Free chapter 路 Read without an account
003
HAIRAN 馃グ鈾ワ笍馃槶馃挃
No. 3
Ayshatuuu
*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her 馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏
***
*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.
***
Contact her on WhatsApp馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏
***
***
Mikewa tayi tana kallon shi, sede maimakon kallon da ta saba Yi Masa na kauna da Kuma soyayya, yau din se yake ganin kamar she's seeing through him, bai damu ba ya karaso cikin parlon da ke tashin wani irin kamshi na turaren wuta me sanyaya zuciya da saka nutsuwa ya zauna, Wanda kyauta ce aka fara kawo mata na turare_by_ruky, tun da ta fara amfani da shi bata Kara bari tayi amfani da wani brand din ba, kamshi royal scent, heavenly scent se turare_by_ruky. Itama se ta zauna tana fadin
" Sannu da zuwa! Yaya tace kunje Zaria"
Ya gyada Kan shi yace
" Munje tana gaishe ki, ta bada kuka da daddawa a kawo miki tana trunk din motata!"
Tace with a blank emotion
" Nagode! Kwana biyu Zaria ta aure ka da yawa!"
Ta fada tana rike idanun shi cikin nata, ya dauke Kan shi Yace
"Mhmm!"
Tare da mikewa yayi hanyar dakin shi Dan watsa ruwa, hakan se ya darsa Mata zargi cikin zuciyar ta, normally zai fada mata yace ga dalilin zuwan shi can din, amma shirun da yayi da wucewar shi yasa dole tasan akwai wani abu, ta mike Dan bin shi daki se ta hanga wayar shi Dake gefe ya Bari ta nufa, har ta saka hannun ta da niyyar dauka se Kuma ta fasa, tunanin ta daya kada tayi bincike , saboda ita din bata son bincike akwai ranar da kanwar ta Dija tazo ta hutu, ya akai ya akai ta kama ta a daki tana bincika Mata drawers, a ranar ta saka Joseph driver din gidan ya maida ta zaria Kuma ta Hana ta dawo Mata gida. To yanzun ma ba zata duba wayar ba, Amma tasan inda zata san ainahin inda suke zuwa shida yaran.
Dakin su A'isha ta nufa, ta samu Hanifa na kwance A'isha Kuma Bata dakin. Zama tayi bakin gado tare da tapping kafar Hanifa wadda ta saka ta tashi ta zauna tana fadin
" Mama sannu da gida!"
Tace
" Yawwa Hanifa! Bayan gidan Yaya Ina kuka je Kuma?"
Hanifa yarinya ce amma Kuma she's bright sosae da sosae, tasan Babu wata mace da take son kishiya Kuma tasan Bai kamata ta fadawa Mama komai ba, hakan yasa tace
"Tab gidan Mama kawai muka je, Abbu yace munje wani gurin ne?"
Ba tare da ta Bata amsa ba ta mike tayi tafiyar ta, tasan yadda Hanifa ke son baban ta ba zata fada ba, zata shiga daki sukai kicibis da A'isha ta fito daga kitchen, ehen tasan A'ishatuu zata fada mata gaskiya hakan yasa tace
" Eesha ta! Ina kuka je ku da Abbu kafin kuje gidan Yaya!'
Tace da excitement a muryar ta
" Wajen Anty Hairan muka je!"
Gaban ta taji ya fadi, Jin wai a sentence din akwai sunan mace a ciki, Kuma an alakanta ta da mijin ta...
" Mama Baki ganta ba kyakyawa, tana da kirki sosae. Abbu yace Yana son ta..."
" Rufe min Baki!"
Ta fada da karfin gaske, saboda gani take se ta Fadi hakan A'isha zata jita tayi shiru, kowacce kalma da take fada saukar Mata take tamkar saukar dalma a zuciyar ta. A'isha wadda ta tsorata saboda ihun da tayi tace
" Mama kin tsora ta ni "
Daga haka ta tafi dakin su ta bar uwar a zaune jugum kamar wadda aka zarewa dukkan lakarta!
A bangare na Ina zaune ne dai cikin wannan lecture hall din, Amma Babu abin da nake fuskan ta, zuciya ta da tunani na gaba daya sunyi nisa sosae daga ajin, sun tafi can duniyar tunani, bansan me Malam Arabi yake koyarwa ba balle nasan har ya sakko daga Kan podium ya nufo inda nake, soft knock din da naji Saman table dina yasa nayi firgigit na dawo tunani na, na dago Naga dukka Yan class din kowa kallo na yake da tausayi a fuskar su, yayin da wasu ke min kallon wannan lafiyar ta daya kuwa, na dawo da idanuna Kan fuskar malam Arabi da ya zuba min idanun shi, nayi saurin sunkuyar da Kai kasa saboda gayen bashi da dadin harka ko kadan.
"Why are you crying?"
Nayi saurin dagowa tare da kallon shi hadi Kuma da saka hannu na na shafa kumatu na, da gaske fuska ta a jike take da hawaye, Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!! Na ambata a karkashin numfashi na tare da lumshe idanu na Ina jiran tijarar da zai min. Amma ga mamakin kusan kowa da ke cikin lecture hall din kawai ce min yayi
"Go and rest!"
Ina zanyi musu Allah ya rufa min asiri, a hankali cikin rashin kuzari na fara tattara lecture note din Dan tafiya, har lokacin hawaye gudu yake a fuskata har sniffing nake na kokarin dainawa amma Abu yaci tura, Shima Kuma bai tafi ba illa kallon na da yake with a pity! Cikin kukan nayi Masa godiya sannan yace gobe na same shi a office din shi, Kai na kawai na gyada na fice zuwa wani guri can bayan wani faculty, na zauna nayi ta kuka Ina hasaso rayuwa ta tun daga lokacin da nayi wayo nake cin karo da kaddara iri iri har ta kawo wadda ta rusa min rayuwa gaba daya, Dan a ganina da Kuma mutane ni ba komai bace ba Banda abun kyamata da Kuma gudu, shiyasa bana sakewa da mutane saboda Ina ganin kamar they can see through me ko Kuma watarana zasu fahimci matsalar da nake da ita su kyamace ni, ko su guje ni tunda basu san ta wacce hanyar na samu ba!
Se daf da maghrib kafin na mike bayan naji zuciya ta ta lafa daga ciwon da take yimin, tap na karasa nayi alwala sannan na dauki Kaya na zuwa massallaci, ana idarwa na zauna ko motsawa daga gurin banyi ba, gaba daya bana son haduwa da ko mutum daya da na sani balle har ya tambaye ni whether I'm okay or not, shiyasa nayi silencing waya ta kada ma a dame ni. Anan nayi har sallar ishai sannan na tafi tutorials duk a kokarin ganin na dauke tunani na daga abun da ya faru. Bayan an Kamalla tutorials na tsaya a wani shop na saya lemu me sanyi sannan na nufi hostel.
Nuriyya na tsaye a kofar dakin mu, I'm sure ta gaji da jira na tana Kuma zuba idanun ta inda Zan shigo, tana gani na ta karaso inda nake tana fadin
" Hairan Ina Kika je? Ina wayar ki?"
Na dubi fuskar ta yadda damuwa ta kwanta sosae a fuskar ta, se naji ban ji Dadi ba, kilan tayi ta Kira na har ta gaji, hannun ta na rike nace
" Kiyi hakuri tutorial naje"
Ta Harare ni cikin Jin haushi tace
" Tun dazun nake neman ki, hankali na dukka ya tashi, gashi Esther tazo tace you cried a class har lecturer yace ki tafi ki huta! Me yake damun ki?"
Nayi shiru Ina tunanin ta inda Zan fara, se ta shige ciki tana fadin
" Nasan ba fada zakiyi ba, Nima da shishigi nake!"
Se naji babu dadi, na bi bayan ta har Kan gado bayan mun Dan gaisa da sauran roomies din namu, Dan wasu tun asuba da suka fita ban sake haduwa da su ba. Zama nayi Kan gadon Nuriyya nace Mata cikin sanyin muryar
"Kar Kiji haushi Dan Allah Zan fada Miki, kawai dai Ina bukatar naji ni ni kadai"
Nuriyya mutum ce me understanding hakan yasa tace
" Take your time, koma menene Allahu ya baki mafita. Kici abincin"
Se naji Dan sanyi cikin Rai na, na dauki flask din na duba naga white rice ce, cikin plate na diba na zuba sauce sannan na fara ci, Babu jimawa na gama, na rage kayan jiki na naje nayi wanka, lokacin da na gama shirin kwanciya already karfe tara da rabi tayi, na hau gado na kwanta sannan na janyo wayar ta, calls na gani sunfi goma, wasu na Nuriyya, wasu daga wajen Anty se Kuma na Prof da few of my course mate! Na saki ajiyar zuciya me nauyi tare da fara Kiran Anty, ta dauka Amma muryar ta ta nuna ta fara bacci hakan yasa nace Mata Zan Kira ta da safe kawai. Na kashe tare da kallon jerun Kiran shi, zuciya ta se ta fara ingiza ni akan na Kira shi naji yadda ma yaje gida at the least, Amma idan na kira ai kamar na bashi kwarin gwiwar zamu kasance tare kenan? Idan Kuma ban Kira ba Ina ganin Zan iya bacci a Daren nan kuwa? Ba tare da na fahimci abun da nake ba kawai na danna Kira Wanda Babu wani Bata lokaci ya shiga, dama ban Kira ba, kila da nayi saving Kai na da zuciya ta daga bacin Rai.
Kafin na farga ego ya dauke ni har wayar ta shiga Kuma har ya dauka, which was odd! Ba halin shi bane ba picking calls di na, he always decline them and call back, amma se nayi la'akari da ya Kira Kuma Yana tsoron kada ya katse ya Kira ni naki dagawa hakan yasa na Kara kunne na murya ta a hankali cikin sanyin ta na kullum nace
"Assalamualaikum !Ya hanya?"
Shiru baayi magana ba, se nayi tunanin ko ansa mu breakage na network ne, na Kara fadin
"Hello are you there?"
Wata uwar ashar kawai naji an kutuntuma min da ta saka nayi saurin bude idanu na da suke a lumshe, surely wayar ba hannun shi take ba, kilan a hannun matar shi take
" Kece karuwar da take bin miji na ko? To tsaya Kiji na fada miki miji na nawa ne ni kadai, Babu wata shegiya Yar iska da ta isa..."
Zuciya ta ta kawo min wuya, se na bude Baki Zan katse ta na kasa, haka inaji Ina gani ta zage ni tas tace idan karuwanci nake ji nayi shi a waje amma baa gidan ta ba, mijin ta yafi karfin na Dan zata iya nakasa ni akan shi....Turkashi
"DiDi meye hakan..."
Shi ne abun da naji a background din, gaba daya nayi miutuwar zaune ko nace kwance tunda a kwance nake, a hankali na saki wayar akan pillow tare da yin shiru Ina auna dukkan kalamanta a cikin kwakwalwar Kai na. Wai ya haka? Wai me yasa haka? Me yasa wannan Abubuwan suke faruwa dani? What have I done to deserve all this? Me yasa rayuwa take min irin wannan abun? To wai ma Dan na so shi laifi ne? Laifi ne kawai tarayyar da nayi da shi?
HAIRAN is not free, contact me via WhatsApp 馃憞馃憞馃憞
***
Wanne labarun kike so? Aure ne bakiyi da wuri ba kike ganin kamar ba zakiyi ba? Karanta *FARA YAR SHEHU* Abu Kika rasa kike ganin kamar ba Zaki samu madadin shi ba, then ki nema *UNAISA* Soyayya ce tayi Miki kamu Kuma wani tsaikon ya Hana kiyi aure? To *ZUMA* ya kamata ki nema, A cikin *BANI DA LAIFI* Zaki gane cuta ba mutuwa bace ba, Kuma rabon kwadon ko ya hau sama se ya sakko, kiba ce da ke ko ke siririya ce da mutane suke shaming din ki har Kika fara samun mental break down ki sani *BINTUN BATUUL* Na jiran ki. Auren dole akai Miki, ko Kuma kina fama da maraici ne? Kuma Baki karanta *AFIYYA* ba jiran me kike Baki karanta *TSINTUWA* , *HIKMA* , *ME RABO KA DAUKA* , *UWARGIDAN BAHAUSHE* ba?
漏Oum A'eesh