Free chapter · Read without an account
3
003
Ya fito ɗaure da faffaɗan tawul a ƙugunshi tare da ɗan ƙarami a hannunshi yana goge sumar kanshi dake ɗigar da danshi lemar ruwan wanka a gaban ƙaton dressing mirrow ya tsaya yana cigaba da tsane jikinshi kasancewar shi mai zafin nama irin na lafiyayyun maza yasa cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala tsane jikin nashi tsaf ya rataye ƙaramin tawul ɗin yana ƙoƙarin ɗaukar Cream daze shafa wayar shi ta kuma ringing da ɗan sauri ya ƙarasa gabanta ganin.
MY BABY yasa shi sakin wani ƙayataccen murmushin daya ƙara bayyana zatin kyanshi kafin yay rejecting kana shi ya kirata murya a shagwaɓe take furta.
"My one and only kayi wankan kasha tea ɗin wallahi duk na damu"
Takai maganar cikin salon kirsa.
Har yanzu tsadaddan murmushin nasa bai gushe ba cike da shauki da jin daɗin kulawarta gare shi ya furta mata.
"yes baby yanzun haka nai wanka tea ɗinne ban shaba shima kuma zan sha dana kammala shiryawa"
Yafaɗa mata hakan cikin lallausar muryarshi mai kashe jiki.
Tura baki tayi gaba kamar yana ganinta kana ta marai raice kamar wata ƙaramar yarinya.
"Nidai ka kunna data zan kiraka VD call yanzu na shirya ka ta wayan"
Tafaɗa tana wani irin narkar masa da murya wadda tasa sauran kaɗan ya sume a wajan dan tsabar daɗin muryar tata.
Cikin lafazin so ya furta.
"Not now my baby sabida ina da ayyuka agabana kinga yanzu mutumin dana zo gani ze shigo mu zauna please ki bari zuwa dare se muyi kafin nan ma ki min kwalliyar ki mai kyau da tsari"
Yafaɗi maganar yana wani ɗage gira kamar tana gabanshi.
Cikin barikancin data saba ɗauke mai hankalin sa akan kowa ta soma rera mai kuka! wanda zahiri na karya ne amman shi bai san hakan ba sema susucewa dayay yana rarrashinta kamar ze tsaga wayar ya shiga ya kamota ya cigaba da rarrashinta haka yake ji aranshi.
Ta jima tana Hargitsa mai lissafi ta cikin wayar na salon kirsa da shagwaɓa kafin suyi sallama ya koma bakin gado jagwab ya zauna yana fesar da zazzafar iska
Hannunshi dafe da kanshi ya tallafe yana sakin ajiyar zuciya akai akai.
Ya jima yana kokawa da numfashin sa kafin ya sami dai daiton nutsuwarshi kana ya kuma ƙoƙarin miƙewa a karo na biyu sedai still ringing na biyu daya kuma shigowa wayarshi shiya katse masa hanzarin sa.
A ɗan tsorace yake kallon screen ɗin wayar yawani zaro idanunshi waje waɗanda suka ƙara haska tsantsar kyawun da Allah ya bashi.
Batare daya iya ɗaukar wayar ba haka ta katse wani kiran ya sake shigowa aro jarumta yayi haɗi da ɗauka muryar shi can ƙasa ya furta.
"Assalamu alaikum Ammi barka da yammah"
Murya a rarrabe kamar na mai tsoron wani abu.
Cikin kamilalliyar muryarta wadda ta bayyana dattakon ma'abociyar maganar tace.
"Amin wa'alaikassalam Baffa ina wuni?"
Wata kunya ce ta kamashi da sauri ya zame kamar tana gabanshi yau ammi ta kira sunan shi gatsal duk irin ɗunbin kunyarta gareshi tabbas da alamun akwai laifin dayay mata wanda shi baida masaniyya akan hakan.
"Ammi dan Allah kiyi haƙuri bai dace ke ki fara gaishe dani ba, kina matsayin uwa mahaifiya afuwan ammi idan laifi nayi kiyi haƙuri"
Yafaɗa yana mai ƙasƙantar da kanshi gareta.
Muryarta a kwance ta furta.
"A'a baffa bakai mini komai ba rayuwarka ce duk yadda ka tsarata hakan zaka tafi da ita naji labarin kayi tafiya zuwa kano ina maka addu'ar nasara da haske idan da hali ina mai roƙonka da ka kira Abban ka,ka shaida masa da bakin ka sannan kuma karka baro kano a wannan karon bakaje gaida Hajja ba"
Tana faɗin hakan ta datse kiran.
Kamar wani sakarai yabi wayar da kallo kafin daga bisani ya fara niman layin nata da zafin shi sedai har tai ringing ta gama Ammi bata ɗauka ba.
Zubewa yayi a ƙasan lallausan carfet ɗin.
Yana mai shafo sumar kanshi dayay mata saisaye maike Damuna? ya faɗa a bayyane.
Cikin nadama ya mike yasan bai kyautawa mahaifanshi ba, har yayi tafiya daga garinsu zuwa wani garin amman ya kasa gayawa mahaifanshi waɗanda suke a gari guda? mai yasa yayi hakan idan bai manta ba har maman basma matarshi yaje yayi ma sallama a jiya amman why beje wajan AMMI da ABBA yayi masu sallama ba sannan hajja kakarshi wadda ta haifi Ammin shi tana cikin garin kano amman sam hankalinshi bai ma kai daya je mata ba seda Ammi ta tuna masa.
Sosai ya zurfafa a tunanin lamarin shi gaba ɗaya kanshi ya kulle yama rasa mai yakamata yayi.
Da azama ya miƙe ya nufi gaban mirrow a sanyaye yake gyara jikinshi bayan yayi ma kanshi ɓarin turarukan shi masu tsada kana ya nufi wajan kayanshi shirya kanshi yayi cikin wani lallausan yadi milk colour mai aikin baƙin zare yayi wani mugun kyau kasancewar shi black beauty se kayan suka amshi jikinsa hula kalar kayan ya sanya akanshi ya ɗora black shoe a ƙafafunshi se shigar tai masa mugun kyau don ya fito a ainihin yarenshi na hausa fulani.
Da sassarfa ya ƙarasa gaban takardun ɗazu ya ɗauki guda acikinsu anan ma seda yayi tsaki tuno wannan banzar yarinyar data watsar mai dasu.
Kafin ya mike wayarshi tai ringing ya ɗauka tare da ƙaro hands free.
"*BARRISTER ALIYU ALI DIKKO* idan ka kammala ina compound na hotel ɗin ina jiran ka"
Daga cikin wayar muryar wani babban mutum ta karaɗe wayar.
Lumshe idanu yayi har zara zaran gashin idanunshi na kwanciya kana ya warasu yana mai taune ƙasan laɓɓansa cike da tarin damuwar furucin Amminsa ya furta.
"Okey give me five minutes insha Allahu gani nan"
Yafaɗa da wani irin sauri yake ƙoƙarin juyawa domin fita sedai sabon kiran mai ɗauke da sabon ringing shiya cika ɗakin
Duru-duru ya shigayi don shikam ban da wayarshi mai ƙirar iphone 13 pro max bai san da wata wayar a wajan ba,
Bin inda yake jin ringing ɗin yake harya ƙarasa dai dai gefen gadon, da sauri ya ware idanunshi kan black phone ɗin dake faman ringing wadda akai save numbern da ke kira da Sis meerah.
Ƙyam ya tsaya yana noticing kafin yayi kokarin kai hannu kai harta katse still sega wani kiran ya ƙara shigowa cikin dakiya ya sanya hannu ya ɗauka tare da danna green side don ya sami damar amsa kiran da aketa faman yi cikin wayar wanda babu ƙaƙƙauta wa da alamu duk wanda ke kiran ya dangan ci mai wayar ne.
Da sauri ya kara wayar cikin kunnenshi cikin wata irin........