Free chapter · Read without an account
ƳAR KARUWA Chapter 3
*ƳAR KARUWA* Arewabook@ayshadansabo
Paid book*
©️ Ayshat Dansabo Lemu ✍🏻
Free pages
Chapter 3
A hankali Hajiya Mardiyyah take taka stairs ɗin benen har ta isa ƙofar shiga bedroom ɗin Abban,ta tura ƙofar ta shige kai tsaye zuciyarta na sake cika da zumuɗin son gabatar masa da zancen haɗin auren da suke son ƙullawa a tsakanin ƴaƴayen nasu ita da Hajiya Barirah.
Ɗakin babu wadatar haske kasancewar Abban ya kashe fitullu masu haske ya bar mai duhun haske,can ta hangosa kwance a saman gadonsa yana riƙe da wayarsa da alamu akwai abinda yake dubawa mai muhimmanci a cikin wayar.Cikin takunta a nutse ta isa bakin gadon ta zauna tana mamakin yadda ya amsa sallamarta can ciki,zamanta a bakin gadon sam bai sanya shi ɗagowa ya dubeta ba duk da cewa tun shigowarta cikin ɗakin wannan sassanyar ƙamshin nata mai cike da sirrika ya gama cika kafofin hancinsa.
"Abban Arfah." Hajiya Mardiyyah ta kirayi sunansa ganin cewa babu alamun zai nuna yasan ma da zamanta a wajen.A hankali ya ɗago idanunsa daga duban wayar da yake ya sauke akan fuskarta yana sake tsuke tasa fuskar da sam babu alamun walwala,cikin muryarsa mai zurfi ya furta,"Ina sauraronki Mardiyyah." Jin hakan ya sake tabbatarwa da Mamie cewa da gaske dai fishi yake da ita,ta kuma tabbatar fishin baya rasa nasaba da kalaman da take zargin yaji ta furtawa Ƴar Karuwar tasa.Saurin ɗauke kanta tayi daga dubansa domin ta tsani irin kallon da yake jifanta dashi,cikin raunana muryarta ta furta, "Don Allah komema nayi kayi haƙuri ka sakar mini fuskarka wannan ɗaure fuskar bana sonsa Abban Arfah,magana nake son muyi mai muhimmanci." Ta ƙare maganar tana kallon fuskar Abban,wanda har lokacin bai sassauta ɗauresa da yayi ba."Nace ina sauraronki Mardiyyah,maganar ɗaure fuska kuma ai kinfi kowa sanin dalilinsa domin ina da tabbacin kinsan naji kalaman da kika furtawa Mamana,Mardiyyah ina gargaɗinki da kiji tsoron Allah akan duk irin ƙiyayyar da kike gwadawa marainiyar Allah ba tare da laifinta ba,ina jiye miki ranar da za ki yi nadama irin wanda ba zai taɓa yi miki amfani ba,sannan abinda ya faru da ita ƙaddara ce irin wanda bai wuce ya sauka akan Arfah ba,don haka ki kula ki kuma iya bakinki." Ya ƙare kalaman yana sake watsa mata wani irin kallon da ita kaɗai tasan ma'anarsa.Zuciyarta ce ta sake cika da wani irin ƙunci,sai dai kuma a yanzu bata da buƙatar su cigaba da magana akan Yarinyar hakan ya sanya ta shanye dukkanin ɓacin ranta wajen yin ƙasa da muryarta ta furta,"Naji Abbansu,ni kaina na sha gwada yadda zan yi na ƙaunaci Yarinyar a cikin zuciyata amma na kasa,tsanar Nuratu da nake ji ba zai taɓa bari na ƙaunaci abinda ya fito daga jikinta ba,kayi haƙuri zan rage dukkanin abinda nake yi domin bazan maka alƙawarin cewa zan iya ƙaunarta irin yadda kai da Hajiya kuke so ba." Ta ƙare maganar cikin karyar da murya tana sake narke fuskarta sosai.Wani irin tsakin tsananin takaici Abbah ya saki kafin ya furta,"Allah ya ganar dake gaskiya Mardiyyah,amma wallahi kina tafka babban kuskuren da nake jiye miki ranar yin nadama." Hajiya Mardiyyah ta sake kwaɓe fuska tana faɗin,"Don Allah Abban Arfah ka aje zancen Jannat a gefe guda muyi maganar daya kamata." Abban sai ya jinjina kansa kafin ya buɗe baki yace,"Ina sauraronki." Hakan ya bata damar fara faɗin, "Dama maganar akan Ammar ne da ƴar wajen aminiyata Hajiya Barirah wato autarta Labibah." Mamie ta ɗan dakata tana kallon fuskar Abban domin ganin a wani yanayi zai amshi zancen? Ga tsananin mamakinta wani irin murmushi taga Abban ya sakar mata kafin ya jinjina mata kai alamun yana sauraronta.Cikin wani irin karsashi ta cigaba da faɗin, "Labibah na tsananin ƙaunarsa kuma nima nutsuwar Yarinyar yasa na jima ina masa kwaɗayin aurenta daya je can waje ya nemo bare,to na fara yi masa magana amma bai wani maida hankali ba,hakan yasa na kawo maganar zuwa gareka domin ka ƙarfafa shi kaga shekarunsa sai ƙara nisa suke amma sam baya son ana ɗakko masa batun aure,ace mutum ya haura shekaru talatin har da biyar amma baya batun aje Iyali sai kuɗi yake tarawa kamar suci kansu,ina tsoron ruɗin zamani da sharrin kuɗi ba tare da aure ba duk da nasan halin kayana baya neman mata,amma auren dai idan yayi ni da kai duka hankalinmu sai yafi nutsuwa da zamansa acan tare da Iyali musamman daya nuna sam ba zai iya dawowa ƙasarsa ta haihuwa ya zauna nan kurkusa ba." Ta sake dakatawa da kalamanta tana sake kallon yadda Abban ya bata dukkanin nutsuwarsa yana sauraron kalamanta.Ganin tayi shiru tana kallonsa ya sanya shi yin gyaran murya kafin ya soma faɗin,"Mardiyyah na ji dukkanin kalamanki,ni kaina na matsu Ammar ya aje Iyali zuwa yanzu,sai dai maganar haɗin da kuke son yi shine bai shafeni ba domin bazan shiga shirginki da Barirah ba,idan har shi ya amince ya kuma ga Yarinyar tayi masa to ni nawa fatan alkhairi ne domin bana son na shiga hakkinsa wajen turasashi auren wacce bashi ne ya ganta yace yana so ba,don haka sai ki jira ya dawo idan sun daidaita kansu sai muyi musu fatan alkhairi,idan kuma ya kawo zaɓinsa matuƙar munyi bincike munga ƴar gidan mutunci ce to ki sani zaɓinsa za mu bashi ba naki zaɓinba." Abbah ya ƙare maganar idanunsa akan Mamien wacce sam ba haka taso ji daga wajen Abban ba.
Cikin son ɓoye damuwarta tace, "Shikenan Abbansu tunda haka kace,In Sha Allah ma Ammar zai amince da Labibah domin ta mallaki dukkanin abinda ake da buƙata a jikin ɗiya mace,fatana dai ka nuna masa ɓacin ranka akan yadda yake watsar da zancen aure,lokaci yayi da ya kamata ace mun fara ɗaukar ƴan jikoki daga garesa domin ga Sameer abokinsa nan Yaransa biyu amma shi ya tsaya shiririta." Abbah ya sake sakin murmushi kafin ya furta,"Har da lokaci Mardiyyah,idan lokacinsa yayi zai yi koda shiri ko babu,mu cigaba da yi masa addu'a tunda Allah ya natsar mana dashi baya aikata zina da sauran ababen ƙi,Ammar nutsatstse ne da nake fatan Ubangiji ya cigaba da kintsa mana shi ya kuma kare Shi daga ruɗin kuɗi da kuma na zamani,domin a yanzu ne yake ganiyan cin lokacinsa,musamman da yake samun manyan kuɗaɗe ina matuƙar son naga ya aje Iyali domin ina tsoron ruɗin zamani ga namiji kamarsa da zarensa ke ja ga kuma kyawu da ƙuruciyar da zasu ja da yawan ƴan mata zuwa garesa,ciki kuwa har da fararen fatan da aikata saɓo baya musu wahala,Allah ya cigaba da tsare masa imaninsa." Hajiya Mardiyyah ta amsa addu'ar kai tsaye da faɗin,"Ameen Abbah,auren dai shine kaɗai abinda zai yi domin ganin ya tsira da mutuncinsa da kare kansa daga faɗawa halaka tunda dai shi ba waliyyi bane, zuwa yanzu dole yana buƙatar mace a gefensa." Abban ya sake jinjina kansa yace, "Hakane Mardiyyah,zan yi magana dashi zan kuma sake haɗashi da Inna domin dama tafi matsuwa taga yayi auren." Daga haka suka cigaba da tattauna batun auren Tilon ɗan nasu namiji guda ɗaya da suka mallaka a duniya.
*********
2:45am
Jannat ce ta farka a rikice sakamakon wani irin kalar hargitsitstsan mafarkin da tayi,ta saki salati tare da karanto addu'a kafin ta kai hannu ta kunna fitillar bedside lamp dake aje bisa saman side drawer ɗin dake gefen gadonta.Haske matsakaici ne ya gauraye ɗakin,ta zuro ƙafafunta zuwa ƙasa kafin ta miƙe akan ƙafafunta ta nufi hanyar toilet tana jin yadda jiki da zuciyarta ke sake ɗaukar rawa.Alwala tayi ta fito ta shimfiɗa abin sallah,hijab ta saka ta fara jero nafilfilin da dama ta saba yinsu domin koda bata farka ba tasan alarm ɗin da take sakawa duk dare dole zai tada ita da zaran uku na dare ya buga.Sai dai kuma ta manta shaf da cewa ta kashe wayar kafin ta kwanta bayan ta share duk wasu saƙwanni ko hotunan da za su cigaba da tuna mata da Aliyu da irin tarin soyyarsa a gareta,koda ta idar da sallar kuka sosai ta dinga yi a cikin sujudarta a gaban Ubangiji tana roƙonsa da yayi gaggawar cire mata soyayyar Aliyu ya kuma bata ikon manta shi cikin gaggawa.Koda ta kammala dukkanin addu'o'inta ta jima tana wani irin kuka mai motsa zuciya,daga bisani wani wahalallan bacci ya sake suranta anan bisa saman daddumar.Kiran sallar asuba da aka doka a masallacin dake wajen gidan shiya tada Jannat,ta miƙe da azama bayan ta karanto addu'ar tashi daga bacci ta nufi toilet domin ɗauro alwala.
Bayan ta idar da sallar ta jima tana tilawar karatun Qur'ani kafin ta rufe ta nufi bed sabida wani irin bacci ne ke fisgar idanunta,tana kwanciya kuwa baccin ya ɗauketa bata farka ba sai wajen ƙarfe tara da rabi na safe.
Wanka ta faɗa a gaggauce tana mamakin yadda ta samu bacci sosai a yau ɗin, koda ta fito direct wajen dresser ɗinta ta nufa tana goge fatar jikinta mai wani irin laushi da sulɓi.Sosai take da wani irin kyawu mai fisgar hankali,kyawu take dashi irin wanda ya amsa sunansa kyau da kuma cikar halitta domin an cika halittarta matuƙa tamkar itace tayi kanta.Kalar farar fatarta mai duhun haske irin wanda bature ke kira da brown skin mai haske ne,sosai take da tsayi wanda ya ƙarawa halittarta kyawu da cikar kwarjini,wani irin tsayi mai kyau wanda sam baiyi yawa ba ya dai dace matuƙa da ƙirar halittarta.bata da jiki sosai sai dai a kirata mai murjajjen jikin dake cike da tsoka ta ko'ina,cikar ƙirjinta da kuma shape ɗin bayanta yakai maƙura wajen sake fiddo zubin kyawun halittar da Allah ya mallaka mata mai matuƙar ɗaukar hankali.Kyakykyawar fuskarta na ɗauke da manyan idanu farare masu wani irin walainiya idan ta juyasu tamkar suna cike da ruwan hawaye,dogon hanci gareta daya tafi zar ga kuma ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da jajayen laɓɓa masu duhu sosai.Gashin girarta dana idanunta sun sake fiddo kyawun halittar fuskarta,ga kuma dimple ɗin da take ɗauke dashi a hagu da dama na kumatunta wanda koya ta buɗe baki da sunan murmushi ko dariya sai sun loɓa.Bata da yawan cikar gashin kai sai tsayi sosai daya sauka har saman kafaɗunta idan ta saki jelar gashin,hakan yasa sam yin kitso bai wani dameta ba.A gaggau ce taja stool ta zauna tare da janyo lotion ɗinta wanda ya amshi fatarta da colour ɗinta matuƙa,ta fara murzashi a hankali bisa lallausar fatar jikinta da kullum cikin glowing yake sabida yadda yake samun gyara da kula.Sosai Jannat ke da son ado da kuma yin gyaran jiki akai-akai,bata iya haɗa wata biyu bata halarci wajen gyaran jiki an murje fatarta da kayan gyara da ƙamsasa fata ba, shiyasa koda yaushe za ka ga fatarta cikin glowing sosai.Koda ta kammala yin shafan wasu haɗin tururaruka masu sanyi da daɗin ƙamshi da Anty Rahama ta sanya aka haɗa musu shi ta janyo ta shafa a jiki kafin ta tabi da body mist,ta miƙe a nutse ta nufi wajen ƙaton drawer ɗin dake manne jikin bangon ɗakin ta buɗesa.Wata riga doguwa ta zaro ta saka tana kallon yadda rigar ta zauna a jikinta,ƙaramin veil ta yafa a saman kanta ta fice da gaggawa domin bata buƙatar Inna ta sake biyo sawunta ta tadda bata tashi ba......✍🏻