Free chapter · Read without an account
6
006
Girgiza kai ta shigayi tamkar wani naganinta.
"No! bazan iya ba soyayyar Dikko ajini na take bana jin koze cire dukkan naman jikina zan iya rabuwa dashi"
Tafaɗa tana mai cije jajayen laɓɓanta dasukai wata irin kumbura sakamakon tsotar dasuka sha a bakin barrister dikko.
Kafin ta miƙa hannunta a hankali tana ɗingishi take tafiya wadda da ƙyar take taka ƙafafunta.
Cikin mawuyacin hali takai gaban motar ameerah ta buɗe ta shiga taja aguje tabar harabar hotel ɗin wanda hakan yayi dai dai da sanda ake ta faman ƙwaɗa kiran sallar magariba.
Cikin rawar jiki ya faɗa saman faffaɗan lafiyayyan gadonsa, yana jin zuciyar shi babu daɗi na ɓacin ran data haddasa masa.
Hancinshi har yanzu yana manne da wani irin sihirtaccen ƙamshin turarenta data bar mai wanda bai taɓa ji ko ganin turare mai kamshi kamar nata ba.
Da wata irin kasala ya miƙe,A hankali yake taka ƙafafunshi har ya isa bathroom ruwa mai ɗumi ya haɗa A bathtube nan da nan ya shiga gasa jikinsa da ruwan sabida wani shegen zazzaɓi dake neman kawo mai bara, Kafin ya kammala ya ɗauro alwala ya fito agurguje ya sanya fara ƙal ɗin jallabiya yayi ma kanshi ɓarin haɗaɗɗan turarenshi kana ya shinfiɗa sallaya ya soma gabatar da sallar cike da nutsuwa har ya idar anan zaunan yayi azkar haɗi da karanta suratul baqrah wadda ya ɗauki tsayin lokaci yana karatun bayan ya kammala ya shafa kana ya miƙe domin gabatar da sallar isha'i wanda lokacin daya ɗauka yana karatu shine yakaishi har zuwa isha'i yana idar da sallar isha ya kuma bada nafila raka'a biyu ya jima yana addu'a cikin sujjadarshi ta ƙarshe kafin ya ɗago yayi sallama ya shafe jikinshi da addu'a tashi yayi tare da ninke sallayar gami da tube jallabiyar jikinshi waya ya kira da akawo masa Coffee.
Kana ya ƙarasa gaban gadon ya ciro laptop ɗinshi a chraging ya kunnata ya cigaba da aiki da ita har sanda akai mai knocking ya miƙe tare da raɓewa jikin kofar batare da mai miko mai coffeen ya ganshi ba ya zira hannu ya amsa ya mayar da ƙofar ya rufe.
Adai dai sanda ze koma wajan zamanshi yaga wayarta watse a wajan tsaki yaja tare da tsugunnawa ya ɗauka ya kunnata ya koma mazauninshi still aikin gabanshi ya cigaba dayi akan shari'ar daze gabatar a gobe, Gefe guda yana shan coffe wanda zafinshi ke saukar mai da kuzarin daya rasa a ɗazu
Bai kammala aikin ba se wajan taran dare sannan ya kashe laptop ɗin ya aje cup ɗin coffee ɗin a gefe ya mayar da kanshi saman pillow idanun shi na hasko mai kamannin yarinyar ɗazu........."Ina son ka! kalmar data ke mai yawo a kwanyar kanshi kenan wannan wace irin hatsabibiyar yarinya ce dazata iya furta kalmar so agareshi babu tsoro? watsar da shirmenta yayi tare da ɗaukar waya ya kamo numbern Amminshi duk da tarin kiran basmah daya gani amman seya share a wannan karon jin kewar ammi yake wadda ya jima bai jita ba, Jiki na rawa yake danna mata kira kuma a wannan karon yaci sa'a ta ɗauka cikin cool vioce yake gaisheta kafin tafara masa nasiha cikin tsanani da shauƙin soyayyah irin ta ɗa da mahaifi tsayin lokaci suna magana da ammi har sukai sallama zuciyarshi fes ya miƙe ya ɗauro alwala ya kashe ƙwan ɗakin bayan yayi addu'a ya kwanta ba jimawa bacci yayi gaba dashi sabida akwai tarin gajiya atare dashi.
Allah kaɗai yakai Ummul khairi Gidansu lafiya tana rangaji ta kashe motar tare da daddafawa da ƙyar ta ƙarasa cikin gidan nasu wanda ya koma kamar wata kasuwar mata banda kiɗa babu abin da yake tashi daga tsakar gidan mata ne birjik suke faman tiƙar rawa cikin sautin wakar data cika gidan.
A hankali take dafa bango tana zubar da hawaye ta ƙarasa ɗakinsu wanda harta kai ga ɗakin babu wanda yasan data shigo ma bare a tanka mata.
BARIKI KENAN GIDAN KAZO NA ZO!
Duhu dumɗin ɗakin babu haske alamun ameerah bata ma ɗakin ahaka ta lallaɓa ta aje mata key ta kuma lallaɓawa ta ɗauki ruwa da dafe bango takai bayin tsakar gida ta kama ruwa haɗi da ɗauro alwala a zaune tayi sallah sabida yadda zazzaɓi da zafin jiki ke damunta ahaka ta zauna ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka! idanunta jajir fuska jajir kamar mai afolo har lokacin isha'i yayi ta tayar anan saman dardumar bacci ya kwasheta wajan ƙarfe goman dare ameerah ta shigo ɗakin tana furta kalmar.
"washh yau fa na gaji"
Jin shuru yasa ta tsugunna ta tayar da ita wadda har lokacin zazzaɓin bai saketa ba da rarrabe tahau saman gado taja blanket jikinta nata karkarwa wahalallan baccine yayi gaba da ita.
Duk irin kiran da ameerah keyi mata bata iya farkawa ba haka tai ta baccinta wanda bata farka ba se asubahi.
Da ƙyar ta yunƙura tayi sallah wadda da ƙyar ta gabatar da ita haka ta takure a gefen gado tana rawar ɗari.
Ameerah bata farkaba se wajan goman safiya ganin ummul rakuɓe tana ta mayar da numfashi yasa taɗan tsorata tana furta.
"Ke ummul lafiyarki?"
Girgiza kai ta shigayi.
"Bani da lafiya amerah kaini gidan Hajjah seki je gidanmu ki gayama Bamu kice mata bani da lafiya jina ke kamar zan mutu"
Tafaɗa tana mayar da numfashi.
"a,a ummul bara na kaiki hospital"
Girgiza kai tayi wanda hakan yasa ameerah ta gane gida take so don haka da sauri tayo alwala rana gatsal tai sallar safe ta zira katon hijab bayan ta tarairayo ummul jikinta ta ɗauki keyn mota suka fita.
Motsi kaɗan ummul tace"washhh amerah kimin a hankali"
Wanda hakan ya tabba tar da tai muguwar buguwa a ƙugunta.
Da haka suka shiga mota domin nufar inda ta buƙata................
Barrister Aliyu Ali Dikko kuwa se.........