Free chapter · Read without an account
ƳAR KARUWA Chapter 5
*ƳAR KARUWA* Arewabook@ayshadanaabo
Paid book
©️ Aysha Dansabo Lemu ✍🏻
Free pages
Chapter 5
A nutse Jannat ke shirya dukkanin kayan data fiddo cikin ƙaramin luggage ɗin zuciyarta na sake cika da zumuɗin son komawa Kd,tana tsaka da rufe luggage ɗin ne wayarta ta fara kukan neman ɗauki.Ta miƙe a hankali ta isa bakin bed inda wayar take a yashe ta ɗauki wayar,ganin wasu ɓakin lambobi na yawo bisa allon screen ɗin ne ya sanya ta bata ɗaga kiran ba sai zubawa wayar idanun da tayi har kiran ya yanke.Bada ɓata lokaci ba wani kiran ya sake shigowa,hakan ya sanya tayi shahadan ɗaga kiran tare da saka wayar a speaker ba tare da tace uffan. "My precious!" Ta jiyo wannan daddaɗan muryar nasa mai cike da aji ya doki kunnuwarta.Wani abu ne yayi tsalle daga cikin zuciyarta ta yadda tayi saurin rintse idanunta jikinta na ɗaukar ƙaramin rawa,bata iya amsawa ba ta cigaba da yin shiru har zuwa lokacin daya sake furta,"Noorie kina jina, talk to me please idan baso kike zuciyata ta buga ba." Yanayin yadda taji muryar tasa tayi zurfi sosai ya sanya jikinta sake ɗaukar rawa zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri.Cikin rawar murya tayi ƙarfin halin furta,"Aliyu why? Meyasa ba za ka ji tausayina ka tayani yin yaƙin da zan fidda soyayyarka a cikin zuciyata ba?Basa sona Aliyu kuma nima sai yanzu na gane cewa bamu dace da juna ba domin duk Iyaye nagari ba za su so ɗansu ya auri Ƴar Karu......" Da wani irin sauri kuma cikin birkitaccen murya A.Wase yayi saurin katse Jannat daga ƙarisa kalamanta ta hanyar faɗin,"Enough! Please Jannatt,ko a tsakiyar gidan karuwai aka haifeki kika girma wallahi summa billahi ba zan taɓa damuwa ba domin kece macen da zuciyata ke so kuma nake buƙatar ki zama Uwar ƴaƴana,meyasa za a hukuntaki da laifin da bake kike aikatawa ba? Please Jannat karki haramta mini jin muryarki da nayi sabo dashi wallahi zuciyata dab take da kamuwa da mummunar cutar da....." Bai samu damar ƙarisa kalamansa ba sakamakon kashe wayar da Jannat tayi baki ɗaya tayi jifa dashi bisa bed ɗin,cikin wani irin yanayi tayi kwance tana sakin kuka mai tsanani da dafa jiki da zuciya.Muryarsa kaɗai da irin kalaman da yake son karya zuciyarta dasu ke son dawo da komi sabo a cikin zuciyarta,ta cigaba da kukan tana jin duk wani rauni na sake rufe zuciyarta.Ta jima tana kokawa da idanu da zuciyarta kafin ta rarrashi kanta ta miƙe ta nufi toilet,wanke fuskarta tayi ta fito tana kallon agogon bangon ɗakin dake buga ƙarfe sha biyu saura.Jiki a mace ta nufi wajen mirrow ta gyara face ɗinta tare da saka kwalli kaɗan domin ɓoye koɗewar da fuskarta tayi sabida kukan data sha,gyalen data rufe kanta dashi a ɗazu ta ɗauka ta yafa a saman kanta ta fito ta nufi ɓangaren kitchen ɗin Inna.So take ta taya Tabawa aiki ko za ta hana kanta tunani,domin tabbas tasan idan ta zauna a ɗaki ita kaɗai tunanin Aliyu da wannan kiran da yayi mata bazai taɓa bari zuciyarta ta huta ba."Uwar ɗakina an fito?" Cewar Tabawa fuskarta na haskawa da murmushi mai faɗi.Jannat ma murmushin tayi kafin ta furta,"Na fito Tabawa so nake yau muyi abincin tare me za a girka ne?" Cike da farin cikin ganin yadda Jannat ɗin ta fara sakin ranta da son danne komi Tabawa tace,"Tuwan shinkafa ce da miyar taushe Hajiya tace ayi,sai kuma tace ayi mata faten dankalin turawa da kaza bamai yawa ba." Jannat ta jinjina kanta tace,"Okay to bari ni nayi faten dankalin in yaso sai kiji da yin tuwan rice ɗin." Tabawa tace,"Aiko na gode da wannan taimakon Uwar ɗakina,Allah ya ƙara miki dangana ya kawo miji nagari wanda yafi Yallaɓai nagarta,kiyi ta haƙuri Jannat ita rayuwa da kike gani dukkaninta jarabawace kuma sai mai Imani aka fi jarabta,wannan abin da ya faru dake ba komi bane domin wasu ma sai a ranar auren ake fasawa,wasu sai an ɗaura a kwance kuma hakan ba shi zai hana Allah ya musanya musu da wanda suka rasa alkhairy ba,don haka kiyi addu'ar Allah yasa hakan shine yafi zama alkhairy a gareku ke da shi baki ɗaya kinji ko?" Jannat wacce ta gamsu da dukkanin bayanan Tabawa sai ta jinjina kanta tana faɗin,"Hakane Tabawa na gode sosai,Allah ya ƙara mini haƙuri ku cigaba da tayani addu'a Allah ya cire mini soyayyarsa a cikin zuciyata da gaggawa." Cike da tausayinta Tabawa tayi saurin faɗin,"Wallahi muna tayaki Uwar ɗakina,tunda hakan ya kasance kullum cikin addu'a nake tayaki,Allah kuma maji roƙon bawansa ne ina da yaƙinin zai amsa mana ya kawo miki mafi alkhairy." Jannat ta jinjina kanta tace,"Na gode sosai Tabawa,ki daure ki saka har da Ummu itama Allah ya shiryeta ta tuba ta daina aikata Zina tana janyo mini abin gori da ƙyamata." Jannat takai ƙarshen maganar muryarta na rawa sosai,domin ita kaɗai tasan irin ciwon da take ji a cikin zuciyarta idan da tuna cewa tabbas da gaske fa ita ɗin ƳAR KARUWA ce mai lasisi.Tayi saurin maida hawayen da suka cika idanunta time ɗin data ji hannuwan Tabawa sun dafa saman kafaɗunta,ta waiwayo a nutse idanunsu suka gauraya dana juna ita da Tabawa wacce tausayi da ƙaunar Jannat suka gama cika zuciyarta,domin babu abinda bata sani game da Jannat ba hasalima akan idanunta aka auro Nuratu har ta haifi Jannat ɗin.Ita ɗin amintacciyar mai aikin Hajiya Inna ce da suka zama tamkar ƴan uwa,sabida yadda Hajiya Inna ta ɗauki Tabawa ba za ka taɓa cewa basu haɗa danganta ta jini ba.Cikin muryar rarrashi take faɗin,"Jannat kiyi haƙuri ki kuma ƙara ɗaura haƙuri kan haƙuri,Hajiya tana cikin addu'a ta dare da rana kuma In Sha Allah,Allah zai shiryar da ita,sanin kanki ne da shiriya a hannun bawa yake tabbas da Nuratu bata koma ruwa bayan mutuwar Mahaifinki ba,karki yarda ki tsaneta domin duk duniya baki da tamkarta mai sunan Hajiya,don haka ki cigaba da yi mata addu'a kowa da kika gani da abinda ake jarabtarsa,ke ki ɗauka taki jarabawar ta Uwace,Allah ya juyo da hankalinta ta dawo gida tayi tuba na gaskiya,Hajiya Nuratu mutum ce kuma mace ce mai imani da zuciyar taimako,muna roƙa mata shiriya ko domin kyawawan halayenta na taimako da jin ƙan marayu." Tabawa ta kai ƙarshen kalamanta tana tuna irin alkhairi da taimakon da Hajiya Nuratu tayi mata a rayuwa,tabbas ita ɗin ta shaidi taimako da kirkin Nuratu domin ta taimaki marayun jikokinta waɗanda suke tsaye da ƙafafunsu akan noma da kiwo kuma duk ta sanadin jari mai kauri da Nuratun ta basu ne.Jannat ce ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin,"Na gode Tabawa Allah ya amsa mana dukkanin addu'o'inmu baki ɗaya." Daga haka suka cigaba da ayyukan gabansu suna yi suna taɓa hira cike da barkwanci,domin Tabawa na son ganin Jannat ta dawo da walwalarta sosai tamkar komi bai faru ba.
Cikin awa guda Jannat ta kammala girka lafiyayyen faten dankalin turawa wanda aka yi amfani da veggies a ciki da kuma zallar tsokar kaza a cikinsa,kitchen ɗin baki ɗaya ya gama cika da ƙamshin lafiyayyun spices data yi amfani dasu a cikin girkin.Allah ya bata baiwar iya girki domin tun tana ƙaramarta take karanbanin ɗaura tukunya da sunan koyon girki,tun Inna na hanawa har ta gane cewa son girki a jinin Jannat ɗin yake.Ta juye komi cikin madaidaicin food flask ɗin da Tabawa ta kawo mata,ta sungumi kular ta fito daga kitchen ɗin bayan ta gama tsokanar Tabawa da cewa shikenan tayi mata wayo ta rigata kammala nata girkin.Direct ɓangaren dining ta nufa ta aje kular,ta juya kenan za ta nufi hanyar ɗakinta Hajiya Inna ta ratso wajen ta sauke idanunta akan Jannat ɗin.Cike da farin ciki tace,"Jikalle kar dai kice kece kika yi faten dankalin?" Jannat ta saki murmushi tare da kashewa Inna idanu guda tace,"Nice nayi Hajjaju ko kinfi son girkin tsowa Tabawa bana sabuwar jini ba?" Hajiya Inna ta saki dariya sosai kafin tace,"Waneni ai girkinki duniya ne inyi ta bakin Arfah,Allah yayi albarka haka nake son ganin kin sake kin manta komi Jannat,Allah ya ƙara miki tawakkali da dangana sai ki je maza ki watsa ruwa nima zan shiga yin alwala yanzu za ki ji kiran Sallah." Jannat ta jinjina kanta tace,"Yauwa Hajjaju godiya nake,bari naje na watsa ruwan tunda zafi ake." Daga haka ta wuce zuwa room ɗinta itama Hajiya Inna ta wuce zuwa nata ɗakin domin shirin ɗaura alwala.
Time ɗin da Jannat ta fito daga wankan data sake sallawa,wasu riga da wando masu faɗi marasa nauyi ta saka waɗanda sukai bala'in yi mata kyau.Kalarsu dark coffee ne da suka haske brown skin ɗinta mai haske sosai,ta ɗauki wani scarf ta ɗaura a kanta kafin ta zura dogon hijab ta nufi saman sallayar da take a shimfiɗe bayan ta gama wadata jikinta da sassanyar turarenta mai sanyin ƙamshi.
Tana idar da sallar ta fice daga ɗakin domin cikinta sosai yake ƙiran ciroma,direct ɓangaren dining ta nufa ta zuba faten dankalin data yi domin bata ji za ta iya cin tuwon rice ɗin sai zuwa yamma.Nan cikin falon Inna ta isa ta nufi wajen da Hajiya Inna ke kalmashe ta tasa plate ɗin tuwo dana miyar da Tabawa ta zubo mata,Inna ta dubi Jannat tace,"Dama nina san shi za ki ci ba tuwon ba." Murmushi kawai Jannat tayi kafin tace,"Hajjaju sai zuwa yamma zanci tunda kinsan bana cin abinci mai nauyi da dare,zuwa dare noodles zanci da grilled fish Allah yasa dai akwai kifin a freezer." Hajiya Inna ta taɓe baki tace,"Akwai mana tunda kudai mayun kifi ne na rasa wanda kuka gado daga ke har Ammar domin Iyayenku duka ba gwanayen cinsa bane amma ku Allah ya zuba muku jaraban son cin kifi." Jannat ta saki murmushi tace,"Kin manta Abbah shima yana so Inna,to kinga shi muka gado don dai kawai mun zartashi a son kifin ne,kuma dama ai ance magaji mafiyi ko?" Hajiya Inna sai ta saki dariya tace,"Ja'ira wannan baki naki dai akwai Hausa,nikam bai wani dameni ba har gara idan kikai irin gashinnan da kike yayi romo ina sonsa sosai." Jannat ta saki dariyar da dimples ɗinta duka suka loɓa kafin tace,"Anzo wajen,to badai irin gashin zanyi ba Inna gwarama ki cire rai." Kafin Hajiya Inna tace komi suka jiyo sallamar Mamie daga bakin ƙofar shigowa falon Inna,haka kawai Jannat ta ji gabanta ya faɗi tayi saurin shiga nutsuwarta tana jin Inna na bata izinin shigowa bayan ta amsa sallamar.Mamie ce ta sanyo kanta cikin falon daga bayanta kuma wata ƙwanƙwasasshiyar budurwace biye da ita,Jannat data ɗago domin satar dubansu sai idanunta suka sauka akan Labibah da ke ƙoƙarin zama bisa seatern da Mamie ta kai zaune.......✍🏻