne? Idan akaiwa yarsa irin wannan zaiji dadi? zan je makarantar in ja masa kunne, ba jiya ta fara zuwa makaranta ba babu wadda ya taba mata irin wannan dukan ko ni ubanta, "Ke wani malami ne Daddy ya tambaya cike da bacin rai."

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol