Free chapter · Read without an account
8
008
Tuƙi yake cike da wata irin nutsuwa wadda a zahiri haka halittarshi take gaba ɗaya soya ke ya ƙarasa gidan hajja don ba ƙaramar wahala ya kwaso ba,da ƙyar yake tuƙin ga unguwar da hajja take mai azabar nisa daga inda ya fito.
Yana tafe yana duba tsarin sauye-sauyen da aka samu a garin sabida yaɗan jima bai shigo ba ahaka ya shiga cikin unguwar su hajja yana tuƙi yana jan tsaki akai akai sabida yadda wajan duk ya cika da tudu da kwari na ruwan sama da akai duk ya sanya hanyar tayi babu kyan gani.
A hankali ya ƙarasar da motar shi cikin layin sosai ya ware ido yana kallon yadda yara ke faman wasannin su rabon shi da gidan hajja tun kafin yayi aure shekaru biyar kenan se yau da Allah ya kawoshi yasan ba ƙaramar mita hajja zata yi mai ba tsintar kanshi yayi da ɗan sakin ƙaramin murmushi kafin ya kashe motar ya fito waje hannun shi riƙe da key tare da wayar shi wadda take faman zuba ringing na kiran da basmah take mai tun jiya wanda bai sami damar ɗagawa ba.
Cikin ɗan zafin nama kaɗan ya ƙarasa bakin gate ɗin lokaci wajan 12:30pm rana taɗan soma fitowa wannan yasa yake ta yamutsa fuskarshi kasance warshi mutum marar son zafin rana da zafi ko kaɗan, Azurfar dake yatsunshi yasa yake ɗan duka gate ɗin cikin ɗaga murya hajja dake ƙoƙarin fitowa take furta.
"Wani marar haƙurin ne ze karyan ƙofar?"
Dariya yaɗan ƙunshe yasan za'a rina hajja da mugun son abin duniya ita komai nata kif kif ne bata son wasa da abin duniya, Harta karaso ta buɗe mai gate ɗin tana faman mita shikuma bai yi magana ba.
tana buɗewa yayi wani irin sauri ya ɗaneta yana cusa kansa a saman wuyanta yana furta.
"I miss you hajjata"
Ture shi tai tare da cewa.
"Da Allah sakar ni gososo dakai zaka ɓallan ƙashi damma ƙashin bana rainon madara bane yasha jar dawar da ya horu"
Taɓe baki yayi tare da langwaɓar da kanshi gefe yayi kalar abin tausayi tare da ce mata.
"Haba hajjata duk duniya in kika cire su ammi wa nake dashi idan bake ba wa ze rungume ni yashafa kaina naji dadi idan bake ba amman shine zaki min haka"
Yafaɗa tamkar ba Aliyu miskilin da magana ma ke masa wuya ba.
"Dallah gafaracan ada dai kake min wannan soyayyar amman ban da yanzu da mace ta fi maka kowa ai yanzu tunda kana da Batsama ai kana da kowa"
Tafaɗa tare da wucewa cikin falonta tana jan mita.
"Wai batsama! ya mai maita sunan Basma da hajja ta lauya ya koma wani daban ya kuwa kwashe da dariyar da bai son ta fito ba wai mai yasa familyn shi suke ɗora laifin su ga Basmah wadda kullum ita burinta taga ta kyautata musu amman sukam kowa ita kowa ita basa duba busy da aikin shi keda sedai suce ta hanashi ziyara kota hanashi yi musu abu.
Shafa saisa yayyar sumar dake kanshi yayi tare da bin hajiya cikin falon haɗaɗɗan ƙamshin turaren wuta ya shaƙa wanda salame tai aikin gyara falon dashi zama yayi a saman three seater yana faman lumshe idanunshi.
"Washh hajja aka womin ruwa ko break fast ban yi ba"
Yafaɗa yana mai ɗora dogayen ƙafafun shi saman kujerar ya riƙe wayar shi yana mai duba tarin kiran da basmah ta bar masa daga jiya zuwa yau ban da messages rututu wanda duk ana lafiya bai ɗauki kiranta ba.
Layin ta ya shiga kira yana mai kwantar da kanshi saman seater ɗin dayake kai.
Ringing! ɗaya ta ɗauka tana mai sauke ajiyar zuciya mai mugun ƙarfi.
"Assalamu alaikum barka da rana"
Tafaɗa sanin bai son ka fara masa magana da hellow! yafi son sallama a tsarin shi.
"Lafiya lau baby ya gida?"
Murya can ƙasa tace.
"Cweet man lafiya tun jiya ina kira user busy amman kuma baka kirani ba?"
Kamar baze magana ba can kuma yace mata.
"Munyi waya da Amminah! shine kuma bacci ya ɗauke ni ɗazu kuma ina court bayan na fito na taho gidan Hajja"
Ya ƙarasa maganar murya cikin sanyi.
"Banji ba gidan hajja? ke nan ba zaka shigo yau ba?"
Tafaɗa muryarta a rarrabe da alamun maganar taɗan soke ta.
"Ban gane baki jiba ina da hausa nayi maki maganar?".
Ya jefa mata tambayar.
Da sauri ta waske sanin da wa take waya tare da cewa.
"Ce wa nai ka gaida hajja yau zaka shigo nai maka girki?"
Aranshi ya furta kamar ta iya amman a fili se cewa yayi.
"Nima ina son haka sedai na gaya maki naje wajan hajja kinga rabona da ita tun kafin muyi aure idan har na gama da wuri zan iya shigowa idan ban gama da gidan ta da wuri ba sedai gobe sabida tafiyar mota nayo kin sani"
Shuru tayi amman a ranta tana tsinewa Ammi don ita ce zata sanya yaje gidan magananniyar kakar shi wadda sam bata kaunar ya raɓi kowa amman a fili se cewa tayi.
"Allah sarki hajiya hajja tsohuwa mai ran ƙarfe inda ka gaya min zaka je dana bada saƙo an kai mata amman pls ka gaishe min da ita da kyau"
Murmushi yayi yana mai kallon saitin hajja data kawo mai ruwa ta dire mai agabanshi tana zaune ta zuba mai ido kamar ma harararshi take.
"Kona bata ku gaisa gata ma can a zaune"
Ya faɗa tare da miƙawa hajja wayar yana cewa.
"Amsa ga kishiyar ki"
Kamar Basmah zatayi kuka ta fara aro yadda zatai ta gaisar da hajja ɗin tun ma kafin tayi magana hajja ta soma cewa.
"A,a giwar mata bakya bora barka da rana Aci ai kashi ba jini bare cibi"
Dumm basmah tayi batare data ce komai ba shiko murmushi yake don bai kawo magana hajja take gayawa basma ba.
A daddafe suka gaisa basmah tayi saurin katse wayar tana auna maganganun hajja masu cike da harshan damo.
Shiko watsar da wayar yayi gefe tare da sauka ƙasa ya miƙe ƙafafu yana mai ɓalle murfin gorar ruwan data aje mai yay bisimillah ya kafa baki ya shanye.
Seda ya shanye tas sannan ya ajeta gefe yana hamdala.
Haɗaɗɗan tuwan shinkafa miyar shuwaka wadda taji tantaƙwashi se kunun aya dayaji kayan kamshi hajja ta tura mai gabanshi da kanshi ya buɗe flaks ɗin yana zuzzuba wa amman fa duk hankalin shi yana kan abincin wanda yayi missing girki mai daɗi don basmah bata iya wani abinci ba ada wajan ammi yake zuwa yaci daga baya ta hanashi dole suka koma siya a wajan saida abinci idan ko ita tayi baya ciyuwa yace taje ta koyi girki tayi biris.
Tanƙwashe ƙafafu yayi bayan ya wanke hannunshi a tasar wanke hannu yayi bisimillah ya soma kai lomar tuwan bakinshi.
Bai sami zarafin bawa hajja amsar tambayoyin data ke mai akan su ammi da ƴan uwanshi ba seda ya cinye malmala guda sabida bai da cin abinci sosai ko wannan ma dan yana jin yunwa ne.
Sannan ya wanke hannu ya tashi da kanshi ya kai kayan kicin ya kuma tattare wajan bai tsaya ba tsakar gida ya fita ya ɗaura alwala ya fice masallaci.
Wanda itama hajjan lokacin ne ta mike ta shiga ɗaki don gabatar da tata sallar.
Har ta idar ta fito falo ta zauna bai dawo ba wajan awa biyu da fitar shi sannan ya shigo gidan lokacin ya cire ƴar saman suite ɗin dake jikinshi yabar white shirt ya cillata mota hannu riƙe da key ya shigo gidan.
Sallama yayi hajja ta amsa.
"Kaiko Baffa a ina ka zauna har na kammala idar da sallah ta baka shigo ba?"
Shafa kanshi yayi tare da komawa ya zauna.
"Na ɗan zaga gari ne kawai kin san ban son zaman kaɗai ci"
Harara ta ɓalla mai tare da cewa.
"Ai ni ba mutum bace ko?"
murmushi ya sanya yana mai danna cikin wayarshi batare daya tanka mata ba.
Juyi ummul tayi wadda bata ma san duk wainar da su hajja ke toya wa ba sabida baccin data farka daga shi yanzu
"Washh bayana hajja ze karye"
Da wani irin sauri Aliyu ya dubi saitin daya ji maganar macen wadda bai san ko wacece ba sabida bayan data bashi kuma sam shi bai ma san da mutum a falon ba sabida rashin lura da hakan.
Cikin kiɗima hajja tai wajan ummul tare da zama a gefen ta.
"Ta shi ummi naga wajan tun ɗazu kike furta ƙugunki bayan ki in babu dama se Baffa ya kaiki wajan masu gyara a duba maki"
Ta faɗawa ummul wadda take ƙoƙarin yunƙura wa ta tashi daga kwanciyar data yi.
Sedai me? juyowar da zatai don ta dafa hajja ta miƙe idanunta ya shiga cikin nasa...