Free chapter 路 Read without an account

006

by A'isha kwalam Hassan 路 HAIRAN

HAIRAN 馃グ鈾ワ笍馃槶馃挃

No. 6

Ayshatuuu

*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.

***

Contact her on WhatsApp馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her 馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

Se dare da ya koma gida sannan ya samu Hanifa a dakin su, har Kuma zuwa wannan lokacin fa DiDi Bata bashi wayar ba, ya ma kasa sake Mata magana, a ganin shi tun da ya Riga ya saya sabuwa to kawai magana ta kare, Amma fa taci albarkacin mahaifin ta ne Dan wallahi ba dan shi ba da kasancewar ta mace, da Bai San irin abunda zaiyi Mata ba, dukda sanyin halin shi Amma ko damo da bahaushe ke kira sarkin hakuri, wani lokacin idan aka kure shi Yana retaliating balle shi, shi abin da yafi damun shi ma, irin extreme raini da tayi Masa. Ya gyada Kan shi Yana ayyana na karshe kenan, yayi knocking softly a kofar dakin su A'isha tare da fadin sunan Hanifa Dan su San shi ne, in case kayan jikin su bana arziki bane ba. Da sauri Hanifa tazo ta bude kofar ba tare da jiran komai ba ta fada jikin shi tana Kara tsananta kukan ta, a lokaci daya taji Kan shi ya Kara cunkushe wa, bayan ta ya Dan bubbuga Yana fadin

"It's ok! Ya Isa haka, daina kuka"

A haka ya jata zuwa dakin nasu, Aisha ya samu kwance Saman gadon itama tana kuka, mamaki ya kama shi, tare da ayyana possible abin da ke faruwa da yaran na shi, Zama yayi gefen A'isha har lokacin Hanifa na rike da hannun shi, Kuma dukka basu daina kukan da suke ba,

"To ku tashi ku fada min abin da yake faruwa Mana girls!"

Dukka Suka tashi kuwa suka zauna, A'isha tace

"Mama ce ta mare ni wai saboda Ina raka ka wajen Anty Hairan"

Ya bude idanun shi cike da mamaki, ita Kuma Hanifa tace

"Kuma ta mare ni nima Abbu sannan ta dauke min waya ta!"

Ran shi yay mugun baci ya Mike, meke damun DiDi ne a kanta, komai zasui suyi tsakanin su amma banda yaran nan da Basu son komai ba, this innocent souls. Tana daki ya same ta, akan couch tana zaune tana taunar chewing gum, looking elegant cikin wani tsadadden lace me launin Baki da milk, tayi kyau har ta gaji, Babu alamar damuwa ko wani remorse na abubuwan da takeyi a fuskar ta, se ma wani cika take tana Kara batsewa, ita ala dole ita akaiwa laifi. Ya zauna daga bakin gado Yana duban ta Dan ko sallamar da yayi Bata amsa ba yace

"DiDi! You're getting on my nerves, me yarannan sukai Miki da zaki Dake su har ki karba wayar Hanifa"

Da farko kamar ba zatayi magana ba se can ta kalle shi tace

"Saboda Kan ka yana rawa zaka Kara aure shi ne zaka fara interrogating di na akan dalilin dukan Yara na. Wallahi wallahi wallahi, kaji rantsuwa uku ba zaka Kara aure ba matsawar Ina numfashi a duniya"

Wani irin Kalli yake bin ta da shi, ta Riga ta Kai shi bango Amma Kuma tana cin darajar iyayen ta da Kuma darajar yaranta yace

" Shikenan Ladidi, I assure you wallahi se nayi aure , mu zuba mu gani Wanda ya gaji ya fasa!"

Daga Nan ya fita a dakin ya koma dakin su Hanifa ya kwashe su Dan fita, har sun fita parlor Prof da har lokacin zuciyar shi babu dadi, abu goma da ashirin ya dubi Hanifa yace taje ta fadawa Maman su zai fita da su, ko da taje a waya ta same ta tana Yi, kafin ma tayi magana tace Mata ta fitar Mata daga daki, Babu wani bata lokaci Hanifa ta juya ta koma, ya tada motar kenan zai fita har an bude gate se gata ta fito, tana tafiya tana bada Fadi, ta karaso inda motar tashi take, se da ya bari ta gama tsayuwa se kuwa ya figa motar shi yayi ficewar shi daga gidan, takaici, bakin ciki da Kuma kunya suka lullube ta musamman data juya taga gardener Dake trimming flowers din gidan Yana nan, ga gate man din gidan da Kuma driver acan gefe dukka suna nan suna kallon ta, kamar guguwa haka ta wuce ciki.

A hanya ya samu ya tambayar Hanifa ko ta haddace digit din Hairan, aikuwa cikin sauri ta saving Masa cikin wayar shi, se da ya kaisu wani favorite shawarma joint din su kafin ya fita Dan Kira na, Amma yayi ta kira waya Bata shiga ba nayi blocking din shi. Haka yayi na kwana ki biyar a karshe ya yanke hukuncin zuwa Zaria, to ni Kuma a wannan ranar na Gama lecture karfe biyu, na Kuma karba excuse hannun level coord din mu, na koma daki na zauna Saman gado Ina harhada abun da Zan tafi da shi, Nuriyya ta dube ni tace

"Hairan wai har yanzun ba ki Kira Prof ba"

Na Dan yatsina fuska dukda Kiran sunan shi da tayi se da naji kamar ruwan sanyi aka zubawa zuciya ta.

"Ban Kira shi ba, haka kurum!"

Ta tabe Baki tace

"Kinsan Allah da ni matar shi ta kira, idan Kinga ban aure shi ba, to Allah ya kaddara Babu aure tsakanin mu, if not wallahi se na aure shi ayi wadda zaayi"

Na tabe Baki dukda a kasan zuciyata Ina Jin Babu dadi kwarai da gaske, Ina Jin Ina son na aure shi yadda ba Zan ma iya fada ba, Amma Kuma wannan factor din da ya Riga ya bata mini rayuwa shi dinne dai zai hanani auren shi, na goge kwallar da ta zo min na karasa zipping jakar Sannan na sakko bayan na canja Kaya zuwa navy blue din abaya na yane Kai na da veil din, cikin half cover na zura kafafuna sannan na dubi Nuriyya da take ta kallo na nace

"Tafiya Zan Yi fa!"

Tayi min murmushi tace

"Kinyi kyau sosae, muje na rakaki"

Sauran Yan dakin na yiwa sallama sannan muka fice, Muna tafe Muna Hira har muka bar hostel, anan wayata ta fara vibration, dama tana hannu na, Ina dubawa Naga class rep din mu, a take zuciya ta ta bani kodai wani class din zaayi holding Kuma, na dauka muka gaisa yace min naje office din Deen, Deen na nema na,

"Deen Kuma?"

Yace

"Eh Deen!"

Na sauke wayar na dubi Nuriyya tare da marairaice fuska nace

"Kinji wai Deen ke nama na fa"

"To meye abun damuwa, kije kawai"

Ta fada non chalantly, na saki nannauyar ajiyar zuciya nace

"To Kuma ba Zaki raka ni ba"

"Cinye ki zasui, ki ta Abu kamar tashin kauye"

Na bata Rai nace

"Ke Kika sani, se munyi waya"

Ta bani side hug tare da fadin

"Allahu ya kaiku lafiya, ki gaida min Anty "

Na amsa da to da Kuma Amin kafin na wuce office din Deen, Ina tafe Ina lissafo possible reasons da zai sa a Kira ni office din Deen Amma gaba daya na rasa menene dalilin. A haka na karasa na samu messenger din shi Yana ta gyangyadi Saman kujera, na Dan matsa nayi Masa sallama wadda tasa yayi firgigit ya tashi, na fada Masa Deen ne ke nema na. Ya tambaye ni sunana nace

" Hairan Bukar Kaila!"

Yayi murmushi tare da fadin

"Dama kece yallabai yake ta nema?"

Jin hakan yasa gaba na sake faduwa, ko kafin nayi magana yayi knocking softly jikin kofar sannan ya murda ya shiga, baiyi munyi daya ba se gashi ya fito yace min na shiga, a hankali na tura kofar, har lokacin gaba na faduwa yake sosae, a shekara ta uku da nake ciki kafa ta Bata taba takowa office Deen say uku ba, ni bana da matsala da kowa, Kuma hukuncin Allah yasa I've a smooth sailing studies. Muryar da ta saka gaba na daina faduwa a Kuma lokaci daya naji wata nutsuwa ta fara shiga ta

"Thank you Dr. Zubair you have no idea how much happy I'm"

Shi ne abun da na Jiyo cikin maganar shi Yana fada kenan Prof ne yazo shiyasa ake Kira na ikon Allah. Ba tare da na kalle shi ba duk yadda idanuwa na ke son kallon shi saboda I can feel his burning gaze akan shi, na dubi Deen da yake kallo na da murmushi a fuskar shi yace

" So you're Hairan!"

Nace cikin murya me sanyi

"Yes Sir!"

Ya gyada Kai tare da kallon Prof yace

" Tohm Bari na danyi attending to few matters"

Bai amsa shi ba se kawai ji nayi yace

"Cute smile ki zauna Mana"

I can swear naga lips din Deen sunyi curving alamar yaji kenan, kunya ta kama ni, haka na zauna jiki a sanyaye, ya dubi fuskata yace

"Cute smile I'm sorry! Kiyi hakuri Dan Allah"

Na saukar da Kai na kasa amma na kasa magana, wanne fushi Zan cigaba dayi Kuma bayan gashi gani, gashi zaune a gaba na.

"I know ban kyauta Miki ba, na bari DiDi ta zage ki, I'm so sorry for that kiyi hakuri kinji?"

Na gyada Kai na a hankali Ina Jin wasu irin butterflies a cikin ciki na. Yayi murmushi tare da tashi ya dawo kujera mafi kusanci da wadda nake Kai yace

" That's my cute smile, Allahu yayi Miki albarka!"

Nayi murmushi har cikin zuciya ta nake Jin dadin yanayin, how many days ko muryar shi banji ba balle na gan shi bayan zuciya ta tana son shi,

" Have you miss me wannan kwanakin? I've missed you sosae Hairan yadda bazan ma iya fada Miki ba. Just give me chance muyi aure I'm sure shi ne abin da zukatan mu ke so!"

Na dago a hankali na kalle shi, idanun shi da fuskar shi yake pleading di na, Nima Zan so haka, bazan taba so shi din ya kubce min ba Amma yayi min nisa hadin namu bai hadu ba,

"Hairan Mana!"

A hankali nace

" Nima Ina son ka kawai dai..."

Wani irin murmushi ya saki, so beautiful so cute da se da na tsayar da abin da nake fada na zuba Masa idanu na masu haske, da wani irin humor yace

" Da gaske kina so na Hairan! Ya Allah ba Zan taba Dana sani zuwa na Zaria yau ba"

Nayi murmushi a hankali tare da duba lokaci Naga har uku tayi, nayi saurin kallon shi nace

" Kano Zan tafi, time na tafiya"

Ya Mike har lokacin Yana murmushi yace,

"Then we tag along, ni dinam kanon zanje"

Daga Nan ya Kira Deen ya sanar Masa ai tafiya zamuyi, Deen yace

"Hairan ba exams din ku ta kusa ba?"

Nayi saurin kallon shi nace

"Eh Sir Sunday in shaaa Allah Zan dawo"

Yayi Mana fatan alkhairi sannan muka tafi....

Hairan is not free, contact me via WhatsApp 馃憞 馃憞 馃憞.

***

Wanne labarun kike so? Aure ne bakiyi da wuri ba kike ganin kamar ba zakiyi ba? Karanta *FARA YAR SHEHU* Abu Kika rasa kike ganin kamar ba Zaki samu madadin shi ba, then ki nema *UNAISA* Soyayya ce tayi Miki kamu Kuma wani tsaikon ya Hana kiyi aure? To *ZUMA* ya kamata ki nema, A cikin *BANI DA LAIFI* Zaki gane cuta ba mutuwa bace ba, Kuma rabon kwadon ko ya hau sama se ya sakko, kiba ce da ke ko ke siririya ce da mutane suke shaming din ki har Kika fara samun mental break down ki sani *BINTUN BATUUL* Na jiran ki. Auren dole akai Miki, ko Kuma kina fama da maraici ne? Kuma Baki karanta *AFIYYA* ba jiran me kike Baki karanta *TSINTUWA* , *HIKMA* , *ME RABO KA DAUKA* , *UWARGIDAN BAHAUSHE* ba?

漏Oum A'eesh

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.