Free chapter 路 Read without an account

008

by A'isha kwalam Hassan 路 HAIRAN

HAIRAN 馃グ鈾ワ笍馃槶馃挃

No. 8

Ayshatuuu

*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.

***

Contact her on WhatsApp馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama  and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her 馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

Na gyada Kai na dukda kukan yaki tafiya, tamkar yau bude min zuciya ta ake ana kwashe abinda yake ciki, I just want to feel that lightness da kake ji idan ka fadawa wani abun da yake damun ka, ta sassauta rukon da tayi wa hannu na tace

" Tell me who's he? Ko shi ne wanda Abban su Usman yace ya kawo ki a mota!"

Na gyada Kai nace

" I met him kin tuna lokacin da muka je Kaduna conference ko? To anan muka hadu..."

"Me yasa Baki gaya min ba Hairan, I thought ni Dake kawaye ne that are meant to share everything together!"

Na danyi kasa da Kai nace

"Kiyi hakuri Anty!"

Ta gyada Kan ta tace

"So tell kin fada Masa condition dinki?"

A take wasu hawayen Suka sake tunkudowa daga idanu na, na kasa magana saboda nasan laifi na ne, duk halin da nake ciki nasan laifi na ne. Ba wai jiya akai diagnosing di na ba, I've been diagnosed for over 15years to me ya dauke min hankali na fara son shi, wannan son ba so ne wanda ya kasance na yarinya da mukai da Yaya Usman ba, ba Kuma wadda nayi da Nu'uman ba.

"Baki fada Masa ba ko?to saboda..."

Kawai tayi shiru saboda yadda nake kuka me cin Rai, nace

"Anty bansan ya zanyi ba.."

Wannan Daren a guri na ta kwana Bata sake ta tafi dakin ta ba, cikin dare inata juyi saboda gaba daya wani irin ciwon Kai nake ga tari ya matsanta ma like every other night, wajen uku Anty ta mike tace

"Hairan tashi kiyi sallah ki nema zabin Allah kinji?"

A hankali na tashi na wuce nayi nayi tsarki sannan na daura alwala na fito, na Jima Saman dadduma Ina sallah da addu'oi nasan su kadai ne abin da zasu saka naji sanyi cikin Rai na. Guess what I felt a lot of comfort Dan da kyar nayi sallar asuba na nade a gado bacci ya dauke ni, dalilin da yasa bamu tafi da wuri ba kenan. Wajen takwas ta tashe ni nayi wanka a gaggauce na shirya cikin skirt da Riga na lace as usual daga wajen omni360 collection, Ina Kara fada muku kuje ku duba IG handle din ta kuga ikon Allah, wani irin kyau nayi dukda fuskata ta kumbura plus na danyi Yar fuska wato na rame, wani kamshi kayan suke saboda turara su da sandal balls din scent by Fayzarl da Anty tayi, na dauki necessary sannan na tafi parlor, nan na samu Abba da Anty suna magana, kamar na koma to mun riga da mun hada idanu da shi, hakan yasa na tsugunna har kasa na gaishe shi kamar kullum, wannan Karan ko amsawa baiyi ba, Anty tayi min alamar na tashi na tafi, na kuwa mike jiki a sanyaye na wuce kitchen na fara kokarin hada tea, se Naga har ta riga da ta dama kunu ma, cikin mug na zuba, na zauna cikin kankanin lokaci na shanye tunda dama kadan na zuba dukda dadin da yayi gardin geron.

Babu jimawa ta shigo tana kallon na da kulawa tace

"Mu tafi ko?"

Na mike nace

" Anty kunun yayi Dadi"

Tayi murmushi tace

"Garin kunun ISLAH FOODS kenan, ai product din ta duniya ne!"

Da mamaki nace

"Kai Anty kema kin Santa?"

Tayi dariya kawai tana Mika min keys din da ta rufe gidan mu da shi, motar ta kirar vibe muka shiga, seda muka gama addua kafin ta fara driving cikin nutsuwa, Muna barin gidan bayan Usman ya tsayar da ita lokacin da aka bude Mana gate ya gaishe ta Nima na gaishe shi a hankali, da dukkan damuwa yace

"Hey what happened to your face? It's swollen"

Na danyi murmushin yake nace

"Nothing!"

Yace

"Ok, idan Kun dawo Zan shigo"

Na gyada Kai na sannan ya koma bangaren Anty yayi Mata Allah ya kiyaye hanya kafin Anty ta fara tambaya ta zancen Prof

"Kawai yace min Yana son zai aure ni, he has been putting pressure lately, shiyasa duk hankali na ya tashi, bansan me yasa na kula shi har ya Fara so na ba"

Tayi murmushi tace

"Haka so yake Hairan baya shawara, it make sure it intoxicate you har Kai losing sanity dinka.  Muna yin Abubuwan Wanda idan ba Dan so ba bana tunanin zamu Yi wadannan Abubuwan, shiyasa nake son idan mun dawo find time ki Kira shi ki fada Masa komai a game Dake, it's left to him to..."

"Ba Zan iya ba Anty gaskiya!"

Na fada Ina kawar da Kai na gefe, Anty tayi dariya tace

"To ya zakiyi da son shi?"

Nace

"Se na hakura!"

Wanda ni Kai na nasan karya kawai nake, Bata Kara ce mini komai ba har muka bar kano, se da muka je Dutse sannan ta bani motar na cigaba da tukawa zuwa asibitin da nake zuwa. Bayan mun shiga muka gaggaisa da ma'aikatan suna Kuma tambaya ta karatu, na amsa da alhamdulillah sannan na zauna aka dakko file di na, biometric nayi sannan aka Yi weighing di na, tun daga weight din aka fara tambaya ta me ya ke faruwa dani nayi losing wannan weight haka a jiki na, Ina zance bana Shan magani, ko da naje wajen clinicians din ko kafin ma nayi magana Anty tace musu Ina tari, so a take aka tura ni TB screening, Wanda Yana fitowa se ga ni positive, aka Kara maida ni dakin masu tari na fara karbar magani kafin na dawo aka bani ART dina, har zamu tafi se clinician din ta yima Anty magana, na koma reception na zauna Ina answering call din Prof Dake fada min bashi da lafiya, Yana ganin ma kamar zai koma Abuja, se naji babu dadi sosae da sosae nace

"To kaje asibiti Mana!"

Ya danyi tsaki kadan yace

"Wanne asibiti zanje cute smile bayan maganin na hannun ki"

Na Dan bude idanu na, I'm sure da yana gaba na da zaiyi murmushi ko ma yayi chuckling, nace

"Ni Kuma?"

"Ba kin Hana na aure ki ba, kinki ki barni nazo na gaida Baba, wai Hairan what's stopping you ne?"

Na Dan Bata Rai saboda ni bana son maganar nan gaba daya, yace

"How much do you want me to tell you cewar wallahi Ina son ki, Kuma in shaaa Allah ba zaki Dana sanin aure na ba, I'll be your everything Hairan Dear"

Nayi shiru Ina Jin wani irin farin ciki Yana shiga zuciya ta, I love this Man to the square of infinity, Anya Zan zauna cikin zaman lafiya a rayuwa ta idan har ban aure shi ba, gosh I so much love him.

"Ko kina ganin Zan Bari DiDi ta zage ki ko tayi maki wani Abu? Wallahi bazan Bari ba a cutar Dake, ba Zan ma fara ba idan nasan bazan iya ba Hairan. Ki bar DiDi it's just empty threat Babu abin da zata iya maki, I assure you darling"

Se yau ma naji wai sunan ta DiDi, I wondered ko me DiDi ke nufi, ko tsabar soyayya ce yake fada mata hakan, wannan dai damuwar su ce, amma ko Sau daya ban taba barin zagin da matar shi tayi min ya dameni ba, saboda shi nake so Kuma inada yakinin he'll do everything in his power to protect me.

"Idan naje gida Zan Kira ka"

Shi ne kawai abin da nace Masa, se yay min sallama na kashe wayar tare da sakin ajiyar zuciya Ina Kuma Jin Babu dadi cikin zuciya ta, wannan abun na rasa yadda zanyi da tunanin all possibilities, na fada Masa bani da lafiya amma ya kasa fahimtar heaviness na cutar da nake dauke da ita, I really can't tell him da Baki na wallahi.

A cikin office din clinicians din Anty na zaune gaban Anty Rabi'a

"Maman Hairan Ina son Kiran ki tun sati biyu baya amma Ina ta mantawa"

Anty tayi murmushi tace

"Ai haka ne dama, ko wani abun ya faru ne?"

Tayi murmushi tace

"Akwai wani client din mu da yake ta yimin maganar yana son mata, Kuma criteria din da ya fada irin na Hairan ne, shi ne nace Bari nayi Miki magana Muji idan Babu maganar wani a kasa"

Anty cikin Jin Dadi tace

"Ma shaaa Allah! Naji dadi sosae Amma Hairan is currently seeing someone, dukda taki fitowa ta fada min komai na fahimci tana sok shi, kawai ta kasa fada Masa status din ta"

Anty Rabi'a tace

"Ki bita a hankali, kinsan fa se a hankali, to yanzun yadda zaayi a gama maganar wancan idan Hairan din rabon shi se kiga Abu yayi clicking"

"Aikuwa dai wallahi! Allah ya zaba Mana Mafi alkhairi"

Daga haka suka yiwa juna sallama sannan ta fito muka nufi pharmacy na karba ART, sannan muka dauki hanyar komawa Kano, lokacin da muka zo hotoro Anty ta dube ni tace

" Ko na kaiki ki gaida kawun ki?"

Nayi saurin girgiza kai nace

"A'a na gaji ni dai"

Tayi murmushi kawai ba tace komai ba, Muna zuwa gida na nufi kitchen saboda yunwar da nake ji, fridge na bude Dan samun abin da Zan Dan ci kafin Anty tayi Mana girki, farar Leda na gani da foil paper a ciki, nayi saurin dakkowa Naga grilled fish ne a ciki anyi topping da onion sauce, da wuri na kunna microwave na zura a ciki, Yana Yi na juye a plate na dakko ruwa na wuce parlor, Anty me kokarin har tayi wanka ni kuwa uwar ci bazan iya ba. Kallo na tayi tace

"Sha magani kafin ki ci abincin!"

Na kuwa karba na Sha sannan nace

"Anty mu ci!"

Tayi dariya tace

"Usman ya kawo Miki jiya da daddare"

Nace

"Wai Yaya Usman?"

Tsam na mike nace

"Ba zanci ba, bansan shi ya siyo ba"

Da kyar ta lallaba ni naci wannan kifin!

To be continued...

Hairan is not free, contact me via WhatsApp 馃憞馃憞馃憞

***

Wanne labarun kike so? Aure ne bakiyi da wuri ba kike ganin kamar ba zakiyi ba? Karanta *FARA YAR SHEHU* Abu Kika rasa kike ganin kamar ba Zaki samu madadin shi ba, then ki nema *UNAISA* Soyayya ce tayi Miki kamu Kuma wani tsaikon ya Hana kiyi aure? To *ZUMA* ya kamata ki nema, A cikin *BANI DA LAIFI* Zaki gane cuta ba mutuwa bace ba, Kuma rabon kwadon ko ya hau sama se ya sakko, kiba ce da ke ko ke siririya ce da mutane suke shaming din ki har Kika fara samun mental break down ki sani *BINTUN BATUUL* Na jiran ki. Auren dole akai Miki, ko Kuma kina fama da maraici ne? Kuma Baki karanta *AFIYYA* ba jiran me kike Baki karanta *TSINTUWA* , *HIKMA* , *ME RABO KA DAUKA* , *UWARGIDAN BAHAUSHE* ba?

漏Oum A'eesh

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol