Free chapter 路 Read without an account

007

by A'isha kwalam Hassan 路 HAIRAN

HAIRAN 馃グ 鈾ワ笍 馃槶 馃挃

No.7

Ayshatuuu

*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her 馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.

***

Contact her on WhatsApp馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

Ina fatan ba tunani kuke tafiyar tamu silent drive bace ba, ko daya tafiya muke yi cikin wani irin shauki da so,  na yadda na Kuma amince tabbas ina son Prof da gaske na Kuma san tabbas shi din mahadin rayuwa ta ne, sede a komai ance ka dinga yin check and balance dan kaga yadda Abubuwan suke, to ni a waje na inaga haka kawai Zan zo na tafi ba tare da naji me ake ji na mallakar abin da nake so ba.

"Hairan!"

Ya fada a sanyaye, na dago na kalle shi nace

" Naam!"

Yace

"Can I ask you?"

Zuciya ta se da ta motsa amma hakan nace

"Sure!"

Yayi murmushin Jin Dadi yace

"Me yasa Kika ce na rabu Dake? Is there any reason behind that!"

Na Dan lumshe idanu na, Ina auna abun da ya kamata na fada masa, me zance Masa da zai yadda lokaci daya ba tare da Muna ta Jan maganar ba,

"Tell me kinji? Kin ganni ko Hairan I've never love a person kamar yadda nake son ki wallahi, Kar kice ko Ina cika Miki Baki, no it should be put like dadin Baki, seriously cute smile ba dadin Baki nake Miki ba, I meant everything I said, like bazan ma iya describing yadda nake ji akan ki ba, the feeling is immense Hairan"

Ya fada Yana dan dukan steerer wheel, irin so yake ya stressing abin da ya fada, zuciya ta ta sake haskawa sede still I can't do it

"Bani da lafiya!"

Na fada a hankali, nayi mamaki ma da yaji, saboda abun yazo kamar whisper, yace

" Me yake damun ki? Rashin lafiya ai Zaki warke cute smile, Dan Allah ki Bari mana!"

Nayi shiru tare da lumshe idanu na ganin Bai bawa maganar muhimmanci ba, ba bacci nake ba Amma zuciya ta hutawa take so tayi, I need to close his chapter soooooon... Bai Kara magana ba tunanin shi nayi bacci, Kuma a haka baccin ya tafi Dani. Dan da maghrib muka shiga Kano, ya danyi tapping gefen seat Dina da ya saka nayi firgigit na tashi tare da yin hamma na rufe Baki na sannan na dube shi a kunyace, Yana murmushi tare da kallo na lovely yace

"Kina ta snoring!"

Na kalalo idanu na waje nace

"Dan Allah da gaske?"

Yayi dariya yace

"Wasa nake Miki, your sleep was so silent har na fara wondering are you still breathing"

Nayi murmushi Ina sauke ajiyar zuciya, da nayi minshari da bansan irin kunyar da zanji ba, yace

" Wacce unguwar Zan kaiki?"

Gyara Zama nayi tare da Kara gyara veil din fuskata na fara Masa kwatance, Muna tafe within mintina talatin se gashi mun karasa kofar gidan mu, ya dube ni kamar yadda nake duban shi kafin yayi magana nace

"Nagode sosae Allah ya saka da alkhairi, a gaida min Hanifa da A'isha!"

Yace

"Ba Zan shigo na gaisa da Mama ba"

Na kalle shi na girgiza kai tare da saurin bude kofar na fita, yayi ta kallo na, a lokaci daya Naga yanayin ya canja, to ya zanyi? Ni ban shirya ba bana ma son wani ya ganmu tare, jaka ta na dauka na Kara duban shi har lokacin kallo na yake wani iri kamar irin disappointment dinnan, Kai na na kawar nace

" Thank you!"

Ban jira amsar shi ba na wuce ciki da sauri saboda nasan ban kyauta ba, bana son waves din son shi su shige ni da yawa har nayi wani abun da zai Kara bashi karfin gwiwa, Baba Dan fillo yayi min sannu da zuwa sannan ya bude min kofa na shiga, kafin na tsaya muka gaisa, na daga kafa ta kenan Zan shiga cikin naji muryar Abba Yana yiwa Usman magana, na tsaya har ya karaso, na tsugunna har kasa nace

" Abba Ina wuni?"

Lafiya kawai yace min ya wuce, Usman ya kalle ni tare da manne min idanu daya ya bi bayan Abba, shi kuwa Najib ko kallo na baiyi ba balle yayi min magana, na saki ajiyar zuciya na mike na wuce can bangaren mu, mukuli na saka na bude kofar sannan na shiga Baki na dauke da sallama, Babu kowa cikin parlon, a hankali nayi inhaling wani kamshi da yake nema yasa bacci ya dauke ni, na saki ajiyar zuciya na shiga ciki, daki na na wuce na shiga bandaki nayi alwala nazo nayi sallah sannan na cire Kaya na na koma Dan yin wanka, Ina fitowa na samu Anty zaune bakin gado na, tana zaune all glammed like always, na karasa inda take na rungume ta nace

" Anty na dawo"

Ta shafa baya na tace

"Sannu da hanya, ai naji shigowar ki sallah nake!"

Nayi murmushi nace

" Kin canja turaren wuta ne, yayi kamshi da yawa!"

Tana murmushi tace

" Na canja, ai tunda na samu turaren wutar Scents by Fayzarl magana ta kare, halut ne, multipurpose room spray, yerwa dambu kada ma Kiji kajiji dinta, they're abin da bazan ma iya fada ba"

Nayi murmushi Ina karasawa gaban dressing mirror, wata khumra na gani kafin nayi magana Anty tace

" I bought that also for you, Zan Baki IG handle din ta da Kuma Whatsapp link se ki karba abin da kike so"

Nayi murmushi tare da juyowa na kalle ta nace

" Anty nagode sosae, Allah ya saka Miki da mafificin alkhairi, Allah ya haska rayuwar ki kamar yadda Kikai ma tawa"

Tayi murmushi tare da mikewa tace idan na Gama na same ta a parlor, na bude khumra wani irin sassanyan, dadddan kamshi ya daki hanci na, Babu shirin na saki inhaling kamshi, OMG wannan Fayzarl ba karamin turare ta iya ba, na shafe jiki na da ita sannan na shirya cikin simple gown, ban daura dankwali ba hakan yasa gashi na dogo baki sidik ya sauka har bayana, zaku ce ya akai nake da gashi ko? Kilan ban gaya muku cewar uwar da ta haife ni is a Lebanese wato Yar Lebanon ce!

Waya ta na dauka na Kira Nuriyya kamar jira take ta dauka tare da fadin

"Har kinje?"

Nace

"Naje har nayi sallah na Kuma Yi wanka!"

Tace

"Ma shaaa Allah, idan Kika bude jakar ki na saka Miki garin danwake na ISLAH FOODS, ki bawa Anty inji ni, ke Kuma Allah ya huta gajiya, we'll talk gobe"

Kafin nayi Mata godiya ta kashe wayar nayi murmushi Ina Jin Sonta a Raina, a hankali nayi dialing number Prof a calculation di na yanzun ya Isa hotel din da zaiyi lodging, bugu daya ya katse ya Kira ni, cikin nutsuwa nace

" Kaje lafiya?"

A hankali yace

" I'm not fine Hairan"

Gaba na ya Fadi, me ya same shi bayan yanzun nan muka rabu, nace

"Me ya faru?"

Yace

"Hairan ki huta zamuyi maganar anjima!"

Na amsa da to a hankali sannan na kashe wayar tare da fita parlor, Anty na zaune tana hada salad, na zauna gefen ta tare da kwantar da kaina a kafadar ta nace

"Anty!"

Tace

"Hairan mage, uwar son jiki"

Nayi murmushi muka fara Hira, har ta gama sannan muka zauna cin abinci, lokaci zuwa lokaci Ina yin tari Wanda na kwana biyu Ina Yi, se da muka gama na kwashe kayan zuwa kitchen sannan na dawo bayan munyi sallar ishai Abba ya shigo, na Kara gaishe shi Amma wannan Karan ko amsawa baiyi ba, haka na wuce daki na Dan na Basu waje, abun da yake min bana Jin Dadi Amma ko Sau daya ban taba ganin laifi shi ba, Wanda ma ka hada jini da su wofantar da kai sukai balle shi da har ya bani shelter ya Kuma bani abinci, na goge kwallar da ta kawo min idanu na na kwanta akan gado tare da lumshe idanu na, can Kuma na mike na dakko sabon Hawii na wajen scents by Fayzarl na fara kunawa, subhannallah! Shi ne kawai abin da zance, Allahu ya karawa kamshi kamshi!

"Hadiza wannan yarinyar wani ya kawo ta a karuwar mota, bana son shashanci, bazan lamunci wannan ya aje ta ba wannan ya dauke ta!"

Anty Dake sauraren Abba tace

"Kayi hakuri, zanyi magana da ita hakan ba zai Kara faruwa ba!"

Ya danyi tsaki tare da mikewa yace

"Me ma ta dawo Yi gida?"

Anty tayi murmushi tace

"Asibiti zamu je gobe in shaaa Allah! Na fada maka se de idan ka manta"

Bai ce komai ba yayi ficewar shi, bayan shi tabi se da ya fita sannan ta fara kokarin rufe ko ina, se taji soft knock , ta dawo ta bude Usman ya shigo fuskar shi dauke da murmushi yace

"Anty Ina Hairan?"

Ta Dan Harare shi da wasa tace

" Ban sani ba, yau duk ban ganka ba shi ne zaka zo kace Ina Hairan to tayi bacci"

Ya Dan Bata Rai yace

"Ai shikenan"

Daga haka ya Mika Mata Leda Dake hannun shi yace

" Ki saka Mata a fridge se tayi breakfast da shi"

Anty ta girgiza Kai tace

"A'a Usman, karka damu nagode"

Ya sake Bata Rai tare da shigewa kitchen, ya aje ledar sannan ya fito Yana murmushi yace

"To Anty Allah ya bamu alkhairi, idan ta farka cikin dare kice Ina gaishe ta"

Daga haka yayi saurin ficewa ta koma ta rufe kofar tana Jin Babu dadi cikin zuciyar ta. A daki ta same ni bacci har ya Fara fuzga ta, nayi saurin tashi na zauna tare daukar hula na rufe bakin gashi na nace

"Anty kin shigo?"

Ta dube ni a nutse kafin tace

"Hairan Ina glasses din ki, ban gan shi a idanun ki ba?"

Na Dan sunkuyar da Kai na to ba Zan iya mata karya ba nace

" Na barshi a school "

Wata muguwar harara tayi min tace

" Kin kyauta ai, sannan Hairan ba Kya Shan drugs din ki wallahi, kina Jin tarin da kike Yi ko?"

Kamar yaji abin da aka fada ya Kara tahowa, na kusa minti biyu Ina Yi kafin yayi sauki nace

"Anty Ina Sha!"

Ta bini da wani kallo wanda duk lokacin da nayi karya tana yimin wannan kallon tana fada min she's seeing through me

"Anty na gaji da Sha, kullum ni a Shan magani Anty na gaji"

Ganin na fara kuka, se tayi saurin matsowa kusa da ni tare da rungume ni tace

"A'a Hairan Dear, bansan yarinya ta da Karaya ba, bansan yarinya ta da taurin Kai ba Hairan, menene matsalar ki? Nasan duk lokacin da Kika ki Shan magani Kika daina saka glasses din ki to wani abun na damun ki. Open up nasan akwai damuwa!"

Duk duniya bayan Allah da manzon shi Anty ce kawai wadda nake da ita, Babu wani Abu na jini tsakanin mu Amma ita ce uwata ubana da komai nawa, so duk zurfin ciki na kalaman Anty kawai zanji na bude Baki, Ina kuka a hankali nace

"Anty Ina son shi, Anty Ina son shi sosae Anty bana son na rabu da shi, Anty ya akai kaddara ta tazo a haka..."

"Shhhhhh..."

Ta fada tana saka fingers din ta Saman lebe na tace

"Kada ki Kara fada, kada ki sake questioning Allah dalilin wannan jarabawar ban koya Miki haka ba Hairan...."

To be continued...

HAIRAN is not free, contact me via WhatsApp 馃憞 馃憞 馃憞

***

Ko kunsan page uku kawai ya rage mu gama free pages, to ya zaayi kusan yadda zata kare tsakanin Ladidi da Prof? Prof da Hairan da sauran questions da suke ringing cikin Kan ku. Hairan N500 ne kacal.

Wanne labarun kike so? Aure ne bakiyi da wuri ba kike ganin kamar ba zakiyi ba? Karanta *FARA YAR SHEHU* Abu Kika rasa kike ganin kamar ba Zaki samu madadin shi ba, then ki nema *UNAISA* Soyayya ce tayi Miki kamu Kuma wani tsaikon ya Hana kiyi aure? To *ZUMA* ya kamata ki nema, A cikin *BANI DA LAIFI* Zaki gane cuta ba mutuwa bace ba, Kuma rabon kwadon ko ya hau sama se ya sakko, kiba ce da ke ko ke siririya ce da mutane suke shaming din ki har Kika fara samun mental break down ki sani *BINTUN BATUUL* Na jiran ki. Auren dole akai Miki, ko Kuma kina fama da maraici ne? Kuma Baki karanta *AFIYYA* ba jiran me kike Baki karanta *TSINTUWA* , *HIKMA* , *ME RABO KA DAUKA* , *UWARGIDAN BAHAUSHE* ba?

Taku ta kullum

漏 Oum A'eesh

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol