Free chapter · Read without an account
27
💞💞💞💞💞💞💞💞
AMATURRAHAMAN
*By*
OUM FATIMA
*(Hakimar D. A. W. A)*
💞💞💞💞💞💞💞💞
*DASHEN🌲ALLAH*
*WRITER'S📚ASSOCIATION*
*TEAM*
*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*
BOOK 1
PAGE 27
*بسم الله الر حمن الر حيم*
Da kuka sosai ta isa ta faɗa jikin Hajiya Sha'awanatu tana ƙara volum ɗin kukanta, hankalin Hajiya Sha'awanatu tashi yayi sosai ta shiga duba jikinta tana tambayata abinda ya sameta take wannan kukan.
"Momy shike nan komai ya lalace Ya Zayyad yace duk wacce ta ƙara zuwa masa da shirme sai ya aura wa sojojinsa ita, shike nan na rasa shi!." Ta ƙare maganar cikin matsanancin kuka.
"A gidan uban wa ya isa ya aura wa sojojin nasa ku? Ke Kinga ki min bayani miya faru?." Tashi tayi tayi mata bayanin abinda ya faru tun farkon zuwan da tayi ta roƙe shi ya aureta. Bata san lokacin data bige mata baki ba tana cewa "Me yasa kika fiye sha-shanci ni kam wai? Uban wa yace kije ki tare shi kice kina son sa? Ba nace kibi komai a hankali ba zan san yanda na biyo masa ta inda bai isa musawa ba amma shine kika je kika lalata komai da shegen gajen haƙurinki!." Momy ta faɗa matuƙar fusace.
"To Momy gani nayi kin kasa yin komai kar Aunty Zaheera ta rigani samun dama, shi yasa na fara yiwa kaina yaƙi."
"To ai kin yi yaƙin, uban me yaƙin naki ya haifar in ba lalata al'amarin ba!." Ta ƙare maganar da takaicin ƴar tata.
"Ni dai Momy kiyi wani abin don ba zan iya rasa shi ba." Ta faɗa a shagwaɓe.
"Wa yace maki nima zan bari ki rasa shi ina kallo yaron da kullum ƙara bunƙasa yake, so yake fa ya zarce Mahaifinsu a dukiya, a yanzu haka shine mai faɗa aji a gidan."
"Yauwa Momy kiyi duk yanda zakiyi ya aureni, so nake in zama nike juya kowa a gidan nan."
_________★
"Wash Allah Ammah, yau Allah ne ya cecemu a hannun Akhi." Haneen ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya.
"Me ya faru? Me ya haɗa ku da shi?." Ammah ta tambaya. Abinda ya faru duka Haneen ta faɗawa Ammah ta ƙare maganar da cewa."Ransa yayi matuƙar ɓaci Ammah don da gaske zai iya aurar damu ɗin."
"To Allah ya kyauta al'amarin Yayan naku ya fara damuna nima, ace kwata-kwata aure baya gabansa ko maganar baya son ayi masa sai kace wanda aka yiwa fsrraƙu tsakaninsa da Mata!." Ammah ta ƙare maganar a dame.
"To Ammah ki masa magana zai yi ai idan kika ce yayin, sai dai kuma duk wacce zai aura a cikin gidan nan abin rigima zai zama."
"Hankalina ma bai kwanta daya auri ko wacce yarinya a cikin gidan nan ba, saboda bana son rigima ko kaɗan Haneen, jin san dai yanda nake zaune da matan gidan nan ba ƙaunata suke yiba."
"Allah Ammah Akhi ne baya kula ƴanmatan, amma kar kiga yanda suke haukar son sa harda ƙawayena a cikin masu son nasa kawai dai suna tsoronsa ne shi yasa ba mai iya tunkararsa, shi kuma baya kallon Matan ma bare yaji yana son wata kullum fuska a haɗe daga bindiga sai aiki shi kaɗai ya iya." Haneen ta faɗa a hankali tana waigen bayanta kar tsautsayi yasa ya shigo bata sani ba ya jita alƙiyamarta ta tsaya yau. Dariya Muzaffar ya ƙyalƙyake da ita yana kallon yanda ta zabura tayi wuri-wuri da ido jin shigowarsa ta ɗauka boss ɗin ne.
"Mutum sai shegen tsoro amma ya iya tsegumi." Muzaffar ya faɗa yana harararta. Ita dai ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin wai Allah kaɗan ya hana in saki fitsari a zaune." Dariya Muzaffar ya saki yana nunata da yatsa yace "Matsoraciya kawai."
"Eh naji dai, ai bani kaɗai ke jin tsoron ba harda Rijalu ma." Zai yi magana Ammah ta katse shi ta hanyar cewa
"Abin nasa ne sai addu'a, muci gaba dayi masa addu'a kawai."
"In sha Allah Ammah." Suka haɗa baki dukansu suka amsa, daga haka suka shiga wata hirar da ban Haneen na masa zancen zuwa Matazu wurin ƙawarta.
__________ "Hajiya Sailuba kiyi maza kizo mu tafi wurin nan kin san ba'a sanya fa a al'amarin in ba haka ba sai abin ya ƙara lalacewa yanda ba zan so ba." Hajiya Ruƙayya data gama shiryawa tana jiran aminiyarta zasu je wurin wani sabon Malami da Hajiya Sailuba ta samo musu a kan al'amarin Hajiya Busaina da ƴaƴanta musamman Zayyad da take ganin duk ayyukan da tayi masa tamkar basa kama shi. Ba irin kuɗin da bata kashe ba akan wannan Companyn da ake ginawa amma a banza saima ƙaruwa da abin yake, abu na biyu Iyayensa sun fara maida hankali akan ganin yayi aure abinda ba zata bari ba kenan don ba yanda za'a yi ta zuba ido tana ganin ci gaban wacce ta datse nata farin cikin, ga kuma Salim sai ƙara lalacewa yake abinda taso gani akan ƴaƴan Hajiya Busaina amma sai Allah ya nuna mata akan ɗanta ɗaya da Allah ya bata Namiji da take tsananin so bayan Matan da take dasu, hakan kuma bai isheta ishara ba take ta ƙoƙarin ganin dole sai ta lalata rayuwar wasu abinda bata da iko a kai. (Allah ka tsare mana imaninmu).
Ba jima kuwa Hajiya Sailuba ta iso gidan suka fita a motar Hajiya Ruƙayyar ko direba bata ɗauka ba saboda tafiyar sirri ce, ko Abba ce masa tayi dubiya zasu je da yake ma baya nan ya ɗan yi tafiya ba mai nisa ba shi yasa a waya kawai ta kira shi ta sanar da shi suka wuce.
__________& Tafiya mai nisa sukayi tamkar zasu fita gari kafin suka gangara wani ɗan ƙaramin ƙauye dake gefen gari. Wani durƙusashen zauren ƙasa ne daya gama shan wuya sukayi sallama a cikinsa. Daga ciki aka amsa musu suka shiga, wani tanƙwashashshen farin tsohone zaune a saman buzu da tarkacen kayan aikinsa a gabansa.
"Hajiya ku ƙaraso daga ciki." Ya faɗa da muryarsa da bata fita sosai tsabar tsufan da yayi.
"Anya mutumin nan zai iya wani abu kuwa? Kalleshi fa yanda yake." Hajiya Ruƙayya ta faɗawa Hajiya Sailuba
cikin raɗa.
"Ke don Allah kiyi shiru, baki san irin waɗannan sunfi hatsabibanci ba." Hajiya Sailuba ta faɗa cikin raɗa.
"Zata iya juyawa zuwa inda zuciyarta tafi aminta da zuwa." Suka tsinci muryar tsohon na faɗa.
"Kayi haƙuri Malam bata san aikinka bane shi yasa, ayi mata aikin gafara." Hajiya Sailuba ta faɗa tana zungurin Hajiya Ruƙayya alamar ta bada haƙuri.
"Ayi haƙuri Malam tuba nake." Ta faɗa kamar yanda aminiyarta tayi. Wuri ya nuna musu suka zauna suka fara gaishe da shi ya amsa kafin Hajiya Sailuba ta fara gabatar da matsalolinta da kuma buƙatunta. Ƙasa ya buga ya mata bayanin abinda ke faruwa da abinda zata yi.
"Sai aminiyata gata itama tana da matsaloli da buƙatun da take so a biya mata su." Ta faɗa tana kallon Hajiya Ruƙayya dayi mata alamar tayi bayani. Zama ta gyara ta fara zayyano bayanin matsalolin Salim da aikin da take so ayi mata akan Ammah da ƴaƴanta. Ta ƙare maganar da cewa "Malam duk irin aikin dana sa aka yi masa baya kama yaron nan koya kama baya zuwa ko ina yake rushewa, kullum sai ƙara bunƙasa yake yana yin gaba ni kuma nawa ɗan kullum ƙara lalacewa yake bayan nice na fara auren Alhaji ni ya kamata ace na haifin ɗan da zai gaje shi tako wace fuska ba wacce tazo daga baya ta aure min miji ba!." Ta ƙare maganar tana bayyana tsananin hassadar data gama yiwa zuciyarta tsatsa irin mai wahalar kankarewa.
Haka kawai ta ɗagawa kanta hankali ba abinda ta rasa na rayuwa, da farko haihuwa take nema ido rufe Allah bai bata ba sai da aka auro wata ta haihu kafin itama Allah ya bata. Maimakon ta godewa Allah sai ma rainawa tayi saboda ba haka taso ba, ta manta cewar shi Allah ba'a masa dole yanda yaso yake yi a kuma lokacin da yaga dama, (Allah kasa mufi ƙarfin zuciyarmu).
Ƙasa ya shiga bugawa yana gogewa, sai da yayi haka sau da yawa kafin ya dakata ya ɗago ya zuba mata ido yace.
"Meye sunan Yaron kika ce?."
"Sunansa Zayyad." Ta faɗa a zaƙe da son jin abinda ya gano. Zanawa ya ƙara yi ya goge sau kusan biyar kafin ya ƙara ɗagowa ya kalleta yana sauke ajiyar zuciya yace "A gaskiya al'amarin yaron ne ya kasa buɗe min, iya bincike na banga komai ba sai haske dake kewaye da taurarinsa..." Katse shi Hajiya Ruƙayya tayi da cewa "Me hakan ke nufi Malam?!." Tayi tambayar a firgice.
"Hakan na nufin cewa taurarinsa suna da ƙarfi sosai, sannan kuma shi mutum ne mai tsananin Sa'ar rayuwa kuma yana da kariyar da taɓa shi zai yi wuya sosai gaskiya."
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!." Ta shiga ambata.
"Amma kuma Malam a baya an min aiki a kansa wanda har yanzu bai sake shi ba."
"Wane irin aiki ne?."
"Nasa an masa aiki ne ta yanda zai ji ya tsani aure, ko maganar aure baya so a masa, sai dai ya nemi matan banza saboda hakan ya zame min makamin da zan yaƙi Hajiya Busaina da shi." Dakatawa tayi kafin taci gaba da cewa "Hakan tabbata don bai taɓa cewa yana son wata ba bare maganar aure, hakan kuma na damun Iyayensa sai dai!." Dakatawa tayi tana jin ɗacin maganar da zata furta har sai da Malam na kan buzu yace. "Sai dai me?."
"Maganar zama riƙaƙƙen ɗan iska manemin mata hakan bai faru ba sai akan ɗana Salim da dama yana ɗan taɓawa a ɓoye, amma sai abin ya ƙara haukata har ya fito fili kowa ya sani!." Ta ƙare maganar tana jin tamkar ta haɗiye zuciyarta tsabar baƙin ciki.
Murmushi Malam na kan buzu yayi yace "A wancan lokacin kinci Sa'a ne dama lokacin aurensa bai yi ba shi yasa aikin naki ya kama, amma idan lokacin yayi zai yi aure wanda zai bawa kowa mamaki, wanda kuma ke cike da alkairi a gare shi." Ya faɗa yana kallon Hajiya Ruƙayya data cika da nadamar zuwa wurin domin hakan ba abinda ya haifar mata da shi face tarin baƙin ciki da ciwon rai.
"Yanzu Malam ba abinda za'a iya yi a kai kenan?." Hajiya Sailuba ta faɗa da son samun mafita ko yaya...
"Ba zai gagara ba akan sauran buƙatunta, akan wannan ɗinma zan ƙoƙarta inga me zan iya yi a kai, sai dai za'a buƙaci kuɗi sosai saboda aikin ba ƙarami bane."
"Karka damu Malam kuɗi ba matsalata bace, kawai ayi aikin." Hajiya Ruƙayya ta faɗa tana buɗe jakarta ta ciro damin kuɗi ta aje a gaban Malam na kan buzu.
Haɗa musu magun-guna yayi yaba Hajiya Ruƙayya wanda zata riƙa ba Salim, itama Hajiya Sailuba ya bata nata akan matsalar ƴarta da taƙi auruwa. Duk wanda yazo rigi-rigi sai a neme shi a rasa, da haka dai suka tarkata suka tafi jiki a sanyaye da abinda suka jiyo.
________★ dawowarta gidan yayi dai-dai da fitowar Zayyad ɗin daga sassan Ammah zai shiga na Baba Alhaji. Wani mugun tsoki ta saki tana jin ina wuta ta saka shi ya ƙone. Oho shi bai ma ganta ba bare ya san abinda take yi yayi shigewarsa zuwa neman da Baba Alhaji ke masa don gobe ne tafiyarsa China kuma daga can zai wuce Poland taron ƙaddamar da sababbin sojojin ƙasar da za'a yi.
Zuwa China ɗin ma don Abba yace yaje da kansa ne da wani zai wakilta, amma dai in komai ya kammala zai turo kayan ne su kaɗai shi kuma ya wuce. Maganar ginin Company kuwa tuni aka kammala sai ƴan gyare-gyaren da baza a rasa ba sai kuma maganar buɗewa da sai ya dawo daga Poland tukun na.
******* Hajiya Sha'awanatu kuwa zuwa tayi ta samu Uncle Maina da yaransa ke kiransa Dady ta fasa masa kuka akan Anisa tace zata kashe kanta idan ba'a aura mata Marshal Zayyad ba. Ransa yayi bala'in ɓaci dajin hakan yasa ta kirawo masa Anisar. Juyawa tayi tana share hawayen tamkar gaske ta nufi ɗakinta inda Anisar take.
"Kizo Dadynki na kira, sai ki san yanda kika yi ki ƙara langwaɓewa mu samu mu jawo ra'ayinsa yasa baki a maganar nan ayi abin nan a wuce wurin."
"To Momy." Ta faɗa tana saukowa daga saman gadon uwar ta sata a gaba suka fice tana ta wani langwaɓe kai." Suna zuwa ta lanƙwashe zata kwanta ya daka mata wata firgitacciyar tsawar daya sakata miƙewa ba shiri tana rarraba ido. Wuri ya nuna mata yace "Zauna!." Cikin rawar jiki ta zauna don bata taɓa ganin Dadyn nasu ya mata magana a wannan yanayin ba.
Ita kanta Momy ba ƙaramin firgita tayi ba don bata taɓa zaton abinda zai yi kenan ba. "Kina jina ko? Daga yau kar in ƙara jin maganar Son a bakinki ko ki ɗagawa Mahaifiyarki hankali akan zaki kashe kanki. Kin daɗe baki kashe kan naki ba, ana so dole ne ko Zayyad ɗin sa'anki ne dan Ubanki da zaki damu mutane? Dukanki ma guda nawa kike da zaki ɗauki soyayyar Namiji ki ɗorawa kanki ki hana kanki zaman lafiya. To tunda auren kike so ki shirya gobe Abdulmajid ɗan wajen Alhaji Maitama zai zo ya ganki, dama tuni Mahaifinsa ya min magana akan yaron na sonki na dakatar dashi saboda karatunki. Amma tunda haka kika zaɓa sai a maki auren kya ƙarasa a ɗakinki. Tashi ki bani wuri sakaran banza, kuma inƙara jin wata magana sai nayi mummunan saɓa maki sha-sha-sha!." Ya ƙare maganar a tsawace tamkar zai rufeta da duka allurar sojojin na motsa masa.
Da mugun gudu Anisa ta fice a ɗakin har tana cin tuntuɓe da ƙafar kujera. Miƙewa Momy tayi jiki na rawa zata bita ya nuna mata wuri yace "Koma ki zauna." Ya ƙare cikin bada umarni fuska a haɗe. Ba don taso ba ta zauna amma hankalinta na kan ɗiyarta ganin yanda ta fita yasa hankalinta bai kwanta ba.
"Daga yau na kashe wannan maganar a gidan nan kar wanda ya ƙara tada min ita, kuma sannan na faɗa Abdulmajid zai zo suka juna kafin a tsaida ranar auren ba fashi kuma aurar ita zan yi tunda ta fara wannan tunanin. Don haka bana buƙatar wasu ƙananun magana da zasu biyo baya ki jawa ƴarki kunne." Ya ƙare maganar yana riƙe kunnensa alamar gargaɗi. Baki ta buɗe zata yi magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu kafin ya nuna mata ƙofa.
Ba don taso ba ta fice tana kumburi sai don ganin yanda ransa yayi matuƙar ɓaci shi yasa ta haƙura ta fita da nufin idan ya huce sayi magana don ba wanda zai yiwa ƴarta auren dole tana ji tana gani tayi shiru kuma ga wanda suka ƙwallafawa rai su saki wasu su kama ina!!!......
(Tofa Anisa kin ɓallowa kanki ruwa da alama).