Free chapter · Read without an account

2

by Sadiyamuhammadnasir · RIKON SAKAINA

RIKON SAKAINA

YA FARU A GASKE

NA

SADIYA NASIR DAN

Arewa Book

sadiya Nasir

SHAFI NA BIYU

Hajiya Indo da tsananin b'acin rai ta isa office, kallo d'aya Aminyar ta Hajiya Turai tayi mata ta hango damuwa a tare da ita, shiyasa ta gaza samun nutsuwa saboda mugun nufin dake zuciyarta akan Hajiya Indo ta nufi inda take zaune fuska a sake, ɗan murmushi tayi taja kujera ta zauna. "Mutuniyar ya haka naga kin shigo fuska babu annuri ke dawa kuma?" Iska mai zafi Hajiya Indo ta furzar tace. "Ki bari kawai Aminya Alhaji ke neman saka min zafin kai , Amma naci alwashi kota halin k'ak'a ba zan bashi damar hakan ba, ina brother d'in sa daya rasu last week ?".

"Eh.... na gane Hajiya Turai ta ambata ta gyara zama Jin fad'an da Alhaji ne. "Yau kawai na shirya zan fito office saiga Munir da kaf yaran da marigayi ya bari wai Alhaji ke fad'a min ni zan rike? Tsakani da Allah akwai adalci?".

"Tabdijam lallai Alhaji bai kyauta ba me zaisa ya miki haka? Wannan daga ji aikin zugi ne, so suke su k'unta ta miki idan kin d'aga hankali su zuga shi ya k'aro miki kishiya".

"Kishiya Kuma?".

Hajiya Indo ta ambata cike da mamaki. Shu'umin murmushi Hajiya Turai tayi tace. "Tabbas kuwa idan kika tashi hankalinki akan ba zaki rike yaran nan ba shawarar da zasu bashi kenan ya auro wata ta rikesu, kinga shikenan zaki tashi a tutar babu kun tara arziki tare dashi wata shegiya za tazo a raba da ita". Cike da gamsuwa da maganar Hajiya Tura tace "Aminiya meye abinyi? Ina mai tabbatar miki Alhaji ya min kishiya zan iya aika su lahira duka, saboda ni kad'ai akayi shi". "Kwantar da hankalin ki zan baki shawara, ki daure wa zuciyarki kar ki k'ara gwada masa cewar ba zaki rike suba, da tuggu da munafurci za kiyi anfani har sai ya kore su da kansa".

"Allah ko Hajiya Turai?".

"Nifa nake fad'a miki wannan zance". Dariya sukayi gaba d'aya Hajiya Turai ta cigaba da d'ora Hajiya Indo akan mummunar turba ta yanda zata musguna wa yaran musamman Khadija.

*****

Tunda Baby ta fice a ɗakin na rabe tuni bacci ya daukeni, Jin kirar sallah dake a kwai masallaci a kofar gidan shiya farkar dani, bakina d'auke da salati na bud'e ido ta tashi zaune, ajiyar zuciya na sauƙe take mahaifina ya fad'o min a rai, siririn hawaye ne ya gangaro min nasa hanu na share na mike na shiga band'aki na dauro alola. Na jima akan sallaya ina Addu'a Allah ya shiga lamarina ya kawo min komai da sauƙi na zaman wannan gida. Ciki nane naji na kugin yunwa nan fa na tuna rabona da abinci tun jiya, jiki babu kuzari na fito na sauƙa k'asa.

Baby na hakimce a kujera tana canza channel ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya. Ɗan murmushi nayi na k'arasa inda take na zauna a gefe. "Khadija kin tashi?". "Na tashi Baby har nayi sallah, akwai abinci?". Ba tare data amsa ba ta soma kwala kiran Sahura, da sauri ta fito ta ɗan rusuna. "Ki kawo mata abinci". To tace ta mike da sauri don cika umurni. Tuwo miyar kub'ewa Sahura ta kawo cikin plate ta ajiye da girmamawa ta fice. Naji daɗin ganin tuwon saboda ni masoyiyar tuwo ne, Amma saboda damuwar da nake ciki sai Ina ji kamar guba nake ci, haka dai naci abinda zan iya na d'auki sauran na kai kitchen, nan na dawo na zauna gefen Baby muka cigaba da kallon abinda bana fahimta. Ina Jin kiran sallar la'asar na mike na koma ɗaki na gabatar, Ina tsaka da Addu'a Aunty Aliya ta shigo, kallo d'aya tamin ta ajiye jaka ta cire kaya ta watsa su kan gado ta shige toilet, ajiyar zuciya na sauƙe na k'arasa Addu'a ta na shafa na mike, kayan data watsa na kwashe na ninke na ajiye a gefe, sai da ta shafe kusan mintuna talatin kafin ta fito. "Sannu da dawowa Aunty Aliya". "Yauwa sannu Khadija". Ta ambata ba tare data kalleni ba ta wuce jikin mirror, fitowa nayi zan sauƙa k'asa har nayi nisa naji ta kwala min kira, amsawa nayi na dawo na tsaya a gabanta a ladabce. "Wannan fa daga ina?". Tamin nuni da akwati na, murmushi nayi nace. "Kaya nane Aunty Aliya Dady ya dawo damu gidan nan da zama". "Ke da gaske kike?". Cike da farin ciki nace mata "Eh... Tunanina murna za tayi sai naji sab'anin haka. "Kuma yace miki anan ɗakin zaki zauna bayan akwai ɗakuna a k'asa? Shuru nayi bance komai taja dogon tsaki. Wannan ne kuma ba zai yuyuba wallahi, ji daga zuwan ki ɗaki har yayi datti, in ba jakanci ba ya za'ayi ki aje mana akwati a tsakiyar ɗaki? Gaskiya da sake bari Momy ta dawo". "Kiyi hakuri Aunty Aliya". Nace da ita murya a sanyaye. Tsawa ta sake yimin. "Kwashe tsiyarki za kiyi na rantse ba zaki zauna a ɗakin nan ba, in ba nemar wa kai masifa ba ya za'ayi Dady ya tattaro ku ya kawo nan gidan? Me gidan uban naku yake daba zaku zauna idan taimakon ne ana muku daga can ba? Mtswww". Ta sake jan dogon tsaki ta fice a ɗakin.

Dogon numfashi naja na durkushe a wajen na zuba tagumi tausayin kaina na k'ara samun muhalli a zuciya ta. Na d'auka zan samu sassauci agun y'an uwana naji da Hajiya Indo ashe ashe?. "Ya Allah kana ji kuma kana gani". Na ambata na share kwallah data gangaro min.

****

Aliya tunda ta sauƙa k'asa take maganganu na rashin mutunci, Jin abin nata yana yawa yasa Baby amsa mata, nan ta dawo kanta suka cigaba dayi a haka Hajiya Indo ta shigo gidan ta riskesu. "Lafiya kuwa?". Ta ambata tana neman wajen zama. "Momy wallahi kija kunnen Baby duk ranar dana riketa abin bazai mana kyau ba, ya kamata ta gane nifa ba sa'arta bace ko Muhammad ba zai min raini na d'auka ba bare ita". "To uwar son girma meya had'a ku?". "Banyi da ita ba Momy na fito ina magana akan kaya dana gani a ɗaki na Khadija tunda zama bana k'are bane akwai ɗakuna a k'asa ta dawo, don ni bazan iya rayuwa da k'azama ba, daga zuwanta kinga ɗakin mu?". Murmushi Hajiya Indo tayi. "Dama babu dalilin da zaisa ta zauna a ɗakin ku, ni nasan me zanyi amma yanzu ya zama dole kiyi hakuri zuwa Alhaji ya tafi, koma miye zai zo mana da sauƙi". "Shikenan Momy Amma yaushe yace Miki zai zafi?". "Nan da 5days".

"Shikenan". Ta ambata tacigaba da aika wa Baby mugun kallo. "Sannu da dawowa Momy". Baby ta ambata gamida mikewa. "Yauwa sannu Auta ina zuwa?" "Ɗaki zani". Tsaki Aliya tayi "Za taje gun Khadija mana shegen munafurci, nifa Allah ya gani Momy bana son Khadija ko kaɗan, tun labarin da kika bani na zaman da kikayi da uwarta naji bana kaunarta, gaskiya Dady bai kyauta ba".

"Bakomai karki damu duk yana cikin sharrin Munir da Kubra kuma wallahi dani suke a sannu zanci ubansu duka". "Ai babu ma kamar Goggo Kubra matar nan na tsaneta Momy". Dariya Hajiya Indo tayi. "Tashi maza shiga kitchen ki jefa min ɗan wake akwai yunwa a jiki na". "An gama Momy". Aliya tace mike ta shiga kitchen. Hajiya Indo tayi ɗakin ta domin rage gajiya.

*****

Baby tun kafin ta k'araso ta soma Jin shesshekar kukan Khadija, Subhanallah ta ambata tayi saurin shiga ɗakin, k'arasawa tayi ta zauna ta dafa kafarta, "Don Allah Khadija kiyi hakuri kinji? Nasan Aunty Aliya ta bata miki rai, wallahi bata da kirki nima yanzu muka gama fad'a da ita, ki daina kuka kar kiyi zazzabi kinji? Ki barta da halinta idan ta zalince ki Allah zai saka miki". Share kwallah nayi nace. "Bakomai na tuna Abba ne". "Eyya sorry". Baby ta ambata tasa hanun rigarta ta share mata kwallah. A gefe na ta zauna tacigaba da min hirar makarantar su har aka kira Magrib, tare mu kayi alola mu kayi sallah, bayan mun idar mikewa Baby tayi ta dubeni. "Ya kamata mu sauƙa ko? Anjima kaɗan za kiji Dady ya shigo kin san zai tambayeki". So nake idan nayi isha'i saina sauƙa gaba d'aya zuwa lokacin bacci". Ok to shikenan. Sai kin sauƙo". Da kai na amsa ta wuce ta fita, kwantar da kaina nayi a jikin garu na cigaba da tunani.

*****

Jim kaɗan da fitar Baby palo Dady ya dawo, sannu da zuwa sukayi mishi gaba d'aya ya nemi waje ya zauna, mai da duban sa ga Baby yayi. "Auta kira min Sahura. To tace ta mike a ladabce ta shiga ɗakin Sahura. "Ina sister din taki ko har tayi bacci ne?" Ya jefo tambayar wa Aliya. Murmushin yak'e tayi "Tana sama idon ta biyu tafi son zaman can ne". "Kirata tazo, ko kuma Baby kirata". To Baby tace ta haura don isar da saƙo. "Sahura su Khalifa sun ci abinci ko?".

"Eh Dady na kai musu". Ta ambata kanta a k'asa. "Yayi kyau jeki, sannan ki tabbatar kina kai musu akan lokaci don Allah?". "In Sha Allah Dady ta ambata ta koma ɗaki.

Baby da Khadija tare suka fito, idon Aliya akan Khadija tana binta da mugun kallo, babu abinda ke d'aga mata hankali da Khadija kamr kyau da Allah ya mata, yarinya sai kace a cikin larabawa ta fito, sai da suka shigo cikin palon kafin ta kauda idon ta akan Khadija taja siririn tsaki ta yanda Dady ba zai jiba. A k'asa na zauna nace. "Sannu da dawowa Dady?". "Tashi ki zauna a sama bana son haka". To nace na mike nayi abinda ya sakani. "Ya zancen makaranta Khadija? Ya kamata a maida hankali akai". "Ina zuwa Dady rasuwar Abba yasa na dakata amma zan koma". "Ya kamata zaman bashi da anfani, kafin ɗan uwana ya rasu ya taba cemin ya nema miki N.C.E har yanzu nan kike?". "Eh Dady acan nake mun kusa jarabawa ma". "Toshikenan Allah ya taimaka Amma gaskiya zan canza Miki makaranta, kinfi dacewa da makarantar lafiya saboda kina da hazaka, kacigaba da zuwa wanda kike idan anfara d'aukar sabbin d'alibai a makarantar lafiya zan nema miki". Murmushi nayi nace nagode Dady Allah ya k'ara arziki". "Wannan ya zama dole ae Khadija, sauran y'an uwan naki ma kafin nabar garin nan zasu tafi boarding school inda Muhammad yake, yaushe kike so kiyi resuming sai na Baki wadataccen kudin abin hawa zuwa na dawo don zan kwana biyu gaskiya". "In Sha Allah Monday lokacin Abba ya cika sati biyu in Sha Allah". Allah yaji kan ɗan uwana ya Kai haske kabarin sa". Ameen muka amsa gaba d'aya. "Shikenan bari na shiga Ina kunci abinci?". Eh muka amsa gaba d'aya yasa kai ya haura sama. ..

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol