Free chapter · Read without an account

ƊANƊANO.

by JamilaUmarJanafty · TURKEN GIDA.

THURSDAY, 24/ARPRIL/2025

DAGA MARUBUCIYAR.

TA FITA ZAKKA

GIDANMU

KANA NAKA

TSAKA MAI WUYA

IDAN AN CIZA

JANAFTY❤️

AREWABOOKS:JamilaumarJanafty.

WATTPAD:JamilaUmar315

A IRIN WANNAN RANAR TA 24/04/... MAMA DA BABA SUKA SAMAR DA NI. NA GODE MA ALLAH DA YA RAYANI, ALLAH YA ALBARKACI SHEKARUNA NA GABA YA YI MA RAYUWATA ALBARKA. IYAYENA KUMA ALLAH YA SA KU GAMA DA DUNIYA LAFIYA AMIN

HAPPY BIRTHDAY TO ME.❤️😍

ƊANƊANO DAGA LITTAFIN TURKEN GIDA.

Gas na kunna na ɗora ruwan tea kawai. Muna da sauran buredi tunda jiya ya shigo da shi. Bayan na juye a fulas sai na ɗumama alalen sannan na soya ƙwai saboda Jidda da Babanta  sai da na gama komai na kai falo sannan na shiga ɗakin su Jidda na tashe ta, ina tashin ta Baby na ji ta yi zaraf ta miƙe tana faɗin" Umma nima zan yi azumin."

Kai tsaye na ce" To ku wanke baki ku fito mu yi sahur."

  Daga nan na fice tiolet  na shiga na yi brush ina fitowa hannuna da danshin ruwa na lallaɓa domin na shafa ma Yallaɓai ruwa a fuska saboda ya tashi sai dai ina zuwa dai dai saitin kan shi wayarsa ta kawo haske alamun ana kira ban saka hannu ba sai na leƙa sai na ga Daughter na kira. Mamaki ya kamani me ya sa ta ke kiran shi yanzu? Sai wata zuciyar ta ce min ko dai jikin Nene ne?

  Tunanin haka ya sa sai na yi niyyar amsa kiran sai na saka hannu na ɗauki wayar na buɗe bayan wayar ta yanke. Tunda na san password ɗin wayarsa ina shirin kiranta ne kawai sai ga saƙon ta ya shigo wayar har ga Allah ba halina ba ne duba wayar miji duk da wayar Yallaɓai ba ta da shamaki a wajena ban taɓa tunanin bin diddiginsa ba. Kuma har ga Allah lokacin da saƙon ya shigo hannuna ne ya faɗa kan saƙo sai ya buɗe kuma ban isa a lokacin na hana idanuwana karanta abin da ta rubuta ba.

  "Daddy na a tashi a yi sahur. Ko duk santin girkin nawa ne yasa ka kasa tashi? Na ga tuƙwaici na gode. Amma ka yi min laifi domin na ce ba zan karɓa ba yanzu haka ma za su dawo wajenka domin zan siya ma ƴa'ƴana kayan kwalliyar salla da su. Thank you so much for been their for me Daddy."

  Na yi ƙoƙarin bayan na gama karanta wannan na fita amma sai zuciya ta rinjaye ni na srolling sama ina ganin saƙonnin da ta ke tura masa. Tun da aka fara azumi  take tura masa saƙo da asuba a tashi a yi sahur sannan sai ta tura masa sakon barka da shan ruwa wani lokacin ya ba ta amsa wani lokacin ya yi shuru. Na duba saƙonin har wanda ta na Abuja lokacin da mijinta ya rasu. Wani saƙo da ya ba ni mamaki ya sa na ji kirjina sai da ya buga dam! Shine ta tura masa" Na yi kewarka Daddy yaushe za ka zo?

Shi kuma sai ya ba ta amsa da Gobe in sha Allahu.

  Kirjina ne na ji ya fara suya, har ina ganin duhu duhu da ya sa ban ƙara gaba ba na ijiye masa wayar a nan saman side drower ɗin da ya ke kwance. Kallonsa na ke yi ina mamakin Yallaɓai ashe shima ya iya munafuncin maza? Ashe jiya ba Nene ba ce ta tsaida shi ba ashe Gimbiya ce ta tsaida shi, bayan ta yi masa girki ya ci har ya na santi daga karshe har ya na ba ta tuƙwaici ni kuma ko oho. Wani ƙolulun abu ya tokaremin a kirji da wani haushin Yallaɓai don Allah menene na ƙarya tsakani ga Allah? Sai kawai na juya da na so na fita ne ba zan tashe shi ba sai dai yau ya yi ɗaure amma sai na danne zuciyata da na yi wani tunani sai kawai na dawo na fara buga gefen gadon yau ko sunan shi ban kira ba. Sannan ban taɓa shi kamar yadda na saba ba. Bai da wani nauyin barci sai gashi ya buɗe idanuwansa da suka yi nauyi yana kallona sai kawai na juya ina faɗin.

"Ka tashi lokacin Sahur ya yi."

  Da ga haka na yi ficewata na bar shi a raina kuma na kudiri niyyar ko bai tashi ba na gama tashin shi. Daga yau sai ita wacce ke tashin sa sai ta cigaba da tashin shi. Ban da munafunci ta san ya na da mata amma wai ta ce duk asuba sai ta kira shi ya ta shi ya yi sahur? Ban taɓa lura ba saboda da na tashi na ke zuwa kitchen domin samar da abin buɗe baki ban taɓa cin karo da kiran nata ba sai yau.

  Tun da na zauna a wajen nan ban yi dariya ba. Tun kafin ya fito na ce ma Jidda ta zuba ma kanta da Baby sai ta kalleni kafin ta ce" Umma Abba fa? Wani kallo na yi mata kafin na ce" Kar ki ci ki tsaya jiran wani Abba."

Ita kanta na san ta yi mamaki domin sai da ta kalleni ni kuma na kauda kaina ina cin alalen da na ɗumama sai ruwan tea wanda ban saka madara ba na ke sha dashi Baby dai sai cin ƙwanta ta ke yi ba ta damu ba Jidda kuma jikinta a sanyaye ta ke kurɓan tea ɗin da take sha tare da buredi ni kuma a raina ina ta roƙon Allah ya sa kar Yallaɓai ya tashi yau sai dai ya yi ɗaure sai dai addu'ata ba ta karɓu ba sai ga shi ya fito ya na sanye da jallabiya mai ruwan ƙasa Baby na ganin shi tana ƙoƙarin miƙewa ban san lokacin da na daka mata tsawa ba.

"Ke koma ki zauna ko na saɓa miki."

Haka na faɗa cikin zare mata ido. Daga Yallaɓai har Jidda da kallo suka bini, ita kuma sai ta kalleni ta ruɗe har ba ta san kafarta ya ture tea ɗin gabanta ba. Sai ga shi ya malale min a saman cafet kallon tea ɗin na yi yana gangarowa wani abu na tokaremin zuciya.

Ganin irin kallon da na ke yi ma Baby ne ya sa Jidda ta yi sauri miƙewa ta na faɗin" Ki yi hakuri Umma bari na gyara wajen."

  Yallaɓai na tsaye hannunsa harɗe a kirjinsa ya na bin mu da kallo barin ma ni.  Kawai sai na yi kyafci ina kallon Baby da ta yi kamar za ta yi kuka na kaɗa kai kafin na ce" Lalle ko za ki ci ubanki Maimuna"

  Ta na jin abin da na ce ta barke min da kuka, tsawa na ƙara daka mata kafin na ce" Za ki yi min shuru ko sai na zo na tattaki a nan wajen?

  Na faɗa ina mata wani kallo, Sai kawai Yallaɓai ya kira ta sai ta kalleni ta kasa tashi shi kuma sai ya ce ta zo mana ya na kiranta ganin na kauda kai ne ya sa ta tashi ta nufe shi ta na kuka ta faɗa jikinsa ya rumgumeta yana faɗin" Shii Umma ce! Kyaleta kun kwance da ita ko?

*****

"Zan kashe wayata yanzu. amma ki kunna data ki hau whatsApp na tura miki saƙo."

Ko kafin na ce wani abu ta kashe wayarta.  Ni fa na gama sakankancewa daman ba alheri Ma'u za ta nuna min ba. Amman ban taɓa tunanin ganin abin da na gani ba. Jikina na rawa na buɗe data saƙonni na shigowa amma ba ta su na ke ba Ma'u na ke nema ina ko ganin ta turamin abu kamar hoto na faɗa hannuna na rawa na danna sama yana buɗewa.

Wallahi tallahi yana buɗewa ne amma kamar yana buɗewa da gudun numfashina ne.

Ya na gama buɗewa na ji kirjina ya amsa. Kaina ya sara, hannunawana sun fara  ƙarkawa saboda jikina da zuciyata suna rawa ne a lokaci ɗaya a lokacin idanuwana sun firfito ba domin na ji mamakin abin da na gani ba ne. Sai domin ban taɓa tsammacin shi a lokaci kusa haka ba. Ina wannan rawan jikin da na zuciyan kiran Ma'u ya sake shigowa ban ɗauka zan samu kuzarin ɗaukan wayarta ba amma sai gashi na ja na ɗauka na kuma ƙarata a kunnina duk da yadda zuciyata ke gudu da sauri da sauri.

  "Ina fatan kin ga irin kyakyawan albishirin ɗin da na ke so na gaya miki ko Sadiya?

Runtse ido na yi zuciya na fat fat! Amma sai wata zuciyar ta ce Sadiya kar ki bari a ga gazawarki daman shi Ma'u take jira kamar an dake ni na dawo hayyacina sai na saki wani mirmishi wanda ya fi yin kuka daɗi na ce" Haba ai kin makaro Ma'u domin Yallaɓai ya riga ki yi min wannan albihir ɗin'

Shuru ta yi domin ni na san ta yi mamakin jin kalamaina. Ban bari ta ƙara mgana ba na ce" Kin yi gaggawa Ma'u da kin jira da ni da kaina zan kira ki na faɗa miki Yallaɓai YA ƘARA AURE"

Ban ƙara ba ta wata damar mgana ba na cigaba da faɗin" Walimar da na shiryama na a gida saboda Anniversary ɗin mu ne da kuma taya shi Murnan ƙaruwan da ya samu na aure."

Ina gama faɗin haka kit na kashe wayar saboda sai na ji kamar santsi na ja na ina shirin na sumulmiyo daga kan kujeran da na ke zaune. Sai na kama jikin kujeran da hannuna ɗaya na ƙanƙame jikina ba inda ba ya rawa. Zuciya ta da tunanina sun tsaya waje ɗaya cak na kasa yin ma wani tunani. Ji na ke yi kamar ina zaune ne amma jiri na ke gani shi ya sa na ƙamƙame kujeran da nake zaune amma ban san lokacin da na ji na sulmiyo ƙasa ba.  Sai ga ni zaune a kan mazaunaina a ƙasan tayel ina kokawa da numfashina wayata ta yi zaman dirshan a kan jikina na saka hannunawa da suke rawa na ɗauka na buɗe na koma whatsApp na shiga kan sunan Ma'u ina kallon hoton da ta turamin sai a lokacin na lura da in da Ma'u ta ga hoton.

"Allahu Akbar alƙwarin Allah ya tabbata. Congratulation Mrs Yusuf Muhammad(Tafida)."

An ce wai ka yi ma hawaye rahama ne. Sai yanzu na amince da wannan mganar, na kasa jin kuka ya taho min ma idanuwana sun ƙeƙashe.

Shi kenan ta faru ta ƙare an yi ma mai dami ɗaya sata. Daman shi ne suprise da Yallaɓai ya ke ta faɗin zai ba ni? Lalle ko na karɓi kyakyawan suprise.

Ban san lokacin da ya shigo gidan ba domin ban ji ƙaran buɗe get da shigowar motar sa ba ba.  Sai da na ji lokacin da ya ke saka ɗan makulli yana ƙoƙarin buɗe kofar falon kamar an jani an mikar dani tsaye sai ga ni a tsaye a kan kafafuna. Wayata kuma ta na jimƙe a hannuna. Ya buɗe kofar kenan ya shigo ni kuma sai na fara takawa ƙwas ƙwas ina ji jikina na rawa amma na daure na isa ga makunnin wuta na kunna dai dai yana ƙoƙarin ciro wayarsa daga aljihu domin haska fitila.

Haske ya gauraye falon. Ya bi ko'ina da kallo dai dai lokacin kuma wasu daga cikin bloons ɗin da na saka afalon suka fashe ji ka ke yi tus! Tus! Sai da ya ɗan waiga sannan  ya juyo yana mai sauke kallon shi a kaina dai dai ni kuma ina tsaye a gaban shi na harɗe hannayena a bayana.

Na ƙasa takawa zuwa gare shi,  saboda sai na ga kamar ba Yallaɓaina bane kamar wani ne wanda ban saba dashi ba, sai na ke jin kamar wannan Yallaɓan yanzu akwai wata tazara da ya shimfiɗa a tsakanimu daga yau.

Kafafuna sun yi sanyi kamar gara ya kama su in na ce zan cire ƙafa zan iya zubewa saboda firgici.

Shi ma sai na ga ya tsaya yana kallona amma kuma bai tsawaita ba da sauri ya kauda kanshi. Mirmishi ya ke gayyato ma fuskarshi sai dai ban bari ya gayyato ma kanshi ba ni na fara gayyato ma kaina mirmishi lokaci ɗaya ina faɗin.

"HAPPY 15 YEARS  WEDDING ANNIVERSARY YUSUF MUHAMMAD TAFIDA."

Na faƊa ina kallon ƙwayar idanuwanshi. Yadda ban je gare shi domin na rumgume shi ba. Shima bai yi saurin takowa gare ni ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya na mai ijiye ledojin da ya shigo da su a hannun shi a ƙasa wanda ban san abin da ke ciki ba.

Kafin ya ɗago kansa cikin ƙwayar idanuwanshi na ga rauni. Kasala tsoro da wani abu da na kasa ganewa. A kuma yanayin ya  kira sunana cikin wata irin muryan da ban taɓa sanin Yallaɓai  na da ita ba.

"HALIMA."

Zan iya kirga sau nawa Yallaɓai ya taɓa kira na da sunana Halima, a da in ya kirani ina jin kaina ya yi girma. Amma ban da yau domin sai na ji kamar ya kwarara min ruwan zafin a cikin jikina. Har ina jin turirinshi da hucin shi daga fatar jikina. Sai na ji kamar komai ya na sauyawa kamar  duk wata kyakyawan alaqa da muka gina ta tare da Yallaɓai ta na zagwanyewa tana komawa ruwa. Kamar kuma ruwan ya fara zuba a ƙasa yana  kwarara da ƙarfin daga ni har shi ba za mu iya tare shi ba.

****

Sadiya ta."

 

Ya kira sunana cikin raunin murya sai na ɗaga ido na kalle shi kwarmin idanuwana suna mai cika kwallah.

"Sadiya wallahi ban ɓoye miki wannan auran da wata manufa ba, sai domin na kasa.  Na Kasa jarumtar sanar da ke na ƙara aure. Ban san da wata kalma zan yi amfani da shi ba,ban kuma san ta yadda za ki karɓi mganar ba. Ba na so na faɗa miki wani abu da zai ɓata farincikin ki na wannan ranar. Ban san dalili ba sai na ji ina jin kunyarki. Ina jin kamar ban kyauta miki ba, har ma a cikin kwanakin nan Sadiya sai na riƙa ji a ƙasan zuciyata kamar na ci Amanarki ne, don Allah ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki ya fe mini don Allah SADIYA TA."

Ya ƙarishe faɗa ya na mai ɗora fuskarsa a saman tafukan hannayena ba kuka ya ke yi ba amma ina jin hucin numfashinsa lokaci ɗaya da bugawar zuciyarsa. Yau fa ban san me ya faru dani ba, kamar ruwa ruwa da an fara mgana sai na ji kamar na fi kowa rauni a duniya sai na fara kuka yanzu ma ɗin ma hawaye nake yi, ina danne abin da ke taso mini a cikin zuciya ta. Kai na ƙara yarda da cewa kishi cuta ne kishi masifa ne da bala'i ne domin a lokacin ji nake yi ko na ce gani na

ke yi yadda ya kwanta a jikina yana lallashina wata rana fa zai kwanta a jikin wata itama ya na lallashinta ko? Kawai sai na ji zuciyata na rufewa da kanta, ƙuncin da ya fara barina na ƙara ziyarta ta.

Bai san ina kuka ba sai da ya ji ɗigan hawayena a saman hannunshi na dama da ya sauke shi a saman cinyata. Da sauri ya ɗago ya na kallona ai sai ya ga ina hawaye wasu na koran wasu da rawan jiki ya miƙe zaune ya samu hannun kujeran ya zauna ya mai sanya yatsun hannunsa  ya na share min hawaye amma kamar sun sani ya na share min wasu suna ƙara ɓulɓulowa.

"In kina kuka Sadiya ta. Ni me kike so na yi?

Haka ya faɗa ya na share min hawaye, kawai sai na fashe da kuka har da buɗe murya saboda ji na yi kamar in ban fittar da kukan ba zan iya mutuwa, tashi ya yi a ruɗe ya cicciɓeni nii ya koma ya zauna ya ɗora ni bisa jikinsa ya rumgume yana ta share min hawaye, yana kuma lallashina ni bai ma san ma lallashin na shi ke ƙara sakani kuka ba, ina shessheƙan kuka na ƙwaɓe hannun shi daga saman fuskata ya ƙara kawowa na ƙara kwaɓewa sai ya tsaya yana nleƙen fuskata da na ke boyeta a saman ƙirjinsa.

Sai kawai ya ɗaga hannayensa sama yana faɗin" To na bari tunda ba ki son lallashin."

Saki na ya yi sai gashi na zamiye kamar zan faɗi kasa kuma shi bai riƙe ni ba, ganin zan sha ƙasa ya sa na ƙamƙame shi ina kallon shi ya na murmishi ya ce" Na kawo hannu ki ture ni?

Ya faɗa ya na kallona wani abi ya soki zuciyata a raina na ce ai in amaryansa ce ba zai bari ta kai ƙasa ba. Kawai sai sai na ƙara saka masa kuka lokaci ɗaya ina saka duka hannayena ina dukkansa a ƙirji bai hanani ba sai da na yi har na gaji sannan na koma na lafe a saman kirjinsa ina maida numfashi hannayena suna zagaye a wuyansa.

Sai da ya ga na yi laushi sannan ya saka hannuwansa ya tare ni sosai a saman jikinsa bai sake yi min mgana ba amma hannunsa guda ɗaya da ke bayana da shi ya ke ɗan bubbugamin bayan alamun lallashi, ina ta jan majina da jan numfashi cikin lokaci kuma sai kukan nawa ya ɗauke na koma ina ajiyar zuciya, har kuma na koma na yi lamo idanuwana suna lumshe amma ba barci nake yi ba. Mun zauna a haka sama da awa ɗaya na san hannayensa da kafafunsa sun gama sandarewa da gangan na ƙi sauka a raina na ce gwara duk na gama more jikin ko ta zo sai dai ta samu saurana.

 

Kuma na samu natsuwa sosai fiye da tsammani na. Ba tare da ya nuna ya gaji ba na sake shi ya saka hannu zai riƙe ni na ce" Zan ta shi.'

Sai ya taimaka min na miƙe hijabin jikina duk ya bushe da ruwan hawaye shima miƙewa ya yi ina gani yana juya wuya da hannayena. Sai da na yi dariyan mugunta a raina, ban ce masa komai ba ya ga na fara ta ku zan bar falon sai ya biyo bayana ya na faɗin"

"Sadiya ba mu karya ba fa yau"

Sai a lokacin kuma ya na mganar na ji cikina na juyawa sai na juyo muna fuskantar juna kafin na ce" In soya ƙwai mu sha tea."?

Na tambaya cikin sarƙewa muryan. Ya ƙariso gabana ya kuma saka hannunshi ya riƙo hannayena lokaci ɗaya ya na faɗin" Za ki iya?

Ko na kama miki?

Kai kawai na gyaɗa masa alamin zan iya. Amma bai bar ni ba duk in da na bi yana bi na, hijabin jikina ma shi ya cire min tare muka soya ƙwanan ko na ce shi ya ma soya a falon yara muka karya dka da shima bai ja ni da hira ba amma zai kalleni da kulawa in ya ga na yi shuru na kasa kurɓan tea ɗin

"Are you ok?

Da kulawa ya ke tambayata amma ga ni na yi ni da ya yi ma kishiya sai na ga kamar tambayar ta renin wayau ne shi ya sa na bi na haɗe rai, duk da haka bai ƙyaleni ba bayan mun gama shi ya kwashe komai ya kai kitchen ya dawo ya iske ni dafe da kai ya na tambayata na ce kaina ne ya fara ciwo jikinsa na rawa ya je ya kawomin panadol ya ɓallo ya ba ni tare da ruwa na sha ya kuma riƙe ni har bedroom ɗin mu na kwanta na ya rufa ma ƙafafuna blanket.

"Ki kwanta ki ɗan huta ina ga kukan da kika yi ne ya sa ka miki ciwon kai."

Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai duƙawa ya sumbaci goshina. Ya juya zai fita sai na riƙe masa hannu sai ya juyo ya na faɗin" Me kike so uhm?

Sai na ce"Ba za ka fita ba ne?

"Ko zan fita sai zuwa anjuma."

Sai na gyaɗa kai sannan na sakar masa hannu

"Menene ko kina son wani abu ne?

Sai na girgiza masa kai alamun babu, sai ya ƙara dawowa ya duƙa ya sumbaci bakina, har zai tashi na riƙe masa wuyan rigarsa da hannuna guda ɗaya na ɗago kaina nima na sumbaci bakinsa sannan na sake shi sai kuma da sauri na juya masa baya har ina runtse ido kamar na yi abin kunya na san ya na ta kallona sannan na ji sautin mirmishinsa kafin na ji takunsa da fitarsa lokaci ɗaya ya na faɗin.

"Ina son ki Sadiya ta."

"Ina sonka Yallaɓai na."

Na faɗa a hankali tare da jin wasu tasowar wasu hawayen amma na danne. Ni fa sai yanzu da kishiya ta faɗo kaina na fahimci halin da waɗanda kishi ke saka su kashe miji ko su illata kishiya, a da in na ji labari in ta mamaki ina zaginsu a raina har ina ji ma a tunanina kawai saboda namiji sai mace ta haukace har da kisa. Wato daga ranar da na san Yallaɓai ya zama namu ba nawa ba na fara yi musu uzuri da gaske ba sa cikin hayyacinsu suke ba. Sheɗan na ƙawata zafin kishi, ka ji kamar ka yi hauka, ka koma kana ganin hotuna kala kala waɗanda in ba ka da imani tsab za su iya saka ka aikata abin da za ka dawo kana nadama. Ka koma kana ganin mutane dishi dishi tsabar kishi, zuciyata ta riƙa suya ta na kai ka in da in ka hasaso za ka ji kamar kowa ma na duniya ya mutu duk a huta. Ni kaina ba domin Allaah da addu'ar da na riƙa yi da dauriya ba da tuni an ji kanmu ni da Yallaɓai tsabar yadda na ke jin haushinsa sai sheɗan ya sarrafa tunanina na yi masa illa.

"Astagafurillah."

Na furta a fili saboda tunanin da ya giftamin a fili na furta" Ya Allah ka sassautamini wannan zafin kishi. Sannan ka  tsare ni da aikata abin da zai jawo min nadama a rayuwata."

Na duba wayata ban gani ba sai na tuna na baro ta can falo sai na koma na kwanta na runtse ido ina karanto suratul Jumma'a tirya tiryan ina cikin yin karatun barci mai cike da natsuwa ya kwashe ni ban farka ba sai sha biyu da wani abu na rana.

****

Ni kuma ina fita daga koridon na buɗe kofa na tsaya a ƙofar bedroom ɗin na kasa shiga, dafe kirjina na yi jin kamar zuciya ta za ta faso ta fito saboda yanayin da na ke ciki, duƙawa na yi ina maida numfashi sama sama kamar wacce ta yi gudun tsere ji nake yi kamar sheɗata na neman ɗaukewa na ma kasa iya daidai ta yanayina ballatana har na tura ƙofa na shiga ɗakin, ina duƙen ban sani ba sai kawai na ji an buɗe kofa Yallaɓai ya bayyana a gabana. Ɗago kaina na yi daga duken da nake a kan gwiwoyiyina ina kallon shi, na ga lokacin da ya ɗan buɗe ido cikin mamakin ganina a wajen, ni kuma kayan jikinsa na ke kallo wata shadda ce sabuwa ce mai ruwan sararin samaniya ɗinkin zamani ne, har saman kaina na ke jin ƙamshin turaran Yallaɓai har kafarsa sabon takalmi ne domin ni ban ma san ya siya takalmi sabo ba, kamar wani cuta ina ganin Yallaɓai sai na ji kawai ina haƙi, daga tsuggune kamar ina ganin hajijiya ne ma.

"Sadiya lafiya? Me kike yi anan?

Ya faɗa ya na kallona yana ƙokarin shima ya duka shima da sauri na yi ƙoƙarin na miƙe kawai sai na ji juwwa ta ɗauke ni na yi baya zan faɗi da hanzari Yallaɓai ya taro ni, nima sai gani na ƙamƙame hannayensa ina cigaba da haki kamar mai cutar Asthma saboda na ɗauka zan faɗi ne, ni fa gabaɗaya ji na ke yi kamar wata cuta ta kamani, kuma irin cutar da ban taɓa samun kaina a cikin sa ba, ina tunanin cutar yau ce ta kamani.

"Ba ki da lafiya ne?

"Subhanallah."

Na ji yo Yallaɓai na faɗa Sama sama ni dai ban dawo hayyacina ba sai da na ganni zaune a gefen gado, kitchen ya koma ya ɗauko min ruwa mai ɗan sanyi ya buɗe min ya kuma kafa min a baki ya ce na sha. Na ɗauka ban ji ƙishi sai ga shi na ɗaga roban ruwa na dire bakomai a ciki shi kan shi Yallaɓai da mamaki ya ke kallona Allah ya taimake ni sai na fara dawowa hayyacina na ji numfashina na daidaita sannan na daina hakin nan, kuma bakina bai bushe yanzu ba sannan ina jin maƙogwarona ya daina kartamin ɗin da ya ke yi ɗazu.

  "Sadiya."

Yallaɓai ya faɗa ya na durƙushe a gabana lokaci ɗaya kuma ya na kallona sai na ɗago ina kallon shi, yadda kuka san na gaji haka na ke jin duk jikina ya yi sanyi kamar an yi min dukan tsiya. Fuskata ya saka hannu ya na shafawa har ya na ɗan tapping ɗin shi da hannun shi sai na ƙara buɗe idanuwana ina kallon shi amma ban yi magana ba.

"Me ke damun ki?

Haka ya faɗa cikin kulawa, a cikin zuciyata na ke maimaita Hasbunallahi wa'niimal wakel. Sai kuma na ji nauyin jikina ya ragu sannan bakina ya saki numfashina ya daidaita, Yallaɓai ya tashi tsaye ya saka hannunsa guda biyu ya ɗago duka kafaɗuna tsaye lokaci ɗaya ya sakani a jikinsa ya rumgumeni ƙamƙam a cikin jikinsa nima ban san lokacin da na miƙa hannuwana na zagaye bayan shi na shige jikinsa sosai kamar zan tsaga jikinsa na koma ciki, shi kan shi ya ji yanayin riƙon da na yi masa duk yadda na so kar kuka ya zo min duk yadda na so kada yau ɗin nan na raunana sai da raunin zuciyata ya rinjayeni sai kawai ji na yi ina kuka har da shessheƙa, hawayena suna sauka a saman kafaɗan shi, ko bai faɗa min ba ni na san jikin Yallaɓai ya yi sanyi, domin kansa na saman kafaɗata kawai ya na riƙe da ni amma ya kasa iya mgana ni kuma ina ta kuka yi yi har da kamar zan shiɗe, kuma in za a kashe ne ba zan iya cewa ga dalilin kukana ba kawai ni dai a raina ji na ke yi kamar na fi kowa na duniya nan shiga matsala, kuma ina ji kamar Yallaɓai zai yi min nisan da tun da muka yi aure bai taɓa min irin shi ba.

Bai hana ni kuka ba sai da muka yi kusan mintina goma a haka, daga ni har shi muna ji ana ta kiran wayarsa da ke saman side drower ɗin gadonmu. Amma bai sake ni ba har sai da na gaji da kukana na yi shuru ni ce ma na sake shi tuna cewa ana can ana jiran shi a waje sannan ita kanta tana can ta na jiran sa. Ban kalle shi ba da sauri na juya baya murya ta shaƙe ina faɗin.

"Su Tariq na waje suna jiran ka."

Na faɗa lokaci ɗaya ina goge hawayena da hannuna guda ɗaya. Ƙaramar jakarsa na gani a saman gado alamun ya gama haɗa kayan shi da zai bukata acan ina kallon jakar sai ga hawaye sharr, amma ina ƙokarin tare su, ya na ƙokarin sake riƙe ni na yi saurin kaucewa ina faɗin.

" Yallaɓai ka je kawai sai da safe."

Na faɗa ina ƙokarin maida kukana da ya taso min amma zuciyata sai da ta rinjayene na fashe masa da kuka na ma kasa iya kallon shi, sai kawai na juya da sauri zan fita amma bai bar ni ba da sauri ya riƙo ni amma ina ƙokarin zamewa daga riƙon shi cikin kuka kamar ina masa magiya na ke faɗin

"Don Allah."

Ina kuka maganar ta tsaya min na kasa cigaba da magana sai ya sassauta riƙon da ya yi mini yana kallona wai ni Yallaɓai ke yi ma kallon tausayi saboda ya san nibɗin abar tausayi ce.

"Don Allah ka ƙyaleni."

"Don Allah."

Na faɗa ina masa magiya kuka na ke yi kamar raina zai fita, sai kawai ya sake ni na juya zan fita daga ɗakin sai ya kira sunana.

"Sadiya."

Sai na dakata amma ban juyo ba, sai dai na saka hanuna guda ɗaya na dafe bakina har sautin kukana ya fito.

"Ki yi hakuri."

"Kin ji."

Wai haƙuri ya ke ba ni? In na ce ban hakura ba zai fasa tafiya ne? Ko kuwa  zai iya maida hannun agogo baya ne, ko juyawa ban yi ba na buɗe kofa na fice sai na rasa ina zani kawai sai na buɗe kofar tiolet na shige na rufe ƙofar da sakata na sulale sai ga ni na yi zaman dirshan a saman tayels ɗin Tiolet ina mai fashewa da kuka da karfin gaske, suya zuciyata ke yi, har hancina na ke jin ya na fitar da wani yaji yaji, idanuwana sun yi min mugun nauyin da na kasa iya juyawasu, kaina na wani irin saramin da ƙarfin gaske, kaina na kasa a cikin gwiyoyina ina cigaba da kukana mai sauti, roƙon da na yi masa ne ya sa ya ƙyaleni na ji fitowarsa daga bedroom sannan jikina ya ba ni ya daɗe a ƙofar tiolet ɗin kafin ya buɗe kofar korido ya fice, ba jimawa na ji buɗe get din sa tunda shima window ɗin makewayin na ta haraban gidan ne, ban san ko shi ya faɗa musu ga in da na ke ba domin can ba jimawa sai ga Farida ta zo har ƙofar tiolet ɗin ta na kiran sunana ban amsa ba, sai ga Sameena, Amina da Rahila kar su yi tunanin wani abu ya sa daga ciki na yi musu gyaran murya.

****

Ya amsa da Amin haka a gajarce, sai na ɗan yi shuru kafin kuma na yaye bargon jikina na sauko da kafafuna daga saman gado na sauke a saman cafet ɗin gefe da gefen gadon.

"Yallaɓai."

"Uhm."

Ya amsa min a ciki hankalin shi har a lokacin na kan wayarsa.

"Na ce ba."

Sai ya ji na yi shuru sai ya juyo ya na kallona bayan ya ijiye wayar a gefen shi, ya na mai kallona kafin ya ce.

"Ina jin ki. Kika ce me?

Kai tsaye na ke kallon shi kafin na ce" Wata shawara na ke so ba ba ka Yallaɓai."

"Ina sauraran ki."

Ya faɗa ya na mai ƙureni da ido amma fa ya wani haɗe rai kamar ya san abin da zan faɗa

"Me zai hana duk ranar girkin ta ka riƙa kwanan ka kawai a can Gwammaja."

Giransa ya tattare waje ɗaya ya na min wani kallo amma ban fasa mgana ta ba.

"Zai fi tunda akwai ɗakuna a can"

"Me ya kawo wannan mganar kuma?

"To ai na ga kana raba mana dare ne da ita. Da zuwan da kake yi kana raba dare barci kawai ke kawo ka nan shi ne na ce duk ranar girkinta ka riƙa kwanciyarka a can har ta koma gidan ta."

Ya daɗe ya na kallona bai ce min komai ba, ni kuma ganin ya yi shuru ya sa na tashi zan fita zuwa tiolet har na ɗan gota shi zaune a gefen gado.

"Kin gama mganarki?

Sai na juyo ina kallon shi kafin na ce" E. Na gama."

Sai kawai na ga ya miƙe ya wani harɗe hannuwansa a saman kirjinsa ya fara takowa gabana cikin wani yanayi, sai na tsaya kawai ina kallon shi ba tare da na yi mgana.

"Sadiya."

Ya kira sunana a kausashe bai ma jira na amsa ba ya ce" Kishi ne ke rufe miki ido ko?

Cikin mamaki na kalleshi ina shirin mgana kawai ya wani ɗaga min hannu a fusace ya ce" Ke kaɗai ce mai bakin magana!? Ko ke kaɗai ce ake yi ma ba daidai ba? Ko ke kaɗai ce ake zalunta ehe?

Ya ƙarishe faɗa ya na mai yi min tsawa, sai na yi baya kawai ina kallon Yallaɓai na kasa mgana.

"Ko domin kin ga bana son ina yi miki faɗa? Ko kina tunanin ina tsoron ki ne? To bari ki ji na faɗa miki ba ki isa ba, ba ke kike aurena ba ni na ke auran ki Sadiya saboda haka ki shiga hankalinki tun kafin ki ɓata mini rai na buɗe miki bakina ba za ki ji daɗi ba."

Sai na fara mamakin sa? To wai ya na jira na ne, me na yi masa da zai wani fara balbaleni da masifa daga faɗin gaskiya ni ma ko a fusacen na kalle shi kafin na ce" To wai me aka yi maka? Daga faɗin gaskiya sai ka fara wasu mganganu da ban gane musu ba! Ni na ce ka yi laifi ne! Rayuwarka ce yadda ka so ai haka za ka tafiyar da ita. Kuma da kake maganar za ka buɗe bakin ka in ka bude ba zan ji daɗi ba, to don Allah Yallaɓai ka buɗe bakin naka ka yi mgana mana sai me?

Na faɗa ina watsa hannayena daman raina a ɓace yake kuma a kusa na ke.

"Ki ka ce sai me ko Sadiya?

Na taso masa ina faɗin" E sai me in ka buɗe bakin? Me za ka faɗa min wanda ayyukan ka ba su nuna min ba. Koma za ka ce ka ce gaskiya na faɗa ina lura da kai kwana biyu nan kake cin abinci kuma ka dawo a kan lokaci kwana biyu kuma kana can Gwamnaja sai dare ka ke dawowa in na yi maka ta yi abinci ka ce ka ci a can, me ya sa ba zan yi tunanin ka raba ma kwanan ba ne kar a cuceta? Ni fa mafita na kawo maka domin kar ma ka yi tunanin alfarma ka ke yi min da kake kwana ranar girkinta a gidana shi ya sa na ce ka je can ka kwana ko ka riƙa tafiya can gidan nata kana kwana babu ruwana tunda in ba ka kwana a nan ɗin ba ba mutuwa zan yi ba, sannan kwanan ma da ka ke yi anan ɗin ba wani amfani kake tsinana min ba."

Raina ne ya ɓaci na riƙa sakar masa mganganu na gama na juya zan bar masa ɗakin sai ya saka hannu ya fizogoni ya dawo dani cikin ɗakin da karfi har ya na hankaɗani na yi baya Allah ya sa ban faɗi ba.

"Ina za ki je! Tun da kin gama fadin na ki sai ki jira nawa Malama."

Ya faɗa ya na nuna min yatsa, sai kawai na koma na yi tsaye na harɗe hannuna a ƙirji ina girgiza jikina kafin na ce" Ai ban hana ka mgana ba."

"Me ke damun ki? Me kuma kike taƙama dashi ne? Tun da na yi auran nan kike bi na da fitina ina ƙyaleki saboda ina ganin kamar ni ne ban yi miki daidai ba, amma me ya sa haka! Me ya sa kike da ɓakin kishi ne Sadiya?

Na buɗe baki na rufe ya fi sau uku ina rufewa na kasa mgana.

"Ni ke kake kira da mai baƙin kishi Yusuf?

"E mana baƙin kishi ke damun ki, kin ƙi ki kwantar da hankalinki ki yi ta zarge zarge. Kar ki manta itama Matata ce kamar yadda kike matata kuma auren da na yi zunubi ne? Ko Allah ya hana ne?

Ai sai kawai na rufe bakina na yi shuru, ganin idanuwan shi sun rufe ya na zaro maganganu.

"To bari ki ji na faɗa miki ba ki isa ba. Ke in har kina da tunani za ki kawo wannan mganar? Gwammaja nan ne gidan Ubana kuma uwata ce ba lafiya ta ke jinya. Matar da kika saka ma ido kike kishi da ita ita ce ta bar komai na ta har da ni mijin da kike takama da ni ta je ta zauna ta na kula da mahaifiya ke ina kike? Ba kina gida akwance ba? Kin taɓa tunanin cewa bari ki je ki taimaka mata! Ko shekaranjiya da na kira ki na ce ki je kin je! Kin je? Na ce kin je?

Ya ƙara daka min tsawa sai na saka hannuwana duka biyu na toshe kunnuwana saboda sosai ya yi min ihu a saman kaina.

"Ki saki kunnuwan ki saurareni da kyau. D ta yi min komai kuma komai za ki ce kin daɗe ba ki ce ba. Kwana kuma babu ruwanki ba ke za ki faɗa min abin da ya kamata in yi ba, in ina son kwana a can ke ba ki isa ki sani ko ki hana ni ba, shawara da zan ba ki ki riƙa saka alheri a cikin zuciyarki Sadiya saboda wata rana kar ki ji kunya."

"Ba ni da alheri a zuciyata ka ke son ka ce mini Yusuf?

Na faɗa muryata na rawa ina nuna kaina.

"To ina alherin. Kin bi kin kwazzabi kan ki tunda na yi auren nan ba ki bar ni na huta ba daga kice na yi miki kaza sai kice ƴan'uwana sun yi miki kaza duk dai na biki da ki yi hakuri saboda a zauna lafiya. In ba zuciyarki ba ta saƙa miki alheri ba yanzu ya kamata a wannan halin ki tare ni da wannan mganar? Gimbiyar da kika tsana ita ce ke son ki tsakanina ga Allah ƴa'ƴanki kamar na ta ta ɗauke su amma ke ko sau ɗaya a zuciyarki ba za ki ɗan mutuntata ba? Tana can ta na wahala da mahaifiyata ko sau ɗaya kin ji a ranki ya kamata ki gode mata! Ai ba ita kaɗai ba ce matata ke ma ɗin matatace kuma akwai haƙƙin mahaifiyata a kan ki Sadiya, kin je? Ba daina zuwa duba ta kika yi ba amma kullum anan gida na ke barin ki kwance amma saboda ba ki da kunya har kina tara ta da wata mganar banza saboda kin ga na yi miki shuru? To ki fita daga idanuwana ki kuma fita daga abin da ya shafe ni da matata babu ruwanki, kamar yadda kema kika ce na daina saka ki a lamarinta tun a baya to kema babu ruwanki da sha'aninta ko wani abu dake tsakanina da ita. Ni ne na ijiye ki, da ni za ki yi ba ita ba."

Ko kafin ya gama mganganunsa na durƙushe a ƙasa ina kuka mai sauti lalle duniya juyi juyi wai ni yau Yallaɓai ke faɗa ma ba ni da alheri a zuciyata.

Ina kuka na ɗago ina kallon shi hawaye wani na koran wani cikin shaƙewar murya na nuna kaina ina faɗin" Ni ka ke faɗa ma ba ni da alheri a cikin zuciyata Yusuf? Ni Sadiya?

"E ke kika ja. Me ya sa zuciyarki ba ta ba ki damar ganin alherin mutanen da ke tare da ke? Kishi hauka ne Sadiya?

Ya sake taso min babu nadama ma a cikin maganganun sa sai kawai na sake fashewa da kuka wani abu mai ɗaci na sukan zuciyata.

kawai sai gani na na yi na miƙe ina faɗin" Yau ni kake yi ma gorin ban kula da Nene ba Yusuf? Ni kake yi ma gori?

Sai ya yi shuru bai yi magana ba sai kawai na yi murmishin takaici ga hawaye wasu na korar wasu, sai kawai na kaɗa kaina kafin na ce" Zan faɗa ba domin ina so ka yarda da ni ba. Tunda Nene ta kwanta asibiti har ta dawo gida ban taɓa fashi ba, ko ban je na kwana da ita a yanzu a baya in ka manta na yi ƙila sama da abin da ka ke jijiyan wuya matarka ta yi. Mganar ban je Gwammaja ba ranar kuma ba ni da lafiya ne kwanciyar da ka ga ina yi ba ta lafiya ba ce, kuma na yi ta kiran wayar ka na faɗa ban samu ba ne, shi ne ka ke tunanin da gangan na ƙi zuwa? Kai iya naka zuciyar alherin kenan Yusuf?

Na faɗa ina kallon shi, ina kuka saboda zuciyata ma zafi ta ke yi min ina numfashi sama sama kamar mai ciwon Asthma."

"Wa kika faɗa ma ba ki da lafiya! Kin faɗa mini? Ko ina da Allah musuru ne da zan san ba ki da lafiya.?

Ya faɗa ya na kallona amma ya ɗan sassauta muryan shi.

Kawai sai na kalle shi, sai ji na yi kamar juwwa za ta kwashe ni sai kawai na taka na fice daga ɗakin ina ji kuka na taso min daga ƙasan raina falon yara na koma na zauna na ci kukana kamar zan shiɗe, na tabbata in na cigaba da kuka nan zafin da zuciyata ta ke yi za ta iya bugawa na mutu Yusuf ba shi da asara. Ni wai yau Yallaɓai ya kalli tsabar idona ya na faɗa mini matarsa ta yi masa komai wato ni kuma ban yi masa ba kenan ya manta tarin alherina a gareshi yau ni ce na zama mara zuciyar alheri, ina hawaye ina tuna baya, akwai wani lokaci a baya lokacin na haifi Jidda Nene ta yi wani ciwon kafafu mai zafin da ko bayi sai an kaita ni na koma Gwammaja da ga ni har Yusuf muna kwana acan ina kula da ita. Lokacin Mimisco ba su kasar ita da mijinta Anty Bahijja da Anty Maimuna kowacce na da iyalanta Halima ce lokacin kuma ta na makaranta ni ce na zauna da Nene har ta samu lafiya sannan na koma gidana a lokacin Yallaɓai ya ce na gama masa komai a duniya shi ne yau zai manta baya ya kalli tsabar idona yana faɗin matarsa ce ta yi masa komai ni kuma ban yi masa ba tunda zuciya ta ba alheri a cikinta, anan na kwana a falo a kan kujera ina kuka kukan baƙin ciki da takaici dare kuma mafi tsawo a wajena, ya ce wai daga na ce ya yi min kaza sai na ce ƴan'uwan sa sun yi min kaza ban da namiji mai manta alheri ni me na ce sun yi mini? Ya manta yadda a baya na bauta musu na yi musu biyayya, amma yau duk ya manta sannan ya ce ni na tsani matarsa yaushe na ce na tsane ta? Kawai dai laifin nawa ne ya yi masa ƙaranci shi ya sa daga ya ce na yi kaza sai ya ce na yi kaza amma na kudira a cikin zuciya zan kiyaye ma komai na Yallaɓai yau ko korata ya yi a gidan shi ba zan buɗe baki na ce masa don me ba! Tunda ya iya kirana mara alheri na tabbata a gaba zai iya aikata komai.

****

Ba ni na samu na huta ba sai da yamma shima ba barci ba tun da yamma ta yi. Dawowar su Jidda ya sa na shiga ciki na kwanta na dai samun natsuwa kawai. Allah ya sa in da ya yi fitsarin ya bushe sai na shimfiɗa wani sabon zanin gado, saboda gajiya ana sallar isha'i na kwanta tun kafin Yallaɓai ma ya shigo. Na dai haɗa masa abincin sa a dining,  ni ban san yadda aka yi ba tun da da wuri na kwanta can cikin barci na ji kuka sannan da muryan Jidda ta na kiran sunan Abba sai na farka a firgice lokacin har Yallaɓai ya farka shima kuma ya kunna hasken ɗakin ma.

   

Waya ta na jawo a gefen gado na duba lokaci ɗaya da rabi na dare. Hankalina ya tashi na ɗauka wani abu ne sai da na ga Yallaɓai ya buɗe ƙofa sai ga Jidda ta ɗauko Khalipa ya na kuka ya na ganin uban ya maƙale masa ya na kuka, shi kuma Yallabai sai ya rumgume shi ya na faɗin.

"Shii ga Abba nan shii."

"Abba ya tashi ne ya na ta kuka ya na cewa sai an kawo shi wajen ka."

"To Jidda je ki kwanta. Sai da safe."

"Sai da safe."

Ta faɗa kafin ta juya, shi kuma sai ya rufo ƙofar ya ɗauko Khalipa, ina zaune sake da baki ina kallon abin mamaki yau ɗin ma wataƙila kamar kullum ya fara barci ne aka kai shi ɗakin su Jidda shi ne ya na farkawa ya ga bai ga Uban ba shi ne ya saka musu kuka.

Na kasa magana ganin Yallaɓai ya kwantar dashi a tsakiyar mu, har ya na lulluɓe shi da bargo.

Zuciyata ta ciwo ni yau ko ɗana ne sai na yi maganinsa ballanta ɗan kishiya. Ina iya ƙoƙarina amma yau kam an zo ƙarshe.

A fusace na miƙe sanye na ke da doguwar rigar barci hulan kaina ma ta saɓule. Kitson kaina shiko ne har ya ɗan fara ma tsufa tun da ban yi kitson bikin nan na Rano ba.

"Me hakan ke nufi Yallaɓai?

Na faɗa ina kallon shi, ƙoƙarin  kwanciya shima ya ke yi kafin ya ce" Zai kwana tare damu. Me ya sa kike tambaya?

"Saboda ban gane ma'anar abin da kake yi mini ba."

Sai ya kalleni kafin ya ce" Me ye ba ki gane ba? Kwanan Khalipa tare da mu?

"E."

Na faɗa afusace saboda na fara harzuƙa ma da tambayoyin shi.

"Miye a ciki? Ai ba yau aka fara ba ko? Kin san ai Khalipa ba ya iya barci sai tare da ni ko can gidan ne ita kanta Mamansa ta san haka."

Ya na gama faɗin haka ya koma ya kwanta ya na faɗin" Ki rage mana haske."

Sai na ga yaron ya yi shuru Yallaɓai na kwanciya ya wani maƙale shi, baki na saki ina kallon shi, na ma kasa magana amma na ji a raina yau dai sai dai Yallaɓai ya zaɓa ko kwana da ni ko kwana da ɗansa.

"Yallaɓai ni ce zan fita na bar maka ɗakin ko kai da ɗanka ne  za ku fita ku bar mini ɗakina?

Na faɗa kai tsaye ina kallon shi, sai ya yi shuru bai motsa ba. Ina ganin haka a fusace na fizgi filo na kuma janye bargon da suka rufu da shi da ƙarfi ina faɗin" Zan bar muku ɗakin."

Sai kawai na ga Yallaɓai ya miƙe a fusace ya riƙe bargon da na fizge ya na faɗin.

"Sadiya me kike shirin aikatawa haka?

"Abin da ka ji ka gani mana "

Na bashi amsa a fusace saboda raina tuni ya gama ɓaci. Kawai sai ya fizge bargon ya shimfiɗa ma Khalipa. Yaron ya lumshe ido ban sani ba ko barci ya ke yi, har gabana ya tako ya na kallona kafin ya ce.

" Sadiya yaushe kika koma haka? Yaushe kika zama haka?

"Yaushe dai ka zama haka dai Haba ba ka yi mini adalci. A ina ne aka ce dole sai da yaro zamu riƙa kwana? Ko ƴa'ƴana ka fi kowa sani suna shekara uku da wani abu muke raba shimfiɗa da su. Me ya sa shi ba za ku koya masa hakan ba?

"Na faɗa miki a can ma haka ya ke. Ba ki ga yaro ba ne? Zuwa gaba zai daina."

"To ni ina ruwana da can ma haka ya ke yi, ai can ɗin in ya yi wajen uwarsa ne, haba ni fa na gaji na yi kara na yi kawaicin amma ba ka gane ba. To daga yau ta kau in za ka kwana da ɗan ka, ka sauya ɗaki ko ni na bar maka daƙin gabaɗaya amma ba zan ƙara kwana da Khalipa ba."

Har na gama faɗa na ya na kallona. Sai kawai na ga ya yi mirmishi kafin ya ce" Ba sai kin bar mana ɗakin ba, tun da ɗakin ki ne mu za mu fita mu bar miki ɗakin."

"Beter."

Na amsa masa ina girgiza jikina.

"Amma kin ban mamaki, ban taɓa tunanin haka kike ba Sadiya. Ashe gudan jinina ba jinin ki ba ne? Ashe Khalipa ba ɗaya ya ke da Jidda da Baby ba?

"Ɗaya suke domin ko su ba ka ga ina kwana a gado ɗaya da su ba."

Hannu ya ɗaga mini yana cigaba da faɗin" Sai yanzu na gano ki. Baƙin ciki kike yi a kan yara nan Sadiya ba tun yau ba, sai dai ban saka abin a raina ba saboda ina ƙaryata hakan sai ga shi yau kin tabbatar min.'

Ya faɗa ya na kallona sai nima na kalle shi cikin mamakin kalamansa.

"Baƙin ciki? Baƙin cikin me?

A fusace ya ce" Baƙin ciki D ta na haihuwa ke ba kya yi shi ya sa kike jin haushin su Khalipa ashe duk ƙarya ce da kike faɗin  ƴa'ƴana ƴa'ƴan ki ne? Ashe duk yaudara ne? Tir wallahi kin ban kunya sannan kin ba ni mamaki "

Na ma kasa magana sai nuna kaina na ke yi amma na kasa mgana.

"A kan ƙaramin yaro kin kasa ɓoyo kishin ki da baƙin ciki Sadiya. Ban taɓa tunanin haka daga gare ki ba amma ba zan ce miki komai ba sai na gode."

Ya juya zai wuce bakin gadon na sha gaban shi da sauri ina nuna kaina kafin na ce" Ni ce yau ka ke kira ina baƙin ciki da ƴ'ayan ka Yallaɓai?

"E baƙin ciki kike yi in ba baƙin ciki ba me kike yi! To ki sani ba ni na ce ki je ki yi planing ya ba ki matsala ba sannan ba D ce ta kai ki ta baro ba, ke kika kai kan ki kika baro saboda haka ki daina zargin kowa sai kanki, haihuwa yanzu Daugther ta fara ƴa'ƴa kuma ba ki da hurumin tsanar su kuma ba ki da hurumin hana su zama gidan nan domin gidan na uban su ne ba na ki ba "

Kafin Yallaɓai ya gama mgana ƙafafuwata sun kasa ɗaukata sai ga ni zuɓe a kasa. An ce kuka rahama ne sai yau na fahinci haka domin na kasa kuka, ina kallon Yallaɓai baki buɗe na ƙasa mgana amma kalamansa na shiga kaina suna kuma min amsa kuwwa!

Ni yau Yallabai ke ma gorin haihuwa? Ni yau Yallaɓai ke cewa ni na kai kaina na ɓaro?

A gaban idanuwana ina bin shi da kallo ya ɗau Khalipa suka bar mini daki. Ni ce yau na zama yar baƙin ciki a wajen Yallaɓai ya kira ni da kowani suna sannan daga karshe ya ce nan ɗin ba gidan ubana ba ne gidan shi ne.

Na so na yi kuka amma na kasa zuciyata na ƙuna. Baƙin ciki da takaici sun cika min zuciya anan wajen na haɗe kaina da gwiwa na saki kuka amma ba hawaye ina kuka amma kuma zafin da ke zuciyata sai ƙaruwa ya ke yi, har da ihu na yi na kwanta ina birgima amma ban ji ko ƙwatan abin da na ke ji a ƙasan zuciyata ya ragu ba. Barcin da ban koma ba kenan idanuwana biyu a ka yi asuba yadda zuciyata ta soye haka idanuwana suka soye suma.

Ina jin fitan Yallaɓai masallaci da dawowar shi, duk ina zaune na kasa tashi domin sai na ji gabaɗaya jikina ya yi mini wani irin nauyi kamar ba nawa ba na kasa tashi ballanta na shiga tiolet na kama ruwa na zo na yi sallah. Ban iya motsawa ba sai shidda saura na safe na iya miƙewa ina jin kaina ya yi min wani irin nauyi, ina riƙe da shi na shiga tiolet na kama ruwa sannan na yo alwala na zo na yi sallar asuba sai bayan da na yi sallar ne ina jan casbaha na ji hawaye na gangaro min saman kumatuna ban san adadin lokacin da na ɗauka ina kuka ba, Allah ya sa na sakaya ƙofar bedroom ɗin na ji Jidda ta zo ta na bugawa lokaci ɗaya da kiran sunana amma na kasa motsi ina zaune kamar status amma kuka na ke yi hawaye na sauka wasu na korar wasu. Ina jin gwara dai na yi kukan kar baƙin ciki ya kashe ni Yusuf Inuwa ba shi da asara.

Ni yau Yusuf zai kalla ya kirani yar baƙin ciki kalmar ta fi baƙantamin rai amma lokacin da ya yi min gorin haihuwa sai na ji komai ya tsaya mini cak. Lalle na yarda da kalmar nan da hausawa ke yawan faɗin namiji ƙanin Aljali, namiji ba ɗan goyo ba ne  ni Sadiya Sulaiman Yashe ni Yusuf Inuwa zai kalla ya ce ina baƙin ciki da y'ayan shi kuma har ya na ce min haihuwa yanzu matarsa ta fara wato sai dai na mutu sannan har yana mini gorin gida. Kuka na yi ta yi kukan abubuwa da dama ne, na ji gabaɗaya gidan ya yi min wani irin ƙunci ji na ke yi ko numfashin da na ke shaƙa a gidan ma gurbattace ne.

Na daɗe a cikin ɗaki, har wajen goman safe na ji fitan yara zuwa makaranta. Ina zaune a in da na yi salla ina kuka Yallaɓai ya yo wanka ya shigo ya sauya kaya bai ce mini ba ni ban ma kalle shi ba amma na san ya ji yadda na ke jan hancina da macijana ya toshe mini saboda kuka a haka ya sa kai ya fice shi da ɗansa. Ya jima da fita sannan na miƙe ina jin kamar kaina zai rabe gida biyu ga wani maƙaƙi da ke damuna a maƙoshina.

***

Ban zan iya sanin ko na ƙarishe salatin Annabi ba, na sallame salla, da hijabin jikina na fito daga bedroom na buɗe kofa na fito korido shima ya buɗe ta falo ya fito sai muka haɗe.

"Na'am. Ina salla ne lokacin da ka shigo."

"Me matata ta yi miki da za ki kwashi mutane ku je ku dake ta ita da ƙanwarta?

Baki na buɗe ina kallon Yallabai yadda ya yi mini tambayar a kausaahe alamun tabbaci ma gare shi ba hasashe ba. Sai na ma kasa mgana har na buɗe bakina sai kuma na yi shuru kawai.

"Ba da ke nake magana ba kin yi mini shuru kamar wani ɗan iska?

Ya faɗa yana mai yi mini ihu a saman kaina. Kawai sai na ɗaga ido ina mai ƙara kallonsa kafin na ce" Ni ban kwashi mutane su je su dake ta ba. Wa ya ce maka an dake ta? Ni dai na san Munnira sun yi faɗa da kanwarta ta shigo rabo ba ta sani ba ta ture ta shike nan abin da na sani. Kuma ni har ga Allah ba da yawuna Munnira ta yi abin da ta yi ba. Ni da hankalina zan kwashi mutane aje a yi tashin hankali? Me matarka ta yi mini da zafi da zan yi mata haka?

"Wa ya sanin miki. Duk abin da ya faru kina sane saboda ai su Munniran da Hauwa tare da ke suke. In kika tsawarta musu ai za su bari amma da yake kema akwai mugun nufi a ranki. Shi ya sa kika yi shuru sai da abu ya faru za ki zo kina faɗamini wai mai matata ta yi miki da zafi? Kika san abin da ta yi miki domin ni ba makaho ba ne tun haihuwan nan na ga take-taken ki, ko barka sai da na yi ta miki magana kika je, asibiti ma ba ki je kin duba ta ba sai da ta koma gida da na yi magana sai ki ce ba ki da lafiya. To duk na gama gano ki. Kin kuma kyauta da abin da kika yi. Saboda ke an targaɗa mini mata a banza a wofi na gode Sadiya kin ji ko? Na ce Na gode."

Ya faɗa cikin hargagi har yana yarfa hannu. Marwa da Baby suka fito da sauri daga dakin su Jidda suka gan mu cirko cirko ni da Yallabai.

"Ni ce mai mugun nufi a raina?. Ni Yusuf?

Na faɗa ina nuna kaina cikin tarim mamakinsa.

"E ke ce fa, kuma kin aiwatar da nufin ki, kin kyauta. Amma ki sani ba ita kika yi ma wannan tozarcin ba illa ni. In ma kin ji haushi tana ta haihuwan Maza ni ba ki yi mini adalci ba. Domin na shafa faɗa miki da mazan da matan duk ɗaya ne a wajena me ya sa ba za ki yi mini kara Sadiya ki boye kishin ki ba? Abin da kika yi dai dai ne? Abin da kika yi sunan shi ne zubar da ƙima. Watarana in Saudatu ta gan ki   ba ta darajaki ba. Juzt bleme your self domin ke kika zubar da girmanki, ta bi kuma ta tattaka shi."

Wai Yallaɓai har yana nuna mini hannu yana gaggaya mini magana ina kallon shi kwarmin idanuwana suna cika da kwallah.

"Na ɗauka in ina da wani mugun nufi tun a shekaran baya zaka sani ba yanzu ba."

"Da ba ki da shi. Yanzu kika ɓullo da sabbin hallaya marasa kyau. Kin bari sheɗan na zugaki. Tare da su waɗanda kika rike a naki. Na daɗe da sanin saboda ke su Hauwa ba sa zumumci da D amma ban taɓa magana ba. Kuma a adalci ai dake da ita duk ɗaya ne yadda za su yi miki haka za su yi mata. Duk na share wannan ban taba magana ba sai abu ya zo har da duka har gidan ta? To ba ki isa ba yadda kema ban kyaleki ba suma ba zan ƙyale su ba na kira Nasir da Mutaƙƙa kowannen su zai ja ma matarsa kunne. In dai ba za su dauke ki ɗaya da Matata ba to sai dai a raba wannan alaqar taku gabaɗaya tun da ba ta alheri ba ce sai ta sharri."

Ai ban san na kwashe da dariya ba, sai da na ga ina yin ta cikin takaici da bakin ciki hawayen da suka zubo mini na share ina kallon Yallaɓai ido cikin ido kafin na ce"Wannan kuma wallahi ta yi kaɗan. Lokacin da tazo tare ta ganmu kuma wallahi tare za ta bar mu. Zama daram in ji mai naguda."

Na faɗa ina mai riƙe kuguna. Domin na lura an gama shiryaa mai mganganu ni zai zo ya tara mini gajiya to wallahi bai isa ba.

"Ni kike faɗa ma haka Sadiya?

"An faɗa maka sai me? Kai waye? Mijina!

Na yi wata bazawar dariya kafin na nuna shi ina faɗin" Mijina ne kai da muka yi zaman aure na shekaru sama da ashirin ashe kai ba za ka iya sanin abin da zan iya aikatawa da wanda ba zan iya aikatawa ba? Wato duk abin da matarka da danginta suka faɗa akaina shi ne gaskiya a wajenka ko? To bari ka ji na faɗa maka ko na ce na ƙara tunasar da kai ko garke matarka za ta haifa maka na Maza wallahi ko a gefen gyalena da yau ban haihu ba da bakin ciki ya kashe ni. Maganar zuwa barka ban yi niyya zuwa ba ne, duk ita a nata haihuwan ka fahimci ni ban je ba amma a lokacin da na haifi Yumna ba ka fahimci sai da ta ga dama ta zo ba? Ita ka same ta ka yi mata mgana kamar yadda ka yi mini? Wato sai ni ce marainiyar ka dole ka zo ka same ni ka sauke mini magana. To bari ka ji na rantse da wanda raina ke hanun shi ina dai dai dakai daga kai har munafukar matar taka."

"Sadiya."

"Yusuf"

Yadda ya kira sunana cikin tsawa nima haka na buɗe murya na kira sunan shi yana huci ina huci.

Sai kukan Yumna muka ji, can sai na Baby ko ni juyawa ban yi ba shine ya juya yana kallon su yara sun ga abin da ba su taba gani ba.

"Marwa ki ja yaran nan ku koma ciiki."

Ya faɗa yana sassauta muryan shi,

"A shiga da su ciki kuma? Daga baya kenan wai an yi sadaka da bazaawara. Ai sun gama ganin ka, kana ci ma uwarsu zarafi a kan wata banza a banza.'

Na faɗa ina haki saboda ɓacin rai.

"Kar ƙi kara ce ma ta Banza."

"Na ce banza a banza Yusuf don Allah ka ɗauki mataki in ka isa."

Na faɗa ina isa gaban shi na tsaya ina riƙe kuguna.

"Da gaske banza ce tun da ba ta iya ramin kanta sai dai na wani. Kuma wallahi tallahi ba ta isa na amsa laifin da ban aikata ba. Rashin kunya ba irin wacce ƙanwarta ba ta yi mini ba shi ba a faɗa maka ba sai gulma da munafunci?

Na faɗa ina zare masa ido.

"Ki matsa daga gabana kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba ki yi tunani ba Sadiya."

Ya ɗan fara saukowa tun da ya daina ɗaga murya ko saboda yara ne oho. Marwa ta ja su sun koma ciki amma har lokacin ana jiyo kukan su.

"Me zaka yi! Na ce Yusuf me za ka yi?

Na faɗa ina ƙara ɗaga murya ni fa tun da ya jawo wannan faɗan to gwara a yi shi kawai kowa ya san matsayin shi.

"Ƙina so ki ga abin da zan yi ne ?

"E. Ina so na gani. "

Sai ya wani nuna kanshi kafin ya ce" Ni kike tsarewa cikin gadara kina faɗin na ɗau mataki akan sadiya?

"E sai me? Tsoron me zan ji? Ƙarshen mataki kenan ka ce ka sake ni ko Yusuf? To ai ba ƙarewar rayuwata ba ce ta zo in na rabu dakai ba, sai me.'

Kawai sai ya tsaya yana kallona nima ko ina kallon shi ido cikin ido.

"Yau yanzu ka ce na fice maka a gida zan fita. Tun da daman ka ce ba gidan Ubana ba ne."

"To ki tafin mana who stop you? Na hana ki tafiya? The door is open Sadiya. A sauka lafiya."

Ya faɗa yana nuna mini ƙofar falo. Na razana da kalamansa amma ina zuciyata ta ƙekashi ban nuna masa na razana ba, kawai sai na yi mirmishi kafin na ce" Da a ce yau Sulaiman Yashe bai da gida da na sha wulaƙanci."

  Ba ni da kuɗi a jikina daga ni sai hijabin salla na amma ina ganin in na koma ciki zai ga kamar na gaza ne. Sai kawai na wuce har na isa kofa falon sai na juya ina kallonsa dafe da kai a kausshe na ce.

"Ni Sadiya ni yau Yusuf ka kora a gidan ka ko?

"Kin ce za ki tafi kina tunanin zan tsayar da ke ne? Ki sauka lafiya na ce Halimaaa.!

Ya ja sunan shima a kausaahe yana kallona ina kallon shi. Idanuwanshi sun kala nima nawa ya kala ya yi jajir sai kawai na buɗe kofar falon na fice ina jin Marwa ta biyo ni tana Umma Umma.

Sai a lokacin na tuna da ita a fusace na waiga ina faɗin" Ki dauki mayafinki mu bar masa gidan shi Marwa."

"Umma..amm"

"Wallahi zan mare ki za ki taho mu tafi ne ko na yi tafiyata."

"Zan zo."

Ta fada tana zakuɗa goyon ta dake bayanta har ta fara hawaye.

Baby ta fito ita da Yumna ina jin Yallabai ya rike su yana mgana da su kasa kasa.

Marwa ta dauko mayafi ta fito na ji ta tsaya tana mgana da Yallaɓai a fusace na ce" Wai ke ubanki ne da za ki tsaya kina masa mgana?

Ki jira har sai ya kai ga haɗa ki da jami'an tsaro sannan sai ki bar masa gidan sa."

Na ga ya buɗe kofar falon ya fito Yumna na hannun shi tana ganina ta fara Uma tana miƙan hannu na juya zan fita Marwa dake bayana ta ce" Umma ko Yumna ba za ki tsaya ki karɓa ba!

"Ba da ita na zo ba. Saboda haka ba da ita zan koma ba."

Baby ta rigo tana Umma Umma cikin kuka na tsayar da ita da hannu ina faɗin" Kar ma ki ƙariso ki koma nan ne gidan Ubanki nima gidan nawa Uban zan koma ya tattaraku ya kai ma Matar so ta haɗa da farar haihuwa duk ta riƙe "

"Sadiya."

Ya kira ni a tsawa ce, ko kallon shi ban yi ba na fice daga falon ina jin kukan Baby da yadda Yumna ta yanka ihu. Ni kaina duk ɗauriyata sai da na ji hawaye sun kece mini. Wani abu ya tsaya mini kahon zuciya, wai ni ce yau Yallabai ya kora daga gidan shi. Lalle duniya juyi juyi na gaba ya koma baya.

*Ban ce ba wanda ya fini ba, amma na ce alƙalamina na dabam ne, sannan ni a fadata ni ce Sarki sannan ni ce kuma Sarauniya. Kun gwadani kuma kun ga irin salon rubutuna. Ku bani kyakyawan shaida da yaƙini ni kuma zan baku abin da kuke so in sha Allahu. Free pages zai fara zuwa muku ranar 07/04/2025 in sha Allahu, sannan kamar yadda tsarina yake book1 kyauta ne ya yin da book2 and 3 zai zo a matsayin paid kamar yadda muka saba. Sannan za ku iya fara biyan kuɗin karatun ku daga yau har zuwa ranar da zamu gama free pages, babu wasa ko jira a cikin tsarina da ikon Allah cikin ƙankanin lokaci zamu ƙare wannan labarin kamar yadda muka saba*

*Na gode da soyayyarku da amincewarku akan rubutuna Allah ya haɗamu a Aljanna firdausi Amin Amin.*

KAMAR YADDA TSARIN YAKE BOOK 1 ZAI ZO MUKU A MATSAYIN KYAUTA ANAN MANHAJAR MU TA WHATSAPP BOOK 2,3 KUMA TSARIN YA SAUYA. SHI ZA KU SAME SHI NE KAƊAI A MANJAHAR TELEGRAM AKAN FARASHIN #1k KACAL. BABU TSARIN VIP A WANNAN KARON MA, AMMA AKWAI TSARIN SPECIAL GA MASU BIBIYATA A MANHAJAR AREWABOOOKS. KU FARA BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN. *** JAMILA UMAR OPAY KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN KAMAR HAKA.

***.

***.

Y'AN KASUWA MASU ƁUKATAR A TALLATA MUKU HAJOJINKU A CIKIN WANNAN ƘAYATTACEN LABARIN ZA KU IYA TUNTUƁATA KAI TSAYE TA WANNAN LAMBAR. ***

#Labarin Soyayya

#Zamantakewar Aure

#Zumunci

#KISHI

#Janafty

#24/04/2025

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol