Free chapter 路 Read without an account

009

by A'isha kwalam Hassan 路 HAIRAN

HAIRAN 馃グ鈾ワ笍馃槶馃挃

No. 9

Ayshatuuu

*ISLAH FOODS!* Har yanzun surfe kike idan zakiyi kunu? Har yanzun wahala kike Sha idan zakiyi kunun Aya! Ya kike Yi idan kina marmarin tuwon dawa Dana alkama  and you have to undergo processes kafin kiyi? Ina masu Yara da zasu fara feeding din su da semi solid, ba dai har yanzun kashe kudi kuke a siyan cereals na gwangwani ba? To kuzo na Baku labarin *ISLAH FOODS* , na maimaita *ISLAH FOODS* wadda ta kawo Mana wannan garin kunun, garin tuwo na dawa da na alkama, garin kunun Aya, pap powder na Koko, ga custard powder processed and fortified cereal na Yara a saukake, daga ziplock se tukunya, a tsaftace Babu ruwanki da surfe da Kuma nika. Contact her 馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

*Turare_by_ruky* I repeat *turare_by_ruky* are you a fan turaren wuta? Luxurious turare? Ko Kuma irin royalty scent dinnan kike so? Oils ne da khumra kike bukata? Then wannan brand din Kar ya wuce ki, turare ne da duk Wanda ya jishi se ya kalle ki saboda heavenly scent din shi, ga shi pocket friendly, lemme tell you ita kadai ce me turaren da Naga tana koyar da yadda zaki turare a gida, body scrubs and more, abinda muke cewa *DIY* Kuma duka free. Your's is just to follow her on TikTok ku bani labari.

***

Contact her on WhatsApp馃憞馃徏馃憞馃徏馃憞馃徏

***

Haihuwar Ibrahim ba karamin tada hankalin Matan Malam Muntari sukai ba, barin ma uwargida Biba wadda tafi daukar abin da zafi, Dan Yana jariri ko arbain baayi ba ta Kona shi da ruwan zafi, kunsan dai a aladar hausawa uwargida ke yiwa jariri sabiwar haihuwa wanka, a ranar da abun ya faru sun Riga sun shirya da hauwaila wadda ta kwasawa Halima ruwan wanka, suka shiga tare Dan Taya ta wanka, anan ita Kuma Biba ta debo ruwa Dan tayi Masa wanka Babu Wanda yasan me ya faru, ta sirka ruwan Bata sirka ba se zuwa akai jikin jinjiri ya salube, da addua da taimako da magnunguna aka samu Ibrahim ya warke, tashin hankali Malam Muntari har yafi ita kanta Halima shigar shi, warkewar shi da Kuma rashin nuna tabo da kunar tayi ba karamin sake harzuka Biba da Huwaila hakan yayi ba, Suka cigaba da bin hanyar da zasu ga sun salwantar da Ibrahim, kamar yadda suke a tsaye haka Shima malam Muntari yake a tsaye da addu'oin shi, a shekara biyar da haihuwar Ibrahim ya sauke izu goma, wata irin baiwa Allah ya bashi ta kwakwalwar, Yana da ilimi, Yana da daukar abu. Malam zance daya biyu to fa na ukun na Ibrahim ne, wannan yasa Matan duka dinga Kai Masa hari, ganin Abu yaki ci yaki cinyewa se malam ya dauki Ibrahim ya kaishi wata tsangaya a Zaria, ko Babu komai yayi Nisa dasu, he'll be safe, dama kafin lokacin Ibrahim na tayiwa Malam nacin ya saka shi makarantar Boko irin ta yaran dagaci, malam ya tabbatar Masa zai saka shi Amma SE yayi saukar qurani. Zuwan shi Zaria malam na zuwa ganin shi duk bayan wata uku, zaiyi masa soyayya sosae ya tafi Masa da ita, kowa a wannan makarantar yasan gatan da Ibrahim yake da shi da yadda mahaifin shi ya damu da shi labari ne da kowa ke fada, shekarun suna tafiya har uku suka hau akan shekarun shi, a lokacin baifi izu goma ya rage ya gama haddace qurani wadda zai iya kawo hadda kamar dazun aka daura Masa, hakan yasa malam ke alfahari da shi ka zalika malam Muntari ma. To anan ne fa yaga Yana kwadayin shiga makarantar Boko, saboda Shima Yana son yayi karatun yaji ya iya turanci, a hakan yake zuwa makaranta.

Wannan shi ne dalilin korar Ibrahim da malam yayi daga makarantar shi ba tare da ya jira mahaifin shi yazo ba, Ibrahim ya cigaba da zuwa makarantar boko, da rana idan an tashi se ya tafi neman kudi inda yake gyaran takalmi ya samu na kashewa da cin abinci, da yamma yaje wata makarantar allo inda ya cigaba da karatun da asali ya kawo shi Zaria, da daddarr cikin primary din su yake zuwa yake kwana. A haka watanni Suka zo suka shude Babu labari zuwan Malam Muntari Wanda hakan ya bawa Ibrahim mamaki sosae saboda Yana yawan zuwa wajen abokan shi da daddare anan yake samun labarai. A takaice dai Malam Bai Kara zuwa Zaria ba, gashi Ibrahim da kyar yake iya tuna sunan garin su, Ina yasan hanyar da zai bi ya koma kiyawa, wasu ma Basu taba Jin sunan garin ba. Cikar shi shekara goma ya sauke qurani gaba daya, ya dawo taihi, a bangaren makarantar Boko kuwa su kansu mamakin kwakwalwar Ibrahim suke. Sau wajen biyar Malam idi wato malamin su na makarantar Boko Yana ganin shi da sassafe ya fito daga daya daga cikin toilet din makarantar yayi wanka. Malam dai ranar ya Kira shi ya tambaye shi me yasa yake kwana anan, baiyi nauyin Baki kuwa ya fada masa duk abinda ya faru da shi, ko da aka tashi Malam idi ya Kira Ibrahim ya tafi da shi gidan shi ya kaiwa amaryar shi me suna Zainabou, gaba daya auren baifi shekara uku ba, se a lokacin take da cikin fari Wanda a kalla ya kai watanni biyar, ya kawo mata Ibrahim ya fada mata ya samo Mata yaro Wanda yake so ta rike shi kamar Dan da ta Haifa, saboda boyayya irin ta ta Bata tambaya daga Ina ba, se kaishi dakin zaure da tayi kamar yadda Malam idi yace. Baba kamar yadda Ibrahim yake Kiran malam Idi ya zamewa Ibrahim uba ita Kuma Yaya ta zame Masa uwa haka Shima ya Zama da a wajen su. Haihuwar farko ta Haifa diya mace aka saka Mata Hafsatu, kafin ta shekara biyu ta sake haihuwar mace aka saka Mata Maimuna kasancewar sunan mahaifiyar Malam idi ne se Yaya take Kiran ta Ladidi, Ladidi tun tana yarinya ta kasance mafadaciya ce, baa taba Mata ta kyale ba Amma dukda wannan halin nata suna shiru da Ibrahim, kyakyawar gaske ce Kuma ga hazaka, haka Yaya ta cigaba d haifar Yara Mata har biyar.

Ibrahim Bai je gida ba se da ya Gama secondary TAs sannan yayi sallama da su Yaya ya tafi kiyawa, ya Sha wahala kafin ma ya gane garin balle gidan su, da tambaya da komai aka Kai shi, sede wani hukuncin Allah Halima ce kadai ta rage a gidan dukka sun rasu daga malam, Huwaila har Biba. Farin cikin da Halima ta shiga ba abun mu zauna fada bane ba, ta sanar Masa ai malam jinya yayi me tsawo kusan shekara hudu kafin Kuma Allah yayi Masa cikawa, Ibrahim haka ya bawa mahaifiyar shi labarun Abubuwan da yayi a can Zaria da yadda Malam idi ya zame Masa uba. A take Halima tace Masa ai Zama Bai gan shi ba Dan kuwa dole ya koma Dan itama sauduyya zata tafi, aikuwa Bai tafi ba se da yaga tafiyar ta kafin ya koma Zaria, Yana zuwa ya samu labarun fitowar waec din su Kuma ya lashe komai har ma an dauki nauyin karatun shi zuwa kasashen turawa. Tafiyar shi Ladidi shekarar ta goma, acan yayi karatun shi a fannin likita in da ya Zama kwararre Kuma cikakken likita,bayan ya gama ya dawo Nigeria wato Zaria ya Fara aiki a ABUTH. Shekarar shi daya da Fara aiki ya gyara gidan da suke ciki a shekara ta biyu lokacin Ladidi tana da shekara Sha takwas Malam idi yayi wa Ibrahim tayin auren ta, Babu ja ya amince tare da komawa kiyawa ya sanar da kawunnan shi, Basu ja ba suka zo tambaya cikin girma kuwa da mutunta juna aka bashi aure, ya kukuta yayi komai na alada sannan ya Gina gidan shi anan cikin Zaria, Babu jimawa akai aure Ladidi ta tare gidan Ibrahim, a hankali zamn su Yana tafiya kowannen su na kokarin kyautatawa Dan uwana shi, musamman Ibrahim da yake ganin dole ne Zama da DiDi ko Dan abin da iyayen ta sukai Masa.

DiDi ta kasance mace me dadin Zama a wajen Ibrahim, ta kasance mace wadda yake son ta Kuma yake ganin he can go to the moon Dan ya kyautata mata, duk wani Abu da ya samu to na Ladidi ne, yadda take haduwa da mutane da yadda Kuma ta kasance mace me son kwaliyya yasa ta Zama mace me hangen na saka da ita, kusan duk abin da ya samu akanta yake karewa da kyar yake kukutawa yayi wa iyayen ta wani lokacin yayiwa Yan kiyawa alkhairi. Seda sukai shekara hudu sannan ta Haifa Hanan me sunan Halima wadda itama acan saudiyya ta rasu ya rage ba shi da kowa se su Yaya dai Wanda yake musu iyakar iyawar shi, abun da yake musu ko su Suka haife shi karshen abin da zai musu kenan, shekara uku ta zagayo ya tafi wata kasar yin wani karatun kafin ya dawo an Haifa Hanifa an saka Mata Zainabou sunan Yaya. Lokacin da ya dawo yayi joining irin non profit organization ya Fara aiki, Allah ya Buda Masa har karshe ya tattare su zuwa Abuja, Ladidi fa miji yayi kudi, Banda fankama da dagawa Babu abin da take Yan gidan su ma ba wani sakar musu take ba, a takaice Bata son kowa ya rabe ta itada yaranta da mijin ta, suna can Abuja tamu馃槅

***

A karo na Babu adadi ya cigaba da Kiran wayar Hairan amma Abu daya ake fada Masa call din shi is forwarded, to tambayar shi ne Ina akai forwarding calls din na shi? Zuwa Ina? Wai Anya kuwa yarinyar nan Hairan tana Jin tausayin shi? Shifa tun da ya hadu da ita a Kaduna wani conference da Bai masan yadda akai aka gayyace shi ba, tunda conference din nurses ne, lokacin da ya shirya cikin wani maroon din yadi me taushin gaske, Babu aiki a gaban rigar, it was plain, ya daura silver agogo a hannun shi sannan ya kafa hular shi wato sharna wadda akace idan baka saka ba to mahaifin ka ya saka wannan shi ne taken ta. Takalman shin bakaken half covered ya saka sannan ya hada jakar shi TAs sannan ya fito inda DiDi ke zaune ita da Hanan wadda ta dawo hutu daga school Dan ita boarding takeyi unlike Hanifa Dake day school. Hanan na rike da waya tana nunawa mahaifiyar ta page din Scents by Fayzarl a IG Dan tana fadawa mahaifiyar tata turaren wutar da take amfani da su dukka basu da heavenly scent din turaren wutar Scents by Fayzarl, tace

"Haba Mama wai kin taba ganin cotton incense? Yerwa dambu? Kin taba ganin colored incense kuwa? To wallahi duka Scents by Fayzarl tana siyarwa!"

DiDi Dake sauraran yarinyar tata tace

"Yanzun ki Bari ya gama bamu kudin kayan wajen Omni360 collection tukunna!"

Fitowar shi yasa Hanan fadin

"Abbu kayi kyau!"

Yayi murmushin Jin Dadi yace

"To nagode uwata, Ina su Hanifa?"

Hanan tace

"Suna daki, Bari na Kira su"

Ya gyada Kan shi Yana bin DiDi da kallo kamar yadda take kallon shi har ya karasa inda take zaune, ya zauna yace

" KD Zan wuce yanzun an gayyace ni wani conference!"

Ta Dan langwabar da Kai tace

"Kayi kyau d yawa har bana son ka fita"

Yayi murmushin Jin Dadi yace

"Yau kishin ya motsa ne?"

Ta danyi murmushi tana wani yauki tace

"Akwai Kaya Hanan ta zaba daga wajen omni360 collection, ka bada kudin"

Ya danyi shiru saboda bayan son titsiye, ita Kuma halin ta ne, saboda a zauna lafiya like always yace ta Masa forwarding rough estimate din zai tura daga haka ya Mike Dan fita se ga Hanifa da A'isha sun fito, a tare suka rungume shi suna gaishe shi, dukka su ukun suka raka shi har bakin mota kafin yayi musu sallama ya wuce airport, ba Bata lokaci se gashi a Kaduna, tunda ya shiga gurin ya zauna acan sama inda guests of honor suke, ya zauna system din shi ya ciro ya aje ya dinga aiki har zuwa lokacin da ya tashi Dan yin presentation din shi, kamar ance Masa ya daga Kan shi ya kalla left side din shi se kuwa idanun shi suka sauka akan Hairan Dake zaune sanye da wata maroon din abaya, kunsan fari da irin wannan colors din yadda suke Masa, tayi kyau dukda fuskar ta Babu ko digon alamar make up, haka kurum yaji wani abu na daban wani Abu da ya kasa tantance menene ya shige shi!

To be continued...

Hairan is not free, contact me via WhatsApp 馃憞 馃憞 馃憞

***

Wanne labarun kike so? Aure ne bakiyi da wuri ba kike ganin kamar ba zakiyi ba? Karanta *FARA YAR SHEHU* Abu Kika rasa kike ganin kamar ba Zaki samu madadin shi ba, then ki nema *UNAISA* Soyayya ce tayi Miki kamu Kuma wani tsaikon ya Hana kiyi aure? To *ZUMA* ya kamata ki nema, A cikin *BANI DA LAIFI* Zaki gane cuta ba mutuwa bace ba, Kuma rabon kwadon ko ya hau sama se ya sakko, kiba ce da ke ko ke siririya ce da mutane suke shaming din ki har Kika fara samun mental break down ki sani *BINTUN BATUUL* Na jiran ki. Auren dole akai Miki, ko Kuma kina fama da maraici ne? Kuma Baki karanta *AFIYYA* ba jiran me kike Baki karanta *TSINTUWA* , *HIKMA* , *ME RABO KA DAUKA* , *UWARGIDAN BAHAUSHE* ba?

漏Oum A'eesh

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol